Free chapter · Read without an account

PAGE-24

by Aisha Sani Abdullahi · SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

_*SADAUKARWA GA SAI NA AURI MARUBUCIYA FANS GRP😘ARADU SAI NA AURI MARUBUCI FANS GRP2 ZAN YI SHARA🥺KAF XAN CIREKU TUNDA BA SHARHI*_

Banda salati ba abin da ke tashi a motarsu Nafseen duk wani Wanda ke wannan wajen saida hankalinsa ya tashi domin duk Wanda yake cikin motan ba Wanda ake sa rai da zai Rayu.

wanine akasamu yayi hankalin kiran yan road safety suka zo da gaggwa aka fara kokarin daga motan da kyar aka samu aka daga motan aka fara fitowa dasu Amma duk basa hankalinsu sannan kuma driver din baya da rai. cikin gaggawa aka wuce dasu asibiti domin ceto rayuwarsu.

Muta sir kuwa tunda ya koma gida wani irin ciwon kai da zazzabi ya rufe shi sosai son Nafesa na Neman halaka shi, zuciyar shi tana mashi zafi sosai ko ruwa ya kasa sha bare abinci duk jikin sa rawa yake, ko ido ya rufe ita kadai yake hange, yanzu kuma kaman ita yake kallo tana masa murmushi shima murmushi ya fara hadda kokarin fita a blanket dinsa ya nufi wajenta yana zuwa ya durkusa a gaban ta "Nafesa kema kin fahimci Irin son da nake miki ko? na san za kiji tausayi na dama, plz give me a chance ."

Momy ce ta ce, "waye ita?"

saiko mutansir ya dago "Momy dama ba Nafesa bane momy plz ki tausaya min zan mutu idan ban same ta ba, wallahi ina sonta." Ya karasa maganar jikin kuka.

yau ce rana ta farko da Momy taga mutansir yana kuka da girman sa dago shi tayi taji duk jikinsa ya dauki zafi sosai.

ta ce, " son yanzu akan mace Kake wannan abin? Daman na San za arina ai,akwa ranar kin dillanci."

"Momy nidai Dan Allah ki taimaka min bakiji yadda xuciyata ke min ba Momy, ji nake tamkar zan Iya rasa raina."

Momy ma duk jikin ta ya mutu ban da hawaye ba abin da take, domin ban da dai fita ta Mutansir da ke Sa basa shiri amman tana matukar son 'dannata.

Kallonsa tai cikeda tausayi ta ce, " Idan Dady yadawo zamuyi magana,kar ka damu kaji, ka san Dadynka zai iyama abun da yafi wannan ma,bare wannan da nake Sa ran shi zai kara shiryaka."

Mutansir ya ce, " Momy plzz kice dady yazo yanzu Dan Allah momy, ni ko yanzu ma a auramun Nafeesa Dan Allah. "

Shafa kansa tayi kan ta ce, "yanzu dai kayi wanka kasha magani kayi sallah kaga sakka kara yin addua ko ? Kan Dady ya dawo ai yama kusa."

da to ya amsa,sanan ya nufi bangarensa, Momy da kanta ta hada masa ruwa sai da ta tabbata yayi wanka yayi sallah sannan ta bashi abinci duk da ya kasa ci Amma yadanci magani ta bashi tace ya kwanta kafin Daddy ya dawo ba musu ya kwanta shi kadai yasan me yake ji rupe ido yayi Kawai ba Dan yanajin bacci ba Momy data ga ya rufe itama ta fito tana mai jin tausayin Dan nata sosai,tabbas So ba karamun Abu bane kuma zai Iya yin illa ga zuciyar kowa..

**** Sai Dare Nafeesa ta bar gidansu Maryam tunda kabeer ya saukesu tare.

Karfi tara bayan tayi karatunta na QUR'ANI ta zauna tare da nufin zata bude data take ko zataga Uncle ya Mata magana.

