Free chapter · Read without an account

PAGE-20

by Aisha Sani Abdullahi · SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

🤗 *A YANZU NAFEESA XAYYEESHER AMMAN A KARSHE NAFEESA BA ZATA TABA ZAMA XAYYEESHER BA😁WANDA YA FAHIMTA YA FAHIMTA KAWAI👌*

*MRS MUBARAK,AISHATUL HUMAIRA,DEEYMUSAH,WALIDA RANO,LEEMAH,JASMINE,NAPHYSERT,FATIMA MUHAMMAD,INA YINKU IRIN TOTALLYN NAN ARADU😍KUNA SHARHI INA KWAMUSAN NISHADI😍*

***

Addu'ah tayi daga nan wani bacci mai dadi yayi gaba da ita tare da cigaban mafarkin Nafseen Wanda ya zame Mata jiki bata,kamar yadda taba tsallake ko da rana dayane ba tare da kallon Nafseen acikin mafarkinta ba,ba ta taba wani mafarki Wanda ba nashi ba Dan yadda har zanensa tanayi Wan da kawarta maryam take cewa ba iya soyayyan Nafseen bane a tare da Nafeesa zanen kaddaransu tamkar guda ne.

Cikin darannan yana ta faman aiki kwatsam sai ga Nafeesa ta fado masa arai ba tsammani murmushi ya sake tare da fadin, " My rigima girl hmmm ko ina take nasan she looks cutie." a zuciyarta sam ya san cewa ba son Yarinyar yake da wata manufar soyayya ba,abu daya yasani kawai dai tana birge shi duk da kasance ba wai ya taba ganinta ba amman yanayinta na nunin cewa yar gidan mutuncice,haka kuma duk da karancin shekaratun hakan bai hanata nuna kamun kai da sanin darajarta na 'Ya mace ba, abu guda Jameel yana da son mutane tare gudun wulakantasu koma ya suke, hakan ya sa in yana ba masoyansa lokaci wasu kan yi ma hakan wani kallo na daban.

Nafeesa kuwa tunda ta kwanta bacci bata farka ba sai da taji kiran sallah a kunnenta tashi ta yi ta shiga toilet tayi alwala tazo tayi nafila sannan tayi sallah ta jima tana addu'ah tare da rokon Allah ya cika mata burikanta tana wajen har gari ya para haske Qur'Ani nata ta dauka ta Karanta bayan ta kammala wayanta ta kalla tana murmushi ta nufi wayan tana son kallon reply din Uncle din ta.

Ta kai hannu kenan zata dauka wayan kenan taji muryan Mammah na kiranta " ki yi maza ki zo ki yi break zamu yi late fa."cewar Mammah

Dan turo baki Nafeesa ta yi cike da shagwaba ta ce, " to Bari nai wanka ina zuwa Mammahn Sabeer."

tana kallon wayan haka ta barta a wajen tayi wanka tazo tayi break suka wuce Mammah hospital ita da sabeer kuma skull.

Ana sauke Nafeesa tun a gate take zuba ido ko za ta ga habibty dinta Dan tayi missing nata.

Ji tayi an rufe Mata ido ta baya ta san ba Mai yin hakan sai Maryam ta juyo da farin cikin ta tana darjya ta ce , "habibaty Miss you ."

itama ta amsa mata da" Miss you more babyn Nafseen." Nafesa tayi wani fari da ido ta ce, " gaskiya yau kina son farin ciki ya hanani karatu." dariya suka sa sannan suka wuce sun rike hannun juna abin sha'awa.

Sun kusa department nasu kenan sai gasu ga su Mutansir zasu wuce shida yaransa suna hada ido da Nafesa yanayin sa ya canja kana kallon idon sa kasan ya gama storata Nafesa ta fahimci hakan, shi ko yana tuna abin da tayi masa a ranan sai zufa ta keto masa bare ya ganta.

