Free chapter · Read without an account

PAGE-22

by Aisha Sani Abdullahi · SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

_*TABBAS ASON RAINA LITTAFIN NAN BA ZAI ZARCE FEJI GOMA BAMA KWATA-KWATA😁AMMAN KADDARA YA SAUYA MASA AKALA YA FITA DAGA SAHUN GAJERAN LABARI,KADA KU GAJI😓 AKARA HAKURI DA RASHIN TYPING DINA KAN LOKACI,NA SAN KUNAYI AMMAN AKARA🥰INA SON KU MASOYANA,SON SO❤️*_

_*SADAUKARWA GA YAN GROUP DINA SAI NA AURI MARUBUCI FANS KUYI YADDA KUKESO DA SHI TARE DA RUWAN SHARHI*_

Tsayawa kallon Wayar tai kawai yayinda messages ke shigowa,idonta ba inda yake illa kan Sunan Ruwan Ranta *NAFSEEN* Amman har messeges sun kusa gama shigowa har yanzu ba alamar nasa, Hawayene ya fara zubowa daga fuskarta,ta San cewa tana da bukatar ganin sakonsa "Amman to miye dalilin hawayen? Tamkar wadda akace ya mutu?, Ah'ah bai mutu ba,me zai Sa ya mutu wallahi bai mutu ba." Nan take ta fara share hawayen tare da shiga tana bin hirar rakinsu.

Murmushi ne ya fara bayyana afuskarta azuciyarta take fadin, "Lallai kai na mussaman ne kamar yadda rubutun ka yake na mussaman,maza da yawa a media da zaran an fara magana da su ta private burinsu daya suga hoton mutum,Amman ko kadan kai bakada wannan akidar azuciya rayuwarka kake mai cike da annushuwa, tabbas ina sonka kuma SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen), ta cigaba da fadin nikam dai ayanzu duk da ban taba ganinka ba Amman na sanka,kuma ina kara ji araina cewa yadda na siffantaka haka kake babu shakka."

Tana karasa maganar ta tashi tare da nufar inda ta saba ajiyar zanen Sahibinta, Kallonsa ta tsayayi na Dan lokaci daga karshe ta shafa fuskarsa tana mai fadin, "INA SONKA, INA SO KASAN DA HAKAN." Ji tai tamkar yana kallonta hakan yasata rufe fuska da hannayenta cikin sauri, tare da nunin jin kunya,a haka har ta bar dakin sannan ta bude fuska.

Dakin Mammah ta nufa saida tai alwala sukai sallah tare kan suka fito falo, dai,dai da shigowar Abhi da Sabeer daga masallaci kenan.

Da sauri Nafeesa taje gun Abhi ta rungumesa, tana ta sakin murmushi.

Dago da ita ya yi yana. "Ammeerna Ya naganki hakane yau sai murmushi ga dukkan alamu yau an faranta miki."

Rike mi shi hannu tai tare da janshi suka zauna sannan ta ce, "Ina Sonka Abhi na."

Cike da so ya kalli Yartasa, "Tabbas nima ina sonki Ammina farincikina,Allah kara rayamun ke mu sha biki,inga ranar aurenki."

Da sauri ta rufe fuska, "Umm Umm nidai bana so."

Mammah da Sabeer ko ban da dariya ba abunda suke domin ba yau Nafeesa da Abhi suka saba irin wannan dramar ba,sun shaku matukar gaske.

Cikin farinciki,nishadi da walwala sukaci abincin darensu,sai da Abhi ya raka Nafeesa har daki kan ya nufi dakin Mammah.

Wa she gari

Da sassafe Nafeesa ta shirya domin da safe sukeda lecture, hijabinta tasa har kasa tare da glass, sai jakar makarantarta,ban da kamshi ba abun da ke tashi, ba karamun kyau Nafeesa tai ba.

Sallama taiwa Abhi domin yau zai koma aiki,sannan ta nufi skul ita da Sabeer,Mammah kuwa ta tsaya sai taga tafiyan Abhi.

