Free chapter · Read without an account

End Of Book 1

by Zainab Bint Abdulrahman · TURƁAYA

JUMM'AT MUBARAK🕋📿


End of Book 1

Last free pages



Page...............20



Receptionist ɗin ya ba ta amsa a taƙaice. "Asad Shareeq Khan?" Ta nanata sunan cikin mamaki. Me hakan ke nufi? Ta yaya sunan Asad ya yi kamanceceniya da na Afeef har a ce kuskuren rubutu ne? To, anya kuwa kayan da gaske na Afeef ne?" Ta tambaye kanta cikin ɗan shakku. Sai kuma wata zuciyar ta ce mata, "To amma ai sunan iyayen ɗaya ne sak. Kuma gida ɗaya aka sani da wannan sunan a garin cairo. 


Ita sai a sannan ma hankalinta ya kai kan sunan da ke jikin reciept ɗin da ba ta duba ba tun a gida. Ai kuwa sai ga sunan Asad nan a kai raɗo raɗo. Nan su ka ce ba za su canza kaya ba sai ta je ta zo da asalin wanda ya siya kayan. 


Haka nan ba don ranta ya so ba ta fito daga cikin store ɗin gwiwa a sage. Amma kuma ƙarƙashin zuciyarta tambayoyi ne fal a ciki game da sunan da ta ji a store. A fili ta furta, "Tabbas akwai lauje cikin naɗi, akwai abin da waɗannan mutanen ke ƙoƙarin ɓoye mata." Da haka ta ƙudura niyyar binciko koma meye a ƙasa kafin auren.....




************


Sheikh zaune a ɗakinsa riƙe da wani hoto a hannunsa cikin damuwa. Tsawon lokuta ya ɗauka riƙe da hoton nan a hannunsa idanunsa fal hawaye. Hoton wata kyakkyawar yarinya ce, da ba za ta wuce ƴar kimanin shekara huɗu a duniya ba. 


Lokuta da dama ya kan keɓance kanshi ya tasa hoton a gaba ya na jin ɗimbin kewar yarinyar da ta kasance guda jininsa ta farko a duniya, yarinyar da ya fara gani a matsayin ƴarsa, yarinyar da ya fara so a duniya wanda ya sa ƙafa ya shure duk wannan soyayyar lokaci guda ba tare da ya yi wani dogon nazari ba. 


Shin ta na raye? Idan ta na raye a wani hannu ta ke? Ya zai yi da haƙƙin wannan yarinyar da ya ɗauka wanda ya yi watsi da ita a lokacin da tafi buƙatarsa a rayuwarta. Shin a wani hali ta ke yanzu? Shi ne tambayar da ya ke addabar tunaninsa a yanzu. Saboda a jikinsa ya ke jin cewa ta na raye ba ta mutu ba. Kuma duk inda ta ke yanzu to tabbas ta na kusa da shi a yanzu domin yadda tunaninta ya ninku a zuciyarsa fiye da da, wanda hakan ke nufin ta kusanto shi..........



*******


Gaba ɗaya sun hallara a kan dinning domin yin dinner. Kamar kullum ta ga Farhat sai kai kawo ta ke yi. Ta goge nan ta goge can. Yayin da Ummie ta shirya mishi abincinsa tsaf a mazauninsa. Cikin mamakin yadda su ke ji dashi haka ta ke bain su da ido. A ranta tana ƙisimar tsiyar da za ta tafka mishi. 


Daidai nan ya ƙaraso wajen ɗauke da jarida a hannunsa as usual. Tashi ɗaya idonsa ya sauka kan cup da Farhat ajiye ba ta goge da kyau ba. "Farhat." Ya kira sunanta, tare da nuna mata cup ɗin da hannunsa. Farhat ta ɗauka ta goge sannan ta ajiye mishi a gaba ya ce, "Thank you." Sannan ya ja kujerar ya zauna. 


A natse kowa ya fara cin abincinsa, yayin da Hajja ke neman hanyar tsokano magana. Kamar wacce aka kitsa wa a kunne ta yi murmushi tana jawo plate da serving spoon. Dama ita ba ta kai ga fara cin nata abincin ba. Buɗewa ɗaya daga cikin warmers ɗin da ke wajen ta yi. Haɗaɗɗen jollof ɗin couscous ta ci karo da shi wanda yaji isassun kayan lambu da hanta anyi slicing ɗinshi ƙanana. 


