Free chapter · Read without an account
65
Wai Hayyo ne ya ɗaura. A ina ya samo Hayyo? Ta ya akai Hayyo ya yarda ya aura masa ita? A'a ba dai aurarwa ba sai dai ko siyarwa, shaidar da zata iya yi akan hakan kenan.
Sai dai kalaman Turaki da suka biyo baya suka katse mata tunani. Ya ɗan ɗago kansa yana kallon Baffa.
"Ni da na je wurin Baban nata, izinin auren na je nema Baffa. Shi ne ya ce sai dai na aureta a lokacin. In ba haka ba zai bawa wani ita."
Baffa ya kalle shi na ɗan lokaci.
"Kai kuma idan baka sameta ba rayuwarka ta ƙare ko?"
Turaki ya girgiza kansa da sauri.
"A'a Baffa. Kawai na ji ina so ta zama mallakina a sanda na san waye mahaifinta."
Baffa ya yi shiru. Sai ya girgiza kansa a hankali.
"Har yanzu labarin film kake bani Muhammad. Why ba zaka haɗa ni da limamin da na ce maka ina so na yi magana da shi ba? Kana ƙara ɓata min rai fa, zan ci mutuncinka wallahi tallahi, ina jin kaman na sa gwiwana na daki ƙirjinka ne na kasheka kafin ka kashe ni. Don ban haifi Ɗan da zai lalata min image ɗina ba. Ka san girman aure kuwa? Ka san ya lamarin auren da ka yiwa kanka yake? Ka san girman abin da ka aikata na tsare baligar macen da ba muharramarka ba a ɗakinka bisa jikinka? Duba nan..."
Ya yi masa nuni da Hajiya Ramla. "Jiya bata runtsa ba. Bata yi bacci ba, so take ta samu hujjar da zata tabbatar mata auren yarinyar nan ka yi, ba lalata mata rayuwa ka so yi ba."
Turaki ya sauke idonsa, ta gefe ya kalli Fullo. Kuka take a hankali. Ya sauke muryarsa.
"Ku yi haƙuri don Allah. Baffa na rasa lambar Liman. Duk na bincika wayana babu, ban san ya aka yi ba. Amma idan ka bani dama zan iya zuwa garin mu zo tare da shi, Ko kuma ka aika Bello."
Baffa ya ɗan dafe gefen kujerarsa.
"Wallahi zan ɗauke ka na kai Kotu a zartar maka da hukuncin haikewa Mace."
Ai fa hankalin Turaki ya kai ƙololuwar tashi. Hannaye na rawa ya zura cikin aljihunsa ya ɗauko wayarsa. Ya buɗe File Manager. Yatsunsa suna ƙara rawa ya shiga cikin folder ɗin recordings. Sakan Ɗaya. Biyu. Uku. Ya gano abin da yake nema. Ya ɗaga idanunsa zuwa Baffa.
"Ban sani ba ko zaku gasgata ni idan kun ji wannan."
Parlon ya yi shiru fiye da da. Turaki ya danna play. Da farko sautin muryar Hayyo ya fito a cikin wayar da ɗan kauri, amma kuma a sarari.
"Idan har ka tafi, ba zan yarda da cewa iyayenka zaka je ka kawo ba..."
Muryar Hayyo ta sake cika falon kamar ba a recording ba, ka rantse da Allah yana zaune ne a wajen.
"Ka ajiye sadakinta na aura maka kawai. Shi ne zan san da gaske aurenta ka zo nema. Duk da ba ƴata ba ce, amma zan yi abin da uba na gari ya dace ya yi..."
A nan Baffa ya ɗan daidaita zamansa. Kallon da yake yi wa wayar ya ƙara tsananta.
"A matsayina na wanda ya ga an haifeta a titi, na taimaka musu ita da uwarta, zan aura maka ita. In kuma babu sadakinta a yanzu, ina mai tabbatar maka kana barin wurin nan zan aurawa Malam Mudi ita, ai ba wani tsufa ya yi ba, shekaru casa'in da biyar ne kawai, kuma ras yake, haƙoran gaba ne kawai babu..."
Baffa ya ɗan lumshe ido a hankali. Yana tattara kowacce kalma yana ajiye ta a wani wuri na musamman a cikin ƙwaƙwalwarsa.
Har sannan dai ba wanda ya iya magana sai cika da tsantsar mamaki. Sai muryar Hayyo ta sake shiga kunnen kowa.
"Tun da zuwanka yasa nasan inda take, sai mu je da hukuma wurin tsohuwar da ta saceta mu karɓota kawai. Ni Allah yasa ma ba yawon ta zubar ta tafi ba kamar uwarta, ai uwarta ma ta shiga duniya. To gaskiya idan aka samu shege, ni ba zan yi rainonsa a gidana ba."
Shiru ba wanda ya motsa. Haka suka dinƙa sauraron maganganun Hayyo marasa daɗi, har zuwa sanda Liman ya ce da Turaki ya bayar da sadaki, ya ajiye maƙullin motarsa. Hayyo na cewa shi indai da Sadaki mai kauri, ko shege ne shi zai aura masa ita, sai su haɗu can su zama shege da shegiya su haifi Ƴaƴan sunnah, ko babu komai shi ya samu ladan ɗabbaƙa sunnah, kai idan ma ɗan yankan kai ne shi bai da matsala, indai kuɗin sadakin akwai yawa.
