Free chapter · Read without an account
11
AL'AJABIN SO
(heart touching story)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Rubutu a kan ruwa... Paid*
And now..
*AL'AJABIN SO*
*BOOK 1*
*Page Eleven*
A hankali ta buɗe idanunta hawaye na gangarowa tace
"Ya..Muktar ba zamu bari da sa...fe in Maami ta z..."
Hannunta da ya fisgo ne ya yanke maganan, ta sauko ta sa takalami cikin tsananin tsoronshi, jan hannunta kawai ya dinga yi har motanshi ya buɗe ya jefata ya zagaye ya shiga, ya ja suka bar wurin da mugun gudu, har wani jiri da amai take ji sbd gudun da yake yi bata taɓa fuskantar irin shi da ita a cikin mota ba, a harabar wani Hotel ya tsaya chan wajen garin ya kife kanshi a jikin steering sbd baccin dake son kwashe shi...
"Ya muktar..! Ya muktar..!!"
Take kiran sunan a tsorace tana ɗan kalle kalle sai kuma ta kai hannu ta tattaɓa shi ko motsi be yi ba, hawayen da dama basu daena zuba bane suka ƙaru
"na shiga uku na ni Fatima"
Ta faɗa cikin karaya da tsantsar damuwa.
Wani tunani ne ya faɗo mata, tayi saurin sa hannu ta murda handle ɗin sede motar a rufe, da sauri ta sa hannu cikin sanɗa ta duba wayanshi ta taɓa screen ɗin ba password, hannu ta kai jikin kofanshi ta buɗe motar daga madannin wurin, jikinta na rawa kaman wacce aka sato ta buɗe ɓangaren ta ta sa kafafunta waje hannunta dake rawa na dialing Layin Maami, kaman an tsikareshi ya farka wani irin fusgo hannunta yayi ta dawo da karfi har tana buguwa dashi ya tsinka mata mari yana kashe wayan da har ya soma ringing..
Kuncinta ta dafe tana kuka
"Zan ɓaɓɓalla ki in baki rufe min baki ba... Wuce mu je"
Ya fito ya zagaya ya fusgo hannunta suka yi ciki.
Key ya karɓa alamar dae regular customer ne suka yi ciki, tana kuka ya cillar da ita a tsakiyar ɗakin
"Meyasa kake min haka? Yaya Mukhtar kaji tausayi na mana... Am not a slav..."
"Will you shut up! In ji wa yace u r not my slave? Ko baki san duk mace baiwa bace a gidan miji? Oya come and remove this clothes for me zan yi wanka"
Miƙewa tayi gudun kar ya kara taɓa lafiyarta taje jikinta na rawa ta cire mishi, hannunta ya ja suka yi toilet wankan ma ita ya saka tana kuka ta mishi, yace tayi nata ta same shi yanzu.
Haka tayi don miji irin Muktar ta fahimci in tace zata ke musu dashi watarana kakkarya ta ze umminta ce kuma da asara.
A daren ma be barta ba ta sha wahala kwarai a wurinshi, haka ya zube ya cigaba da bacci ta miƙe da kyar ta shiga bayi ta gasa kanta da ruwan zafi, ta fito da alwala, akan sallaya ta tsaya tana sallah tana kuka, anya suna da rabon farin ciki?
Sai kuma ta tuna maganan umminta
"Fatima tun da nayi sallama da ƙasata na shigo wannan na san nayi sallama da farin cikin rayuwa, na fuskanci kalubale iri iri da damuwa kala daban daban kan Allah ya haɗa ni da mahaifinki ya maida ni tamkar sarauniya ya bani duk wani farin ciki da na rasa a baya amma shima Allah be bar min shi ba, tafiyar shi ga rabbissamawati ya sarar dani, na ɗauka nima zan bishi a kowani lokaci amma tunda na tsallake baƙar wahalar da na sha daga rasuwarshi zuwa haihuwar ki na sa a raina cewa komai ze zo ya zama tarihi, iko na rabbi ne kawai dawwamamme, na sa a raina zan raineki kila sirrin farin cikina na gareki, sai kuma gashi yadda kema Allah yayi dake.
