Free chapter · Read without an account

Hs 41

by Sayyid · HASASHEN SOYAYYA COMPLETE

Shafi na Arba'in da ɗaya. 
  (41)

A hankali Bhatool ta bude idonta da ta ji ya yi ma ta wani irin nauyi, da sauri ta sake runtse shi da faɗin. "Hasbunallahu wani'imal wakil." Sakamakon wani azababben jiri da taji. "Kamar magana ta yi." Sautin Muryar Umma ya fito, a hankali Bhatool ta gyaɗa sannan ta ce. "Uhm!." Abdul ne ya yi saurin zuwa kanta yana faɗin. "Bhatool! Bhatool me ya faru?." 

"Kar ka yi ma ta ihu dan Allah." Umma ta faɗa, daidai lokacin aka turu ƙofar ɗakin aka shigo, Mom ce tare da Dad suka shigo a tare, Umma iya Mom ta kalla ba ta bari sun haɗa ido da mai shigowa bayan Mom ba ta kauda kai, amma haka kawai ta ji bugun zuciyarta na ƙaruwa, mussaman lokacin da ya yi sallama. "Bhatool ya jikin naki?." Mom ta faɗa tana ƙarasawa kusa da ita. "Yanzu ta fara magana." Umma ta faɗa a hankali. "Ina yini?." Abdul ya faɗa yana gaida Dad. "Lafiya ƙalau my son, ya jikin na ta?." 

"Alhamdulillah." Abdul ya faɗa yana kallon yadda Dad yake bin Umma da wani irin kallo, ba tare da Umma ta kalleshi ba ta ce. "Ina yini?." Dan ita gaba daya ya cika ɗakin, tana mamaki ko sirikinta mahaifin mijin Karima ba ta jin kunyarsa haka. "Lafiya ƙalau ya mai jikin?." 

"Da sauƙi." Ta faɗa muryar na dawo mata a kunne, ita fa tasan wannan muryar. "Umma, ina Senate?." Bhatool ta faɗa murya cike da wahala. "Zaki sha ruwa?." Mom ta tambayeta. Gyaɗa kai ta yi alamar 'Eyh.' 

"Miƙo ma ta ruwan." Mom ta faɗawa Umma, Umma ta sa hannu ta miƙo ruwan daidai lokacin idanunta suka faɗa cikin na Dad dake zaune kan kujera ya kafe ta da ido, kamar walƙiya haka Umma ta gani, da sauri ta sake kallonsa. "Innullahi wainna illahir raji'un." 

"Lafiya?." Mom ta tambaya, da sauri Abdul ya ƙaraso inda take yana faɗin. "Umma me ya faru?." Hannu tasa tana nuna masa Dad dake zaune. "Umma mahaifin Senate ne fa." Mom ce ta juyo ta kalli Umma ta kalli Dad. "Lafiya wai?." 

Miƙewa Dad ya yi ya matso kusa da Bhatool. "Daughter Allah Ya baki lafiya." Ya faɗa tare da ficewa, a take Mom ta miƙe ta yi bayanshi tana fadin. "What's wrong?." Mom na fita Abdul ya masto kusa da Umma. "Umma waye wannan din, kinsan shine?." Hawaye ne suka fara zarya a fuskar Umma wanda ya matuƙar daga hankali Abdul da Bhatool. "Umma ya sake ni." Bhatool ta faɗa. "What!." Abdul ya tambya. "Senate ya sake ni." Ƙofar ɗakin ce ta bude Mom ta shigo, a bayanta kuma Ahmad ne wanda ya kaɗe Bhatool kwanaki, a yanzu ya zama abokin Abdul sosai da sosai, sun yi waya ne ma dazu yake ce masa yana asibiti Bhatool ba lafiya shine ya zo. " Bhatool me kike cewa haka?." Mom ta faɗa cike da tashin hankali, ga abinda ta ga ya faru yanzu mijinta da surikarta, ga kuma yanzu ta ji ance wai Senate dake mugun son Bhatool ya sake ta. 

