Free chapter · Read without an account

Hs 39

by Sayyid · HASASHEN SOYAYYA COMPLETE

_Page 39_

"Banyi niyya ba." Bhatool ta yi mamakin wannan maganar ta shi, "Wai Senate mai yake nufi, zaman rashin mutunci yake so mu yi kamar ba masu aure ba ko me?." Ta tambayi kan ta. "Dan Allah." Ta faɗa kamar za ta yi kuka. "Na ce bazaki koma ba, idan kuma zaki koma ga hanya nan." Ya faɗa a fusace kamar zai dake ta, tashi ta yi ta shige ɗaki ta fara kuka. Har cikin zuciyarsa yake jin zafin kukan na ta, amma kamar an ɗaureshi da igiyoyi. 

Bhatool na shiga ɗaki ta dau waya ta kira Mom, tana kuka Mom ta ɗaga wayar. "Subahanallahi Bhatool me ya faru?." 

"Mom, wai bazan koma makaranta ba." 

"Bangane ba?." 

"Wai ya ce bazan koma makaranta ba kuma gashi jarabawa zamu fara." 

"Ki yi shiru Bhatool, zan kira shi gobe ku zo gaba ɗaya."

"Tom Mom." Ta faɗa tana kuka. "Ki daina kukan kin ji zaki koma karatunki kin ji?." 

"Na daina Mom." Ta faɗa, Mom takashe wayar ita kuma Bhatool ta kwanta. 

Washe gari da safe ta tashi ta fara aikinta na gida, tana cikin kicin ya shigo ya ce. "Kishirya zamuje gidan Momi." 

"Tom." Tafaɗa tana kashe gas ɗin. A mota ta same shi yana jiranta, sai dai suka yi nisa da tafoya sannan ya ce. "Bhatool mene matsalalki?." Da mamaki Bhatool ta kalleshi, a ranta ta na maimaita kalmar Matsalalta. "Shin ni ce mai matsalal?." Ta tambayi a kan ta. "Eyh Bhatooɗ?." 

"Babu." Ta faɗa ba tare da ta ƙara kallonshi ba, shiru shima ya yi bai ƙara ce ma ta komai ba har suka isa gidan, tun da suka shig gidan Senate ya ji wani irin sanyi a ran shi, a fili ya furta. "Sweet Home Sweet." Ita dai Bhatool ba ta kula shi ba ta shige ciki, Mom na zaune a falo Bhatool ta yi sallama ta shigo, fuskar momi fal da fara'a ta amsa ma ta. "Momi ina kwana?." 

"Lafiya kalau daughter." Mom ta amsa dai dai lokacin da Senate ya shigo. "Momina." Ya faɗa yana shigowa ciki. "Uhm da bamu da uwar da munyi kuka." Bhatool ta faɗa a cikin ranta tana taɓe baki. "Ina kwana Mom." Ya faɗa yana zama kusa da ita. "Lafiya Kalau." 

"Mom yana ga bakya murna da zuwana." Hararshi ta yi sanan ta ce. "Kawai ka hana yarinya komawa makaranta, sabida me?." 

"Au shine ta faɗa miki?." 

"Bazata faɗa mun ba?." 

"A'a." 

"To me yasa ka hana ta?."  Kallon Bhatool ya yi sanan ya ce. "Mom ta faɗa miki abinda take mun a gidan, komai tana mun a gutsire, magana a gajrace. "Gashi, zaka ci, sannu da zuwa, zan koma makaranta, Momi Babu girmamawa babu kulawa, babu soyayya." Kallon Bhatool Mom ta yi sanan ta ce. "Me yasa Bhatool?." 

"Mom, ko abinci bai fiya ci ba, da ya shigo xai fara haɗe rai yana cin magani, idan na ce mai ya yi hakuri sai ya ce wai me na yi?." 

"Mom har ni yarinyar nan za ta ce wai daman ba son ta nake ba na aureta." 

"Oh Allah, ashe ba zaman daɗi kuke yi a gidan ba kenan, to kusani kuna dauke da Ɗa, Bhatool na da cikinka, ke ma kina ɗauke da ciki a jikin idan kuka ci gaba da hauka ku kuka sani." Har cikin zuciyar Bhatool ta ji wani abu, wai tana ɗauke da ciki. "Mom did you mean she is pregent." 