Kuma ba tare da ɓata lokaci ba aka ɗaura aure, hatta jawaban da Liman ya zayyanowa Turaki na batun halaccin auren babu wani nasa, duk sun ji. Baffa ya dinƙa kallon wayar Turakin kamar Hayyo yake gani a cikin wayar, Kaka ta zabga salati tana faɗin,"Wallahi tallahi wannan muryar Hayyo ce gata nan tarrr, Hayyo annoba ne, banda ƙaddara mai zai kai mu haɗa iri da Hayyo. Yanzu lalacewar tasa har ta kai ya sheganta ƴarsa? Kai jama'a wannan duniya ina zaki damu? Me ya sami Hayyo ni ƴar nan? Ni da na ke uwar matarsa ma yana cewa bai sanni ba? To wallahi summa tallahi Fullo ƴarsa ce ta sunnah, na rantse muku da girman Allah da igiyoyi uku na aure aka samar da yarinyar nan. Rashin tsoron Allah ne kawai irin nasa yake faɗin waɗannan maganganun, amma ai Allah yana ji yana gani, Hayyo ba zai gama da duniya lafiya ba".
Ummi na kuka sosai ta ce,"Akwai Allah, akwai ranar hisabi, ko da na yafe zaluncin da Hayyo ya yi min a zaman aurenmu, ba zan yafe sheganta min ƴa da ya yi ba, ba zan yafe masa ɓata mu da ya yi ba a idon duniya, sai Allah ya saka mana".
Fullo ta yi jikin Ummi tana kuka sosai, da jin maganganun Hayyo da suka yi mata zafi, ace wai wannan ubanta ne? Ita kuwa wacce irin ƙaddara ce wannan ta zargeta. Kukan da duk ya taɓa zuƙatan kowa a wajen.
Kaka na hawaye ta ce,"Waye kuwa zai so haɗa jini da Hayyo banda Ƙaddara. Kaico! Tirrr da halinka Hayyo".
Baffa ya ce,"Waye shi ɗin ne?".
Kaka ta ce,"Hayyo ai sheɗani ne, ba zaka tabbatar da hakan ba sai ka aura masa ƴarka, matansa sun fi goma kuma duka babu wacca ya saka, tsagwaron jahilci ke ɗawainiya a shi. Kowacce gajiya take da muguntarsa da baƙin halinsa ta bar masa gidansa. Shi fa idan ya auri mace da zarar ya sami abin da yake so a wajenki shikenan ta zama abar banza, shara bola ta fi ta daraja. Tun balle ki sami ciki, za ki sha wulaƙanci iri iri, saboda baya son haihuwa, kuma sai Allah ya yi masa jarabawar samun ƴaƴa. Hayyo ba ya aje abinci a gidansa, kuma baya yarda masu taimakawa su kawo wa Iyalinsa taimako, zai ce sun fita duniya za su wulaƙanta shi su tona masa asiri.."
Ta numfasa ta ƙara cewa,"Ka ga wannan".
Ta faɗa tana nuna masa Ummi, ta ce,"Maraicin uba ne yasa ta yi zaman gidan Hayyo, har ta haifi wannan ƴa bai daina dukanta ba, saboda kawai ta haihu har sau biyu, kuma taƙi ta yi zuciya ta bar masa gida kamar sauran Matan. To mu kuma bamu da tsayayyun da za su tsaya mata wajen nuna masa ita ɗin da darajarta har a ƙwatar mata ƴancinta. Ita kuma zaman ƴaƴanta kawai take yi a gidansa. Tana tsoron lalacewar tarbiyyar yaranta. Da ace baƙin ciki farat ɗaya yake kisa, da yanzu bama zaune da ita a wurin nan. A kan dalilin barinta gidansa, abinci aka aika mata daga gidan wata Ƙawata, yana zuwa ya haɗa da ita da wadda ta kawo abinci da wannan Ƴa Halimatu ya yi musu duka, sannan ya yi mata zagi na ƙare dangi, zagi na ƴan ƙwayan da ko gabas basa kallo. Mahaifinta da ke ƙasa na san sai ya yi baƙin cikin wannan aure, saboda kiran sunansa da Hayyo ya dinga yi yana zaga."
Ta rafka sabon tagumi cikin jimantawa, tana jin kamar abin da take shirin faɗa ya fi ƙarfin bakinta. Ta ja numfashi mai nauyi kafin ta ɗago idonta ta kalli Baffa.
"Wallahi banda Allah yasa wannan yaro ya yi jihadi ya aureta, kuma Allah ya taimaka da iliminsa, ina mai maka rantsuwa da Allah, siyar da ita zai yi."
Ta ɗan yi shiru.
"Ehh siyarwa dai da ka sani."
Fuskokin kowa ya nuna tsagwaron mamaki. Maama da Mum kamar za su furta wani abun. Kaka ta cigaba da magana, muryarta yanzu ta ƙara nauyi, alamar zuciyarta cikin ciwo take sosai.
