Free chapter · Read without an account

Chapter 12

by Hauwa’u Abdurrasheed · SULTANIM

SULTANIM
      Na
Mss Samher

Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher


Page12

Bayan tafiyar su Dady Abba ya rasa meke masa dadi farin ciki zayyi ko kuma damuwa.
Anya beyi ma Nadrah gaggawa ba kuwa, wata zuciyar kuma tana ƙarfafa shi yasan zata samu rayuwa mai kyau da farin ciki a inda zai turata fiye da zaman gidansa.
Yana da tabbacin zatayi karatu har sai takai matakin da taji tanaso ta tsaya dan kanta.

Mahmud dake zaune tare da Abba har lokacin yace 
“Abba amma ita Nadrah tasan da duk wannan, wata ɗaya fah”

“Batasani ba Mahmud, amma nasan zatamin biyayya kuma in sha Allah auran zai zama alkairi a gareta, kafini sanin halin da take ciki a hannun Ummanku, harga Allah naso haɗasu ita da Baffa amma kwanciyar hankalinta nafi buƙata, wanda na tabbata bazata sameshi tare damu ba.”

Kansa ya girgiza alaman gamsuwa, Abba yace 

“kuma karka faɗama kowa tukunna, saboda jiya mahaifiyar ku ta sameni da zancem Baffa sun faminci juna da ƴar kawunku Nafisat”

Cikin rashin fahimta yace “Nafisat kuma Abba, ban tabaji ba gaskiya?”

“Nima nasan akwai abun data ƙulla, amma zan bincika idan ya tabba haka ne za’ayi bikin lokaci ɗaya kawai”

“Shikenan Allah yasa albarka”
Abba ya amsa da Amin.

Wuraran ƙarfe huɗu Abba ya kira Baffa akan duk inda yake yazo yana san ganinsa, bai wani ɓata lokaci ba dan dama yana kusa da gida.

Kallansa Abba keyi na wasu daƙiƙu kafin yace “Baffa menene tsakaninka da ƴar wajan Yaya malan?”

Tabbas yaji a ransa dalilin Abba na kiransa kenan, saboda yasan Umma bazata taba yin shiru a  al’amari irin wannan ba.

Bai ɓoyewa Abba komai ba har zuwan shi wajan Nafisat jiya.

“Dalili biyu zaisa na amince da wannan haɗin, na farko idan ya tabbata kana santa na biyu kuma sanin Yaya malan mutumin kirki ne na yaba da tarbiyan yaransa.”

Abba yayi shiru sannan ya cigaba da cewa
 “yanxu kai nake saurara ka amince da Nafisat ɗin”

Kansa ya ɗaga alamar eh.
“Alhamdulillah, Allah ya maka albarka yasa hakan ya zama alkairi agaremu duka.”
Baffa yayiwa Abba godiya sannan ya fita.

Abba ganin lokaci ya riga ya ƙure yasa a ranan yaje gidan Yaya malan da daddare, a take Yaya malan ya amince saboda babu wani abun da zai gagara a wata ɗaya.

Zuwa washe gari labarin auran Baffa da Nafisat ya baza dangi, Umma kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha dan farin ciki.

********

Ɓangaran su Mami ma haka, zuwa ƙarfe ɗaya gidanta ya gama cika daƴan taya murna, kasan cewar yau asabar babu makaranta Auntie mama da duka yaranta tazo.
Farin ciki bayyane akan fuskokinsu, shi uban gayyan besan wainar da ake toyawa.

Zahra dasu Ameera ne a ɗaki cike da zumuɗin fara shirye shiryan bikin Ya Faruq.

Zaina tace “I’m just so speechless, ya kamata mu fara tsara event ɗin da za mu yi and lot more.”

“Ke ma kin san babu wani event na musamman, saboda amarya a Kaduna take.” Ameera ta faɗa cikin rashin jin daɗi.

“You guys should relax, angon nan bai san me ake ba, kar ku ci buri da yawa.” Zahra ta faɗa tana murmushi.

Tsakin da Hanifa ta yi yasa duk suka kalleta.
“Ni fa ina so Ya Faruq ya yi aure, ba wai ba na so ba, amma idan na ce ina farin ciki da auran nan, wallahi na yi muku ƙarya. Saboda me za a yi masa dole? A bari ya zaɓi wacce yake so da kansa mana.”

“Sai ki je ki samu Mami, tunda mu babu abin da za mu iya. Biki ne dai, muna murna wallahi.” Ameera ta faɗa tana hararan Hanifa.

Tun da su Auntie mama suka tafi Mami take saƙa da warwara a zuciyarta, Dady ya kalle yadda ta zauna tayi shiru yace “Aishatu yadai”

“Umar nake tunani koya zai ɗauki al’amarin”

Wayarsa ya ɗauka ya kira Faruq amma bai ɗauka ba sai ya kira Zahra yace ta kira masa Umar yazo yanxu.

 Sannu a hankali yake takowa harya ƙaraso cikin parlorn 
“Dad Mamina barkanku da dare” ya furta a hankali yana ƙara gyara zaman sa.

Dad ne kawai ya amsa Mami kam kallonsa kawai takeyi.

“Umar kamar yadda muka riga mukayi magana dakai a baya, ba ra’ayinka nakeso naji ba zan faɗa maka ne saboda kana da haƙƙin ka sani, naje kaduna jiya kuma mun tsayar da ranan auranka nan da wata ɗaya in sha Allah”

Waro ido Faruq yayi yana kallon Dady, tunaninsa ya tsaya cak na wucin gadi, ya tsatstsare Dady da ido.

“Bakaji me nace bane kake kallona?”

