Free chapter · Read without an account

Chapter 18

by Hauwa’u Abdurrasheed · SULTANIM

SULTANIM
      Na
Mss Samher

Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher


Page18

Sautin tarwatse wan kwalban ya cika dodan kunnanta harya haifar mata  da runtse idanu, daga zaunen da take ta rungumo gwiwoyinta ta fashe da kuka, cikin fitar hayyaci take faɗin 

“Why Why babe Why Faruq?”

Hannu takai ta ɗauko wani kwalban haƙori tasa ta buɗeshi takai bakinta saida ta shaye duka sannan ta ajiye tana sakin wata irin gyatsa mai wari.

“Wallahi bazan bar mata kai ba, ko ni ko ita.” Tana faɗa tana bajewa a kan kujera.

********
Kiraye kirayen sallan magrib ya farkar da Nadrah  a bacci, cikin natsuwa ta taka zuwa banɗaki, sai data sake watsa ruwa tayo alwala.

Bayan ta idar da sallan magrib alkur’ani ta ɗauko ta fara karanta har aka kira isha, ta ɗaɗe tana addu’a sannan ta miƙe, yunwa takeji hakan yasa ta yanke shawaran duba parlor ko zata samu abinci.

Auntie mama ta turo ƙofan ganinta a tsaye yasata faɗin “Amarya kin sha bacci, maza zoki shirya na ƙarasa aikina gida nima zan tafi yau ɗinnan.”

Atampa ta saka ta ɗaura lafaya a sama, Auntie mama ta riƙe hannunta suka isa ɓangaran Mami, yammatan ne kawai a parlorn sai Hanan.

Kai tsaye parlorn Dady suka wuce, yana zaune shi da Mami, cikin natsuwa suka ƙarasa ta zauna saman carpet Auntie mama ta zauna gefan Mami tana faɗin 

“ga ƴarku nan na kawo muku ita bisa al’ada.”

“Allah ya miki albarka, kiyi haƙuri, kiyi haƙuri kuma kiyi haƙuri, Allah ya baku zaman lafiya, amanarki na karba wajan Abbanki in sha Allah zanyi bakin ƙoƙari na wajan riƙe wannan amana, mahaifinki mutumin kirki ne Fateema Allah ya yafe musu baki ɗaya, Allah kuma ya kyautata namu ƙarshen.” Dady ya ƙarasa maganan cikin juyayi.

Suka amsa da Amin.
Mami tace “ba sai nace komai ba muna tare kullun, nikam ƴa aka kawomin ba suruka ba, Allah ya bamu haƙurin zama da juna.”

Sun ɗau lokaci a haka kafin Hanan ta leƙo faɗa musu mijinta yazo ɗaukanta, hakan yasa suka fito dukansu.

Tafiyanta baifi da minti goma ba Baban su Hanifa yazo saida yaje suka gaisa da Dady kafin suka masu Mami sallama suka tafi, taso ta tafi dasu Ameerah amma Mami tace ta barsu gobe zata saka driver ya kawosu.

Zaina taja ta zuwa dining ta zuba mata abinci sosai taci dan dama yunwa takeji, ƙamshin turaransa ya fara masa iso bata iya juyawa ba amma koda su Hanifa suka gaisheshi bataji ya amsa ba.

Mami tace “a kawo maka abinci daga ina ma kake ne?”

“Naci abinci Mami, tare dasu Musty nake, wani shirmen suka sake haɗawa.” Yayi maganan yana jan tsaki.

Murmushi kawai Mami tayi, yanajin ƙannansa nata maganan biki ko kallan inda suke beyi ba, wajan goma saura ya miƙe yana faɗin

 “Mamina good night.”

Har yakai ƙofa Mami ta dakatar dashi ta hanyar faɗin “ita anan zata kwana kenan?”

Chak ya tsaya daga inda yake tsaye bai juyo ba kuma beyi magana ba, a hankali ta miƙe tayiwa Mami sallama, jin ta taho yasa shi buɗe ƙofan ya fita tana binshi a baya.