"To manyan ƴaƴansa mata guda uku wallahi tallahi duk siyar da su ya yi. A taya ɗan mutum a ɗau kuɗi a ba shi, ya ɗauko yarinyar ya bayar a tafi da ita. Kuma da bakinsa yake faɗa. Yana cewa ya siyar da wance, shi bai da asara."
Ta girgiza kai da tsananin takaici.
"Hmmm lamuran Hayyo in ba mutum ya san shi ba, hankali ba zai ɗauka ba. Na ce muku yana siyar da Yaransa ko? To kar ku ce min yana cikin wata ƙungiya ta asiri ne. Ko da yake idan yana ciki ma wa zai sani?"
Ta sauke numfashi, ta furta a hankali.
"Allah abun tsoro, Hayyo abun tsoro."
Kamar an jefa kalmar a tsakiyar parlon, kowa ya furta,"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
Baffa ya kasa motsi yana jin zuciyarsa na tafarfasa. Ya ƙi jinin Miji mai irin waɗannan mugwayen halayen, shi ya sa duk lokacin da case ɗin Miji da Mata irin wannan ya zo gabansa, sai inda ƙarfinsa ya ƙare wurin ƙwatarwa mace ƴancinta, sai ya tabbatar shari'a ta ladabtar da Mijin kafin ya raba auren.
Numfashi mai nauyin gaske ya sauke, yana ƙara jinjina girman abin da Kaka ta faɗa.
"Siyar da ƴaƴa?"
Muryarsa ta fito da wani irin ƙunci. Ya ɗaga kansa ya kalli Kaka.
"Kamar wanda bai san darajar ɗan Adam da haihuwa ba? Kamar wanda bai amsa kalmatush shahada da bakinsa ba. Anya wannan mutumin ya yi imani da Allah da kuma ranar lahira? Anya ba ya cikin wata babbar ƙungiyar asiri? Anya babu taɓin hankali a tare da shi?"
Kaka ta sauke idonta.
"Allah masani."
Ta faɗa tana buɗe tafin hannunta. Shiru na ɗan lokaci, sannan ta ƙara da murya mai sanyi,"Amma dai in ace ƙungiyar asiri yake, sai abubuwan da yake yi sun fi haka muni. Don ƙila mu kanmu yanzu duk babu mu. Kuma ƴan ƙungiyar asiri ai suna yin kuɗi ko? To shi fa a tsiyace yake, kullu yaumin baƙin talauci ke ƙara rufe shi, ko da yake ai tsiya ta aure shi, kuɗin babu albarkar ubangiji, ga haƙƙin iyali."
Baffa ya ɗan girgiza kai.
"Ƙwarai masu wannan halin ba za a kallesu a matsayin matsalar mutum ɗaya kawai ba. Idan mutum yana sayar da ƴaƴansa, yana tura su cikin irin wannan rayuwa, tabbas fitina ne ga al'umma baki ɗaya."
Ya ɗan jingina bayansa ga kujera, sannan ya ce, "Dole a shiga shari'a da shi, zai yi bayani dalla dalla."
Kaka ta ɗaga kai ta kalle shi. Murmushin takaici ya bayyana a fuskarta.
"Wacce hukuma ce zata kama Hayyo har ta masa hukunci?"
Bata bar Baffa yay magana ba ta tari numfashinsa. "Yo Matan nawa ne suka kai ƙararsa? Iyayen Matansa biyu ma sai da suka yi ƙararsa. Shi fa wuyarta aje ga shari'a, a ranar farko shari'ar za'a kore ƙarar. Don yana da manyan lauyoyin da ke tsaya masa. Yo kai kuwa bawa idan ba wasu mashahuran kuɗi ko babbar hanya gareka ba ina zaka iya shari'a da shi. Sai dai kawai ka barwa Allah komai. Ban san ta yadda zan tsage muku Hayyo tas ba ne. Da duk sai kun gagara zama."
Ta sauke numfashi.
"Lamarin Hayyo sai dai a bar wa Ubangiji. Amma na tabbatar talala Ubangiji ke yi masa, don yana ta ba shi damar gyara kura kuransa ne shi kuma bai gane hakan ba. Sai dai zai yi bayani a madakata."
Baffa ya gyara zamansa. Wannan karon kallonsa ya canja. Ba kallon wanda yake sauraron labari ba ne. Kallon mutumin da ya ɗauki abin a matsayin nauyin da ya hau kansa ne.
"A'a Kaka."
Muryarsa ta yi ƙarfi kaɗan.
"Lamarinsa ba na a ƙyaleshi ba ne. Fitina ne kuma iskanci ne lamarin nasa. Dole ya gane kuskurensa. Idan bai gane da kansa ba, shari'a zata ta haska masa fitilar da ta dace da shi."
Kaka ta girgiza kai a hankali. Baffa ya ci gaba, a wannan karon cikin cikakken nutsuwa,"Ba saboda ku da Fullo kawai ba, saboda sauran rayukan da ke rayuwa ƙarƙashinsa."
Ya ɗan kalli Fullo, wadda take ta kuka a gefen Ummi, sannan ya maida kallonsa kan Kaka.
"Zan tsaya tsayin daka sai na ga an ƙwatar wa iyalansa haƙƙinsu, in sha Allah. Ƙarshen iskancinsa ya zo."