"Ina waya ta?." Bhatool ta faɗa. "Tana gida." Abdul ya bata amsa. "Wallahi ya sakeni, wai ina cin amanarsa." Bhatool ta faɗa tana rushewa da kuka, Mom ce ta ɗakko wayarta ta fara neman lambar Senate, sai dai har ta ƙara ci bugunta bai ɗauka ba. 

"Innullahi wa'inna illahir raji'un." Abinda kowa ke maimaitawa. "Wannan auren tun farkon shi yaran nan basu sami zaman lafiya fa, ga dai soyayyar suna nunawa junansu amma abubuwan kamar an riƙe su." Umna ta faɗa jikinta duk ya yi laushi. "Wallahi Maman Bhatool, kwanaki haka na ce kamar lamarin asiri ne fa." Mom ta faɗa. "Yanzu gashinan har ta kai ga saki ya shiga." 

"Ai wannan sakin yanzu zai warwarshi." Mom ta bawa Umma amsa. "A'a mene dalilin yin sakin, Senate fa kowa shaidane yadda yake matuƙar ƙaunar Bhatool." Abdul ya faɗa. Ƙara gwada lambar Senate Mom ta yi amma ba ta tafiya, ita yanzu duk tsoronta kar wani abu ya sami Senate ɗin. "Umma ina kwana?." Sai a lokacin ma idon su ya kai kan Ahmad da ke tsaye. "Lafiya ƙalau Ahamd." 

"Ya mai jikin?." 

"Jiki Alhamdulillah wallahi."

"Allah Ya ƙara lafiya." 

"Amin Amin." 

"Bhatool sannu." Ya faɗa yana kallon Bhatool. "Yawwa." 

"Ya jikin naki?." 

"Da sauƙi." 

"Allah Ya ƙara sauƙi." 

"Amin na gode." Daidai kuma lokacin likita ya shigo, kallon Bhatool ya yi sannan ya ce. "Ma sha Allah, ta bude idon kenan?."

"Eyh wallahi Dakta." Umma ta faɗa. "Daman na faɗa miki, ba wata matsala ba ce kuma Alhamdu Lillah cikin jikinta bai sami matsala ba, sai dai tana buƙatar dogon hutu sosai da sosai." 

"Tom in sha Allah za ta huta." Umma ta faɗa. "Yanzu zuwa yaushe za a iya sallamarta?." Mom ta tambayi likitan. "Ko yanzu ma, magunguna kawai za a amsa." 

"Okay tom ba matsala, Maman Bhatool me zai hana Bhatool ta tawo gidana?."

"Amma da ta ce gidan Yaya Karima zata zauna, kuma ina ganin kamar hakan zaifi sabida 'yar uwarta ce kuma zata fi sakewa ta yi magana da ita akan abinda ke damunta." Abdul ya faɗa, sabida ba ya so ta je gidan Mom. 

"Eyh hakan ma ya yi tom." Mom ɗin ta faɗa. "Ai Abdul da taje can ɗin, ko ina ɗaya ne ai." Umma ta faɗa. "A'a ai ba matsala gidan Kariman da gidana ai duk abu daya ne, kuma kinga kusa ne, sannan kinga ni bamfiya zama ba." 

"Tom babu matsala hakan ma, Allah yasa hakane yafi alheri." 

"Amin Amin." 

Tashi Abdul ya yi ya riƙe hannun Ahmad suka fice, daman Abdul haka yake buƙata bai bari sun gama fita ba ya ce. "Wai sakin Bhatool yaron can ya yi?."

"Wallahi haka ta ce." 

"Amma fa yaron nan baida hankali, gaba daya an sangarta shi da kudi a gida, ya dauka aure hauka ne?." 

"Zafin kishi ne kawai ya yi masa yawa, kwanaki da muka yi magana da ita ta ce wai zarginta yake tana kula ka." 

"Ni kuma?." Ahamd ya tambaya. "Eyh kuma ya ga yanzu muna mutuncu shine yake tunanin ni nake so na kashe mata aure na baka ita." 