“Amm… Dady aure fa kace kuma wata ɗaya”

“Eh nariga na faɗa maka ka shirya tunba yau ba”

“Amma Ammi…” dakatar dashi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu.

“Karma ka ɓata bakinka, nama siyo lefe yanxu haka suna cikin gidan nan, kuma zaka biyani kudina dan ba kyauta na siya maka ba”

Kansa ya saukar ƙasa batare da yace komai bah.

Dady yace “tashi kayi tafiyarka kuma ka fara shiri dan babu lokaci, Allah ya maka albarka yasa ta zame baka sanyin idaniya” 
Bai iya amsawa ba ya tashi ya fita.

Tafiya kawai yake bai ma san inda yake saka ƙafanshi ba, jijiyoyin kansa sun fito har wani zafi kansa ke masa saboda ciwo.

Yana shiga ɗaki rage kayan jikinsa yayi ya haye gado ya kwanta, tunani kawai yakeyi taya zai iya rayuwa da matar da bayaso, meyasa Dad zai masa haka kuma harda Maminsa sanan suce nan da wata ɗaya, ya sukeso yayi da rayuwansa.

A hankali ya lumshe idonsa yana jin yadda zuciyarsa ta masa nauyin da ace ba a kwance yake ba zai iya faɗuwa.

Duk yadda yaso yayi bacci hakan ya gagara yana nan kwance har ƙarfe uku sai kawai ya miƙe ya shiga ɓan daki yayi alwala yafito ya tada sallah.

********
Farin ciki da walwalan gidan Umma na musamman ne, kowa yasan Umma ya ganta tsakanin jiya zuwa yau sai ya shaida tana cikin annashuwa.

Idan Abba zaiyi breakfast tare dasu ne kawai yake sawa a kirata, idan taji shiru tasan a parlonsa ya karya.

Mafarkin Baba tayi bayan ta koma baccin bayan asuba, bece da ita komai ba sai dai murmushi kawai har ya ɓacewa ganinta, ta dade zaune a bakin gadonta kafin ta tashi ta shiga ɓanɗaki tayi wanka.

Ta shirya cikin lemon green lace ɗikin riga da siket ba ƙaramin tayi mata ba, duk da ba wani makeup tayi ba amma hodar data shafa ta kwanta a fuskanta sosai ta ƙawata farar fatanta.

Tana fitowa sukayi ido biyu da Abba tare suke da Mahmud da alama fita zasuyi.

“Kinyi kyau sosai Mamana” Abba ya faɗa yana kallonta fuskanshi ɗauke da murmushi.

Murmushi tayi wanda ya bayyana jerarrun fararan haƙoranta cikin muryanta mai sanyi kamar koh yaushe tace “nagode Abba, barka da safiya”

Abba ya amsa mata da “barka da safiya Mamana,” yana gyara agogon hannunsa. 

Mahmud ta kalla kafin tayi magana ya rigata faɗin “am doing well, as you can see”

Abba yace “muje muna ɓata lokaci”
Adduan fatan alkairi ta musu sannan suka fice.

Tana gama karyawa ɗakin Umma taje, ta tura ƙofan bakinta ɗauke da sallama.
Umma dake waya ta juyo ta kalleta ganin hannunta riƙe da tsintsiya yasata faɗin “fita min a ɗaki gulmamma”

Juyawa tayi tana murmushi  wani lokaci Umma nishaɗi kawai take bata, gurin Talatu taje ta zauna jefi jefi suna kawo zancen bikin Baffa.

********

Faruq har garin Allah ya waye bai samu ya rintsa ba, tunda dama sunday ne ba office zaije ba ko fitowa beyi ba, Mami ce tasa aka kai nasa breakfast.

Wayarsa ta cika masa kunne, koda yaga Hisham ne ke kiransa haka ya kashe wayan gaba ɗaya.

Throughout ranan Faruq bai fito ba, sallah ma a ɗaki yakeyi.
Da rana basu kai masa abinci ba, da daddre ne Mami tasa Zahra takai masa ta kuma duba mata ya yake.


Daran ranan ya samu bacci sai ƙarfe goma ya tashi, wanka yayi yafito ya karya sannan ya sake komawa ɗaki.

Wujan ƙarfe biyar ya fito sanye da jallabiya. A hankali yake tafiya kamar mai tsoron taka ƙasa.

Duk a parlour ya tarar da su, kallon sa ƙannensa suke yi cike da tausayawa.
Koda suka gaishe shi da kai kawai ya amsa, ita kam Mami kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai.

“Mamina, fushi kike yi da ni ko?” ya faɗa a hankali.

Miƙewa tsaye tayi ba tare da ta kallesa ba tace
 “Biyo ni.”
Ba tare da musu ba yabi bayanta.

Akan jerin akwatuna ya fara sauke idonsa, zuciyarsa ta buga da ƙarfi. Ya janye idonsa daga kansu, ya ƙarasa kusa da Mami ya zauna.

“Kiyi haƙuri Mamana.”

“Bana da wani dalilin da zan ji haushinka Umar. Amma inaso ka sani, rufe kanka a ɗaki bazai chanza komai ba. Wannan auran shine burinmu, bazaka iya mana wannan ba.”

Ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin
“Hakan bazai sake faruwa ba Mamina.”

“Wannan shine yaron Mamin dana sani, Allah ya maka albarka.”

“Amin… amma har na fara tunanin Mami ta daina sona” ya faɗa yana ɓata fuska.

Kallansa tayi tace “Zaka turamin kuɗin kayana yanzu ko bashi zan biyo ka?”
kallonta yayi itama shi take kallo……..

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.