Free chapter · Read without an account
PAGE 17
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM
*WANNAN FEJIN NAKINE DOTE HAUWA SULAIMAN😍😍BARKA DA KARA SHEKARA,INA MIKI FATAN NASARA ARAYUWARKI,MIJI NA GARI,ILIMI MAI ALBARKA INA YINKI IRIN SOSAI DINNANDINNAN*❤️
*TUKWICE GAREKI ANTYNA FARIDA MUSA (SWEERY)😍IDAN BABU KE KUSA DANI DOLE NAYI KUKA MATUKAR GASKE,BA ZAN IYA MIKI SO KADAN BA SON SO SABIDA ALLAH❤️ALLAH KARA BASIRA DA HAZAKA*
******
Nafeesa Ta Fara Kuka, "Habibbty Ban san ya zanyi da raina ba wallahi,kin fi kowa sanin muradin raina, Amman ba yadda zanyi farincikin Abhi da Mammah ya zarce nawa koda kuwa karshen rayuwatane zan ba su farinciki,na hakura da wayar in sha Allah na hakura."
Ta rike hannun Maryam gam tana, "Zasuyi Farinciki ko Habibbty? Indai za suyi ya fi nawa mahimmanci na hakura kinji."
Tsabar Tausayin Nafeesa ya gama mamaye zuciyar Maryam bata San lokacin da itama ta bige da kukan ba, sautin kukansu kadai ke tashi adakin, Nafeesa ta fara sharewa Maryam Hawayen tana, "Habibbty ki daina kuka kinji,bana so ina saku damuwa, In sha Allah zan jure dukkan radadin da zanji Dan ganin na faranta maku ki daina kukan kinji Nima na daina, Amman fa.....
Kawai sai ta kara fashewa da kuka ta kasa karasa maganar da za ta yi.
Maryam ta ja dogon numfashi kan ta ce, " Yawwa Habibbty Kinga mu yi shiru kar Mammah ta gane ko."
Nafeesa ta kakalo wani murmushi Wanda da ka gani zaka fahimci cewa na karfin haline.
Maryam ta ce, "Yawwa wai meya farune Ranar Kinje Skul Amman ban ganki ba."
Nafeesa ta tsaya Chan kuma sai ta ce, "Ranar! Hmm Mutansir ne." Sai kuma tayi shiru.
Maryam ta zaro ido tare da fadin, "Mutansir me? Me ya miki? Fadamin Habibbty."
Abubuwan ne suka fara dawo mata cikin wani yanayi kamar mafarki,kan ta ne ya fara juyawa ta fara kallon Dakin Uku Uku.
Tallefa kanta tayi da hannunta na dama tana, "Maryam ba zan Iya ba ki bar maganar nan kai na zai fice ni ban san meya faru ba."
Tana gama fadin hakan ta kwanta awajen kamar yadda ta saba ba barci tayi ba kuma ba suma tai ba.
"Innalillahi-wa'inna-ilaihir-raji'un." Abun da Maryam ke Iya furtawa kenan yayinda hawaye ke saukowa daga idanunta.
Riketa Kawai tai tamkar wata jaririya tana kallonta gabadaya ta ma rasa me za ta yi,ba abun ta kira Mammah ba hankalinsu ya tashi.
Kuka take bilhakki da gaskiya tausayin Nafeesa ya gama mamaye zuciyar Maryam ,ji take inda tanada dama da ta dawo da radadin da Maryam ke ji cikin jikinta.
Chan kuma ta tuna da maganar Nafeesa, "Habibbty ba abun da ya gagari ubangiji aduk lokacin da wani Abu ya samemu addu'ah ce Kawai mafita koda ace da maganin abun ta addu'ah na kan gaba domin itace babban magani ga dukkan mumini."
Tana gama tunano maganar Nafeesa ta share hawayen da ke fuskarta kan ta fara jerowa Nafeesa addu'o'i daga bisani ta dauko gorar ruwa ta fara tofa addu'o'in ciki.