Murmushi Mami tayi mai sauti ita kaɗai tasan abinda yake cikin ranta.

Bai ko kalla side ɗin da take ba ya shige ɗakinsa, nannauyan ajiyar zuciya ta sauke, fridge ta buɗe ta ɗau ruwa tasha kafin ta shiga ɗaki.

Mama kullun tana mata addua Allah ya baki miji na gari, yanxu gashi tayi auran amma kuma dukansu basa duniya, a sanyaye tace 

“In sha Allah kuna matsayi mai kyau.” Wannan din addu’a ce da kullum rana batasan sau nawa nake yinshi ba.

A haka ta isa ga gadonta ta kwanta, ba wani wadataccen haske a ɗakin amma haka take bin lungu da saƙon ɗakin da idonta, tanajin kamar bata chanchanci zama a ciki ba, sannu a hankali idanuwanta sukayi nauyi bacci ya tafi da ita.

Washegari tunda ta idar ta sallar asuba bata koma ba, tana ta azkar amma kusan rabin hankalinta na chan tunanin yadda rayuwa zata kasance mata tare da bawan Allah nan alamu sun suna baya ra’ayinta.

A kan sallayan ta kwanta sai dai batayi tsammani ba bacci ya ɗauke ta, ba kuma ta farka ba sai wajan ƙarfe goma saura na safe.

Ta miƙe tana ninke abun sallar, duk da dakin beyi wani ƙura ba haka ta sake gyarawa ta chanza zaman abun da bai mata ba, daga nan ta wuce toilet tayi wanka.

Cikin mayukan dake sama mirror ta buɗe ta shafa, sannan ta nufi makeken wardrobe dinta.

Kayanta wanda tazo dashi daga gida ne kawai a ciki sai wanda suka aika mata dashi, cikin na gidan ta ɗauko wata atamfa purple mai ratsin fari ɗinkin riga da siket wanda bata tama sakawa ba, sun zauna a jikinta sun mata kyau sosai, tasa lipgloss a bakinta.

Kayan dake cikin akwatin ta fara curowa tana jerawa a wardrobe ɗin, ya ɗauketa tsawan lokaci kafin ta gama, tsayawa kawai tayi tana kallon tarin suturun yanxu duka wannan mallakinta ne, farin mayafi ta ɗaura saman kayan jikinta sannan ta fito parlorn.

Shima sama sama ta gyara ta saka komai yadda takeso, zama tayi taci abincin data gani a saman dining da alama shima yaci sai ta tattara kayan ta shiga kitchine.

Girman kitchine ɗin ya burgeta matuƙa, ga wata ƙofa da take da tabbacin store ne, sai da ta wanke kayan sanna ta fito, ɗaƙinta ta koma ta kunno turare ta kawo parlorn.

Dai dai sanda ya fito daga ɗaki, sanye da jallabiya navy blue color, sumar kansa ta ɗan hargitse, fuskansa fes da alama ya sha bacci.

Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke idonsa, cikin muryanta mai natsuwa da sanyi tace 

“Good morning.”

Kansa ya jinjina kawai badan tana kallonshi ta ƙasan ido ba tabbas da baza tasan yayi ba, sai da taji motsin fitarsa sannan ta samu damar ajiyar zuciya ta rasa me yasa take tsoransa.

Tunda ta koma ɗaki bata sake jin motsin kowa ba, gaba ɗaya gidan sai takejin shi wani iri babu dadi, a chan gida ko ba komai tana hira da talatu.

Tana nan kwance sallah kawai ke tada ita, bayan tayi sallan la’asar wajan ƙarfe huɗu dogon hijab ta saka ta kwashi kayan da aka kawo abinci tafita zuwa ɓangaran Mami.

Mami ce zaune a parlorn sai Abu dake tsaye da kwando a hannunta, shiga tayi bakinta ɗauke da sallama, suka amsa suna murmushi.

