Free chapter · Read without an account
A NIGHT OF DESPERATION
Kanta suka yi gaba ɗaya su, suka fara tambayar Ummu.“Ummu,Ummu, me ya faru?”,Gaba ɗaya Ummu ta kasa magana, sai nuna ɗakinta kawai take yi.Ɗakinta suka ta fi da gudu.“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”.Husna suka gani kwance ba ta numfashi.
Numfashin su ne ya ɗan ɗauke na wucin gadi. Kafin su dawo hayyacinsu, bala’in rikicewa su kayi hijabin Atti ma a bai-bai yake. Haka Ammar ya goya ta,Ummu ta ja ƙofar, suka fita a tsakar daren.
Garin ya yi duhu, babu kowa. Haka suka fito titi suka fara tafiya, babu ko ƙyallin ɗan Adam.A lokacin tuni Husna ta fara jijjiga, haƙoran ta na harhaɗewa. Ummu kuwa sai kuka take tana kiran sunan Allah.
Kafin su ƙaraso wani asibitin gwamnati da ke ɗan kusa da unguwarsu.Asibitin suka shiga a rikice.Suna shiga suka haɗu da wata nurse. Duk da nurse ɗin ta gan su, kuma ta ga halin da suke ciki, sai ta yi kamar ba ta gan su ba.
Ganin tana shirin barin wurin, Ummu ta mata magana tana cewa.“Baiwar Allah, don Allah taimaka mana. Kin ga yarinyar nan, rai a hannun Allah.”Banza ta yi musu kamar ba ta ji su ba, ta yi shigewar ta.Shiga suma ciki su kayi.Koda suka shiga ba wanda ya kulasa ko ya kalli inda suke.
Sai da suka ga kamar za ta mutar musu a asibiti kafin wata nurse ta zo ta mata allurar bacci.Asuba aka kira, inda suka fita famfo suka yi alwala. Ɗankwalin kansu suka shimfiɗa, suka yi sallah.Shima Ammar ya fita masallaci ya yi tasa, ya dawo.
Har ƙarfe shida ta yi, ba a ba su ko gado ba, ballantana su ga likita.Wata mai karɓar haihuwa ce da ta zo shigewa. Ammar ne ya tambaye ah ina ake ganin likita,har yanzu,be zo bane inda ta ce masa,“Likitan dare yanzu ta fita, amma na safe yanzu zai shigo.” Kafin matar ta ɗora da cewa,"Amma in kuna da wani abun a hannun ku kawo yanzu sai inje in mata magana ta dawo ta duba ta.Naga tana cikin mawuyacin hali".Atti ce tace "Ba asibitin gwamnati bane".Matar ce ta ja tsaki ta yi gaba tana,cewa zaku wa ku ruɓe anan.
Wata mata ce ta shigo wajen ƙarfe shida da rabi da ɗanta wanda zai kai shekara biyar.Wannan nurse ɗin da ta yi musu banza ɗazu ce ta fito daga reception, sai washe baki take kamar mai tallan makilin. Ta je wurinsu tana cewa,“Ah Anty Sa'a, har kun shigo?”Tana maganar tana ɗaukar yaron da ke tafiya da ƙafarsa.
Anty Sa'a ce ta fara magana sai wani ɗaɗɗaga hanci take tace,“Wallahi Sister Baraka, baya cin abinci sosai. Shi ne nace bari in kawo shi.”Har taune harshe Sister Baraka take yi wajen cewa,“Gaskiya ne. Wannan gwanda a duba shi. Mu je ciki gurin likita.”
Haka suka shige ciki, ko shashin da su Atti suke suna jiran tsammani ba su kalla ba.Ganin zaman jiran ya yi yawa ne, sai Atti ta kalli Ummu, wacce gaba ɗaya fuskarta ta yi ja, ta ce,“Ummu, bari in je in tambaye su. Shirun ya yi yawa".Ɗaga mata kai ta yi,inda Atti ta tafi reception.
Wasu nurses ne guda biyu a wurin, da wacce ta yi musu banza ɗazu da wata.Sallama tayi musu.Ɗayar ce ta amsa tana wani basarwa.