Cikin fakan ido ta ɗebo da yawa kamar za ta zuba a plate sai ta zuba a dinning da aka shimfiɗe shi da farin ƙyalle. "Oops!" Gaba ɗaya duk suka juyo su na kallonta. Kafin su kai ga tambayar me ya faru? Idonsu ya sauka a kan ta'adin da ta yi. Ta marairaice fuska ta na faɗin, "I'm so sorry. It wasn't intentionally. Lemme clean it up." 


Ummie ta ce, "It okay." Ta yi maganar ta na kwashe abincin da tissue. Nan ta ke kuma ta ji babu daɗi ganin yadda ta saka Ummie aiki, ita sam ba da nufin haka ta yi ba. Gashi wanda ta yi domin ya yi maganar ma bai yi ba. Kafin ta kai ga ƙarasa zancen zucinta ta ji saukar muryarsa ya na faɗin, "When are you going to start eating like a human?" 


Ta zaro ido ta ce, "Oh my goodness! What's wrong with you? I'm eating like a human, of course. But if you say so, fine. Maybe the day you stop living like a robot and start living like a human being, even you won't find it that strange."


Kafeta yayi da ido na ƴan daƙiƙu, yana mata wani irin kallo mai haɗe da mamaki da takaici, sannan ya ɗan cije leɓensa tare da saurin maida kansa kan plate ɗin abincin ganin yadda Ummie da Farhat su ke kallon juna su na murmushi duk sai ya ji ya tsargu. Ƙaramar yarinya sa'a ƙanwar na neman kunyatasa a gaban mahaifiyarsa da ƙanwarsa. 


Sosai dariya yake cin su Ummie da Farhat ganin wani irin salihar amsa da Hayat ta bashi cikin sanyi da nutsuwa ba tare da wani hayaniya ba ta yi mishi gugar zana. Wannan shi ake kira da idan baki ya san abin faɗi bai san irin amsar da za'a dawo masa da shi ba. Haka ta kasance a ɓangaren Asad. 


Ita kuwa Hayat zuciyarta fari tas don murna ta kasa hajarta kuma an kwasa. Hankalinta kwance ta shiga cin abincinta ƙarƙashin zuciyarta cike da farin ciki da annashuwar game over da ta bawa Asad ɗin ganin yadda ta kashe bakinsa lokaci ɗaya....


Farhat ce ta fasa shirun da faɗin, "Yauwa Ummie, na manta Ummien Aneesa ta ce wai na faɗa miki an kusan kawo kayan auren Batool idan za ki samu zuwa." Cikin fara'a Ummie ta ce, "Ma sha Allah, Allah ya nuna mana lokacin." Ta kalle Asad ta ce, "Asad zan iya zuwa?" Ya ce, "Why not Ummie. Sure."  Sannan ta mayar da kallonta kan Farhat ɗin ta ce, "Yaushe za'a kawo?"


"Saura kwana biyu fa, On 20th july ne." Nan ta ke ƙuzarin Ummie da annashuwarta ya kau. "Indai haka ne kuwa tom ba zan samu damar zuwa ba." Ta ƙarasa cikin wani irin sanyin murya mai cike da ɗimbin damuwa a ciki. 

Asad ya ɗago ya kalle ta, ta yi saurin kauda fuskarta. 


Farhat ta ce, "Ummie saboda me?" 


"Kawai haka nan, indai a wannan ranar ba zan samu damar zuwa ba. Na je mata daga baya." Cewar Ummie da juriyarta yake dab da ƙarewa. 


"Amma Ummie....." Kafin ta ƙarasa faɗin abin da za ta faɗi Asad ya katse ta da, "Amma kin san na tsane yawan surutu idan ana cin abinci ko?" Ta haɗiye saurar maganarta a maƙoshi ba tare da ta sake cewa komai ba ta ci gaba da cin abincinta. 