Bayan ta kammala Addu'o'in dago Fuskar Nafeesa tai tare da shafa mata ruwan afuska,Sanan ta bude mata Baki kadan ruwan ya samu damar shiga.
Bayan ta gama shafa mata tagumi tai kawai tare da zubawa Aminiyarta ta ido,acikin zuciyarta tana rokon Allah da ya tada Nafeesa ayanzu batare da kowa ya fahimci halin da suke ciki ba.
Kamar wasa Nafeesa ta kusa yin Rabin awa kwance ba motsi ba alamar motsi sai numfashi.
Maryam ta rasa abun yi gabadaya zuciyarta ta jagule kwatsam ta hango inda littafan Nafeesa yake,da hanzarinta ta karasa wajen aiko ta ci Karo da Al-Qur'ani kamar yadda ta aiyya na aranta.
Dauka tayi yayinda tashinta kwatsam ta bige wani littafi takarda mai dauke da zanece ta Fada kasa, batare da ta waiwaba da ta lura takardane ne kawai sai ta nufi inda Nafeesa take.
Dai,dai lokacin da wannan takarda ta fada kasa,Nafeesa ji tai tamkar allura akayo mata, a hankali take fadin, "Kin Yar min da shi,ki daga min shi,nace ki daga shi."
Tsayawa Maryam tayi cak kasancewar tana jin magana Amman ta rasa ta inda maganar ke fitowa.
Nafeesa ta kara da"Habibbty nace ki daga min shi,ki daga min shi."
Cikin dimuwa Maryam ta kalli Nafeesa tare da waigawa kallon inda Nafeesa ke nuni da hannu,wannan takardarce dai data bige batare da saninta ba.
Da sauri ta karasa tare da dagawa zanene ta gani irin Wanda Nafeesa ta sabayi akullum tana fadin cewa Nafseen dinta ne.
Mik'o mata hannu Nafeesa ke yi alamar ta bata zanen.
Karasawa gareta tayi tare da mika mata, kamar wasa Nafeesa na karban zanen ta dawo normal tashi tayi ta zauna tare da jero addu'o'i.
Bayan ta kammala ta shafa hamma ta fara" Habibbty wallahi yunwa nakeji muyi wanka na San Mammah ta kammala Abinci yanzu."
Maryam da ke cikin tsananin mamaki ta ma rasa bakin magana murmushi tayi tare da girgizawa Nafeesa kai kawai.
Ta shi tayi tayi wankanta tsaf Kai kace ba ita ba,Abu dayane kawai da ya tsaya mata rashin waya ga shi ta tsinci kanta da tsananin son ganin sakon da Nafseen zai yo mata,amman in ta tuna da maganar Maryam sai tai kokarin kawar da damuwarta.
Bayan ta fito daga wankan zama tai bakin gado dauke da zanen sahibin nata ahannu sai kallo kawai take tana ta sakin murmushi,Allah ne kadai ya San me take aiyyanawa cikin ranta.
Fitowar Maryam daga wankane ya katse mata tunani, "Habibbty abani kaya in Sa,kin San dai ba zan maida na jikina ba." Cewar Maryam.
Dagowa tai ta karewa Maryam kallo cikeda shagwaba take maganar, "Haba Habibbty wannan ai wulakancine kayanma sai na baki? Yaushe ki ka zama haka,ni fa bana so Allah na Fada miki ban so."
Murmushi Maryam ta yi, "To al-shagwabatu bara in dau abuna."
"Eh din naji." Ta kare maganar cikin murguda baki.
Maryam ko ba abun da take ban da dariya.
**Bayan Maryam ta shirya tsaf riko hannun Aminiyarta tai tare da fadin, "Oya bebe Muje aci abinci tun tuni kike kukan yunwa Amman tunda kika dau Zane kin manta da komai."