Kaka ta yi shiru. Ba don ba ta yarda da ƙudurin Baffa ba, ko kuma tana jin tsoron abin da ka iya zuwa ya dawo. A'a. Sai don su sun san Hayyo fiye da yadda yake zato. Ta san irin rayuwar da ya daɗe yana yi. Shi ɗin hatsababi ne, don har wasu mutanen na kiransa hatsabibin aljani. So ta san abubuwan da ya aikata waɗanda ba za ta iya furta su a gaban kowa ba.
Abin da ta faɗa yanzu ma ba komai ba ne face ɗan abin da za a iya faɗa. Akwai wasu sirrika. Sirrika masu nauyin da ba a furtawa ko a gaban Alƙali haka kawai, kuma Baffan ya lura da hakan.
"Kaka ki faɗa min dukkan abubuwan da kika sani game da wannan azzalumin mutumin."
Kaka ta ɗan kalle shi tukunna ta sauke idonta. Shiru Baffa bai matsa mata ba. Ya san ma'anar shiru irin wannan. Shiru ne na mutum da yake auna abin da zai faɗa, da abin da zai binne a ransa.
Ummi wadda take zaune kusa da Kaka ta ɗaga kai ta kalli Baffa. Fuskarta ta nuna tsananin damuwa ƙarara.
"Don Allah Alhaji..."
Muryarta ta fito a hankali.
"Ba sai ka ɗauki kowanne mataki a kansa ba."
Baffa ya kalleta. Ta haɗe hannayenta biyu alamar roƙo.
"In har don ta ɓangarenmu ne buƙatar hakan ba bu. Ka yi haƙuri don Allah. Ba wai ina hana ka ba ne... Ni zan fi so ace Ubangiji ne ya rama mana. Saboda ban san irin abin da zai iya faruwa ba idan aka shiga wannan lamarin sosai."
Ta ɗan yi jimmm.
"Don girman Allah, maganar nan ta tsaya iya nan tsakaninmu da ku. Alhamdulillah, tun da har Allah ya sa ɗiyata ta fita daga hannunsa, wannan kaɗai ya isa ya sa na gode wa Allah. Shi Namijin da ke hannunsa zan ci gaba da masa addu'a ba dare ba rana ubangiji ya tsare shi yo halin mahaifinsa. A yanzu aurenmu kawai na ke so a raba in rabu da nauyi."
Kalmarta ta ƙarshe ta fito da rauni. Kowa a falon ya sauke wani irin numfashi kamar ba a daidai ba. Baffa ya yi shiru na ɗan lokaci. Kallon Fullo ya yi, sannan ya maida kallonsa kan Ummi.
"Haka ne."
Sai ya yi ɗan jim.
"Amma ba zan iya yin kamar ban ji abin da na ji ba. Kuma ba zan iya cewa saboda kun ce kun bar shi ga Allah ba. Allah ne Mai hukunci, gaskiya ne. Amma Ubangiji ya ba mu hankali, Ya ba mu doka, Ya kuma ba mu ikon kare wanda aka zalunta."
Sai dai da ya ga yadda Ummi ta ƙara damuwa, sai muryarsa ta yi laushi wajen faɗin.
"Shikenan ba zan matsa muku ba. Idan wannan shi ne abin da kuke so, zan bar batun Hayyo a nan."
Ya sauke numfashi a hankali.
"Allah ya kyauta. Allah kuma Ya shirye shi, Ya ganar da shi."
Ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu, sannan ya ƙara da cewa,"Amma duk da haka, akwai wani abu da ya rage."
Kallon Turaki ya yi.
"Batun auren yaran nan."
Ya ɗan karkatar da kansa.
"Ni da Ɗan uwana da waɗanda suka kamata za mu je mu sami Mahaifin nata. Ba wai saboda ina son in sake tayar da maganar da ke tsakaninku ba. A'a. Ina son in ƙara samun tabbaci ne game da wannan auren."
Ya sauke numfashi.
"Domin wannan hujjar da muka ji yanzu kaɗai ba ta gamsar da ni ba gaba ɗaya."
Sai ya ɗan yi murmushin takaici.
"Zamani ya lalace. Yanzu babu abin da ba za a iya haɗawa ba. A wannan zamanin don computer ta samar da muryar mutum ta zama tamkar tasa ce a zahiri ba komai ba ne.... Saboda haka, ba zan ce kai tsaye record ɗin nan bana gaskiya ba ne. Ina dai son mu sami wata hujja da ta fi wannan ƙarfi. Shi ya sa nake ganin ya fi dacewa mu je wajen mahaifin yarinyar, mu ji daga bakinsa da bakin Liman yadda aka yi komai. Ta ina aka hau ai ta nan ake sauka."
Ummi ta ce,"To Allah yasa ya ji tsoron Allah ya faɗi gaskiya. Wataƙila idan gaskiyar kake son ji sai kun sakar masa kuɗi, don barazana ba zata tsorata shi ba. Sannan shi bai san wani mutumci da hanyar arziƙi ba.... Kuma nan gidan da yake ya tashi, da yake mun je kwanaki. An ce ya yi kuɗi sun bar unguwar ne ma, ko garin ne Allah masani. Ba wanda ya san ina ya koma."