Hayat kuwa tuni ta yi zurfi a tunanin sauyin fuskar Ummie lokaci guda tun da Farhat ta ambace date. A ranta ta ji koma mene ne akwai wani abu mai girma da muhimmanci da ke da alaƙa da wannan date ɗin da Farhat ta ambata a wajen Ummie. "Then what could this be?" Ta tambaye kanta ba tare da sanin mai ba ta amsar tambayarta ta ba..........



******** 


Abie zaune a garden ɗin gidan shiru ya tafi zurfin tunanin da ya zame wa rayuwarsa aboki kuma amini tun bayan shekara ashirin da su ka shuɗe. Dafa shi aka yi ta baya. Ya yi firgit ya juyo, sai ya ga Jaddah ce. Cikin ƙoƙarin ɓoye damuwarsa ya shiga ƙirƙiro murmushin yaƙe ya ce, "Ummu ba ki kwanta ba? Wani abu kike so na yi miki?" 


Ba tare da bashi amsar ko ɗaya daga cikin maganarsa ba ta nema waje ta zauna ta na fuskantarsa. "Na san irin raɗaɗin da kake fuskanta, Lateef. Kuma na fahimci cewa a ƴan kwanakin nan kullum wannan ciwo ƙara tsananta sosai a zuciyarka." Cewar Jaddah da ta riƙo hannunsa cikin tsananin kula da tausayawa irin na uwa ga ɗanta. 


Cikin sanyin murya ya ɗaura kanshi a cinyarta ya ce, "Ummu, ina matuƙar ƙoƙarin ganin na manta da abin da ya shafe rayuwata ta baya gaba ɗaya. Amma kullum abin da ya wuce sake dawo mim ya ke yi yana farautar zuciyata. Akai-akai ya ke dawowa, ya ke yi mini zafi a zuciya, yana cutar da ni Ummu. 


Na sani Lateef, amma don Allah ka manta da abin da ya wuce yanzu Lateef. Kar ka manta ka yi wa Arwa alkawari, ko ba haka ba?"


"Ummu. Kema kin san cewa har yanzu ban karya alkawarina ba. Tsawon shekaru ashirin da suka wuce, ban taɓa zuwa inda Leen take ba, Ummu." 


"Na sani. Amma ba ka nesanta zuciyarka daga gare ta ba Lateef. Na san har yanzu kana ƙaunar Leen da dukkan zuciyarka. Sai dai me? Ko da ƙaramin mataki guda ɗaya ka ɗauka zuwa gare ta, to, tabbas komai zai lalace Lateef. Yanzu magana ake yi ta rayuwar Hamra a zahiri. Ba gargaɗi na ke yi maka maka ba, shawara na ke ba ka a matsayina na uwa kuma mai son ganin farin cikin jikokinta ya tabbata. Daga haka ta miƙe ta shige ciki. Ji ta yi idan ta ƙara wasu mintuna a wajen tsaf za'a iya rasa wanda zai rarrashe wani tsakanin ita da ɗan na ta saboda wani wutar tausayinsa da ya ke taso mata.....


Da wani irin murmushi mai ciwo ya bi bayanta ya na kaɗa kai. A fili ya ce, "Shekaru ashirin kenan ina ƙoƙarin yin hakan Ummu. 

Har yanzu ban hasko ko hasaso ta yaya zan yi nasarar mantawa da ita a rayuwata gaba ɗaya ba........




On 20th july.....


Kamar ko wani shekara a rana mai irin ta yau 20th july. Ranar ce ta kasance ranar annivesary ɗin auren Ummie da Abie. Wanda duk shekara su ke zuwa Masallacin Amr ibn al-As, domin yin addu'o'i na musamma da nuna godiyarsu ga ubangiji da ya mallaka musu junansu a matsayin mata da miji kuma ya ba su zaman lafiya da fahimtar juna. Hakan ya sa ko bayan rabuwar su Ummie ba ta daina martaba wannan ranar ba. 


Duk shekara sai Ummie ta je masallacin kamar yadda su ka saba. Sai dai yanzu zuwan ya sha bambam da na baya, domin kuwa a baya su na zuwa ne ita da mijinta cikin farin ciki da annushuwa. Saɓanin yanzu da ya zame mata ranar kuka da alhinin begen mijinta wanda ta kasa haƙura da shi a zuciyarta har yanzu, sai dai a zahiri ta kan nuna lafiya qalau babu sauran maganarshi a ranta wanda a baɗini ba haka abin ya ke ba. 