Duk da haka, Atti ba ta yi qasa a gwiwa ba. Ta fara magana,“Haba, bayin Allah. Yanxu fisabilillahi, abinda kuke mana ya kamata? Tun ƙarfe 4:00 muka zo asibitin nan da yarinyar nan, rai a hannun Allah, amma ko kulamu kun ƙi yi.”Wacce ta amsa sallamar ta a farko ce ta fara magana cikin faɗa-faɗa,“Me haka za ki zo ki haɗa mu da faɗa? Sai ka ce wasu yaran ki, Likita bacci take yanxu. Ba a tashin ta in tana bacci.”
Wani malolon baƙin ciki da takaici ne ya taso wa Atti, amma haka ta haɗiye. Ta kuma kwantar da muryarta tana cewa,“Ni ba na neman rigima. Abin da nake nema shi ne ku taimaka mana. Yarinyar nan fa tana cikin mawuyacin hali tun da muka shigo asibitin nan.”
Wannan ƙeƙashashshiyar nurse ɗin farko ce ta wani tashi a fusace tana ɗaga murya, ta fara magana,“Ke dalla, banza! Ballagaza! Dangin tsiya.Tunda kuka shigo na gane babu wani maiqo a jikin ku ajje mu ku ne kayi,kar ki raina mana hankali. Ko an gaya miki ajje mu kika yi? Nan ba wurin iskacin da kika saba zuwa ba ne da za ki zo kina mana ƙarairayi. Ko an gaya miki wannan kyakkywun naki zai ruɗe mu ne,d?
“Toh, ki sani nan ba gidan gala ba ne. Ki kama kanki, don nan ba asibitin matsiyacin ubank......"Ba ta ƙarasa ba.Sai ganin ta aka yi ta kife a ƙasa saboda wani azababben mari da Atti ta ba ta.
Gaɓa ɗaya idonta Atti ya yi wani masifar ja.Wani ihu nurse ɗin ta buga wanda gaba ɗaya hankalin mutanen da suka fara shigowa ya dawo kansu.Nurse ɗin, cikin abin da bai wuce ’yan daƙiƙu ba, rabin fuskarta ya kumbura kamar fanke🤣.Gaba ɗaya ta kasa magana, sai ihu take.
Ummu ce ta shigo reception ɗin sakamakon hayaniyar da ta fara ji.Ganin abinda Atti ta aikata ne tasan zance ya ɓaci. Fara jan hannun Atti tayi,tana tazo subar gun, kafin ta jawo musu wani bala’i.
Ɗayar Nurse ɗin ce ta fara magana,ganin suna shirin fita,“Yaya za a yi ku illata ta, kuma ku yi ƙoƙarin guduw.......”Maganar ta ce ta maƙale sakamakon wani deadly look da Atti ta ba ta.Ko tari ba ta ƙara ba, har suka fita daga reception ɗin.
Janta Ummu tayi suka fito daga reception ɗin.Zuwa tayi inda Husna ke kwance a gurin kamar matacciya . Ammar tace ya ɗauke ta su tafi.Fita daga asibitin sukai Ummu na tayiwa Atti faɗa akan mesa ta tan ka mata Saboda Ummu tasan zafin ran Attin.Atti kuwa sai haɗiyar zuciya take.
Wani qaramin private asibiti suka nufa.Suna shiga aka karɓe su hannu bibbiyu,cikin mutunci.Atti ta tsaya tana kallon ma'aikatan suna ɗaukar Husna.Sai lokacin ne ta ji wani irin sauƙi.Aƙalla an taimake su duk da dan kuɗi a kayi musu.Tunanin ta ne ya katse sakamakon, maganar da taji anayi mata,“Za a buƙaci a fara biyan kuɗin admission ɗin,” wata ma'aikaciyar asibitin ta faɗa.Atti ta kalli Ummu,Ummu ta kalli Ammar tana cewa,"Ammar maza jeka gida ka haɗo min duka kuɗin da nake ajjewa a wannan Jakar",da tohm ya amsa yayin da Atti ta ɗora da,"Nima kaje Jakar dana fita da ita jiya ka ɗakko duka kuɗin ciki".Fita yayi cikin sassarfa inda su kuma nurses ɗin suka shiga da Husna emergency.
