Free chapter · Read without an account

PAGE 11

by SultyWrites · BELOVED HEARTS

Ko da suka koma gida aka buɗe kyautar da Momma ta bayar turaruka ne masu tsada da siririyar sarkar gold, sosai Ummu ta rufe su da faɗa akan karɓar kyautar saboda kayan sunyi yawa ai, ya Zeenah ce ta dinga bata hakuri tana faɗin hakan bazata Kara faruwa ba dan Allah kar ta fadawa Abbah, daƙyar dai ta hakura.

Da daddare bayan sunyi dinner Maesha ta samu Abbah a ɗakinsa, bayan yar hira irin ta tsakanin ya da uba, Abbah ya gyara yace, "Mamana yanzu ya karatun naku kuwa?

"Lpy kalau whl Abbah, komai yana tafiya daidai

"To Alhamdulillah haka akeso ai, ni ba dan kince iya diploma kike so ba ai da degree ɗinki zaki wuce gabaɗaya to amma duk ba laifi Allah ya amfani wanna ɗin ma.

" Ameen Abbah .

"Ummunku ta miki magana kan mutanan da suka zo dasu ne?

"A'a Abbah ".

"Eh wasu ne wai suka zo neman auranki........" Nan ya kwashe komai ya faɗa mata yadda sukayi sannan ya dora da cewa na bashi izinin zuwa wajen ki ɗin amma ni bance na basu ba kuma ni nace bana son a dinga min sintiri a gida in har kun daidaita shikenan yaje ya jira tukunna.

"Hakane, but Abbah karkace ko na fadama yadda zakayi ne, Abbah kaikace Karna Kula kowa saboda kar hakan ya taɓa karatu na, me sa shi za'a bashi izinin zuwa, shi ma ya jira mana har sai na gama in har zai iya din.

" Uwata baza ki gane matsin number mutanan nan bane, suna da naci kuma sun matsa sosai banason in samu matsala da wasu ta dalilinki saboda rayuwarki shiyasa na musu hakan, amma ke ai kinsan yadda zakiyi basai kin saurareshi ba amma ki kula karki yadda ku rabu ta hanyar da zai kullaceki kinji ko?"

"In sha allah Abbah ba za kaji wata matsala ba.

"Yauwa haka nakeson ji maman abbah tashi kije kinji, Allah ya muku Albarka gabaɗaya .

"Ameen abbah Saida safe. Ta faɗa tana tashi.

NOTE 

YAM MATA KARKUCE ZAKU WULAKANTA SAURAYI SABODA KUNA DASU DA YAWA KARKU YAUDARE WANDA BA YAUDARA BACE TAKAWOSHI WAJENKU DOMIN HAKAN ZAI IYA TAƁA RAYUWARKU SOSAI. AKWAI WATA DA TA WULAKANTA WANI BAWAN ALLAH TO THE EXTEND DA SAI DA YA MATA FURUCIN ITA DA AURE SAIDAI TAGA ANAYI HAR GABA IYAU BATAYI AUREN BA AN MASA NEMAN DUNIYA BA'A SAME SHI BA, IT'S TRUE LIFE STORY HAKAN YANA FARUWA BA BAYA FARUWA BA, AKWAI WANDA KASHE TA MA YAYI GABA DAYA SABIDA IYAYEN TA SUNYI REJECTING DIN SA YACE GWARA KOWA YA RASA. IDAN HARKIN SAN BAKYASAN MUTUM KO BAI MAKI BA TO NEMI HANYAR DA ZAKU RABU LAMI LAFIYA BAI KULLACEKIBA BAKI KULLACESHI BA. ALLAH YASA MU DACE.

MOHA

Ko da su faez suka dawo sun lura da canji a tare da moha domin shi kaɗai suka ga yana ta murmushi wanda har hakan yasa Faez yakasa yin shuru saida yayi magana. "Kai Moh yau kuwa anya lpy kake?

"Meka gani? ya tambaya still da murmushi akan face nasa.

"Naga Kana ta murmushi Kai daya kamar wanda yayi gamo.

Dariya ya sakar masa wadda ta sa Faez ya saki baki da hanci da hanci yana kallonsa, "Ehhh akwai buqatar in cigaba da tsayuwar ko na cikawa wando na iska, tabbas ba lpy ba". Ya faɗa da iyakar gaskiyarsa yana ƙoƙarin barin falon, tashi Moha yayi yana kai masa dukan wasa a dantsen hannunsa Kana yace "Kana da matsalar da ido da gulma whl.

"Maganar gaskiya fa, ni har yanzu ban yadda da kai ba whl, kawai dai in tayi wari maji.

"Ni dai tawa kamshi zatayi. ya fada yana shigewa daki, Kan gado ya fada tare da kallon number maesha da ɗazu ya saka numbersa awayar ta ya kira yasa sannan ita kuma ya goge mata tasa number. Kallon number yake kamar maeshan ce a gabansa can kuma ya danna save bottom sai kuma ya tsaya tunanin wani name tayi deserving murmushi yayi Kana yayi saving da HEARTBEAT 💓💓 sannan ya rufe wayar ya Ajje gefensa.

Shi dai faez ya kasa yadda da canjin da idonsa ya gane masa game da moha, wai yau moha ne yayi doguwar magana har haka dukda Yana doguwar maganar amma sai ya watsar da kai kafin ka samu amsa, amma yau shi ne harda dariya tabbas dawata akasa. A haka Nashed ya shigo ya sameshi nan yake labarta masa abinda Moha yayi kai su Faez duniya ba hutu😂

Nash ne yace to ko dai ya fara love ne?