Asad da kan shi ya je ya ajiye ta a masallcin, sannan ya ce zai dawo ya ɗauke ta idan ta gama. Ta gama addu'arta ta fito ta shiga raba wa mabuƙata kuɗi sadaka da kyakkyawar yaƙinin a zuciyarta. Sai da ta ƙarar da kuɗin hannunta tas sannan ta haƙura da bada sadakar, ta fito ta na tafiya.  Daidai shima ya fito kenan daga masallacin zai nufa inda mabarata su ke ya ba su sadaka. Cak su ka tsaya su na kallon kallo a tsakaninsu ko wanne ya kasa yarda da abin da ya ke gani a gaban shi. Kallon kusan minti biyar su na tsaye a wajen cak kamar an kafe su. 


Ummie ce ta fara saukar da idanunta ƙasa hawaye fal a cikinsu. Ta raɓa gefe za ta wuce ya yi saurin riƙo hannunta. Hawayen da ta ke ƙoƙarin riƙe wa ya gangaro saman kuncinta. 


"Meye haka ka ke yi Lateef? Sake min hannu. Ka san ina zuwa nan to meye sa ka zo?"


Abie ya ce, "Don Allah Leen ki tsaya ki saurare ni. Wannan tsarin Ubangiji ne ya haɗa mu a nan." 


"Tsarin Ubangiji Lateef ko tsarinka? Ka sani sarai ina zuwa nan shi ne ka zo." 


Abie ya ce, "A'a Leen ba yadda kike tunani bane, tsawon shekaru ashirin ina zuwa nan a rana mai kamar ta yau, na ɗauka kin sani ai."


"Na san da haka."  Ta faɗa a taƙaice ta na share hawayenta ta sake juya za ta wuce yayi saurin sake riƙo hannunta. Ta juya a ɗan fusace ta na faɗin, 


"Wai Lateef meye haka ba ka ganin cikin jama'a mu ke?"


Maimakon ya sake mata hannun kamar yadda ta buƙata sai ya mayar mata da, " Na kira lokuta daban-daban da ba ki ɗaga ba. Na tura miki saƙonni duk babu wanda kika yi min reply. Da gaske ina buƙatar ganin ki Leen. Ina buƙatar mu zauna mu tattauna abubuwa da yawa." 


Tsayawa ta yi tana kallonshi nan take maganar shekaru ashirin da ya wuce su ka dawo mata kunne kamar yanzu ya ke faɗa mata su. "Arwa matata ce yanzu." Kalmar da ya fara tarwatsa zaman lafiyar da ke tsakaninsu, kalmar da raba zukata da yawa, kalmar da ya kawo mafarin haddasa ƙiyayya a tsakanin zukata da yawa. Nan ta ke ta fisge hannunta ta ce, "Ai ka rasa wannan damar Lateef tun shekarun baya da su ka ce, idanunka ma ban cancanta na zamo matarka ba Lateef. Haka zalika tsakanin ni da kai bamu da damar haɗuwa da juna. Saboda haka kama daina wannan tunanin a zuciyarka Lateef. Ta na gama faɗin haka ta juya ta bar wajen da sauri hawaye masu zafi su na ɓalle mata.

Shima hawayen da ya gagara riƙesu su ke zarya ɗaya bayan ɗaya a idanun tamƙar ba namiji ba. Namijin ma magidanci da zuƙa zuƙan ƴaƴansa........


Ƙarƙashin wani bishiya ta samu ta zauna sannu a hankali ta na tariyo abubuwan da suka faru a baya ɗaya bayan ɗaya. Asad da kusan minti goma da zuwansa wajen sai faman nemanta ya ke yi bai ganta ba, gashi ba ta zuwa da waya duk ranar da za ta zo wajen. Da ƙyar ya hangota a ƙarƙashin bishiyar ya ƙarasa ya same ta. 


"Ummie lafiya na ganki zaune a nan cikin damuwa? Duk da na san yau rana ta musammance a gare ki shiyasa kike zuwa nan duk shekara. Ki na kasancewa cikin damuwa a ranar amma ban taɓa ganin ki cikin irin wannan damuwar ba. Meye ya faru?" 


