Free chapter · Read without an account

Hs 43

by Sayyid · HASASHEN SOYAYYA COMPLETE

Shiru ya ratsa ɗakin na wasu mintuna, baka jin komai sai ƙarar fanka dake juyawa a hankali tana raba iska. Bhatool tana zaune ta jingina bayanta da jikin gado, idanunta sun yi jawur saboda kuka, yayin da Yaya Karima take zaune a gefenta, tana kallon yadda ƙanwar tata take abun tausayi. 

Yaya Karima ta gyara zama, ta kalli Bhatool cikin nutsuwa sannan ta ce, "Bhatool, kinsan rayuwa tana da ban mamaki. Wani lokacin mutumin da muke gani a matsayin garkuwanmu, shi ne yake zama silar rugujewarmu. Ba na son in yanke miki hukunci akan kawayenki, amma ina so ki duba abubuwan da suka faru a baya da idon basira. Shin babu wani abu da kike gani ya yi hannun riga da gaskiya?"

Bhatool ta numfasa, sanna ta ce. "Yaya ƙawaye na guda biyu ne, daga Amrah sai Jannah sai kuma Suhaima, tun da ta yi aure suka bar ƙasar, ada ina ganin Jannah kamar ba mutuniyar arziƙi ba, tana mini baƙin ciki ne janye jikinta daga gare mu sabida bakin ciki." 

"Me yasa kika yi wannan tunanin?."

Yaya karima ta tambayi Bhatool, shiru Bhatool ta yi tana son ta tuna da abinda ya faru, sai kuma can ta ce. "Ranar da na faɗa musu zamuje honeymoon sai ta ce wai na dinga riƙe sirri na, da na fa ɗawa Amrah sai ta ce wai baƙin ciki take mini, na auri Senate." 

"Yanzu kuma ya kike gani?." 

"Yaya Amrah ce kawai ke mini yawo a raina, kuma bana so ace ita ce ta yaudareni, bana so ace ita ce ta ci amanata wallahi."

"Ki nitsu Bhatool, ki yi tunani duk wasu matsaloli da kika samu a rayuwarki tun kafin aure da lokacin aure, sai kiga akwai mai alaƙa da Jannah ko Amrah?." 

Shiru Bhatool ta yi ta fara lissafa abubuwan da suka faru a baya a cikin ranta. Can kuma sai ta tuna wani abu, ta kalli Yaya Karima da sauri. "Yaya, kin tuna ranar da Dr. Haisam ya kira ni ya ce mini zan yi aure, har ya ce zanga abinda zai faru ko?." Gyaɗa kai Yaya Karima ta yi sannan ta ce. "Ranar babu wanda na faɗa wa maganar daga Jannah sai ita Amrah, kuma ita Jannah a lokacin muna tsaka da waya ya kirani sabida ita Amrah mamansu ta kira muna voice call ɗin ta sauka, to ni dai su biyu na faɗawa wannan labarin, na aure na da Senate kafin maganar ta fita. Sannan akwai wata rana da Amrah ta kirani ta ce mini wai Dr. Haisam yana yi mata barazana akan sai ta ba shi address ɗina. Ta ce mini tana tsoron abin da zai faru idan ba ta ba shi ba, shi ya sa ta ba shi gidanmu. Ranar da yazo gidan nan ɗinnan har naƙi fita, yaya wai me ke faruwa ne tsakanina da Amrah daman ba soyayya ba ce, ba ƙawance ba ne, to mene?." 

Yaya Karima ta girgiza kai cikin tsananin takaici. "Bhatool, a ko da yaushe ina faɗa miki cewa kiyi hattara, amma kika ce ƙawaye ƙawaye, yanzu wa za ki tin kara ki ce. Ƙawar ki ce ta kashe miki aure, wannan abun ya yi kama da na hankali Bhatool, Amrah tana amfani da rauninki ne wajen cin miki dunduniya. Ta yaya Dr. Haisam zai yi mata barazana akan address ɗinki alhali tana da ikon ƙin ba shi, ko kuma ta ba shu na gaibu, Wannan duk dabarun raba miki hankali ne."