Mum ta ce,"In dai ɗan garin ne, sai aje gidan iyayensa. A kama mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole zai kawo kansa."
Ummi ta yi wani murmushi mai ciwo, wanda ke nuna nadama. Kaka ma ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin ta yi ƙarfin halin cewa,"Babu wanda ya san iyayen Hayyo balle danginsa. Duk iyayen da yake amfani da su wajen neman aure na bogi ne. Hayarsu yake yi. Kuma wallahi duk binciken mutum ba zai san su ba iyayensa ba ne. Hmmm... Hayyo fa sai Allah. Wanda ya sansa kawai shi ya sansa, amma hatsabibin aljani ne."
Su Hajiya Madina suka shiga jijjiga kai, suna jinjina lamarin. Tausayin Ummi ya kama su, tausayin da ya haɗe da wanda ya cika zuƙatansu akan Fullo. Yanzu sun fahimci cewa yarinyar da suka yi tunanin ta jefa kanta cikin wani hali, ita ce a zahiri rayuwarta ke cikin wani hali.
Baffa ya daɗe yana kallon Turaki. Turaki bai iya ɗaga ido ya kalleshi ba. Maganganun da suka fito daga bakin Kaka har yanzu suna yawo a cikin kansa. A wannan karon dai bai san ko ya kamata ya ji kunyar abin da ya yi ba, ko kuma ya ji daɗin cewa a ƙarshe an fara fahimtar dalilin da ya sa ya yi shi.
Baffa ya yi ajiyar zuciya. Sai ya ce a hankali,"Muhammad."
Turaki ya ɗago kansa. Baffa ya kalleshi kai tsaye.
"You did the right thing at the right time My son."
Turaki ya yi shiru. Yana jin wani abu mai kama da daɗi na tsarga masa.
"Amma ka saurare ni da kyau," Baffa ya ƙara faɗa, muryarsa ta zama irin ta uba mai magana da ɗansa ba don ya faranta masa rai ba, sai don ya koya masa abin da zai ɗauka darasi ya tafi da shi har ƙarshen rayuwarsa.
"Abin da ka yi wa yarinyar nan jihadi ne. Ka ga halin mahaifinta, ka ga abin da yake shirin yi da rayuwarta, sannan ka nemi hanyar da za ka fitar da ita daga ƙangin. A irin wannan yanayin, ni kaina idan na kasance a inda ka kasance, zan so in ceci rayuwar ɗiya Mace mai daraja."
Ya ɗan dakata. Turaki ya ɗan sauke numfashi. Sai dai Baffa bai ƙyale shi ya ji daɗin kalaman ba tukunna.
"Amma hanyar da ka bi, ita ce kuskuren da nake magana akai tun farko, kuma ita ce ta ɓata rai da tayar da hankalin kowa."
Muryarsa ta yi nauyi. Ya nuna kansa da ɗan yatsa.
"Ni mahaifinka ne. Iyayenka Mata suna nan. Mutanen da suke da haƙƙin sanin irin wannan shawarar da ka yanke duk suna nan a raye. Ya kamata ace ka nemi ko da mutum ɗaya a cikinmu."
Ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ƙara da cewa,"Ko da ka san za mu ƙi. Ko da ka san za mu yi maka faɗa. Ya kamata ka bamu darajarmu da girmanmu."
Turaki ya sunkuyar da kansa.
Baffa ya ci gaba,"Ka raina haƙƙin iyayenka ne a lokacin da ya kamata ka fi tunawa da su."
Ya sauke numfashi. A wannan karon sautin muryarsa ya ɗan yi laushi.
"Na ji daɗin abin da ka yi. Da gaske na ji daɗi."
Turaki ya ɗago kansa. Baffa ya kalleshi da wani irin kallo na uba mai alfahari, amma har yanzu akwai tsantsar tsayuwa a tare da shi.
"Idan da ka zo ka gaya min halin mahaifinta tun farko, ko na ka ƙudurin. Wataƙila ni da kaina na nema maka aurenta. Wataƙila ma kafin ka kai ga tunanin hakan, ni na riga na ɗauki matakin da ya da ce."
Sai ya yi murmushi kaɗan, murmushin da ya ɗauki nauyin tausayi da fahimta.
"You saved the girl from a terrible situation my son. And I am proud of you for that."
Ya ɗan ɗaga hannu yana hana Turaki magana.
"But being right does not make the way you did it right."
Turaki ya sake sunkuyar da kansa. Baffa ya ce,"Ka yi abu mai kyau ta wata hanya mara kyau. Ka taimaki yarinya, amma ka cutar da amincin da ya kamata ya kasance tsakaninka da iyayenka. Kuma ina so ka koya daga wannan kuskuren."
Ya jingina bayansa da kujerar yana kallonsa sosai.
"Abin da ba zan sake yarda da shi ba shi ne ka sake ɗaukar irin wannan babban lamarin kai kaɗai. Ko ya shafi aure ne, ko duk wani abu da zai iya sauya maka rayuwa. Iyayenka ba mutane ba ne da zaka sanar da su bayan komai ya riga ya faru. Ba daga sama ka faɗo ba, ba baki ne yake binka ba. Hakan kuskure ne, ka kasance a Ɗa nagarinka ka ji ko."
Sai ya ce a hankali,"Ka fahimta?"
