Free chapter · Read without an account
Chapter 19
SULTANIM
Na
Mss Samher
Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher
Page19
Guraran ƙarfe uku ta shiga kitchen bayan tsawon lokacin data ɗauka tana tunani, ta yanke shawaran yin tuwo duk da bata da tabbacin zai ci.
Zuwa ƙarfe biyar da rabi ta kammala lafiyayyan tuwan shinkafa da vegetable soup wanda ta ƙawata shi da naman rago, ganda and some tilapia fish, ƙamshin miyan ya cika ilahirin kitchen ɗin.
Sannu a hankali ta jera komai saman dining tana fatan Allah yasa yaci ko kaɗan ne.
A hankali yake takawa, duka hannayensa cikin aljihun rigansa, duk da yadda ya gaji ga yunwan dake damunsa amma yaje Mami tace bazata bashi abinci ba meye amfanin auran da suka mishi, zuwa yanxu bai san me su Mami suke nema dashi ba.
Store ɗin ya fara dubawa dan tabbatar da an kawo duka kayayyakin daya saka a kawo, sannan ya rufe ya fito ya tsaye a kitchen yana wanke hannayansa.
Dai dai lokacin da Nadrah ke shigowa kitchen ɗin, tayi wanka ta chanza kaya zuwa doguwan rigan material, tayi rolling ƙaramin mayafi a kanta.
Ƙamshin turaransa tafara ji haka yasa ta tsaya chak tare da ɗago manyan idonta, karaf idanuwansu ya sauka cikin na juna, matsa masa tayi daga hanya cikin rarrabewa murya tace
“Sannu… da zuwa” ɗauke idonsa yayi daga kan labbata, yadda tayi maganar kawai cike da yarinta, guntun tsaki yaja a ransa yana faɗin they would only carry her corpse the day he says he will sleep with her.
Bai ko sake kallon ɓangaran da take ba ya wuce, cikin juriya da ƙarfin hali ta kuma cewa “abincin ka dinning.”
Bai waiwayo ba kamar yadda bata iya jin ya amsa ba, sai da taji ya shiga ɗaki sannan ta samu natsuwan ƙarasa ciki, tuwan ta zuba dai dai yadda zata iya cinyewa sannan ta lallaɓa ta koma ɗaki.
Tsaye yake a ƙasan shower ruwa na dukan kansa, zuciyarsa a jagule yake, tunani mai tsawo baya iya yi akan damuwansa, amma kowane drop na ruwa kamar yana wanke wani ɓangare na nauyin da yake ji a zuciyarsa.
Ya ɗau tsawan lokaci a haka sannan yayi wanka ya fito.
Jikinsa ya goge sannan ya shirya cikin ƙananan kaya brown ɗin riga da farin wando sunyi masa kyau matuƙa.
Yana fitowa akan kyawawan kulolin dake jere a dining idanshi ya fara sauka, ƙafafunsa suka jashi zuwa wajan batare daya ma lura ba, a hankali yaja kujera ya zauna yana tsina fuska.
Ganin tuwo yasa shi ɗan waro idanu, lokaci ɗaya kuma ƙamshin miyan yashiga hancinsa, yunwar da yake ji ce ta ƙaru take ya haɗiye miyau.
Guda ɗaya ya zuba sannan yasa miya, fuskansa a yamutse ya ɗiba kaɗan ya kai bakinsa, daɗin daya bazu a harshensa ya wuce tunaninsa, sake diba yayi a karo na biyu tare da lumshe idanuwan sa a hankali, zuciyarsa ta cika da mamaki wannan ƴar yarinyan ce ta iya girki haka.
Wasa-wasa sai da Faruq yaci tuwo malmala biyu, ya haƙura ne badan bakinsa ya ƙoshi ba sai don cikinsa ya cika.
Ɗaki ya koma yayi brush sannan yayi alwala jin an fara kiran sallan magrib, sai da ta tabbatar yayi nisa sannan ta fito, sosai taji dadi ganin yaci abincin har hakan ya bayyana a kan fuskarta.
Kitchen ta kai kayan ta wanke kafin ta koma ɗaki, Faruq bai dawo ba sai wajan ƙarfe tara, yana shiga ɗaki kayan jikinsa kawai ya sauya ya hau gado saboda baccin da yake ji.
********
Cikin kwanakin nan sosai ya maida kansa busy kwarai, duk wani tunani nasa da kulawarsa na ga company, ya kanyi kwana uku zuwa huɗu bai sakata a idonshi, tana tashi da wuri ta haɗa masa breakfast kuma kafin ya dawo tayi girki ta ajiye masa.
Zuwa yanxu ta saba sosai ta mutanan gidan, ko taje waja Mami data lura ya kusa dawowa dake komawa ɓangaransu ta shige ɗaki, su Zaina sun koma makaranta, sai gidan ya rage daga ita sai Mami dan Abu babban mace ce sosai aikin gabanta kawai takeyi.
A haka suka kwashi sati uku, yau ta ɗan makara da sauri tayi wanka ta shirya kanta cikin wata red ɗin atampa me ash ɗin ado ɗinkin riga da siket, sunyi mata cif a jikinta.
Dankalin ta fara ferewa tanayi tana kallon lokaci, sai da ta fara soyawa sannan ta ɗora ruwan tea ta haɗa kayan ƙamshi, tana aiki ta tunane tunane, ta saƙa buri da yawa a cikin rayuwanta amma ƙaddara ya ruguza mata komai.