Bhatool ta runtse idonta, tana jin wani irin daci a ranta. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Yaya, ashe Amrah ba ƙawa ba ce, ashe ita ce take kitsa mini dukkan wannan masifar?" 

"Idan Amrah da kitsa miki ai kina da babban laifi, har da daukan suttura ki ara mata, me ya shiga kanki ne?."

~~~~Hausari. 

Gidansu Goggo Larai ya cakuɗe, su Hari da Furee yan maza sun daina zuwa sabida yadda su kawu Ilyasu suke roƙarsu kuɗi kai tsaye, Goggo Larai ta matso taga yaran sunyi aure amma iyayensu maza basa bari samarin su zauna, yau tun safe aka tashi da tashin hankali akan jiya kawu Mufi ya roƙi saurayin Furee shi kuma ya ce ya daina zuwa. Furee da Habi duk sun rasa inda za su sa kansu, ita kanta Goggo Larai ta yi danasanin karɓo su
"Wannan wane irin hauka ne haka? Yanzu abin da ake gudu ya faru kenan? Saurayi ɗaya da ya rage ya ce shima ya daina zuwa, mene amfanin haka, bakwason yaran naku su auro ne ko ya?." Goggo Larai ta faɗa tana kuka tana.
Furee ta kalli Habi, sannan ta ce, "Mu tafi gidan Umma kawai. Ba za mu iya zama a nan ba muna ji muna gani. Kowa zai gudu mu aure muke so."

"Ku tafi na amince wallahi, ku tafi ni ƙiyayyar Habiba da 'ya'yanta ba ta yi minu rana ba, wallahi na yi danasani, na tuba ku tafi dani na nemi yafiyarsu haba."

****

Amrah tana zaune a ɗakinta, ta kira wayar Anty kusan sau biyar amma ba ta ɗaga ba. Gaba daya abun ya tsaya ma ta, ita ta raba auren Bhatool da zuciya biyu ne, ita duk ƙiyayyarta ba ta kai ta ga raba auren su ba, amma wannan matar tai ta ɗora ta akan hanya ba ta yi mata alkwarin aura mata ɗan ta bayan ta raba auren, to amma yanzu gashi kwata kwata ta daina daukar wayarta, ƙara buga wayar ta yi amma still ba a ɗaga ba, ba shiri ta miƙe ta ɗau mayafinta. "Banga ta zama ba wallahi." Ta faɗa tana ficewa. 

Kai tsaye gidan Anty ta nufa, duk da ba mazauniyar garin ba ce amma tana garin babu wamda yasan ta na nan sai Amrah, ita ma sabida tana bata abinda za ta sawa Bhatool a gida ko Senate a ɗaki. Tana cikin napep tana faman tuna-tuna ne kala kala. "Yanzu idan matar nan ta yaudare ni ina na kama?." 

"Ai walalhi ita ma sai na yi mata tijara, kan uba." Ta faɗa daidai lokacin da ta ƙaraso ƙofar gidan. Tana shiga gidaan ta tarar da Anty zaune a babban falonta tana kallon talabijin cike da natsuwa. Amrah ta shiga da sallama ta durƙusa tana gaisheta, wani mugun kallo Anty ta watsa ma ta. Wadda ba kowa ba ce fa ce  Maman Anas, ƙanwar Mom uwa daya uba daya. 

"Ina kiran wayarki bakya gani." Amrah fa faɗa ganin baza ta amsa ma ta ba. "Ina gani Amrah me zan yi miki?." Da mamaki Amrah ta kalleta sannam ta ce. "Kinsani ayyuka kuma na yi miki su, kin yi mini alƙwari kala kala ciki har da na zaki auran ɗanki Amas bayan na raba Bhatool da Senate, sabida acewar ki 'yar ki Namrah ce ta da ce da Senate, kinsanni duk wani aiki, ki bani magani na zuzuba a gidan, kin sa naje na jawo ta waje, kin haɗa tuggu da hoton Ahmad wanda kika sa aka kira shi da muryar namiji akan yazo su haɗu da abokinsa, wanda ba komai ba ne fa ce son haɗa Bhatool da Senate faɗa, bayan ta fito kika ɗauƙi hotonsu suna gaisawa aka turawa Senate, kinsa na ari kayanta na kawo miki, kinsan na jata cafetria da kayan kinsa anyi mata huto, an turawa mijin kuma auren ya mutu, na cika miki alƙwarin da na yi miki a lokacim bikin, dan haka nima a yanzu ina buƙatar nawa cikon alƙwarin." 