Turaki ya gyaɗa kansa.
"In sha Allahu Baffa. I won't repeat such a mistake again."
Baffa ya ɗan gyada kansa.
"Allah ya sa haka."
Sai ya kalli Fullo na ɗan lokaci, sannan ya maida kallonsa kan ɗansa.
"Allah ya yi maka albarka a abin da ka yi daidai. Kuma Allah ya shiryar da kai a inda ka yi kuskure."
Turaki ya yi shiru, yana sauraren Baffa yayin da yake tambayar su Maama ko suna da wani abu da za su faɗa.
Maama da Mum suka kalli juna, kafin Maama ta ce a nutse,"Baffa kai ne shugaban wannan gida. Abin da ka yanke, shi ne namu. Mu ba mu da wata magana a kai."
Baffa ya ɗan gyaɗa kai, sannan ya dube su duka.
"To daga ɓangarenmu kenan. Alhamdu Lillah."
Ya ɗan yi shiru kafin ya juya kallonsa zuwa Kaka da Ummi.
"Yanzu saura mu ji cewar ku akan auren ɗiyarku da aka yi ba a daidai ba. Idan baku amince da yadda Ɗan mu ya auri ɗiyarku ba, duk hukuncin da ku ka zartar babu laifi."
Ya ɗan kalli Fullo, wadda har yanzu take cikin jikin Ummi, sannan ya koma kallon Kaka.
"Su Ƴan uwana zan je in same su mu zanta. And I will try my best to make Boɗejo understand, so that ba za a sami wata matsala ba. Domin abin da muke magana a kai ba ƙaramin abu ba ne. Aure ne, kuma aure ba haɗa mutane biyu kawai ayi rayuwa ba ne. Haƙƙi ne, amana ce, kuma nauyi ne da za a ɗauka har gaban Allah."
Sai ya dubi Turaki.
"Idan har Mahaifiyarta, Kakarta da ita kanta yarinyar sun amince. Fatana gare ka Muhammad, shi ne ka zama adali a tsakanin matan da Ubangiji ya ƙaddara maka aurensu. Kada ka bari son ɗaya ya sa ka zalunci ɗaya, kuma kada ka bari wata ta rinjaye ka har ka manta da haƙƙin wata. Ka ji tsoron Allah a tsakaninsu, ka kiyaye mutuncinsu, ka kuma tuna cewa kowacce mace da igiyoyin aurenka suka rataya akanta, ka ɗauka amana ce da aka damƙa maka, don haka ka yi ƙoƙarin samun Allah lafiya, haƙƙin iyali ba abun wasa ba ne."
Ya ɗan yi shiru, kafin ya ƙara da cewa,"Allah ya yi wa rayuwar aurenku albarka. Ya sanya zaman lafiya da fahimta a tsakaninku, ya kuma ba ka ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyanka."
A wannan karon Turaki ya kasa ɓoye abin da yake ji. Wani irin relaxation breath ya saki, kamar wanda aka cire wa kwalbar da ta soke shi mai girma daga ƙirjinsa. Ya sunkuyar da kansa kaɗan, ya furta,"Alhamdu Lillah…"
Ƙwayar idonsa a ƙasa yace.
"Thank you Baffa. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana. Ya ba ni ikon faranta muku har ƙarshen rayuwata, kuma ya sa ba zan taɓa zama sanadin da za ku yi nadamar haihuwata ba."
Baffa ya amsa da ɗan gyada kai. "Ka riƙe Thank you ɗinka tukunna. Ai baka ji ta bakin Iyayen Matarka ba ko? Wacce godiya kuma zaka yi bayan baka da tabbacin sun baka."
Allon ƙirjin Turaki ya ɗan girgiza. Sai dai bai tsorata sosai ba. Don yadda bai zaton Baffa zai fahimce shi ta sauƙi haka ba, to ya san amincewar su Ummi ma zai zo da sauƙi. Ita kuma rigimammiyar zai ji da ita daga baya.
"To Kaka baku ce komai ba."
Kaka ta yi murmushi mai cike da nutsuwa. Ta ɗan gyara zamanta, sannan ta ce,"Wa zai ƙi haɗa jini da nagartattun mutane irinku Alhaji? Sai dai wanda bai samu irin wannan damar ba. Kuma wa zai ƙi yarda ya aurawa ƴarsa mutum kamar Muhammad? Yaro mai hankali, mai sanin ya kamata, kuma abin da muka gani a cikin halinsa tun da muka san shi ya ishe mu ai."
Ta kalli Turaki, sannan ta koma wajen Baffa.
"Ni abin da zan ce shi ne Allah ya albarkaci wannan aure. Ya sanya alheri a cikinsa."
Ta yi ɗan shiru, kafin ta ƙara,"Mu ma muna gode muku sosai. Abin da ka yi wa wannan ƴa a lokacin da ya dace, ba ƙaramin taimako ba ne Mai Babban Suna. Domin idan da baka amince da wannan aure ba, Hayyo zai iya siyar da ita. Wallahi babu wani mutum da ya yi masa alƙawari a kan aurenta da gaske. Shi abin da yake nema shi ne wanda zai ba shi kuɗaɗe."
Ta girgiza kai a hankali.
