Free chapter · Read without an account

THE WEIGHT SHE CARRIED

by Maryam · THE THRONE OF THORNS

           Toshe kunnuwanta ta yi saboda sautin da ta ji kamar yanzu komai ke faruwa.Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka fa ra,amma saboda gaba ɗaya ba ta hayyacin ta ,yasa bama tasan me ake ba.Jin shiru ba'a buɗe ƙofar bane, yasa aka buɗe ƙofar daga ta waje.Ummu ce ta shigo da sallama ɗauke a bakin ta,sai baza ido take taga ta inada za ta ganta.Carbin hannunta ne ya faɗi sakamakon ganota da tayi a lungu ta riqe kanta duk ta fita hayyacinta,a sukwane ta yi kanta ta na kiran sunan ta ,tana qarasawa inda take ta durqusa ta na kiran sunan ta ,"Atti, Atti, Maleeka, Maleeka". Maleeka",ji ta yi kamar ana kiran sunan ta da ga wata duniyar,a hankali ta fara sakin kanta.Ummu kuwa ganin ta fara shawo kanta,yasa ta qara riqo ta jikinta ,kanta ta riqe tana yi mata addu'a tana tofa mata.A hankali a hankali jikinta ya dai na rawa ta fara dawowa hankalinta,sai da suka ɗau wajen awa ɗaya suna zaune a gurin kafin ta da wo hayyacinta gaba ɗaya.
          Buɗe idonta ta fayi a hankali,sauke su ta yi akan Ummu wacce ta ke mata wani kallo me cike da tausayi da shiga zuciya wanda ya ƙunshi wasu abubuwa masu nauyi acikin sa me wahalar fassaruwa.Cikin wata murya wadda Ummu ce kawai ta santa da ita me ɗauke da gajiya,tsoro,da kasala ta ce "ummu na", Ummu ce ta amsa ciki wata murya me dauke da kwarin gwiwa,kwalla na taruwa a idonta ta ce,"ban sanki da karaya ba,ban sanki da saurin nuna gazawa, wannan ba maleekar dana sani bace, maleekar dana sani jaruma ce a cikin jarumai,me kwarin gwiwa,bata karaya,bata tsoron jarrabawa". Wani numfashi taja me nauyi tana haɗiye wani raɗaɗi mai ciwo,ta ɗora da cewa"Ni jaruma na haifa ,ni nasani ,za ki iya ne shi yasa Allah ya ɗora miki,kiyi komai kai tsaye cikin gaskiya da tsoron Allah, albarkata ako da yaushe tana tare dake".Maleeka ce ta rungume ta tana jin wani ƙwarin gwiwa da jarumta na shigar ta lokaci guda,itama haka ta rungume ta,a haka har bacci ya ɗauke ta ,sai da Ummu taga baccin nata yayi nisa kafin ta kwantar da ita,addu'a tayi mata taja mata bargo,ta fita zuciyar ta cike da tausayin ƴar ta ta.
       Kiran sallar asuba ne ke tashi daga mabanbantan masallatai, yayin da iskar asuba ne sanyi da nutsuwa take ta kaɗawa .Ummu ce zaune akan sallaya ta idar da raka'atanul fajr tana adduo'inta kamar ko da yaushe.Jin an fara kiraye-kirayen tada sallah ne ya sata tashi ta nufi gadonta don tashin husna sallah,tashin farko ta farka,fita ammy tayi daga dakin ta na cewa taje tayo alwala suzo suyi sallah,dakin ammar ta nufa, ƙarar ruwan da taji a toilet ya sata gane cewa ya tashi,bata je ɗakin Atti ba saboda tasan ta tashi.Komawa ɗakin ta tayi cikin abinda be fi 10minutes ba ,duk sun shigo dakin ,sallar asuba sukayi a jam'i,bayan sun idar azkar sukayi.Ammar da Husna suka fara maimaita haddar islamiyya, yayin da Atti ke gyara musu, basu tashi ba sai wajen karfe 6:00,a lokacin gari yayi haske, har yafara sake daukar wata hayaniyar.Ganin gari yayi haske ne yasa ta naɗe sallayar ta tashi,inda tabar su Husna da Ammar na karatunsu,Ummu kuma na lazumi,waje ta fita ta fara aikace aikacen ta by 7:30 gaba ɗaya ta gama gyara gidan nan tsaf ba abinda ke tashi sai kamshin turarrukan su na shuwa arab.Inda ɗan karamin kitchen ɗinsu yake ta nufa,taga me zata dafa musu.Wani numfashi me dumi ta saki ganin abinci ya qare saura taliyar guda biyu.Tunani ta fara yacce zata samu kuɗi dan ko albashin ta da za'a bata yayi kaɗan ga kuɗin makarantar su Ammar da husna ga kuɗin project ɗinta ga kuɗin graduation ɗin su daya matso,gashi yanzu abinci,rashin samun mafita ne ya sata fita waje dan kunna wutar girkin, zuciyar ta cike fal da tunanin yacce zata shawo kan matsalolin dake gaban ta.
