Free chapter · Read without an account
THE PRICE OF A CHOICE
Tsume fuskarta tayi kamar ba itace suka gama wasa da dariya da ita ba.Nan da nan suka gane magana ce mai muhimmanci suka qara shiga taitayinsu.Fara magana tayi da cewa,“Duk ku saurare ni da kyau,sati me zuwa za'ayi wani taro",wasu suka kalli juna, yayin da wasu suka gyara zamansu.Hajiya Jamila ta sauke numfashi a hankali kafin ta ci gaba da cewa,“Ku sani taron ne ba kamar taron da kuke zato ba.Duk da wasu a cikin ku,sun san taron,ko sun taɓa jin labarin sa.Toh ku sani ba ordinary taro bane,taro ne mafi hatsari.Kafin nan ina so ku fahimci abu ɗaya tun kan komai ya fara".Ta ɗan dakata,“A gurin, ƙaramin kuskure kaɗai zai iya zama kuskuren da ba za ku samu damar gyarawa ba".Fuskokin wasu daga cikin ma’aikatan suka sauya,“Wannan ba irin event ɗin da muka saba karɓar baƙi a nan ba ne,Mutanen da za su shigo gobe ba irin mutanen da za ku iya yi wa sakaci bane,mutane ne da zai fi kyau kada ku san komai game da su".Shiru ya sake mamaye ɗakin,ta ɗora da cewa,“Saboda haka, idan wani abu ya faru, ba za ku yi tambaya ba.Ba za ku yi magana ba.Ba za ku shiga inda ba'a ce ku shiga ba, Kuma mafi muhimmanci shine…Idanunta suka yi tsanani,“Ku yi aikinku,saboda qaramin mistake zai iya raba ku da numfashin ku".Wata yarinya daga gefe ta haɗiye yawu tana cewa,“Amma Hajiya…”, “Na sani,” Hajiya Jamila ta katse ta cikin sanyin murya. “Na san kuna tsoro",ta ɗan yi murmushi, amma murmushin bai isa ya rage nauyin da ke cikin ɗakin ba.“Shi ya sa ba zan tilastawa kowa ba".Ta ɗora wata takarda baqa me rubutun ja da tambarin zaki a jikin ta a kan tebur tana cewa“Duk wanda yake son yin aiki a taron, ya zo ya rubuta sunansa. Wanda baya so, babu wanda zai tambaye shi dalili".Nan take aka fara kallon kallo.Tsofaffin ma'aikata sun san abinda ake nufi,tunda an taɓayi , mutane har shida aka kashe cikin ma'aikatan gurin, ba kuma wanda yayi ko tari dan haka da yawa acikin mutane gurin suna da labarin taron.
Hajiya Jamila ce ta kuma ɗora wa da cewa "zaku samu ninkin albashin ku sau 10 a rana ɗaya,amma farashin shine kushiga da tunanin dawo a raye ko a mace",gurin ne ya qara rikicewa.Har gurin 20 minutes babu wanda ya rubuta sunan shi.Hajiya ce ta qara magana da cewa "Babu wanda zeyi cikin ku.Mutum ɗaya muke nema".Kamar saukar aradu haka akaji Muryar Atti tace "zanyi",gaba ɗaya kallon ta aka fara, da masu yi mata kallon baki da hankali dana tausayi dana mugunta.Murmushi Hajiya tayi saboda tasan zata aikata,cewa tayi zo ki rubuta sunan ki ,fito wa tayi zata rubuta Halima ta riqe hannun ta tana girgiza mata kai kwalla na cika idonta.Zare hannunta Atti tayi daga hannun Halima.Biro Hajiya Jamila ta bata ta rubuta sunan ta da signature ɗinta.Haka taro ya tashi kowa jikin sa a saɓule, musamman ƴan group ɗin su Atti.Hajiya ce ta kira Atti office ɗinta su kayi ƴan maganganu tana qara kwantar mata da hankali tana gaya mata tsare-tsaren taron wanda zai faru wani satin.Bayan sun gama sukayi sallama saboda gari ya fara duhu.
