Free chapter · Read without an account

THE LIES WE BURY

by Maryam · THE THRONE OF THORNS

Ummu ce tsaye a bayan ta idon ta cike da ƙwalla.Atti bata san lokacin da ta sauke hannunta daga kunnen ta ba. Buɗe baki tayi za tayi magana, Ummu tayi saurin ɗaga mata hannu, tana juyawa ta koma ciki asibitin da sassarfa. Ɗora hannun Atti tayi a kai, ta fi minti 30 a gurin a tsaye, ta rasa abin yi. Ita damuwar ta ma yanzu shine ta ina zata fara fahimtar da Ummu. Ganin tsayuwar ta a gurin ba inda zai kai ta haka ta ja kafafun ta da ƙyar ta bar gurin koma ciki. Tarar da Ummu tayi a zaune a reception ɗin ita kaɗai, shiru. Da ka ganta kasan tana cikin matsananciyar damuwa.

Zama tayi kusa da Ummu tana riƙo hannunta, ta marairaice murya ta fara da cewa, "Ummu, wallahi ba abin da kike zato bane, bana son ƙara miki damuwa ne akan wacce kike ciki. Ummu, kinsan bani da wata sama da ke, haka bani da abokiyar shawara sama dake. Kuma taron nan na da matuƙar mahimmanci sosai".Numfasawa ta yi kafin ta cigaba da cewa, "Nasan Ummu kinji cewa yana da haɗari sosai, amma ke kika koya min rashin tsoro. Kuma dole ne in ɗau wannan kasadar, ko dan cikar burkina da na ABBU....."ta kasa qarasawa sakamakon kirjinta da yayi wani nauyi.

Tunda Atti ta fara magana Ummu bata jiyo ta kalle ta ba, amma tana kiran sunan ABBU ta juyo ta kalle ta. Idonta na tara wasu ƙwalla masu zafi.

Ummu ce ta buɗe baki ta fara magana, muryar ta na rawa,ta ce "Maleeka, kin san naji ban isa ba. Naji ku sancin dake tsakanin mu bai kai ba.Yanzu har akwai wani abu da zaki iya ɓoye min. Nasan ba da wani abu kina ɓoye min bane dan wani abu. Kinyi ne dan kar na damu kika gwammace ki riƙe damuwar duka ke kaɗai.Maleeka kisani ni UWA ce. Yanzu idan kika je wani abu ya faru da ke, wani hali kike tunanin zamu shiga. Da wani ido kike so in fuskanci mahaifin ku idan na mutu."

Shiru Atti tayi na wasu mintina kafin ta ɗago idon ta da suka yi jajir tana cewa, "Ummu, ya zama dole ne sai nayi, ko dan gano gaskiya....." Wani ciwo Atti ta famo musu mai zafi da raɗaɗi gaske, wanda suke ta ƙoƙarin su binne shi. Maganarsu ce ta tsaya sakamakon wata Nurse da tazo ta gaya musu su zo, mara lafiyar ta tashi.

Cikin farin ciki da ɗoki haka suka shiga ɗakin ɗazu. Husna ce a zaune, fuskar ta tayi fayau, abin tausayi. Ummu da sassarfa ta ƙarasa gare ta, ta rungume ta, sai sauke numfashi take kamar wacce tayi uban gudu. Ƙanƙameta tayi a jikin ta kafin ta cire, kuma ta fara dudduba ta tana cewa, "Ba abin da ke miki ciwo yanzu ko?" Murmushi Husna tayi tana cewa, "Ba abin da ke min ciwo, Ummu." Dariya Ummu tayi tana cewa, "Allah mun gode maka, Allah ya ƙara miki lafiya, kinji Asma'a."

Atti da ke ta murmushi a bakin ƙofa da Ammar da ya shigo yanzu ne suka amsa da, "Amin ya Allah." Ƙarasowa ciki suka yi inda Atti ta zauna gefen gadon, Ammar na tsokanar Husna yana cewa, "Aike nayi tunanin kin margaya in gaje ki in zama Auta." Hararshi Husna tayi tana cewa, "Kuma gashi ban mutu ba, dole ka haƙura." Atti ce ta ce mata, "ƙyale shi Husna, duk abinshi dole ya haƙura." Ta ɗora da, "Ya jikin naki yanzu, Allah ƙara sauƙi, yasa kaffara ne." Husna ta amsa, "Amin addāta."

Haka suka cigaba da hirarsu, kiran sallar Zuhr aka fara, inda Ammar da Atti suka lallaɓa Ummu da ƙyar akan ta koma gida tayi wanka ta ɗan huta ta dawo da yamma. Ummu ma ganin jikin Husna yayi sauƙi ne, kuma ita ma ta san tana buƙatar hutun yasa ta yarda ta tafi, aka bar Atti da Ammar a asibitin.