Bata ɗauki lokaci ba ta gama har soya kwai, ta zuba tea ɗin a flask ta haɗa da dankalin ta fita dashi dining.
Ajiyewanya yayi daidai ta fitowansa, fuskarsa mai cike da haiba da kwarjini tana nan yadda take babu fara’a ko walwala, sumar kansa zuwa ta fuskarsa nata sheƙi tare da fidda ƙamshin hair mist mai kwantar da hankali.
Idanunsa ya bude a kanta a hankali lokaci ɗaya kuma ya ɗauke su saboda ko ɗan mayafin da take sakawa ma yau babu, sannu a hankali ya tako zuwa dining ɗin, ta ɗan matsa gefe tana faɗin
“Good morning”
“Morniny.” Ya amsa lokacin da yake zama, kitchen ɗin ta koma a nan ta zauna ta karya, koda ta gama abin da zatayi bata fito ba sai da taji fitarsa kafin tazo ta tattara wajan.
********
Shaƙuwa da ƙauna ce ta ban mamaki ta shiga tsakanin Baffa da Nafisat, idan ka gansu zaka ɗauka sunyi shekaru tare suna soyayya, duk da kasancewar shi miskili ita kuma mai yawan magana, amma sun iya zama da junan su.
Zaune take a ɗan stool ɗin dake gefen gadon, taci kwalliya ta zuba masa ido, sannu a hankali yake buɗe idansa tana murmushi tace
“Good morning Oney.”
Ɗan murmushi a kan fuskarshi cikin murya irin na wanda ya tashi a bacci yace “irin wannan kyau haka.”
“Thanks oney, ka tashi ka shirya mu karya, dan ni na fara jin yunwa.”
Hannu ya kai ya goge idonsa tare da tashi zaune yana faɗin “yunwa da wuri haka ko dai kin shirya wani abu?.”
Nafisat ta ɗan juya idonta sama da ƙasa ta kama hannunsa zuwa banɗaki “Kayi sauri ka shirya ina jiranka.”
Shi irin mutanan nan ne masu daɗewa a wajan wanka, kafin ya fito ta ajiye masa kaya kaftan yanayin irin atampar dake jikinta, ya shirya ya feshe jikinsa da turare sannan ya nufa farlorn.
Da mamaki yake kallon decoration ɗin, an ƙawata parlorn da balloons ga wani ɗan ƙaramin cake data shirya haɗe da breakfast.
Dubansa ya mayar gareta har yanxu yana mamakin yaushe ta shirya wannan abun, ƙarasowa tayi gareshi tare da rungume shi a hankali ta fara faɗin
“Happy one month anniversary to us Oney, it may seem like just a short time to some people, but to me, this one month has been filled with beautiful moments, laughter, and so much, every single day with you has shown me that I made the best decision of my life, thank you so much Ya ishaq, I Love You.”
Ƙara rungumeta yayi sosai a jikinsa “Love You to darling.” Yayi maganar yana sakar mata little kiss a goshinta.
********
Babu kowa a parlorn kuma tasan su Zahra suna makaranta haka yasa ta wuce ɗakin Mami kai tsaye.
A ƙofa ta tsaya tayi knocking daga ciki taji Mami na tambayar wane, ta amsa mata sanna Mami ta bata izinin shiga.
A tsaye ta sameta a jikin wardrobe taba shirya kayanta da aka kawo daga wajan wanki.
“Sannu da aiki Mami.” Ta faɗa lokacin data karasa shiga.
“Yawwa Nadrah, an fito.
“Eh Mami, ki barshi bari na ƙarasa shirya miki.”
“Yi zamanki nama gama.” Mami ta bata amsa tana rufe wardrobe ɗin.
A yalwataccen carpet ɗin dake ɗakin suka zauna Mami ta dubeta sannan tace
“Nadrah badai wata matsala ko?”
“Eh Mami babu komai.”
Idanta ne ya sauka kan wani frame dake wurin mirron Mami, hoton Faruq ne lokacin bazai wuce shekara sha biyar ba, ya sha ado cikin kaftan har da babban riga yayi kyau sosai, ta shagala a kallon photon har bataji shigowan shi ba.
A kanta idonshi ya fara sauka kafin ya lura da abin da take kallo, wajan mirron ya fara ƙarasawa yasa hannu ya juya frame ɗin ya koma kallon bango, ta wajan mami ya dawo ya kwanta sannan yasa kanshi saman cinyarta.
Ganin tana ƙoƙarin tashi yasa Mami faɗin “yi zaman ki.”
Ita kuwa ƙasan ranta ya cika da mamkin wannan taɓara, dama haka yake jibgege dashi yazo ya wani kwanta ma baiwar Allah ajiki.
“Mami inaso zanje kaduna gobe, kuma zan ɗan jima wata ɗaya ko biyu.”
Maganan shi ya dawo da ita daga tunaninta.
“Amma dai da matarka zaka tafi ko? Tunda zaka ɗaɗe.”
Da sauri ya ɗago ya kalla Mami, kansa ta cire ɗaga cinyarta tana faɗin
“Nadrah ki shirya tare zaku tafi kaduna goben.”
Duka kallon Mami suke yi amma babu wanda yayi magana, a hankali ya miƙe ya bar ɗakin ransa a ɓace………