"Yes, tana ɗauke da ciki." 

"Kai Alhmadulillah." Senate ya faɗa yana kallon Bhatool, fukarsa fes da farin ciki. "Mom ki yi hakuri ta ci gaba da zuwa makarantar." 

"Allah Ya yi muku Albarka, ya baku zaman lafiya mai ɗorewa." Mom ta faɗa suka amsa da baki. "Mom zanje gidan Yaya Karima." Bhatool ta faɗa. "Okay Bhatool." Tashi ta yi ta fice, Senate ya miƙe zai bi ta Mom ta kama hannunsa ya tsaya, sai da Bhatool ta yi nisa da fita sannan Mom ta ce da Senate. "Kasan wani abu?." 

"A'a sai kin faɗa." Ya bata amsa yana zama. "Wai Abbanka aure yake son ƙarawa."

"Aure Kuma?." Ya tambaya. "Eyh, wai aure." Mom ta ba shi Amsa tana taɓe baki. "To shi yanzu wace zata aureshi?." 

"Wai wata frist love ɗin shi ce, daman already ya taɓa bani labarinta.  Amma haka ya ce ta mutu, to yanzu ya gano mijinta ya mutu shine yake so ya aureta, yayata uku ma." 

"Chaɓ, Dad ya fiya matsala." 

"Kabarshi kawai Allah Ya ba shi sa'a, amma wallahi ya jamun surutun da bazai ƙare ba cikin ƙawayena, tun da yarinta ba ayi mun kishiya ba, sai yanzu da girmana har na kusa fara ajiye jikoki." 

"Gaskiyya Mom bai kyauta ba, amma zan yi magana da shi."

"A'a kar ka fara, kar ma ka nuna mai kasan maganar ka barshi kawai." 

"Okay." 

Yaya Karima na zaune a ɗaki ta ji an faɗo a kan ta, ba ta kai ga tantance wand aya faɗo ba ta ji anfashe da kuka, a firgrcr ta ɗago Bhatool tana faɗin. "Ke lafiya?." Kuka Bhatool ta ci gaba da yi. "Bhatool bana son iskanci, kawai zaki shigomun babu sallama ki fara kuka."

"Shine baki ƙara zuwa gidana ba, da nice da tuni nazo kamar mara mafaɗi har kwana nake yi a gidanki." Dariya Yaya Karima ta yi sannan ta ce. "To bikiga banda lafiya ba, haihuwa ta fa ta kusa." 

"Amma ai bai hana ki zuwa unguwa ba." 

"To wai ma ke Bhatool me ya fito dake da wannan safiyar?." 

"Gidan Momi ya kawo ni." 

"Shine kika bar gidan kika tawo nan?." 

"To me zan musu, ashe haka auren yake duk wahala, gashi har na sami ciki. Ni bana wani farin ciki wallahi." 

"To ai daman a ko da yaushe ana faɗa miki aure gaba ɗayanshi ɗan haƙuri ne, ke ce daman kile wami Hasashen soyayya zalla a gidan mijin, bawai ba a samu ba ne amma tana ɗauke da ƙalubale kala kala." 

"Uhm, to Allah Ya kyauta." Bhatool ta faɗa tare da kwantawa a kan kujera. "Yaya soyamun ƙwai." 

"Ba ki ga banda lafiya ba ne?." 

"Nima ai ba lafiyar ce dani ba, ciki gareki ciki gareni." Dariya Yaya Karima ta yi sannan ta ce. "Allah Ya shirye ki Bhatool, bara na sa mai aikin nan ta yi miki." 

"Ni kinga Momi ta aikon mu da masu aiki, amma iya share share na ce suna yi sai su tafi, idan ɗaya ta yi na safe, ɗayar ta yi na yamma." 

"Eyh hakan ma ya yi, ni dake cikin nawa ya tsufa ai." 

"Aini Yaya cikina ya na fitowa zan tafi gida, ko ya yarda ko bai yarda ba."

"Wai ke waya faɗa miki a aure ana cewa ko ya yarda ko bai yarda ba." 