"Mu a wajenmu babu wata magana sai godiya da addu'a."
Mum wadda take zaune tana kallon Ummi, ta ce,"Ummin Fullo ke baki ce komai ba?"
Ummi ta ɗaga kai ta kalli Fullo dake jikinta, wadda har yanzu hawaye ke zuba mata. Ta shafa bayanta a hankali, sannan ta ce,"To ai ni abin da nake gani shi ne, yaronku ya fi ƙarfin auren wannan Ƴa. Amincewar da ya yi ma tausayi ne kawai."
Ta ɗan yi murmushi, tana kallon Turaki.
"Abin kamar kwata-kwata babu haɗi. Ina shi, ina Auta?"
Ɗan murmushin ya sake bayyana a fuskarta, wanda ya samar da natsuwa a gareta.
"Amma ba zan ƙi ba. Domin na san Ƴata hannun na gari za ta shiga in sha Allah. Kuma idan har Muhammad ya ɗauki wannan nauyin da gaske, ni ba ni da abin cewa sai Allah ya sanya alheri... Kawai dai akwai wani abu da nake dubawa ne…"
Ta tsaya a nan, kamar akwai wata magana mai nauyi da take son ta zaɓi kalamanta da kyau kafin ta furta ta.
Ummi ta ɗaga idanunta zuwa ga Turaki, ta ɗan daɗe tana kallonsa kafin ta yi magana.
"Zaka iya zama da ita?"
Ya yi shiru. Ummi ta ci gaba a magana cikin nutsuwa, amma kalamanta cike suke da tarin muhimmanci.
"Ka sani tausayi daban yake, so kuma daban. Kada ka ƙwari kanka ka ce zaka zauna da ita saboda kawai ta taɓa taimaka maka. Aure ba haka yake ba... Idan za a ce mutum ya auri wani saboda ya taimake shi, ko ya rama wani alheri da aka yi masa, ba lallai ne zaman ya yi daɗi ba. Domin taimakon juna abu ne mai kyau, amma aure rayuwa ce. Ana so a shiga cikinsa da so da ƙauna, da sha'awar zama tare, ta yadda ko bayan shekaru da yawa har yanzu mutum yana jin daɗin kasancewa da wanda ya aura cikin So, Ƙauna da Rahma."
Ta yi ɗan shiru.
"Idan don rama alheri ne kuwa, ai kun riga kun rama mata. Tun da har kuka tsaya mata kan karatunta. Kuma kun bamu muhallin zama mai kyau. Saboda haka ba sai ka ɗaure rayuwarka da ita saboda kana ganin kamar tana binka bashi ba."
Turaki ya sunkuyar da kansa. Hannunsa ya tafi wajen wuyansa, ya shafo shi a hankali, amma bai ce komai ba. Mum ta kalle shi.
"Ka yi magana mana. Baka jin kalaman suna da matuƙar muhimmanci ne. Domin ba zai yiwu a baka Ƴa sukutim guda ba alhalin baka shaida mana cewa kana sonta ba... Don duk wannan dambarwar nuna mana yake tausayinta kawai kake, da son ka yi ramakon alheri."
Ta ɗan dakata, sannan ta ƙara da murya mai tsauri amma cike da kulawa,"Tausayi daban, so daban Malam. Idan har ka san baka sonta, to a miƙo maka takarda da biro."
Kafin ma ya yi tunanin abin da zai ce, kalmar ta fito daga bakinsa da sauri babu shiri.
"Ina sonta fa Mum."
Hajiya Madina ta ɗan karkatar da kai.
"A ina ɗin? Ina son yake?"
Turaki ya yi shiru. Ya sake shafo wuyansa, wannan karon kunya ta bayyana sosai a fuskarsa.
"Allah ina sonta sosai Maama. Tausayin na ta ne ya haifar da Sonta..."
Sai kuma ya kasa ƙarasawa saboda jin kunya. Hajiya Madina ta tsaya daga inda take, sannan ta miƙe. Ta nufi Fullo, ta kamo hannunta cikin nata, tana kallon Turaki.
"To idan da gaske ne ka fara neman amincewarta. Don gaskiya saboda na ka son, ba zan bari a ƙwari yarinyata ba."
A nan ne hankalin Fullo ya dawo jikinta. Ta waiga ta dubi Turaki, sannan ta kalli Maama, kamar sai yanzu ne ta fara fahimtar maganar da ake yi.
"Maama…"
Hawaye suka sake cika idanunta.
"Ni ai bana sonsa. Ba zan iya aurensa ba."
Mum ta kalleta, sai murmushi ya bayyana a fuskarta. Amma ga Fullo, ganin kamar babu wanda ya ɗauki maganarta da muhimmanci, ta fashe da sabon kuka.
"Allah Maama ni bana sonsa. Ba zan iya aurensa ba, don Allah ki ce ya sakeni. Ni taimakon da na yi masa saboda Allah na yi. Ba don ya aure ni ba. Don Allah Maama ki ce ya sakeni…"
Ummi ta buga mata tsawa.
"Keee."
Fullo ta firgita ta yi shiru na ɗan lokaci.
"Kar na ƙara jin wannan furucin daga bakinki. Domin Miji yake a gareki."