"To yanzu ai ya kashe auren, ba a jindaɗi da mutuwar aure, amma kuma ance wani hanin ga Allah, baiwa ce." 

"Allah Ya kyauta." Abdul ya faɗa. "Yanzu ina zaka?."

"Zan kira Yaya Karima na faɗa mata ne, sabida ba tasan komai ba akai." 

"Okay yakamta kam." 

*****

A motar Mom aka dauƙi Bhatool, Umma dai ta ce gida zata tafi tazo daga baya, Senate kuma da Ahmad suka bi su a baya. 

Yaya Karima ba ƙaramin Mamaki ta yi ba da aka ce wai Senate ya saki Bhatool, abun ma kai bazai dauka ba. "Yaya nifa ba duk wannan ba ne ya dameni, akwai wani abu da Umma ke ɓoye mana tsakaninta da Abban Senate." 

"Waye Abban Senate?." Yaya Karima ta tambaya. "Baban Senate dai, ɗazu ni da Bhatool mun ga abinda muka gani a asibiti." 

"Me kuka gani?."

"Ni nasan komai." Bhatool ta faɗa. "Me kika sani?." Inji Yaya karima. "Abba Senate shine Yunusa wanda Umma ta so shi kafin aka aura mata abbanmu." 

"Tabbas Abba ya sha faɗan mana cewa, Umma mutuniyar kirki ce ta aureshi ba tare da tana son shi ba, amma ta yi masa biyayyar da ba ta taɓa saɓa masa ba." Yaya Karima ta faɗa. "Ke waye ya ce miki shine?." 

"Tun ranar da na fara ganinsa a gidansa naji a jikkna kamar nasan shi, kwanaki da muka zuana a gidan ni da Senate, na shiga babban falonsa kai masa fruit da Mom tasa Senate shi kuma yasani, log book ɗinsa dake kan table na bude hoton Umma ne a farko amma tun ba ta kai shekaruna ba, sao dgaa baya ma na yu tunanin yana sane yasa naga hoton sabida na fahimci komai."

"Ikon Allah." Yaya karima ta faɗa, Abdul kam cewa ya yi. "To sai mene, a yanzu dai yasan baza ta taɓa auren sa ba." 

"Abduk kai yaro ne bakasan soyayya ba, kai nufinka hawayen da ka ga Umma na yi na mene idan ba na soyayya ba." Bhatool ta faɗa. "Nine yaron dan ubanki abinda nasani baki sani ba."

"Dan Allah ku bar wannan maganar haka, ni hankalina yana kan mutuwar auren Bhatool." 

"Wallahi ni Yaya mamaki abun yake bani fa." Abdul ya faɗa. "Ni kaina haka me yake damun Senate." 

"Yaya ba abin mamaki ba ne idan kika duba hotonan da ya turumun." 

"Wanne hotona?."

"Shi yasa na tambaya ina wayata, hoto ne a zaune cafteria kuma asalin hoton ni da Jannah da Amrah ne, amma aka yanke su, sanan wani kuma ina rungume da namiji." 

"Rungume kuma, innullahi wainna illahir raji'un." Yaya karima tafaɗa, Abdul kama ta shi ya yi ya fice. "Ina zaka?."

"Zanje na ɗakko wayarta ta ne." 

"Eyh yakamata kam." Kuka Bhatool ta fashe da shi, gaba ɗaya abun ya dawo ma ta sabo, wane irim abu ne haka me aka shirya ma ta haka. 

"Ki yi hakuri Bhatool, komai zai zo da sauƙi." 

"Yaya me na yi haka, waye yake son kashen aure haka?." 

"Koma wane komai zai bayyana in sha Allah."

*****

Amrah ce zaune kan gadon ɗakinta wayarta na riƙe a hannu ta kara ta a kunne. "Salamu alaikum." Ta faɗa bayan an ɗaga wayar, bayan amsa ne ta ce. "Anty aiki ya cika, Senate ya saki Bhatool." 


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.