Free chapter · Read without an account
Hs 57
(57)
An kammala bikin Abdul da Ahmad lafiya cikin nasara da albarka. Amaryar Abdul, wato ƙanwar Ahmad, ta tare a gidanta dake kusa da su Umma, yayin da Ahmad shi ma ya tare da tasa amaryar cikin kwanciyar hankali. Wannan aure ya ƙara danƙon zumunci tsakanin gidajen guda biyu, inda kiyayya ta koma soyayya, zargi kuma ya koma yarda.
Bayan bikin, hankali gaba ɗaya ya koma kan Bhatool. Senate ya ware kusan dukkan lokacinsa a kanta. Babu inda yake zuwa idan ba asibiti ko wajen aiki ba, to yana gidan Umma. Soyayyar da suke nuna wa juna a wannan lokacin ta zarce kowace irin soyayya da suka yi a baya. Senate yakan zauna ya yi ta yi mata tausa a ƙafarta, yana mata hirar yadda gidan nasu zai kasance idan ta dawo.
Wata rana da yamma, suna zaune a tsakar gidan Umma, iska mai daɗi tana kaɗawa. Bhatool ta jingina kanta a kafaɗar Senate, tana kallon cikinta dake ta motsi.
"Senate," ta kira sunansa cikin muryar dake cike da natsuwa.
"Na'am rayuwata," ya amsa yana ƙara gyara mata zaman mayafinta.
"Gaskiya na gaji da wannan zaman gidan Umman. Na matsu in haihu lafiya, in ga jaririnmu, sannan mu koma gidanmu mu ci gaba da rayuwarmu. Ina son in riƙa tashi a kusa da kai, in riƙa kula da kai kamar yadda ya kamata."
Senate ya yi murmushi, ya sunbaci goshinta. "Bhatool, nima abin da nake jira kenan kullum a raina. Amma kin san dokar Mom; tace sai kin gama jegonki sannan zaki dawo. Ko kina son mu karya dokar Mom ne?"
Bhatool ta ɗan yi fushi na wasa, "A'a, ba karya doka ba, amma gaskiya kewarka tana sanya ni kuka wani lokacin idan dare ya yi."
Senate ya ji daɗin wannan kalaman nata. Ya rungume ta, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa don ƙaunarta. "Kiyi haƙuri ragowar kwanaki ne suka rage. Insha Allah duk yadda kike so, haka za a yi. Zan sake gyara miki gidan nan ya fi yadda kika sani, domin ke ta musamman ce a gare ni."
Haka suka ci gaba da nuna wa juna soyayya mai tsayawa a rai. Kowa ya gansu yakan yi musu fatan alheri, domin sun zama ababen koyi wajen haƙuri da yafiya. Amma a tsakanin wannan annurin, Bhatool tana yawan jin wani irin bacci da kasala dake ziyartar ta, wanda take gani tamkar nauyin ciki ne kawai.
Washegari da safe, Senate ya dira a gidan Umma da wani irin hanzari. Fuskarsa dake cike da annuri ta bayyana cewa akwai wani abun farin ciki dake tafe. Bhatool tana zaune a falo tana shan kwanon tatacciyar madara, ta kalle shi tana murmushi.
"Wannan annuri haka? Ko an kara maka girma ne a wajen aiki?"
Senate ya yi dariya, ya kamo hannunta ya mike da ita. "Tashi mu fita waje, ina son nuna miki wani abu."
Bhatool ta mike tana dambarwa saboda nauyin jiki har suka isa kofar gida. Tana fita, idanunta suka sauka akan wata hadaddiyar mota kirar Lexus 2024, fara sol, wadda aka yi mata ado da furanni da kuma rubutun "For My Queen" a jiki.
Bhatool ta zaro ido, ta rufe bakinta da hannu biyu saboda mamaki. "Senate Wannan motar fa?"
"Kyautar ki ce Bhatool. Kyautar hakurin da kika yi da ni, da kuma farin cikin da kika shigo mini da shi. Ina so ko da yaushe kije asibiti ko wani waje, kije cikin girma da mutunci," Senate ya fada yana mika mata makullin motar.
Tana cikin murnar nan, ashe Umma tana tsaye a bakin kofa tana kallonsu tana dariya. Ganin yadda Senate yake ta faman sosa keya da nuna damuwa akan Bhatool, sai Umma ta katsa musu hira cikin barkwanci.
"Wai kai Usman, yaushe ne zaka daina wannan rashin kunyar taka? Ka dame mu, kullum kana gidan nan tamkar a nan aka haife ka. Na gaji da ganin fuskarka kullum!" Umma ta fada tana boye murmushin dake fuskarta.
Senate ya yi dariya, "Umma, ai kece kika ce na jira sai ta haihu."
Umma ta tabe baki a wasa, "To na janye maganar nan. Na gaji da takura, zo ka dauke matarka ku tafi gidanku kawai, tunda gani nake yi kusan tare kuke kwana."
Bhatool ta fashe da dariya, ta rufe fuskarta da mayafi saboda kunya. Senate kuwa ya saki wani uban murmushi na jin dadi. "Umma gaskiya kika fada? To yanzu ma zan dauke ta mu tafi!"
Haka suka yi ta barkwanci, inda Umma ta kara nuna musu cewa ta yafe wa Senate kuma tana kaunarsa matsayin danta. Wannan ranar ta kasance ranar farin ciki mara misaltuwa. Senate ya dauki Bhatool a sabuwar motar suka zagaya gari, suna jin dadin haduwar kawunansu.
Amma a cikin wannan murnar, Bhatool ta kalli Senate ta ce, "Usman, na gode sosai. Amma ina so ka sani, babban burina ba mota ba ne, babban burina shine mu rayu tare cikin aminci har karshen rayuwarmu."
Suna tsaka da wannan murnar ta sabuwar mota da kuma barkwancin Umma, farat ɗaya sai yanayin Bhatool ya sauya. Ta saki wani ɗan gajeren nishi, ta dafe ƙugunta yayin da zufa ta fara keto mata a goshi. Senate ya kalle ta cikin firgici, "Bhatool, lafiya? Ko nakuda ce?"
"Usman... marata... marata tana murɗawa," ta faɗa cikin murya mai rauni.
Ba tare da ɓata lokaci ba, Senate ya sungume ta ya sanya ta a sabuwar motar nan, Umma ma ta rigo ta ɗauki jakar kayan haihuwa suka nufi asibiti a guje. Senate yana tuƙi yana addu'o'i, hankalinsa gaba ɗaya ya tashi, yana kallon yadda Bhatool take ta faman nishi da ambaton sunan Allah.
Suna isa asibiti, ma'aikatan jinya suka karɓe ta suka kai ta ɗakin bincike. Bayan kusan mintuna talatin, likita ya fito yana murmushi. Ya kalli Senate da Umma dake jiran jin bayani.
"Alhaji, ku kwantar da hankalinku. Wannan alamun nakuda ne ba naƙudar ba. Duban da muka yi mata ya nuna cewa lokacin haihuwarta (EDD) bai cika ba, akwai sauran mako guda cur. Yanzu za a iya mayar da ita gida ta ci gaba da hutawa."
Legendspen
***