"Asad ji na yi kamar abin da ya faru a baya ya na ƙoƙarin dawo ya riske ni yanzu."


"Meye ya faru Ummie?" Cewar Asad


"Wani lokaci, abubuwan da suka shuɗe suna dawowa cikin tunaninmu har su fuskance mu ta yadda za mu ji kamar suna tsaye a gabanmu ne."


Asad ya ce, "Ummie, kar ki taɓa barin abubuwan da suka shuɗe su tsoratar da ke ko su hana ki kwanciyar hankali. Sannan kin fa yi min alkawarin cewa za ki yi ƙoƙarin mantawa da abin da ya faru a baya har abada, Ummie. Amma kina ci gaba da waiwayar abin da ya wuce. Ba zai haifar miki da komai ba face ciwo."


Ummie ta yi ɗan murmushi ta ce, "Na sani, kuma ina lafiya karka damu. Amma wani lokaci zuciyata takan cika da baƙin ciki ne." 


"Ta shi mu tafi gida." Ya faɗa cikin tattausar kalamai..........



***********


Zaune ya ke cikin ɗakinsa hannunsa ɗauke da jita ya na kaɗawa cikin salo mai sanyi. Humairah ta shigo ɗakin ɗauke da sallama a bakinta dama ƙofar ɗakin a hangame ya ke shiyasa ba ta tsaya yin knocking ba. Da fara'a ta ke kallonsa cikin wani irin shauƙi ta ce, "Zan iya tambayarka wani abu?" Ya ɗaga kai ya kalle ta na seconds biyu sannan ya mayar da kansa kan jitar da ya ke kaɗawa ba tare da ya ce mata komai ba. 


Ta ce, "Wai me ya sa kake son abin da ya shafi soyayya bane bayan kuma kai ba masoyin asali bane?" Cak ya tsaya da kaɗa jitar ya ce, "Kamar ya ni ba masoyin asali bane? To cikakken masoyin asali ne ni a nan ki na gani na." 


Humairah ta ce, "No you're not Afeef. Ba ma ka taɓa faɗa wa soyayya da wata ba a rayuwarka Afeef. Sannan yanayinka, halayyarka, duk a cikin shirinka na fake love ya tsaya. Shin ka na ma da wajen son mai sonka a cikin zuciyarka kuwa Afeef? Ka taɓa zama ka yi tunanin irin yarinyar da ya kamata ka so Afeef?" 


"Irin yarinyar da ya kamata na so? Kuma dama akwai irin wannan abin a soyayya? Huh? Ok come on Humairah, faɗa mini ta ya za a yi na gane true love ɗita? Kuma ta ya ya zan san hakan? Sannan what would she be like?"


Humairah ta yi murmushi mai ƙayatarwa tare da zama kusa sa shi ta ce, "Idan mutum ya kamu da soyayya, ya kan ji hasken rana yana bayyana tamƙar ya fi zinariya kyalli, Afeef. Launuka sukan bayyana masa da zurfin gaske. Ja ya rinu ya zama kamar ya fi ja sosai, rawaya kuma sai ta ƙara turuwa fiye da rawaya."


Afeef ya ce, "Wannan ai alamar cutar jaundice ce." 


Ta yi murmushi kamar mai karanta labaran hikaya ta soyayya ta ci gaba da faɗin, "Idan ka ga wacce kake ƙauna, za ka iya shafe wasu lokuta da babu adadi kana kallonta, har ka ji da za ka samu dama ka dawwama kana kallonta har abada. 


Kuma za ka ji kamar kai da ita kaɗai kuke a duniya, ko da kuwa kuna tsakiyar taron jama'a mai yawa. Idan da dariyarta ta zama maka kamar kiɗa kuwa, to za ka iya tabbatar da cewa ka dawwama cikin jin wannan daddaɗan kiɗar."


Afeef ya tuntsure da dariya ya na faɗin, "Haba  miss Humairah ta ya ya dariya za ta zama kamar kiɗa? Kin yi kuskure. Kai, wane irin tsohon tatsuniya ne wannan? Bugun zuciyarka ya ƙaru. Tab, to ai ni kam, wannan ya fi kama da viral infection fiye da soyayya. 