Dukda haka ban sare ba, kema ina me karfafamiki gwiwa da kwantar miki da hankali a kan cewa in shaa Allahu zaki wayi gari kiga duk wannan sun wuce, imani da yaƙini akan ubangiji yana riskar da bayi zuwa ga magantuwar matsalolinsu, wallahil azeem ubangijinmu na sane da lamuranmu kuma ina da tabbacin wata rana ze fidda mu daga cikin wannan jarabawa, ko ban riski lokacin ba in shaa Allahu wata rana zaki yi farin ciki, zaki yi murna zaki tuna kuma da cewa na faɗa miki hakan"
Hawayenta ta share ta zurawa muktar ido, kila watarana shine ze zama farin cikinta, kila kuma karshen zaman su na iya zuwa ko kusa ko nesa, amma ka fin nan tayi alkawarin yunkuri wurin chanza shi, zata kasance me yi mishi Adu'a a ko wani motsinta zata taya mahaifiyarshi yakin mai dashi mutumin kirki da yardar Allah ko da kuwa ita baza ta samu ribar komai ba.
Anan kan sallayan tayi bacci da asuba ma jin mutum kawai tayi ya ɗauke ta zuwa gado, bata mishi tirjiya ba ta hakura saide fuskanta be huta da ruwan hawaye ba don ba daaɗin abun take ji ba banda azabar ciwo, seda ta sake wanka na ruwan zafi sossai tayi na tsarki ta fito tayi sallah, yana kwance yana bacci, a hankali ta matsa kusa dashi ta sa hannu ta na ɗan bubbuga kafafunshi
"ya Mukhtar! Ya muktar ka tashi kayi sallah don Allah, lokacin sallah na wucewa"
Ko motsi be yi ba, da ta matsa mishi ya ja dogon tsaki tare da kaiwa hannunta harbi da kafa da sauri ta ja baya ya samu iska, tagumi ta zuba tana kallonshi har bata san sadda bacci ya kwashe ta a wurin ba.
Sai misalin karfe goma ta tashi, yunwa ne ke dawainiya da ita kuma har lokacin bacci muktar ke yi, idanu ta zuba mishi tana aikin kallo, da zai shiryu muktar ba karamin kyau yake dashi ba, tana nan tana kallonshi tana sake-sake, ya buɗe idanu.
"Wani maitar ne kike yi da zaki tasani a gaba kina kallo haka?"
"Ba komai, ina jin yunwa ne"
"Ni zaki cinye kenan sai ki koshi?"
Da sauri ta girgiza kai, tsaki ya ja kan ya sauka seda ya tsaya wurin landline yayi call kan ya shige bayin, tana nan zaune har ya fito yayi wanka sede ya maida kayanshi ne don shima babu komai nashi anan ɗin, tsayawa yayi da niyyar sallah kaman kar tace komai sbd tsoron shi sai kuma tace
"Ya Mukhtar namiji fa daga cibiyar shi zuwa guiwowinshine al'auranshi, Kaga zaka yi sallah kuma wandon be kai guiwa ba be kamata ba"
Ta faɗa a tsorace
"karki karɓa in nayi" ya faɗa yana jan tsaki tare da tada Sallar shi ita dae ta san sallahn nan kam se a hankali karfe sha ɗaya sallahn asuba sannan da gajeren wando.
Knocking aka yi ta miƙe ta buɗe, tray ne me ɗauke da abinci kala uku da ruwa da wani energy drink, karɓa tayi ta zo ta ajiye ta zauna jiranshi har ya idar ya juyo.
"Ɗauki abin da zaki iya ci"
Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba.
Shinkafa jollof ta ɗauka da ruwa, ya ja sauran, tana ci tana satan kallonshi ga mamakin ta ya cinye duka abincin trayn nan bata ma yi rabin nata ba, energy drink dinshi yake sha sai wayanshi ya fara ringing don yanzu ya kunnata, dubawa yayi ganin Maami yasa ya ƙi dagawa kiran duniya ta mishi ya ƙi ɗauka, chan kiran Alhajinsu ya shigo mishi kaman kar ya ɗauka ba sai ya ɗaga.