Hajiya Madina ta kalli Ummi, sannan ta ce a hankali,"A'a, yi mata a hankali. Da gaskiyarta ai. Don shi yana so sai aka ce shikenan? Ita ma tana da baki da nata haƙƙin. Ba za a yi aure a kan son mutum ɗaya ba kawai."
Sai ta kalli Turaki kai tsaye.
"Saboda haka ka je ka nemi yardarta da Amincewarta. Ba kawai ka ce kana sonta ba shikenan. No! Dole ka sa ta fahimci son naka, ka sa ta yarda da kai, sannan ta ba da amincewarta akanka."
Ta ɗan yi shiru, kafin ta faɗi hukuncin da babu wasa a cikinsa.
"Zan baka kwana biyu."
Turaki ya kalleta.
"Idan cikin waɗannan kwanaki biyu ka samu nasarar sa ta yarda da kai da kanta, Allah ya sanya alheri, zan fi kowa farin ciki. Zan baka Matarka salin alin ku wuce. Amma idan ba ka yi nasara ba, za ka rabu da ita. Mu kuma mu aura mata wanda take so yake sonta."
Shiru ya sake ratsa falon. Turaki ya kalli Fullo. Fullo dai ta sunkuyar da kanta, hawaye na zubar mata. Wani haushinta ya tsarga masa, ya yi ƙwafa wadda babu wanda ya ji.
Mama na gama faɗin haka, ta ja hannun Fullo suka fita daga falon, ranta cike fal da farin ciki.
Fullo cikin kuka take ta maimaita,"Maama ki ce ya sake ni yanzu. Ni ba zan zauna da shi ba, wallahi ba zan iya ba. Ki ce ya sake ni."
Muryarta ta ragu a hankali yayin da suka yi nisa da falon. Bayan fitarsu, Baffa ya ɗaga hannayensa ya yi addu'a. Daga nan aka watse. Ya rage saura Baffa da Turaki, ƙirjinsa na ta lugude kar Baffa ya ce a yiwa yarinyar abin da take so. Don shi dai ko sama da ƙasa zata haɗe ba zai saketa ba. Yanzun ma za su gamu ne, zai ja mata kunne.
Na ɗan lokaci babu wanda ya yi magana. Baffa ya jingina bayansa da kujerarsa, sannan ya ɗaga idanunsa zuwa ga Turaki. Kallon da ya yi masa wannan karon ba irin na Ɗan da yake yi wa nasiha ba ne kawai, akwai wani abu na lissafin rayuwa a cikinsa.
"Kenan ita Fullo ce uwar gida? Ka aureta tun kafin Ilham ko sai bayan da ka auri Ilham aka yi hakan?"
Turaki ya ɗan yi shiru, kansa a ƙasa, kafin ya amsa da.
"Baffa kafin auren Ilham ne."
Baffa ya numfasa a hankali. Ya yi shiru na wasu daƙiƙu, kamar yana haɗa bayanan da ke gabansa a zuciyarsa.
"To yanzu ya zaman nasu zai kasance? Haɗe su zaka yi, ko kuma akwai wani tsarin da kake tunani a kai?"
Turaki ya yi ɗan jim. Bai yi saurin ba da amsa ba. Daga ƙarshe ya ce,"Yanda ka ce Baffa."
Baffa ya ɗan ɗaga gira.
"Yanda na ce?"
Sai ya girgiza kai.
"Ah, wannan kuma ba ni zan yanke maka ba. Kai ne Mijin matan. Kai ne zaka yi making decision a kan yadda gidanka zai kasance."
Ya ɗan yi shiru, sannan ya ƙara,"Sai dai idan ka nemi shawara zan baka. Amma ba zan zauna in tsara maka yadda zaka gudanar da gidanka ba."
Turaki ya sunkuyar da kansa.
"To Baffa ka bani shawarar."
Baffa ya kalle shi na ɗan lokaci, sannan ya ce,"Ka bari sai mun fara zantawa da Ƴan uwana tukunna akan auren naka. Ina so mu san abin da yake cikin wannan aure, mu fahimci komai yadda ya kamata kafin ka fara ɗaukar wani sabon mataki. Daga ɓangarena dai babu wata matsala na amince kuma nasa albarka. Goben zamu wuce can garin na su da wuri, ko bamu samu Mahaifin nata ba, Limam da Shaidun auren na ku sun isa."
Ya ɗan karkata kansa.
"Bayan haka sai mu zauna mu duba yadda ya dace a tafiyar da lamarin."
Sai ya yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ce,"Now you can leave. Duk ka saka mun ciwon kai."
Turaki ya miƙe.
"Na gode Baffa. Kuma ina ƙara bayar da haƙuri don Allah."
Baffa ya ɗaga hannu kaɗan.
"Ka je kawai."
"A huta Lafiya, Allah ja kwana mai albarka."
Turaki ya juya ya fita. Baffa ya rage zaune shi kaɗai, yana kallon inda Turaki ya bi, kafin ya sauke idanunsa a hankali. A gabansa dai aure ya zama gaskiya. Abin da ya rage shi ne yadda za a tabbatar da cewa gaskiyar nan ba ta zama sanadin rushewar wani abu daban ba. Yana fatan ya ji magana mai kyau a goben idan Allah ya kaimu.