Wani kallon Ka rainawa kanka wayo faez ya masa Kana yace wannan ja'irin bawan ne zaiyi wata soyayya bayan magana ma wuya take masa.

"Hmmmm kawai Nash yace yaja bakinsa yayi shiru.

WASHE GARI

Ameer ne ya shigo ɗakin da sallama. "Salamu alaikum!!

" Wa alaikum salam ameer, ina ka shiga tun dazu nake neman Ka.

"Me aka samu ne ake nema na haka, amma dake yanzu tun kafin ina manta ina maesha ?

"Tana daki mana.

" To tayi bako a waje

" Bako kuma waye ?

" Wani ne dai wai ko me ma sunan yauwa Nawab mailafiya, ALLAH ya Zeenah jin sa yafi ganinsa. Ya faɗa yana kunshe dariya.

" To ko shine Wanda jiya parents nasa sukazo wajen Abbah ? Zumbur ameer ya mike daga dan zaman da yayi a hannun kujera yana faɗin, "Aii aii kuwa ina zuwa barin kirata. Ya fada wucewa da sauri har yana tuntube da center table.

" Ameer Ameer, kaga dawo.

"A'a tsaya ina zuwa ya Zeenah.

Tashi tayi ta shiga wuce Ummu domin ta faɗa Mata, shi kuwa yana shiga ya sameta kwance tayi zurfi cikin duniyar tunani, lallabawa yayi ya kashe wutan ɗakin a zabure ta buga tsalle tana neman hanyar waje ta kwalla kiran, "Wayyoooo ummu.

Kunna fitilar Ameer yayi yana dariya yace, "Matsoraciya kawai. Robar swan din dake kan bedside ta dauka ta wurga masa, da sauri ya kauce still Yana dariya.

"Wai kai Ameer yaushe zakayi hankali ne ?

"Sai kin fara yi tukunna. Kwafa tayi tana komawa ta zauna .

" Ni fa dama kiranki nazo yi wai kinyi bako sunansa Nawab Mailafiya

"Allah yasa shine ma likitocin Aminu kano bame lpy ba, ameer kafita a idona whl. Ta fada a fusace. Dariyar da yake ta kunshewa ce ta kwace masa ya shiga yi.

"Ai sai ma kin ganshi, sunan sa ma ya fishi daɗi, ko me zakiyi dashi ma oho amma dai kije ki ganshi ko zai miki.

Sake kulewa Maesha tayi shi kuwa ya cigaba da zuba yana fasalta Nawab me lpy.

A fusace tace uban wa yace yana nema? cikin ƙoƙarin rike dariyarsa yace whl wai maeshat yace, harda kara wani shat.

" Jekace baku da wata maeshat a gidan nan

" Kika sani ko wanda sukazo wajen Abbah ne jiya.

Shuru tayi daidai lokacin ummu ta shigo. "Maesha kinyi bako a waje, Wanda sukazo wajen abban ki jiya Yana parlour ma.

Kamar zatayi kuka tace "Ummu nii....

"Shiiiiiiiii Maesha, tashi kije kawai nasan abbanki ya miki magana jiya ai.

Ba yadda ta iya haka ta miqe tana jan kwafa ta warci hijabin datayi sallah ta fice Ameer Yana faɗin baza ki dawo ki san gyara fuskarki ba, ta masa banza.

A zaune ta sameshi harda su babbar riga uwa mai zuwa daurin aure ko nadin sarauta, akalla zaikai 42yrs, a zuciyarta kuwa cewa tayi Inaaa tab wanna ai ubana ne. Ta fada tana karasawa ta durƙusa har kasa ta gaisheshi.

Da fara'a ya amsa yana washe baki, wuri ta nema ta zauna suka sake gaisawa kafin ya gyara zama ya zayyane mata duk yadda sukayi da Abbah jiya da kuma yadda akayi yasanta ta dalilin wani program da sukaje yi a gidan TV.

Jinjina Kai tayi Kana tace a gsky bazan boye ma ba, ni inada Wanda nai ma alqawarin aure kuma saboda dokar gidan mu na tsayar dashi harsai na gama makaranta , kar ma na rufe ma daga baya azo ana whl tlh.

Dan shuru yayi can kuma yace "Hakane Aysha naji dad'i dakika faɗamin gsky amma ba a saurin yanke hukunci, ki dai sake tunani. Ya karashe yana fiddo wani Kati a aljihunsa ya Ajje mata. "wanna number tace zan baki lokaci kiyi tunani duk abinda kika yanke kya fadamin in kuma naji shuru to Allah ya sa hakan shi ya fi alheri.

Saida ta maka masa harara a fakaice kafin ta ɗauki katin tai masa saida safe ta wuce, tana shiga ɗakin ta yaga katin ta wurga a dustbin ta fada gado tana dariya.

" Lpy kike ta dariya ko kun daidaitane. ya Zeenah ta fada itama tana dariyar

"Kai kema yaya Zeenah da wani zance kike, ina zan wani daidai ta da wanna abun kawai dai na masa kora da hali nasan na jefar da kwallon mangwaro na huta da Kuda, ni yanzu in aure zanyi sai in ɗauko wanda zai tsufa ya barni da kuruciya fisabilillahi.

"Ahh gsky to Allah ya kawo nagari wanda kike so yake son ki, wai wa yaga yan matan Ummu da soyayya. Ya zeenah ta karashe da sigar tsokana. Rufe fuskarta tayi da pillow tana dariya.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.