"Muktar ina ka kai ƴar mutane Maaminka ta kasa natsuwa? Kana so sai ka tayar mata da hawan jini ko?"
"Dad naga dae matata ce, me nata?"
"Ka amsa mini kuna ina? Taje gidan ku bakwa nan"
"Hotel"
Ya faɗa yana haɗe rai.
Ita dae tausayin Maami ne ya rufe ta ta san duk don ita ne hankalin Maamin yake a tashe, a hankali tace
"ya Mukhtar ka bani Maamin zan yi magana da ita don Allah"
Harara ya zabga mata kan yacewa mahaifinshi da ya gama ce mishi su dawo yanzu
"gaskiya ba zan dawo ta rabani da matata ba, ni ban rabata da mijinta ba haka kawai"
"Don Allah yaya Mukhtar"
Wayan ya jefa mata har yana dukan kirjinta ta dauka tana gaida Alhajin cikin girmamawa ya amsa yana tambayar lafiyanta tace da sauƙi Maamin na kusa?
muryar Maamin ta ji tana cewa
"Fatima? Kina lafiya kam?"
"Lafiya ta ƙalau Maami, eyaa Maami ki mana alfarma ki kwantar da hankalinki kinji don Allah, in sha Allah babu abunda zai faru"
Ta faɗa a karye cikin son karfafawa Maamin gwiwa, Maamin da taji hawaye na son zuba mata ne tace
"Fatima ki yafe mana mun kuntata miki rayuwa"
Girgiza kai tayi tana share hawayen da ya zuba mata
"ko ɗaya Maami idan da ba don auren ba ai da ban sanki ba, amma yanzu na sameki bayan Ummina babu abin da ya kai hakan farin ciki a gare ni"
"Ki bashi wayan"
Maami ta faɗa, miƙa mishi ta yi.
Karɓa yayi yana kau da kai daga kallonta yana taɓe baki
"Ina kwana?"
"Baka damu da kwana na ba ai muktar da ka damu da ba haka ba, ka ɗauki yarinyar nan ka maida ta gidanta ka bar Hotel da ita, sannan ka tabbatar ta cigaba da zuwa makarantar ta ranar Litinin"
Tana kai nan ta kashe wayan, hawayenta ta share Alhj dake tsaye yace
"menene kuma ne Maamin su? Ina dae yarinyar nan tace miki babu komai ki rabu da ita da mijinta mana"
Cikin takaici ta kalle shi tace
"Zurfin tunani da tarin tarbiyar da yarinyar nan take dashi she's too good for muktar wallahi"
Tana kai nan ta miƙe ta bar mishi ɗakin.
Su kuwa bayan ya ajiye wayan ya taɓe baki yace
"Maami matsala"
"Subhallah"
Ta ambata chan ƙasa, ba don tana tsoron yin magana ya zama laifi ba da tace yayi saurin tuba da wannan kalma da ya je fi mahaifiyarshi dashi in har yana son rabauta duniya da lahira iyaye ba abin wasa bane amma inaa.
"Ke! Tashi mu tafi"
Da sauri ta miƙe tabi bayanshi, a cikin harabar gidansu yayi parking, ajiyar zuciya me karfi ta sauke ko ba komai zata je ta samu tayi magana da Mahaifiyarta, bata jirashi ba tayi ciki zuwa ɗakinta ta ɗauko wayanta ta fara turawa ummi text message.
"Alaya ina kika shiga kwana biyu nayi sako shiru babu amsa? Kina lafiya dae ko? Ko ciwonki ne ya tashi? Ina ma ina da bakin kiranki in ji muryarki don tabbatar da lafiyanki... Don Allah kar ki min karya baki da lafiya ko?"
Kuka ta fashe dashi a fili tace
"Ummi bani da lafiya, ummi bana son wannan aure bana son shi, mugu ne, ummi marar tsoron Allah ne, bashi da ibada be san menene addininshi ba, ummi abubuwan da nake son faɗa miki kenan amma ba zan iya ba..."
Typing tayi
"na ɗan yi rashin lafiya amma da sauki Maami ta kula da komai yadda ya kamata"
"Subhallah ya jikin? Allah ya sakawa Maami da alkhairi"
"Alhamdulillah ummi babu komai yanzu, Ameen thumma Ameen kefa ummi? Babu wani damuwa? Su Hajiya Zeenat basa takuraki? Aiki be miki yawa ba ummi?"
