Free chapter · Read without an account
PAGE 7
Saida suka shiga makaranta sukayi submitting assignment ɗin sannan suka wuto gida, gidan su Meela suka fara tsayawa ta ajje motarta sannan ta shaidawa umma zataje yiwa ya zeenah sannu da zuwa dukda basu da tabbacin ko sun iso din amma dai in ana nemanta tana can.
Da sallama suka shiga ba kowa a parlour amma yasha gyara ko ina sai kamshin turaren wuta da room freshener yake, akan kujera suka zube "ina ganin basu iso ba, barin ji suna ina?". Maesha ta fada tana dannawa yar uwarta ta Kira "hello ya zeenah kuna wajen ina yanzun?
"Ai kin gan mu nan har yanzu maesha, ba lalle mu samu zuwa yau ba saidai ko zuwa gobe in Allah ya kai mu.
"Kai ya xeenah dan Allah meysa Saida kika saka mana rai.
"Ba laifi na bane maesha wani aiki ne ya rike daddyn Nabil saisa.
" To shikenan ba damuwa da yau da goben duk daya ne, Allah ya kaimu. ta fada a sanyaye tana kashe wayar kamar zatayi kuka.
"Ya akayi ne?". meela ta tambaya tana gyara dankalinta ajikin mirror show glass din dake parlourn. "Wai cewa tayi baza su samu zuwa ba.
"Ba zasu samu zuwa ba kuma? To meysa?".
"Sai gobe wai". ta fada tana tashi kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki hular kanta ta cire tare da cire rigar ta ta ya zama daga ita sai dogon wando legging fari da milk colour vest. Maesha ba doguwa bace kuma ba za'a kirata gajeriya ba bata da kiba amma tana da shape din da ake kira da coca cola ga fatar jikinta kamar ta jarirai luwai luwai tsabar gyara da kula. Duk Inda ake neman mace full option a dai halitta Maesha ta kai harma ta zarce.
Ribbon din kanta ta cire take kyakkyawan lallausan dogon bakin gashinta ya sauka har Kan bayan ta daga gani kuma trimming ɗin sa take domin bakin gashin ya daidai ta.
"Ke kam maesha Allah ya sallame ki whl. Cewar meela data juyo tana kallonta.
" To karki cinyeni danya, sai kace yau kika fara gani na baki abun magana. ta fada tana debe kayanta tayi daki, meela tabi bayanta tana fadin yanzu saida kika yanke gashin nan
"Ni ina zan iya idan na barshi ma ba iya gyarawa zanyi ba, ahakama ni gani nake bai min ba tafada tana ɗan nannadeshi kasa kasa ta sa ribbon ta daure.
"Jin daɗi ne ya miki yawa whl Maesha, amma dukda haka wai ba za'a bar mana layi ba, mu ma muji da kan mu dole kema sai kinyi joining, in yar kwalliyar nan ce kice sai kinyi komai dake.
"Masu iya magana na cewa ko kana da kyau kara da kwalliya, kinga laifi na ne, kuma da kike gani mutum baya taba hada komai 100%, Ni kai na Nasan akwai abinda bana dashi, yanzu dai barinje in fadama ummu sun fasa zuwan ni ban ma san Inda ta shige ba, allah yasa dai tana nan". ta fada tana daukan ƙaramin dankwali ta yafa akanta
"To Ni dai barin jiraki anan. ta fada tana fito da wayarta a jaka.
Dakin ummu ta shiga ta sameta tsaye gaba mirror tana shiryawa. "Masa al Khair Ummu". Ta faɗa tana ƙarasawa.
"Masa an nur ya qalbi, hal adat al'an ?. Ta faɗa tana juyowa ta kalleta.
" Naam laqad ji'itu walam araka fiy saluni ma'a jamilat hiya fil gurfah, ta'ati litarhibi ukti xeenah walakin hum lan ya'tu qulta ukty xeena, annahum taajilu hatta ghadan". Maesha stated looking so sad.
"Min yakbiruka bi haza maesha ? "
" Inaha takbirni ummu.
" Mafi mishkila, Al yaum wa ghadan mutashabihan, la taqlak. Hal raayt ameer indama ta'ati ?
"la ummu aina huwa ?
"Zahabat ila suq maa abuk .
" Shikenan to ummu barin koma wajen meela, na barta ita kadai
" ki dauka maku abinci
" I'm ohk fa Ni bana jin yunwa.
"Haka dai kullum, to sai kiyi serving dinta ita.
Da to ta amsa Sannan ta fita, dakinsu ta koma tare da zubewa kan gadon , "Wash Allah na. Meelah dake chat ta kalle ta. "Miye ne?
"Ummu tace kije kici abinci.
"Saidai muje ki zuba min. Maesha ta harare ta tare da fadin, "Kin ma rainawa kanki wayo, gidan bakon ki ne? Ta fada tana miqewa zata fice Meela ta tashi ta biyo ta sai kuwa ta kara a guje.
Tana fitowa suka kusan yin karo da Ameer da ya shigo. Da sauri ya matsa yana faɗin, "Ahab ni na san ai sai ke galma galma.