Fitowa tayi waje dare yayi har wajen 10:00 tayi compound ɗin shiru baka jin komai sai haushin karnuka, gabanta ne yafadi saboda ita bata lura dare yayi haka ba kwata kwata.Checking ɗints akayi sai,ta yiwa securities ɗin sai da safe din tana fita daga main gate ,the street of Victoria Island is so lively kamar ba dare ba a lot of luxury cars sai wucewa suke with a high speed , the road was full of street lights kamar da rana,ta fiya ta fara yi ta fita inda zata iya samun napep , kuɗin salary ɗin da aka bata ta ciro ta na qirga wa , murmushi tayi na godiyar Allah still the money is not enough she has more to go,wanda yana ɗaya daga cikin abinda yasa za tayi wannan taron apart from sauran dalilanta ,tuna nin ta ne ya katse sakamakon karasowar ta babban titi ,canja mind dinta tayi ta fasa hawa napep because that 500 naira will help in more important way,tafiya ta fara a qafa ba tare da tunanin uban nisan inda ta nufa ba , after 1hr ta qaraso unguwar tasu at that time it's already 11:30pm ,but the adegunle streets is still lively saboda they don't care about night and day it's all thesame to them, a wannan lokacin ita kanta tasan daga kafarta kawai take saboda muguwar gajiyar da tayi, tsayawa tayi a wani provision store dake farkon street ɗin su, wani tsohon bayerabe da zayin shekara 40 da ka gansa kaga gangster baqi qirin ne gashi da wasu irin muscles kamar dan dambe ga uban datti gaba daya ma abin firgitarwa ne ya baje akan benci yana haɗa kan kudi sai zuqar taba yake , yana hango Atti tayo gurin yayi maza ya kashe tabar yana tasowa yana washe baki yana cewa ""The most beautiful girl in Lagos... those eyes of yours will one day cause trouble."saurin katse shi Atti tayi tana cewa " UNCLE EZE ba wannan ne yakawo ni ba food stuffs nake so yacce kasa ba ban" , kallon ta yayi with his scary eyes yana cewa " "Kai, achalogu! Kin sake zuwa sayen rabin shagona da kuɗi kaɗan?" Murmushi tayi tana mamakin oga EZE ace mutumin da kowa yake tsoron sa amma yake da wannan sauƙin kan duk da kowa yayi mai shedar bad guy ne kuma taji ana rumors din member ne na wani political gangster,kuma yana da gang na kanshi a qasan gada ,amma ita batayi believing ba, saboda suna good time Sosai dashi yana mata kirki ,food stuffs ta siya na 3/4 na kuɗin duka.Bata oga Eze yayi yana ta mata kirari , karɓa tayi,su kayi sallama ta nufi gida.
Tana shawo kwanar layin su ta gano Ammar ah inda yake zama ya ke sai da pure water,kuma Allah ya sa mai albarka dan tun yana saida pieces yanxu leda-lleda yake siyarwa.Gano ta Ammar yayi ,gurin ta ya taho da fara'a yana cewa "Adda Atti sannu da zuwa sai yanzu kika dawo" yana karɓar kayan hannun ta ,"wallahi Ammar yau wani abu ya ɗan riqe ni ",cewa yayi "bari in qarasa haɗo kayana,sai mu tafi tare". Kayan sa yaje ya qarasa haɗo wa .Su ka jera suna nufar gida". Kwanƙwasa ƙofar sukayi kamar jiransu ake zuruf aka buɗe ƙofar .Husna ce ta fito da gudu tana ɗane ta sauran qiris su faɗi,"Oyoyo Adda ",Atti ce ta langyaɓar da kai tana cewa "Yanzu Husnaty in kika karyani fah",dariya ta kyalkyale dashi tana cewa "Ay bama zaki karye ba inshaAllah",Ammar ne ya harareta yana cewa "Aku kawai",Shiga ciki su kayi Husna na tayi musu surutu.