"Amma Amrah baki da hankali, kina tunanim yadda kika sam amfanin bin malamai a yanzu zan bari na haɗaki da ɗana ki yi aure shi, tabbas Amrah, kinyi mini aiki mai kyau. Dan haka kingama amfanin ki." 

"Wallahi kin cuceni wallahi Allah." Dariya Anty ta yi sannan ta ce. "Ban cuce ki ba, kika cuci kanki, ni kawai na yi amfani da kishinki, mugun halinki, baƙin ciki irim naki, na haɗa su da hikimata na yi amfani dake wajen ganin na raba su." Anty ta faɗa sannam ta ce. "Yanzu ki tashi ki bani waje sannan karki sake zuwa inda nake." 

"Wallahi baki isa ba, sai kin biya farashin abinda kika yi kuma sai na tona miki asiri, sai kin hulaƙanta, wallahi." Amrah ta faɗa tana tashi.

*****

Su Bhatool suna zaune Abdul ne ya shigo gidan, hannunsa ɗauke da wayar Bhatool. " Sannu da zuwa." Bhatool ta faɗa. "Yawwa Bhatool, ga wayar nan an gyara." 

"Ka fara cin abinci." Bhatool ta faɗa, zama ya yi sannan ya ce. "Na ci a waje." Karɓar wayar ta yi ta buɗe wayar ta shiga cikin gallery, idanunta suka sauka akan hotunan da Senate ya turu. Hoton farko ita ce zaune a cafeteria, an yanke hoton su Amrah an bar ta ita kaɗai. Amma babban tashin hankalin shi ne hoton gaba wanda take rungume da wani. 
Wani irin kuka ne ya ƙwace wa Bhatool lokacin da ta ga yadda aka shirya hoton. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Yaya kalli hoton! Wannan fa ba ni ba ce, kina gani, yaushe na kai haka ƙiba, wallahi wata macen ce aka saka da kalal kayan nawa." 
"To ko Amrah ɗin ce?." Yaya karima ta tambaya tana amsar wayar. "Ita ma ba ta kai haka ƙiba." Abdul ne ya karɓa bayan Yaya karima ta gama gani. "Wannan hoton wata ne aka sanya fuskarki a jiki ta hanyar amfani da computer (AI). Yaya kalli yadda wuyan macen yake daban da na Bhatool."
"Amrah... Amrah kin cuce ni!" Bhatool ta faɗa tana kuka mai ban tausayi.

A Abuja kuwa, Mom tana ta ƙoƙarin kiran Senate. Daga ƙarshe ya ɗaga wayar, amma muryarsa ta fito a shake, irin ta mutumin da ya sha kuka ko kuma ya rasa natsuwa.
"senate me kake yi haka? Ka dawo gida yanzu! Ina son mu tattauna wannan maganar fuska da-fuska," Mom ta faɗa cikin murya mai zafi.
Senate ya yi shiru na wasu daƙiƙoƙi, sannan ya ce, "Mom, don Allah ki yi haƙuri. Ba zan iya dawowa yanzu ba. Zuciyata tana mini zafi, kuma ba na son in ga kowa a halin yanzu. Na san abin da kike son faɗa, amma hotunan da na gani sun riga sun yanke mini hukunci."

"senate karka zama mai saurin fushi! Shin baka san cewa makiya na iya shirya komai ba?"
"Mom, please... zan dawo idan na samu natsuwa. Amma yanzu, bar ni in kaɗai Bhatool kuma na haƙura da ita har Abada." Ya faɗa  tare da kashe wayar cikin halinsa na rashin son yawan magana idan ransa ya ɓaci. Ya kashe wayar ya bar Mom cikin damuwa.

"Na haƙura dake Bhatool... na haƙura dake har abada Bhatool, ki je ki yi duk abinda kike so, duk abinda kika ga dama."

Legendspen
***


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.