           Ɗakin Ummu ta koma,gaishe da ita tayi cikin ladabi tana riqo hannun ta tayi kissing ɗinshi,amsa mata Ummu tayi cikin kulawa tana bata side hug.
        Shirin makaranta tasa su Ammar da Husna suka fara,saboda yau Saturday,suna da tahfiz,ita kuma tana da aiki yau. Wanka kowa ya nufa don kar su makara.Da misalin karfe 8:30 kowa ya hallara a tsakar gida cikin shirinsa , Husna da Ammar sanye da uniform dinsu white and blue black, Atti kuma sanye da maroon doguwar riga tayi rolling da mayafinta da tray a hannun ta na jollof taliya sai kamshi take , zama su kayi har ammi suka karya ,qarfe 9:00 duka sun gama komai, Atti ce tafito sanye da bakin flat shoes sai bakin shades daya rufe oily grey eyes dinta, sai baqin face mask riqe a hannun ta.Ko powder bata saka ba amma tayi wani musulmin kyau kamar wacce a kayiwa kwalliya,fatar ta a sai glowing takeyi.
         Gurin Ummu ta nufa, ummu kam kallonta take ita dai kullum cikin mamakin wannan zallar kyawu take na atti da kullum ƙaruwa yake kamar aljana.Ita fa har abun yafara bata tsoro.Inda ma ta godewa Allah shine attin bata damu da kyan ba, dan da tuni yanzu ta fada hanyar halaka.Musamman da suke cikin wann jarrabawar rayuwa amma dake Allah al-musawwiru ne, sai ya bata mace ɗaya da tafi maza 100 .
         Kullum cikin qara yaƙini take akan BURIN ƴar tata da na MAHAIFIN ta zai cika.Saboda ita kan ta ta yarda zata iya.Tunanin ta ne ya katse sakamakon tsugunnawa da Attin tayi a gabanta,ɗora hannunta Ummu tayi akanta, suma su Husna da Ammar tahowa su kayi inda ummu ta ɗora ɗayan hannun nata akansu tana cewa " Allah ya tsare ku ya albarkace ku, ya kare ku, ya baku abinda kuka fita nema, Allah ya cika muku burikan ku, ya baku ikon yin juriya ga duk wani tsananin rayuwa, haka dai tai ta kwararo musu addu'a suna amsawa da ameen .
           Fita sukayi suna yiwa Ummun sai sun dawo,ita kuma tana musu Allah ya tsare.Komawa cikin gidan Ummu tayi, hawa kan keken ɗinkin tayi ta fara ɗinki saboda akwai waenda zasu karɓi kayansu yau kuma bata ƙarasa ba.
Yayin da su Atti suka fita bakin titi napep suka hau ta gaya mai in da zasu,wata private islamiyya me kyau suka qaraso,dai-dai mai rufin asiri.Husna ce ta kalli Atti tace"adda yau ba kuɗin makaranta",murmushi Atti tayi tana ciro naira ɗari ta bata tana cewa " ungo ke da Ammar shikenan " ,farin ciki ne ya rufe Husna ta karɓa tana cewa " mungode sosai addata shiyasa nake sonki" ,harararta Ammar yayi yana cewa "bayan kin karɓe mata kuɗi ay dole kice kina sonta ".Rungumesu atti tayi tana cewa " ya isa hk ayi karatu da kyau kunji my friends",me adaidaitan ne yayi magana wanda hakan yasa sukayi sallama ya wuce da ita sukuma suka shiga cikin makarantar.
          Mai adaidaitan ne yayi gaba, inda suka nufi "Victoria Island ". Bayan sunyi tafiyar wajen 40minutes suka ƙaraso,sauke ta yayi tun a farko unguwar,saboda security ba'a barin napep ya shiga.Sauka tayi ta biya shi kuɗinsa.
        Gate ɗin da zaka shiga unguwar ta nufa, securities ne a gurin kamar barrack ko headquarter ɗin ƴan sanda.Sai da ta nuna katin ta kafin aka barta ta shiga cikin unguwar. Wasu gidaje ne Ƴan ubansu a unguwar,gaba ɗaya kamar ba Nigeria ba.Hatta da iskar gurin da ban take. Gaba ɗaya babu hayaniya ko kaɗan,komai cikin tsari da class yake.Dakatawa tayi sakamakon ƙarasowa da tayi wata aljannar duniya,hawa huɗu ne gurin,shi kansa gate ɗin guri abin kallo ne ,baƙi ne gate da wani tambari a jikin sa ,a can saman gate ɗin an rubuta"GRAND CREST" da golden abu wata wuta na haska shi sai ƙyalli yake.......................end of chapter two..... written by Muraimaa Naabba...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.