Ummu ce ke ta ɗinki akan keke, gaishe ta su kayi suna mata sannu da gida,amsa musu tayi.Kafin ta fara faɗa akan mesa Atti tayi wannan daren.Haquri ta bata ta na cewa Hajiya ce ta riqe su.Haqura tayi tana tambayar su cike da kulawa ta na tambayar su ya suka yini.Atti ta kalla ta ce,kije ki ɗakko madara kusha dare yayi abinci bazai yiwu yanxu ba.Madarar ta ɗakko ta ,inda Ammar ya shimfiɗa musu tabarma a tsakar gidan suka sha. Kowa wanka yaje yayi ya kwanta saboda dare yayi sosai.
Tsakar dare da misalin karfe 3:18 ,Atti kamar a mafarki ta ji wani gigitaccen ihu na Ummu,hantsilowa da ga kan katifar tayi tana fitowa waje da wani bala'in gudu,tare da Ammar suka fito wanda shima ihun ya tashe shi. Ummu ce a tsakar gidan a million su kayi kanta..................
_____________
Kano state
Nassarawa GRA
Gaba ɗaya unguwar ba ka jin komai sai harbin bindiga da ke tashi daga wani gida.For over 1hour wanda yaci ace y'an sanda sun iso ko kuma ƴan unguwar sun kawo dauki amma shiru.Daga ta cikin gidan kuma wasu ƴan fashi ne,fuskar su a buɗe alamar taqadirai ne basu damu da'a gane su ba.Babbansu ne a zaune a kan kujera.Mace da namiji ne durqushe a gurin,duk sun fita a hayyacin su,mace ta suke, yayin da namiji yake cikin wani mawuyacin hali,ga ƴan aikin gidan duka an kashe su.Gaba daƴa gidan ya karaɗe da ihun wata budurwa kamar ana zarrar ranta.Babbam ƴan ta'addar dake zaune a gurin ne yana dariyar shaqiyenci ne ta ɗaga murya yana cewa "SPIDER kayi a hankali karka farka ƴar mutane",spider ya ɗaga Muryar sa yana cewa "BOSS baza ka gane bane"wata arniyar dariya suka ɗauka.Hankalinsu kwance kamar ba ƴan fashi ba.Haɗiye dariyar sa Boss yayi kamar ƙiftawar ido ya na ɗaukar bindiga ya sai tawa me gidan wanda ga ba ɗaya idonshi ya bushe yayi jajir yana cewa "Senator A.A BALA zaka bani ko saina fasa kanka",Senator A.A BALA ne ya ɗago idonsa na fitar da wani taratsatsin huta yana cewa "sai dai ku kasheni",bai gama rufe bakin sa ba,"sai ji yayi daram Boss ya harbe matarsa".A haukace A.A BALA yayi kanta Amma ina rai yayi halinsa.Lokaci guda gaba ɗaya ya zare,ga ihun ƴar sa da yake ji baya da ikon cetar ta.Rarrafawa yayi yana cewa ku kyaleta.
Dan Allah zan ba ku abunda kuke so.Boss ne ya fashe da wata dariyar zalunci yana cewa "da dai ya fima sauqi".Jikin Senator A.A BALA na rawa ya nufi wata akwatin sirri, password ɗin yasa ka nan da nan ya buɗe,wata takarda baqa me rubutun ja da tambarin kan zaki ya fito da shi.Hannun sa na rawa ga ba ɗaya baya hayyacinsa ya miqa wa Boss,"wata dariya mara daɗi yayi, yana cewa "ka ceci kanka",be qarasa faɗa ba,wannan yarinyar dake ihu ta qwalla wata qara daga nan kuma tayi shiru.Senator A.A BALA na jin haka ya gama zarewa ya durqusa yana riqe kafar sa yana mai magiya shi kansa be san me yake faɗa ba.Spider baqi bushashshe da shi ya fito daga ɗakin yana gyara belt ɗinsa,yana wani geɓare baki ya ce "kasan yaran yanzu ba juriya ba daga ɗan wannan abun har ta garzaya barzahu".Kamar saukar aradu haka A.A BALA yaji zancen.Suman tsaye yayi a gurin ,kafin kamar ƙiftawar ido BOSS ya qaraso inda yake ya murɗe kanshi,faɗuwa yayi a gurin matacce...............end of chapter 4......... written by Muraimaa Naabba ✍️✍️