Sallar Azahar su kayi, inda suka zauna suna hirarsu ƙasa-ƙasa dan kar su tashi Husna.Fatima ce ta kira ta a waya, inda take gaya mata kwana su kayi a asibiti, jikin Husna ya tashi. Nan da nan hankalinta ya tashi, inda tace ta bata address ɗin asibitin, zasu zo ita da Moma (maman su Fatima, Hajiya HAMEEDA).

An fara kiraye-kirayen sallar La'asar, sai ga Ummu ta dawo tare da su Fatima da Moma, da suka haɗu a bakin gate. Fatima ce niƙi-niƙi da manyan luxury warmers. Karɓa Atti tayi, inda Ummu ke cewa, "Hajiya HAMEEDA, har da hidima haka." Murmushi Moma tayi tana cewa, "Kinji ki Ummun Husna, har ina kayan suke ma?" Maganar ce ta katse sakamakon kiran da ya shigo wayar Atti. Hajiya Jamila ce. Ɗaga wa Atti inda Hajiya Jamila ke ce mata ta ƙaraso tana ƙofar asibitin.............

_____________________

Wani ɗaki ne baƙi ƙirin, baka jin komai sai ihun wani mutum kamar ana zarar ransa, sai kuma daga baya yayi shiru sai sauke numfashi a hankali, a hankali. Ɗakin ne ya gawraye da haske sakamakon kunna fitilar ɗakin da akayi. Mutum ne zaune a kan kujera, an ɗaure shi da kacha, duk ya gama galabaita, fuskar sa a kife, duk gashin kansa ya barbazu. Hannunsa ne ke ta fitar da jini sakamakon farcen sa da aka zare masa yanzu.............

__________________

Kano State
Gidan Radion MIKIYA

Rahoton safe kuke saurara daga Gidan Radion MIKIYA da ga bakin Kabir Sani.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Yau mun tashi cikin jimami da tashin hankali sakamakon kisan gillar da Matar Senator A.A BALA tayi wa mijinta da 'yarta cikin rashin imani, yayin da itama ta kashe kanta bayan ta kashe su. A rahoton da muka samu, an tabbatar da matar ta taɓun hankalin ta ne ya tashi, inda cikin yanayin hauka ta kashe su gaba ɗaya da mutanen gidan, daga ƙarshe ta kashe kanta. Muna taya mutanen gari jaje. Bamu da abin cewa sai dai Allah ya kyautata makwancin su, ya kuma bamu mata masu hankali. Ameen ya Rabbi."Haka ya ɗora da sauran rahotannin har ya gama.

Numfashi ya sauke kafin wani abokin aikin sa dake zaune a gefen sa ya miƙo mai shayi a kofi yana cewa, "KB, amma fa an raina mana hankali fa akan rahoton nan. Anya kana da tabbacin gaskiya ce?"

Hararshi yayi yana cewa, "Ina ruwan ka? Wai kai Tijjani (TJ), me na tsare maka ne? Ai kasan in ba ingantacce bane bazan faɗa ba. Aikin banza," ya ƙarasa faɗa yana fita daga ɗakin rahoton, yana banko masa ƙofa.TJ ne ya girgiza kai yana cewa, "Allah ya kyauta."

Bayan KB ya fita ne ya shige wani lungu, ya ɗau wayar yana kiran wata lamba. Ɗagawa akayi, inda KB yayi sallama, sai rawar jiki yake. Cikin wata dakakkiyar murya, wata mata ta amsa. Kamar zai yiwa matar da suke wayar da ita sujjada, ya fara cewa, "Ma'am, komai ya kammala kamar yadda kika ce."A taƙaice ta amsa da, "Toh, turo account ɗinka a cika ma kuɗin ka."Kashe wayar KB yayi yana daka tsallen nasara yana cewa, "Yessss!"

A ɗaya bangaren kuma, matar da ta kasance kamar wata 'yar daba, taci uban gashin doki, ta kira wata tana cewa, "Hello Boss, an gama da wannan matsalar."

Boss ne da su Spider ne suka kece da dariya, duka sun ji abinda CHIOMA tace. Katse wayar shima Boss yayi kafin ya danna wani kiran shima....... Ɗaga kiran akayi, an fi minti biyar kafin ayi magana cikin wata ishashshiyar murya da ta ƙama.... Boss ne ya fara magana yana cewa, "HAJJAJU, HAJJAJU, komai fa ya kammala.......................End of Chapter 6...........Written by Muraimaa Naabba ✍️✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.