Bayan awa ɗaya suka fito inda aka buqaci suje office ɗin likitar.Zuwa su kayi inda likitar ta fara musu bayanin cewa ciwon tane ya tashi (kasancewar Husna sikila ce tun haihuwa)jinin ta ya qone da yawa.Dan haka sun saka mata wani jinin,inshaAllahu zata samu sauqi.Sannan likitar ta miqo musu Bill ɗin su.
Bayan wajen rabin awa daga fitowar su daga gurin likita duk sunyi jungun-jungun sai ga Ammar ya dawo da flask ɗin abinci da kuɗin.
Duk da suka haɗa kuɗin duka bazai isa ba.
Ammar ne ya zaro kuɗin da yake samu na siyar da pure water yana cewa "Adda gashi a haɗa da wannan".Atti ta kalli kuɗin da ke hannunsa.A da in a kace mata za suyi irin wannan rayuwar sai ta qarya ta, tunawa tayi da irin rayuwar da suka taɓa yi.Rayuwar da irin wannan kuɗin sai sun yi kyautar ninkin sa sau goma kuma ko a jikin su.
Yanzu kuwa...duk abin da suke da shi suna haɗawa ne domin a ceci rayuwar mutum ɗaya daga cikinsu.Ta rufe idanunta na ɗan lokaci wani abu na taso mata zuciyar ta na mata zafi,“Allah Ya taimake mu,” Ummu ta faɗa a hankali.“Amin,” Ammar ya amsa.Alhamdulillah kuɗin ya kai.Haka Atti taje ta biya komai.
Zuwa tayi ta tarar da su,Ammar na ta fama da Ummu ta ci abinci taqi.Da qyar suka lallaɓata su ka ci abincin.Bayan awa ɗaya wata nurse tazo takirasu su akan yanzu zasu iya shiga,amma banda hayaniya.
Shiga ciki su kayi a hankali.Husna ce kwance a kan gadon tana fitar da numfashi a hankali,tayi fari sosai.Baka jin komai sai qarar na'urorin dake jone a jikin ta.Sai lokacin Ummu ta samu nutsuwa ganin ta dawo hayyacinta.Addu'a su kayi mata inda su ka fito reception suka zauna.
Bayan fitowar su da wajen minti 20 wayar Atti ta fara ringing . Kallon su Ummu tayi ta ga hankalin su baya kanta.Tashi tayi da ga gurin.
Bayan asibitin ta tafi inda ake yin wanki da shanyar su bedsheet da kayan marasa lafiya ,kafin ta ɗaga kiran Hajiya Jamila.
Gaisawa su kayi ciki wasa da dariya,kafin Hajiya Jamila tayi gyaran murya ta kira sunan Atti "Maleeka", Atti ta amsa, Hajiya Jamila tace,"Kinyiwa Ummu maganar da mu kayi da ke zaki yi mata". Shiru Atti tayi na wasu mintina saboda rasa abin da zata faɗa.
Hajiya ce ta ɗora da cewa" Maleeka kinsan bazan taɓa barinki kije gurin nan ba tare da sahalewar Ummu ba kema kinsani.Gashi abun nan sai qaratowa yake.Kuma nace Miki zan mata maganar da kaina kinqi yarda".
Atti ce tace "Anty ba haka bane Husna ce ciwon ta ya tashi.Kwana mu kayi a asibiti ".Hajiya Jamila tace "Subhanallah,amma shine ko ki kirani ki gaya min. Allah ya bata lafiya , inshaAllahu anjima zan shigo.Kinga ko dole ki haqura da taron nan dan abun sai yayi wa Ummu yawa da wanne zata ji". Zuruf atti tayi ta ce"A'a Anty inshaAllah,zanyi duk hatsarin sa,kuma da izinin Allah zan fito da rain...... maganar ta ce ta katse sakamakon haɗa ido da su kayi da ..........end of chapter 5 ...... written by Muraimaa Naabba ✍️✍️
.