"Ni dai tashi kika soyamun, ɗan cikina yunwa yake ji." Bhatool ta faɗa tana danna wayarta, ta shi Yaya karima ta yi fa shiga kicin, ta lallaɓa ta soya mata ƙwan, tana addu'ar Allah Ya kawo Senate yazo ya kwashe ta su tafi. Bhatool kam na gama cin ƙwan ta miƙe ta kwanta, ba ita ta tashi ba sai azhar, lokacin zuwa Senate biyu, amma ganin tana bacci sai ya ce abarta. "Yaya Shinkafa." Bhatool ta faɗa tana miƙe ido. "Ki tashi ki bi mijinki." Sai a lokacin Bhatool ta kula da Senate dake zaune yana kallonta. "Ni anan zan kwana." Wata uwar harara ya watsa ma ta sannan ya ce. "Sannu cin kai." Ba ta ba shi amsa ba ta sake mai da kan ta ga Yaya Karima. "Ni yunwa nake ji." 

"Bhatool tun ɗazu fa yake jiranki, idan kun je gida kwanci. Kinga ni nan ban ɗora shinkafa ba, kunnun gyaɗa na yi."

"To zan sha." Ta shi Yaya Karima ta yi ta shige kicin. "Ke ta shi mutafi." 

"Nifa na dawo gidan yar uwata, idan ba za a dinga hulaƙanta ni ba." 

"Na daina fa, ki ta shi dan Allah."  Ya faɗa yana karyar da kai. "Sau nawa kana cewa ka daina?." 

"Bhatool ke zuma ce sai da huta." 

"A'a sauro ce, ka ta shi ka tafi gidanka ni ba inda zani, daga nan ma gidanmu zan tafi, bari na kira Abdul ya zo ya ɗauke ni." Ta faɗa tana ɗaukar wayarta, ganin tana shirin ɓa ta masa rai ya sa ya miƙe tsaye to na tafi. "Kafi ruwa gudu." Ai ba ta yi aune ba ta ji ya kinkice ma ta, ya ɗaga ta cas kamar wata yar baby ya yi waje da ita. Yaya Karima na fitowa taga sun fice. "Kai ma shaaa Allah, Bhatool ko rigima." 

Ko ɓangaren Mom bai kai ta ba ya tura ta a mota suka bar gidannan,  tun da suka fara tafiya ran ta a haɗe yake ko kallon inda yake ba ta yi, ƙasa ma ta mayar da kan ta. "Ki yi haƙuri Habibty." Ba ta ɗago ta kalleshi ba ta ce. "Yanzu muna komawa gida zaka daina duk wannan murmushin, duk wannan dariyar, ka wani haɗe rai." Dariya ya yi sannan ya ce. "Na ce fa na daina gaba ɗaya in shaaa Allah." 

"Tom Allah Ya yarda." 

"Kalli inda muka zo." Ɗagowa ta yi, ina zata gani idan ba gidansu ba, yau za ta ga Umma. Koƙarin buɗe motar ta fara, ya riƙe ma ta hannu. "Ki jira ni mana." 

"Thom." Ta faɗa, sannan ya cika ta ya buɗe suka fito, hannunshi cikin na ta suka shiga cikin gidan, sai dai shi kaɗai ya yi sallama ita ba ta yi ba sakamakon jirin da ta ji yana ɗibarta. "Ash." Ta faɗa. "Bhatool are you okay?." Ya tamabaye ta, girgiza kai ta fara yi sannan ta ce. "Kai na." 

"Me ya samu kan?." Ba ta iya buɗe baki ba ta ji jikinta ya sake, shuuu ta faɗa. Da sauri ya riƙo ta ta faɗo jikinsa. "Bhatool! Bhatool." Ya shiga kiran sunnanta, amma ba ta ko numfashi bare motsi. "Bhatool!." Ya sake faɗa, Umma dake xaune ɗaki ba ta san me yake faruwa a tsakar gidanta ba sai murya ta ji daga sama kamar ana kuka. "Umma! Umma!! Umma!!!, Bhatool." Miƙewa tsaye Umma ta yi tare da faɗin. "Subhanallahi." Amma ba ta kai ga ƙarasawa ba ta ji ansake kiran sunnan na ta. "Umma! Bhatool." Da sauri ta fito, tsaye ta yi turus ganin Senate da Bhatool a kwance.

follow for more update, ina gab da yi muku wani free novel din, in sha Allah.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.