"Babu wani matsala Alayah, Allah ya baki lafiya"
Tattaunawa kaɗan suka kara taji an turo kofan, da sauri ta ɗaga kai ta kalleshi..
"Ina da baƙi da dare ki shiga kitchen ki shirya musu abinci"
A hankali tace
"Toh"
Har ya juya ya ce
"Ki tabbatar mutane akallah ashirin zasu ci su koshi"
Yana kai nan ya fice, bata kawo komai ba bayan tayi la'asar ta shiga kitchen dinta Allah ya sa tana jin karfin jikin nata sossai Alhamdulillah, sossai ta zage tayi girkin har kala biyu jollof nd fried Rice pepper chicken sai ta ɗan yi snacks ta haɗa fruit drinks masu daaɗi, dab Magrib ta fito daga kitchen din wanka ta sake da alwala ta zo tayi sallah, ta jima tana karatun alqur'ani da rokar wa kanta mafita a wurin rabbisamawati har aka yi isha ta tashi ta gabatar kaman wasa tana zaune nan ta soma jin hayaniya a ranta take ayyana baƙin sun zo kenan.
Bata gama nazari ba ya shigo
"Tashi ki shirya jarrey baƙi na na jira a yi serving ɗin su"
A hankali tace
"Amma Ya muktar abincin ai yana dining naga be kamata sai na fita na sassa......"
"Kina so in wanka miki mari?"
Shiru tayi ta miƙe shine ya shiga drawer ɗinta ya duba ya zaɓo wani pencil gown ya wulla mata, seda ta gama kallon kayan kan ta saka a hankali babu shape na jikinta da be nuna ba.
Hijab ta fara dubawa yayinda shi kuma yake sake da baki yana kallonta don ba karamin gigita shi tayi ba sai gani yayi ta saka hijab
"ke ina zaki je da wannan abin?"
"Wurin baƙin naka ba?"
Tsaki me karfi ya ja yarinyar nan an yi bagidajiya
"ke kin san me sunana kuwa? PIYA-PIYA nake maganin kwari shine matata zata fita cikin abokaina da wannan abun a samu abun nuna ni? Kin cire ko kuwa?"
Ya daka mata tsawa daga karshe
"Ya Mukhtar ba zan iya fita da wannan rigan cikin maza ba hakan ya sabawa Addi...."
Wani wawan mari ya sauke mata har seda ta faɗi
"ke wai yaushe na zama sa'anki da zan faɗa ki faɗa?"
Tana dafe da kunci cikin gunjin kuka ta miƙe
"Babu biyayya a bijirewa ubangiji ya Mukhtar ba zan iya..."
Sake kifa mata mari yayi ya ja hijab ɗin ya fisge ya yar kan ya janyo hannunta suka yi cikin parlorn tana tirjewa.
Chak ta tsaya tana karewa parlorn kallo, mata da maza ne daban daban cikin shiga irin ta rashin sanin darajar kai wasu na rurrungume da juna yayinda kwalaben shiha suka yi bakwai a parlor hayaƙi har ya fara cika parlorn yana maida wutan wani fari fari baki baki, ganinsu tare yasa aka hau ihu sai kallon maita mazan suke mata da sauri ta koma bayanshi ta ɓoye.
Rita wacce tsab Alaya ta gane ta ita ce ta kawo shi daren farkonsu a Buge tace
"Ga dae kyau sede babu wayewa duhun kai yayi yawa"
Shewa suka ɗauka don a yadda tayi maganan har da kishi.
"Omoo kuna ganin kaya!"
Wani ya faɗa yana zuƙar shisha ɗin shi yana wani karkata kai yana kare mata kallo.
Fusge hannunta tayi da karfin tuwo ta juya da gudu tana ji suna mata ihu akan bayanta ta faɗa ɗaki ta rufe kofar da key ta zube a wurin tare da fashewa da matsanancin kuka tana squezing zuciyarta dake zafi da hannu biyu gwanin tausayi...
Want the next chapter?
Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.