Nafeesa na isa dai-dai da lokacin da driven su Maryam ya tsaya.

Da gudu Nafeesa zata karasa gun Maryam tayi kicibis da wani duzu zata fadi, da sauri Mutansir ya karaso zai tareta, dagowa tai tare da galla masa wata hamshakiyar harara ta wuce.

Binta da kallo kawai yayi azuciyarsa yana kara jin tsantsar so da kaunar ta.

Rungume Maryam tai tana, "Oyoyo Habibbty Mie,nayi kewarki aradu."

Maryam tai Murmushi , "Umm Habibbty kenan yau fa tin daga nesa nake ganin hakoranki me muka samu ne?"

Nafeesa ta kyalkyale da dariya, "har yanzu nima bansan me aka samu ba ko za asamu,Amman ina ji araina cewa abun da Nagani ne jiya,duk da kasancewar ma ya tafi ya barni batare da ya min ko magana ba."

Maryam ta ce, "Habibbty kina bani Mamaki,soyayyarki abun karantace mai zaman kanta a makaranta,na saba da ke na jima da ke Amman har yanzu Mamaki kike bani yadda kika dauki so da matsayin da ba kowa zai Iya hakan ba, tabbas kina tare da boyayyen sirri da ya kasa bayyana agaremu Allah ne kadai inyaso zai bayyana mana,bama wannan ba nasan maganar bata wuce na Sahibinki ba to me kika gani?"

Nafeesa ta ce, "Yo to wa zan gani bayan shi?.ta karasa maganar tana dariya.

Maryam ta galla mata harara, " daman nasani ai, kuma fa ina binki bashin labaran Sirri."

Nafeesa ta saki murmushi, "With Time inji bature, muje saura 2minit afara lectures."

Rike hanun junansu sukai har sai da suka shiga tare da zama awajensu da suka saba.

Karatu ake Amman gabadaya hankalin Mutansir na kan Nafeesa, shi dama ba zaman lectures din yasaba ba,Amman yau Dan ita kawai ya shigo kowa Mamaki yake, in aka lura da yadda yanayinsa ke kan Nafeesa, zaka fahiimci ita kawai yake kallo.

Gajiya ya yi abunka da ba sabanba ya tashi zai fita, Lecturern ya ce, "Kai Mutansir Ina zaka yanzu kuma? I think saura 30minit mu kammala ma." Ya karasa maganar yana kallon agogon hanunsa.

Mutansir ya ce, "Wallahi Nafeesa.......

Sai ya kasa karasa maganar domin bai ma San yadda akayi abun da ke ransa ya fito filiba.

Kallon Nafeesan yayi suna hada ido yayi saurin kawar da kai.

Daga Lecturern har sauran yan class din dariya kawai suka fara

Kunyace ta kama Mutansir ya fita kawai. Zama yayi acikin mota ban da kallon Inda Nafeesa zata fito ba abun da yake yi,ji yake tamkar ya kara komawa domin kuwa tunda ya fito ya rasa nutsuwarsa.

Karfe 2 dai,dai Suka fito,Idon Mutansir kuwa Kur akan Nafeesa, cire tsoro yayi tare da tunkararta azuciyarsa yana mai fadin koda marinsa zatayi t dakesa da kanta ba zai fasa bayyana sirrin ransa ba.

Haka kuwa akayi Karasa wa yayi yana yi mata magana kamar bazata tsaya ba ji tai ta tsinci kanta da tsayuwar.

Mutansir ya durkusa yana fadin, "Dan Allah ki yafemun Nafeesa Sharrin shedanne ki bani dama in nuna miki hakikanin soyayyar da nke miki Dan Allah,ina sonki Nafeesa."

Kalmar son da ya furta ya sauya Nafeesa nan take wani irin yana yi ta shiga batare da ko hanunta yayi motsiba Jefar da Mutansir gefe akayi,aka kara dagasa sama kan aka sauke,ban da ihu ba abun da yake.

Nafeesa ta........

Urs Xayyeesherth [3/16, 2:24 PM] Xayyeesherthul-humaerth: ***

_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

***

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.