"Ka shiga hankalinka dani kaga dai ban kula ka ba.
"Zaki sani ne whl, ta gaban goshin ummu yau kece agidan". Ya Ƙarashe yans duban meelah dake musu dariya.
"Kai za'a tambaya ai shikenan kuma tunda abokinka ya tafi malaysia aka daina ganinka umma ma sai tambayar ka take.
"Allah sarki umma whl ba haka bane kinsan muma anata fama jamb ya karato.
"Ahh kuma hakane fa ashe anzo gamawa to Allah yabada saa, mutumin naka kam ai yanzu yazama dan gari.
"Eh ai in sha Allah results na fitowa Nima can zan ware.
"Ai saidai ka ware bola dan ba inda zaka kana Nigeria.
"Saiki hana ai munafuka".
Dariyar mugunta Maeshan tayi kafin tace, Zaka ga kwarewa ta a munafurci kuwa, ke kuma aku Sarkin magana zaki karaso kunci abincin ko zaki tsaya kula malam zubairu.
Ba zato ba tsammani Ameer ya karaso ya cafki hannunta ya nurse Yana faɗin, "Waye zubairu?".
"Ni ce Whl nice zubaida, wayyoooo Ummu, hannu na ya ɓalle. Ta fada tana fashewa da kuka. Sakinta Ameer yayi suka shiga mata dariya shi da meelah.
Ummu ce ta iso wurinsu da sauri tana faɗin, "Kai meke faruwa ne?
Cikin kuka tace ummu "wai kawai dan nace zan fadawa Abbah Karya barshi ya tafi Malaysia sbd ba karatu zaiyi ba shine ya karyamin hannu, wayyo hannuna". Ta fada tana Kara volume din ihun nata.
"Kai Ameer meysa kuke wasan banza ne haka, Maganar baki bata isa bane ko ance ma karfinku daya.
"Allah Ummu sharri take min ga dai Meela a tambaye ta, sangartace kawai irin tata". Ya fada yana kunshe dariya ummu ta kai masa duka ya kauce yana fashewa da dariyar.
"Zaka hadu dani ne ke kuma mu ga hannun. Ta fada tana kama hannun Maeshan, wani ihu tasa kamar wadda ake yankan jikinta, buge bakinta Ummu tayi tana faɗin, "Mey haka ne Maesha kanki Daya ko bakiji yadda kike ihu ba muryarki na fita har waje" .
Turo baki tayi kana tace, "To ummu ciwo yake fa. Tsaki taja ta saki hannun ta wuce.
"Ameer ayi serving dakai?". Meelah ta faɗa tana daukan serving spoon.
"Yauwa ta gaban goshin Ummu". Ameer ya fada yana dawowa dinning ɗin, zama Maesha tayi tana Binsu da kallo saida meela tazo Daidai wurin Maesha batayi aune ba ta sakar mata dundu, "Wayyo ta balle min spinal cord. Ta fada tana dafe bayanta.
"kikara min dariya ki gani. Aikuwa kamar ta Kara zuga ta tayi dariyar ta shiga yi harda riqe ciki.
Chocolates Ameer ya zaro a aljihunsa ya miqa mata yana faɗin, "Yi shuru shalele ga wannan.
"Kana tunanin zaka iya ban cin hanci ne. Ta faɗa tana hararar sa haɗe da goge fuskarta.
"A bawa Meelah bakyaso kenan?". Saida ta murguda baki kafin ta tashi ta kwace ta bar dinning ɗin. Meela ta shiga dariya tana tsokanarta.
Suna gamawa suka dawo falon suka cigaba da hira, sallamar ya zeenah sukaji ai kuwa Maesha ta tashi da gudu ta rungume ta tana dariyar murna, itama dariyar take hadi da faɗin, "Ohh ni zeenah karyani ki huta kinji, kaga yam Matan ummu sai girma ake. Sake rungume juna sukayi cike da farin ciki, Ummu ta fito tana faɗin, "Muryar wa nake ji kamar tasu zeenah".
"Mune Ummu". Ya Zeenah ta faɗa tana gaishe da Ummu.
"Ni dama ban yadda da abinda Maesha ta faɗa ba wai kun fasa sai gobe kawai dai na mata shiru ne". Ta Ƙarashe tana amsa gaisuwar mijin ya Zeenah ɗin da suka shigo tare da yaran.
Nabeela ta taho wurin Ummu tana faɗin, "Oum Ina Abbah".
Ummu tayi dariya tana ɗaukan ta ta daura kan cinya kana tace, "Auran ne ya tashi kenan. Duk sukayi dariya cike da farin ciki kafin su Meela su shiga gabatar masu da abinci, Nabil yana makale da maesha suka wuce ɗakinsu Meela tabi bayansu. Can kuma ya Zeenah tayi joining din su bayan mijinta ya tafi, sun sha hirar yaushe gamu har Abbah ya dawo shi ma aka dora dashi, Meelah dai dai 10 Maesha ta rakata gida ta dawo.