Messegese nata shigowa Amma na shi shiru duk jikinta yayi sanyi ko lafiya kuwa uncle baya online ko dai zan tambaya a group ne can kuma tace hmmm danke kadai ne me baki ko ? to ko na kira shine?

Ta ba kanta amsa ehh Bari na kira number dinsa ta duba harzata danna call sai ta ji duk jikin ta na rawa Gaban ta na faduwa numfashinta na fita da karfi wayan ta jeda kan gado itama ta kwanta tafi mintuna ashirin a haka nan da nan ta fara kuka tana cewa "uncle meya sameka kasan inason ka Dan Allah karka min nisa jikina yabani wani Abu ya sameka,Kayi hakuri please." kukanta ne yayi yawa sai da Mamma ta shigo dakin cikin,hanzari ta ce, "meke faruwa ne? Nafeesa kina lafiya kuwa?"

Cikin shidewa take fadin "Mamma wani Abu ya same shi wallahi, ba zan Iya....... Kawai sai ta jita shiru ,ta leka ko harta tafi baccin data saba addu a ta mata ta fito, tana gaskiya lamarin Nafeesa ya fara yawa da bukatar fadada Neman magani...

A bangaren Nafseen kuwa asibiti aka wuce dasu cikin ikon Allah duk sun dawo hankalinsu sai dai sunji ciwo sosai.

doctor ne yazo yana dubasu ana tambayan su daga inda suke sai lokacin ya tunada wayarsa da bai san ina zai ganta ba.

tambaya yayi sukace su dae basu samu waya a motan ba. rike Kansa yayi" ohhhh my God." kadda8 ace masa wayan shi ya bata kuma sai wata zuciyar tace masa ka gode ma Allah da abin ya tsaya akan waya azahiri ya ce, "Alhamdu Lillah Allah nagode maka."

baa dauki lokaci ba yace a bashi Aron waya Dr din ya bashi , ****

Rukayya na zaune ita kadai ban da kuka ba abun da take Kanta har ya fara ciwo ta rasa meke faruwa tunda ya tafi bai kirata ba kuma ita ta Kira shi Amma bata samunsa switch of.

wayanta taji ya fara kara da gudu tayi daki a tunanin ta zataga sunan sa Amma sai ta ga number wani haushi ne yakamata har kiran ya katsewani ya kuma shigowa sai da yakusa katsewa ta daga muryansa daya daki kunnenta ne yasata Kara sa wani kuka .

yace" haba my rukky meye na kukan kidaina plzz ."

Ajiyar zuciyata tana ,"ina kashiga meya faru da kai ka fada min plzz."

Murmushi ne ya bayyana afuskarsa kan yace, " ki yi shiru zan dawo gida ina lafiya banson kukanki kema kin sani ko?"

tace, " har yanzu hankalina be kwanta ba,ni wallahi."

da kyar yasa ta hakura akan zai dawo ta ganshi .

" to e Ina wayanka ?" Cewar Rukayya .

Nafseen ya ce, " ba caji ne shiyasa na karbo na abokina Dan hankalinki ya kwanta to yi murmushi mana babyna."

murmushin tayi tareda Masa sallaama akan yana hanya.

Maryam ce zaune itada Ummi suna cin abinci wayan ta ya fara kara number din Kabir ne danta gane number din nan da nan yanayinta ya sanja tayi rejecting kiran Ummi ta ce , "waye yake kira?"

" hmm ummi wata course mate dinane kuma shirme zata min shiyasa bazan amsa ba."

Ummi murmushi Kawai tayi Wai Maryam ni zata nuna ma wayo kaman banina haifeta ba Allah dai ya shirya min ke Maryam.

kiranne ya kuma shigowa take ta kara rejecting wayan tana ta fishi karshe ma abincin dabata Ciba kenan tace bacci take ji dakinta wuce, tana shiga kuwa kiranne ya kara shigowa, cikin fushi ta amsa tare da karawa akunnenta.......

Urs Xayyeesherth ***

_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ***

NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.