“Shikenan kin hutar dani matan Alhaji ƙarami.” cewar Abu.

Cikin natsuwa ta ƙarasa gaban Mami zata zauna a ƙasa Mami ta riƙeta ta zaunar da ita a gefenta tana faɗin 

“Zauna a nan, nifa Mami ne kar kiji kunyata.”

Sai da suka gaisa ta ajiye kayan data shigo dasu Abu ta zuba mata abinci saboda dama chan zata kai, nan Mami tasa aka kawo mata abincin tana ta jan ta da hira tace ita mahaifiyarta ce ba suruka ba, sosai kuma natsuwan Nadrah yake burgeta.

Bata wani ci abincin da yawa ba haka kawai takejin bakinta babu ɗaɗi, suna nan zaune su Zaina suka fito tare dasu Ameera sunyi shirin tafiya.

 “Laaa yanxu mukeso muje miki sallama ashe kina nan.” Hanifa tafaɗa tana murmushi.

Manyan idanta ta buɗe a kansu “banga kunzo ba shi yasa na fito ai.”

“Na kai breakfast Ya Faruq kawai na samu a parlor yace kina bacci.” cewa Zaina.

Da mamaki ta ɗan kalleta sai kuma ta saukar da kanta ƙasa.

“Auntie Nadrah kuna ta trading keda yaya a media shi muketa kallo throughout.” Ameerah ta faɗa tana miƙa mata wayarta. 

Mami tace “munyi maganan ɗazu da Halima, jama’a kowa da kalan bakinsa, Allah ya tsareku daga sharrin masu mugun baki.”

“Mami ko wani comment kika duba sai dai kiga ana rubuta God when, jama’a ya mukaji da murmushi, Allahumma bareek the outfit is given, couples are looking so ma sha Allah, they are made for each other.” Zahra ta ƙare faɗa tana murmushi.

“They are following me everywhere, at this point i think this couple are after my life, na kalla yafi sau ashirin” cewar Zaina tana dariya.

Hanifa tace “amma naga wata tace wai angon baya dariya ne, aka mata reply da sanin darajan kai ne.”

Duk suka kwashe da dariya, Zaina tace “just imagine event ɗaya fa kawai.

Nan hira ta ɓarke, kowa na faɗan irin comment ɗin dayaci karo dashi, Nadrah dai binsu take da ido idan anyi abun dariya sai tayi murmushi, kafin Mami ta matsa su tashi dan magrib ya gabato, har bakin mota suka rakasu bayan sun shiga Nadrah tace 

“Ku gaishemin da Auntie mama.”
Suka amsa da in sha allah zataji.

Da dade a ɓangaran Mami suna hira jifa jifa Mami na jefo mata tambaya tana amsawa, har sukayi sallan isha. 

Bataso ya dawo ya sameta a nan karta takura masa shiyasa ta Mami tace 

“Mami zan tafi saida safe.”

“Allah ya kaimu lafiya, nagode Allah ya muku albarka.” ta amsa da Amin Mami. Tare dazu Zahra suka wuce ɓangaranta.

Ganin suna niyyan tafiya yasata cewa “hey bangane ba tafiya zakuyi ne?”

Zahra tace “Ya Faruq baya dare a waje yanxu nan zaki ganshi.”

“Balle yayi amarya.” Zaina ta faɗa suna dariya. 
Da kallo ta bisu har suka fice, wai amarya ta maimaita a hankali.

Fitanta babu jimawa Faruq ya shigo dan koda su Zaina suka koma tare da Mami suka sameshi.

Sosai Mami ta sake mishi nasiha tare da bashi kaɗan daga cikin labarin Nadrah, kuma tace zuwa gobe yasa a kawo mata komai na kayan abinci gudun kar a shiga haƙƙinta ko akwai abin da takeson ci.

Yaji tausayinta matuƙa, yarinya ƙarama irin wannan ace bata da iyaye abun tausayi ne ƙwarai, sam bata chanchanci rayuwa dashi ba she deserve more.