Sai da ta ajiye takardar zanen tamkar kwai Dan tattali kan ta ce, "Habibbty Zanennan tamkar rayuwata yake, na kan kasa ganin komai aduk lokacin da ba glass a idona Amman ban da wannan zanen kullum cikin shege yake ga idanuna,ina son zanen nan fiye da tunaninki,kinga ko ba ma yunwa ba zan Iya daina jin komai,mantawa da komai aduk sanda nake tare da shi."
Maryam ta kara janyota tare da fadin, "Kinga nifa yunwa nake ji muje kawai."
PSuna fita kuwa suka Tarar da Abhi Da Sabeer zaune Mammah na zuba ma su abinci.
Murmushi Abhi ya yi, "Ma sha Allah,Ammie na ta fito, kinga karfan wayannsn jiya fa har kiba kika kara aiko ban baki ita yanzu kam."
Daga Nafeesa har Maryam wani Ras sukaji acikin ransu,cikin sauri Maryam ta radawa Nafeesa magana akunne aiko ta sake murmushi tare da fadin, "Ina kwana Abhi,Ina kwana Mammah,Ina Kwana Little Bro."
Daga Abhi har Mammah amsawa sukai cike da fara'ah. Sabeer ya ce, "Ina kwana Anty."
Maryam ma gaishesu tai suka amsa kamar yadda sukaiwa Nafeesa.
Mammah ta zubawa kowa na shi Nafeesa ta ce ,"'Ni bana ci na Abhi na zance." Cikin shagwaba.
Abhi ya ce, "Sorry Ammiena zo muci waya isa hanaki cin abinci da Abhin ki."
Kusa da shi ta koma ta zauna sannan ya fara bata abaki tana ci,ban da shagwaba ba abun da Nafeesa ke zubawa Abhinta kowa kawai sai dariya domin inda sabo an saba Da ganin halin Nafeesa in tana tare da Abhi.
Suna gama cin abinci Abhi ya ce, "Oya Ammiiena ta rufe Ido,ita zan fara yiwa kyauta agidannan."
Cikin Sauri kuwa ta rufe.
Kwalin waya ya Ciro awata Leda kirar INFINIX Sabuwa gal, Murmushi Yayi Oya bude.
Tana budewa me za ta gani,sai waya, bata san lokacin da sake wani irin ihu ba cen kuma sai ta ce, "Alhamdu Lillah, Na gode Abhi na."
Ta rungumesa.
Ba karamin Dadi Maryam taji ba aranta domin ta san matsalar Aminiyarta ta kau kenan.
Sabeer ya ce, "Abhi to ni fa?"
Murmushi Abhi ya yi, "Sabeer kai kam agogo ne na siyama domin ba ka kai rike waya ba Amman in ka kai nama alkawari."
Karban agogon yayi yana Murna tare da godiya ga mahaifin nasa.
Maryam kuwa miko mata wata sarka Abhi ya yi cikin fara'a yake fadin, "Na san dai duk kinfi karfin wannan Amman karamar kyautace na miki daso Allah yayi albarka."
Murmushi Maryam tai ta durkusa har kasa ta karba , "Na gode Abhi Allah kara budi."
Abhi ya amsa da "Ameen, kallonsa ya koma ga Nafeesa."yawwa Ammina Bana so hankalinki kullum yana kasancewa kan waya ki tuna cewa yanzu kika fara karatu indai kina son muna shiru to ban da shiririta,kuma ki kulama da lafiyar idonki,ga dayar wayar nan ki kwashe abubuwan ciki."
Nafeesa ta ce, "In sha Allah Abhi na gode."
Mammah ta bata rai , "ka gama da kowa wai ni ba za azo kaina bane?"
Duka falon suka fashe da dariya.
Abhi ya ce, "Sorry madam naki ai na mussamanne."
Daga nan suka bige da hira ita kuwa Nafeesa tuni ta dauki tsohuwar wayarta tare da shiga whatsApp.
Kamar yadda ta saba sakonsa take fara dubawa.
Tana Shiga...........
😍😍😍ADDU'AR NAN DAI KAR AFASA MASOYAN ASALI❤️❤️
Urs Xayyeesherth _*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ***
NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH
✨6STARS INDEED
_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_