Kawai nafeesa ta bata rai ta canja murya kaman Wanda ta jima bata hankainta ta ce , "kai zo nan." abokansa suka ce, " keeee lallai yau kina so ki koma gida a na kashe."

Duk da kasancewar suma atsorace suke gudun dai kar ya ci masu zarafine.

Mutansir ya ce, " ina ruwan Ku? Ku nace min dagani ku aka kira koni duk suka saki baki suna kallon sa,Aran su kuwa sun san dalili,tuni suka fara watsewa.

Nafeesa ta ce, "duk kace su dawo ayi komai a gaban su." Mutansir ya ce, "ku tsaya kowa ya dawo ta ce."maganar yake cike da tsoro.

Nafeesa ta gyara zaman glass dinta tare da gyaran murya ta ce, "kowa yazo ya dalla ma sa mari ."

suka fara zare ido. Kallonsa kawai Nafeesa tayi ba tare da tace komai ba.

ya ce, "wai ba magana ake mu ku ba ne?"

nan da nan suka fara daya bayan daya suna wanke Mutansir da mari kafin kace me fuska ya kumbura dama duk abokan haushinsa suke ji yadda yake nuna musu isa da walakanci amman ba yadda suka iya tun da suna cin arziki.

sai da Nafeesa ta tabbata ya maku sannan ta ce, " dauki takalmanka a hanu ka bace min da gani ."

maryam me take idan ba dariya ba haka sauran students ma akko nan da nan mutansir ya sheka da gudu waje ba abin da kake ji sai dariya.

Maryam kan hadda su faduwa kasa Dan dariyar mugunta

Nafeesa ta ce, " tashi Wlh mu wuce hall nikan."

Taja Maryam suka wuce ban da tafi ba abun da ake yiwa Nafeesa ,domin tayi maganin wanda ya addabi dalibai har ma da daliban kowa na da cikin Mutansir.

suna shiga hall Maryam ta ce, "ke habibaty Wai meke faruwa ne dama tun a wancan ranan naga kaman akwai abin da ya faru ."

Nafeesa tayi dariya tare da fadin, " wallahi nima ban san komaj ba habibaty naga dai Kawai yana tsoron hada ido dani shiyasa Kawai na ma shi haka yau amma ni bansan meya faru ba."

Maryam ta ce, " aiko kin burgeni sosai wallahi kinyi maganin Dan iska,ashe ma ragone matsoraci." duka dariya sukayi tare da daukan handouts nasu su suna dubawa.

Mutansir ko kunya be barsa ya kasa zama a skull s motor shi ya shiga tare da nufan gida kawai Domin kuwa Allah ya sanya Mashi tsoron aljanu, afadarsa Nafeesa ba Mutum bace Aljan ce babu tantama yana tafiya yana jin takaici Wai yar talakawa ne Zata dizga shi duk yadda yake ji kansa dinnan,har yaransa su maresa shi ke nan raini ya shiga tsakani!

....bayan an gama lectures suka fito zasu wuce gida sun ci sa'a sun samu Nafe da wuri suka shiga kowa ya nufi gida kasancewar yau baza azo daukan Maryam ba.

Nafeesa na isa gida dai,dai kofar gidansu taci karo da bayan wanni sauri,bata gabansa ba amman ayadda tsarin bayan sa yake saurayine dogo madaidaici sanya da bluen shadda wadda tun daga nesa shekinta ke tashi,kamshi kuwa da ka dumfaro wajen kamshin zai maimaye hancinta.

Kasa magana tayi yayin da kamshin ke shiga cikinta abu daya ta iya furtawa , "Subhnallah!

Kalmar da ta furta ne ha sa saurin juyowa cike da kasaita,ban da murmushi ba abun da ke bayyana afuskarsa.........

"Subhannallah,"kalmar data kara furtawa kenan.

Urs Xayyeesherth [3/16, 2:24 PM] Xayyeesherthul-humaerth: ***

_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.