Idan ka kalli mutum, sai ka kasa daina kallonsa, idan ya yi dariya, sai ka ji kamar kiɗa ne. Hhhhh! Wannan ba soyayya ba ce miss, alama ce  na cewa ya kamata ya je asibitin masu tabin hankali ya likita. Saboda ƙarya ce ba ta existing a wannan duniyar, a fina-fine kawai ake ganin su da littafan hikaya na soyayya, amma babu shi a gaske. Saboda haka ni ban yarda da soyayya ba kwata-kwata."


A zuciyar ta ce, "To, indai haka ne kuwa, ka kai ni can, Afeef. Domin ni kam, na kamu da soyayya. A fili sai faman murmushi ta ke ta zuba kamar wacce ta samu taɓin ƙwaƙwalwa da gaske.......


*********


Ummie zaune a ɗakin Asad ta haɗa musu coffee su na sha su na hira. Ummie ta ce, "Wai ni kam Asad wace irin mata kake burin aura?"


Cak ya dakata da shan coffee ɗin. Sai kuma ya ce, "Ta kasance mai riƙo da al'adarta, mai tarbiyya, ilimi da sanin ya kamata. Ai kin riga kin san irin matar da nake so Ummie." 


Ummie ta kurɓi coffee ɗin ta a tsanake sannan ta ce, "Amma waɗannan abubuwan da ka lissafo duka, ka lissafo abuwawan da su ke waje ne. Ya zuciyarta zai kasance? Ya tunaninta zai kasance? Duk ba ka yi wannan lissafin ba. Kuma su ne mafi muhimmanci." 


Ya na jujjuya cup ɗin coffee da ke hannunsa ya ce, "Ummie idan al'adarta da ɗabi'unta duka su na da kyau, to zuciyarta da tunaninta su ma za su kasance masu kyau tabbas. Halayyar mutane ta zahiri shi ya ke nuna halayyarsu ta baɗini Ummie. Bana son mace wacce ba ta damu da al'adarta da yanayin mu'amala da waɗanda su ke tare da ita ba. Bana son irin wannan matan sam. 


Ko na yi kuskure ne Ummie? Mace ta kasance ƴar gayu, ta kasance mai girmama na gaba da ita, ta kasance mai kawo farin ciki a cikin ahali, ta kasance mai kula da damuwar da waɗanda su ke tare da ita, ba wai iya damuwarta kawai ta sani ba. Ta kula da farin cikin mutane da take tare da su baki ɗaya. Yarinyar da za ta shigo cikin rayuwata ta kasance kamar ki Ummie. Mai natsuwa, hikima da kamala. Ba zan taɓa son yarinyar da ba ta da waɗannan qualities ɗin ba. 


Ummie ta yi murmushin manya ta ce, "Abin da kake tunanin kenan a yanzu Asad. Amma ita al'amari ta zuciya da soyayya canzawa ta ke yi a ko da yaushe, abu daban su ke faɗi ba abin da baki ya faɗi ba. Ba za ka iya controlling ɗin shi ba, saboda zuciya ita zuciya ce ta ke controlling ɗin mutum. 


Mutum ba ya faɗa wa soyayya a yadda ya tsara wa kanshi list ta hanyar neman irin qualities ɗin da ya ke so. Ita soyayya ta na faruwa da kai ne lokaci ɗaya. Kuma idan ta faru, ba ta ƙarewa a kwana ɗaya."


Ummie ba fa zan taɓa faɗawa wannan soyayyar da ku ke faɗi ba, saboda ban yarda ya na existing ba a gaske. Wannan shi ne hukunci na. Me ya sa mu ke yawan maimaita magana ɗaya ne Ummie?" 


Ummie ta ce, "Hakane na san wannan shi ne matsayarka, amma na san da yawan lokuta zuciya ke yanake maka hukunci ba wai kai ka yanke mata ba."  Ta kalla sama ta na pointing ɗin saman da hannunta ta ce, "Mai sammai da ƙassai ya riga ya gama tsara mana duk abin da zai faru Asad. Kawai kai dai ka tsaya ka zuba ido ka gani za ka faɗa soyayya wata rana." 


Asad ya ce, "Well, Ummie. Ko da ya na faru, to ni ba zai taɓa faruwa da ni ba ina da wannan yaƙinin." 



Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.