Da wannan tunanin ya isa ɗaki, a sanyaye ya gama shirin bacci ya dade yana tunani ga Swafiyya ta dameshi da kira amma bashi da natsuwan ɗaga kiranta.

Da safe da wuri ya tashi ya shirya ko ɓangaran Mami beje ba ya fice office, ma’aikata ƙalilan ne suka riga shi zuwa dan duk sammakom Hisham ranan ya rigashi zuwa.

Cikin natsuwa yake duba file ɗin dake gaban shi sannan yayi signing a duk inda ya kama ta ace yayi, sannu a hankali ya miƙe ya nufi inda aka ajiye na’urar haɗa coffee, ya haɗa sannan ya dawowa ya zauna.

Buɗe ƙofan Hisham yayi ya shigo mamaki bayyane akan fukarsa yace 

“Da naga motarka nayi mamaki, kuma banasan shariya, meya kawoka yau malan?” Hisham ya faɗa yana ƙarasa shigowa.

Sipping coffe ɗinsa yake hankali kwance, idansa akan Hisham amma bece dashi komai ba, yana son yayi magana amma kalmomin sun maƙale masa a maƙogwaro.

“Ko zaka koreni.” yayi maganar kamar bashi yayi ba.

“Aa amma dai wallahi baka kyata ba, gaskiya ce saina faɗa maka ko bakaso.”

Ƙayataccen murmushi ya sake tare da lumshe idanuwansa, hararansa Hisham yayi sanan ya fice.

A chan gida Nadrah sai ƙarfe goma da rabi ta tashi, ta miƙe a hankali ta nufi toilet, tayi wanka ta shirya cikin doguwan rigan atampa, sannan ta fito ta karya.

Tv dake parlorn ta kunna da farin ciki akan fuskanta ta koma ta zauna bayan ta ɗau remote ɗin, Zee world ta kai suna haska shirin ‘Unfortunate love, da kewa take kallon saboda lokacin har sai Mama tazo ta kashe tv take tashi tayi mata aiki.

Kallon ya debe mata saba’in da biyar cikin ɗari na damuwarta, nauyin da takeji a ƙirjinta ya ragu sosai, suna gamashi suka sako wani haka Nadrah tayi ta bin shirye shiryen da suke sakowa har aka kira sallan azahar.


Koda tayi sallah sanye da hijab ɗin ta fito parlor, ƙofan da taji ana knocking yasa ta nufeta kai tsaye, zahra ce tare da ita akwai wasu maza uku.

“Auntie Nadrah good afternoon”

Murmushi akan fuskarta tace “how are you doing.”
 
“Am good”

Sai da ta shigo sannan ta kallesu tace “ta ƙofar chan zaku shiga da kayan bari na buɗe.” 

Tana gaba Nadrah na baya suka ƙarasa kitchen ɗin, Zahra tasa hannu buɗe store ɗin sannan ta buɗe wanchen ƙofar dake baya.

Nan fa suka fara shigo da kayan abincin, baki buɗe take kallon su saboda kayane da ko nan da shekara biyu bata tunanin zasu iya cinyewa.

Sai da aka gama shigo dasu Zahra ta taimaka mata suka shirya komai, har wanda za’a saka a freezer sun saka, sai kitchen ɗin ya kara mata kyau.

Kayan breakfast ɗin safe Zahra ta kwaso ta fito dasu, Nadrah tace 

“Nagode sosai.”

“You don’t have too” har ta kai ƙofa ta tsaya juyowa tayi batare data dawo ba tace

“Yawwa naso na manta Ya Faruq yana cin komai dan na faɗa miki baya wasa da abinci, amma favorite food ɗinshi tuwo da ko wani irin miya, kuma yana san waina  i think shikenan.”

Kanta ta gyaɗa tana murmushi har haƙorinta na bayyana, fita Zahra tayi tanaji har ranta Nadrah na burgeta…...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.