Free chapter · Read without an account

PAGE 17

by SultyWrites · BELOVED HEARTS

Zaune Momma da Hameedah suke a falo, Momma tace, "Hameedah baza kigayyaci kawar taki bane.

"Wa Kenan momma? Hameedah ta faɗa still tana chatting ɗin da take da ƙawayenta.

" Maesha mana". dagowa tayi kamar Mai nazarin ina ta san sunan ita tama manta da wata Maesha ta dai san tayi saving number ta kuma suna ganin status din juna amma basa wata magana ita hameedah kanta da fadi ita kuma Maesha batasan tayi magana Ka watsar ta kuma tunda taga bata Mata magana ba ai bata bukatar maganar Kenan shiyasa ta kama mutuncin ta.

"Ohhh momma whl na manta, kuma ma ai ba kawar mu bace.

"Amma ai ko dan mutuncin da yayarta suke da safna kya aika mata, ba sai ta muku ƙawance ba, kawaye ai basa yawa especially a biki.

" To momma ni ai bansan gidansu ba

"Ki tambayeta mana ba kina da number ta ba.

"Zan duba momma, yanzu ma dama gidan aunty safnan zani akwai sakon da zan karbo sai na fada mata, in ita zata aika mata to in ni zan kai ma sai ta min kwatance.

"Ba damuwa.

..................

"Hello maesha".

" Naam meela ykk ?

"lpy klau, kinga results ya fito kuma ance gabaɗaya na semester biyun aka saki".

"Ke dan ALLAH

" Whl, hala baki leqa online bane.

"Whl ba na kai, ke kin duba naki ni ne?

"Ni kinsan ai dama nawa email din baiyi activating ba ina ta cewa zan koma a duba min banje ba amma naji ana cewa fa na first semester din nan an raba C O kamar ruwan sha

" Innalillahi, barni haka Meela karki sa in kasa dubawa.

Dariya tayi tace, " To duba ɗin in kin duba ki kirawo ni.

Kashewa tayi ta kunna data ta shiga dubawa amma still nata baiyi uploading ba, kiran Meela ta sakeyi, tana dagawa tace, "Ya kinduba ne?

" To ai nima nawan ba'ayi uploading ɗin sa ba, yaushe zaki shiga school din muje tare kawai.

" Ina ga mu bari sai gobe ko jibi ko.

" Ke fa shriritar ki tayi yawa, dallah shirya gani nan zuwa, kinsan tunda kika faɗamin to bazan iya hakuri ba.

" Matsalata dake kenan azarbabi

"Naji dai, da zafi zafi ake dukan karfe ke dai shirya gani nan". Ta fada tana kashe wayar ta dauki jilbab dinta ta zira ta sanya canvas dinta ash kalar jilbab din, sannan ta dauki Jakarta da kudin mota da wayarta tayi waje, "Ummu zan shiga school yanzu, ance results ya fito kuma ni nawa baya nunawa, ummu kimin addua". Ta ƙarashe kamar zatayi kuka.

"Ai kullum ina maki Maesha saidai in ƙara.

"Yauwa ummu na, Allah ya bar min ke". ta fada tana kissing forehead dinta ta nufi waje.

"Amma a me zaki tafi sbd kinga tunda zeenah tayi complain abbanki yace ki dai na fita a kasa.

" To ni kam ummu ya zanyi wanna dan rawar Kan ba ya samu dama ba yaje ya bugata, ai saidai inyi haƙuri kawai". Ta fada tana hararar Ameer dake karatu sai a lokacin ya dago yace, "Dalla ban ma fiki iyawa ba, kuma ai bani nace motar tayi rashin lpy ba ko da sani na zan bugata ne".

"Ummu Allah ki shiga tsakani na da yaran nan kina ganin yana min rashin kunya ko.

"Rabu dashi, yanzu ya za ayi gashi abbanki bai kai ga dawowa ba ballantana ki ari tasa ko zaki jirashi ne.

"A a ummu ai gidansu meelah zan shiga dake itama tanada irin problem dina tare zamu tafi.

" Ohk to shikenan, ki kula da kanki, Allah ya miki Albarka.

"Ameen ummun Maesha, saina dawo".

"Dadinta mu ma ba tsine mana akayi ba". Ameer ya fada yana hararar maesha, dariya tayi ta masa gwalo ta fice .

MOHA

"Wai moh har yanzu Kana nufin baka bayyana Mata ba kuma kuke tafiya a haka, wai yaushe kafara rashin daukar shawara ne, ka tsaya ganin ruwa kwado ya ma ƙafa, kana ji kana gani wani zaiyi wuff da ita".

Murmushi moha yayi yana gyara zama yace, "Abbanta ai bazai bari ta tsaya da wani ba har sai ta gama makaranta kuma she has one year left, akwai wanda yaje kwanaki ma abbanta ya kora shi, kuma bara kaji mamy tasan ina santa kuma itama tana so na kawai bayyanawa juna ne bamuyi ba shima akwai ranar da nake jira".

Sakato Faez yayi yana kallonsa to Kai ya akayi kasan duk wanna ko itace ta fadama?

" Ko ɗaya, kawai dai nasa ana min monitoring duk wani moment nata ne ba tare da ita kanta ta sani ba.

" Abin naka azimun ne moha".

Murmushi yayi yace, "Duk abinda kake so dole ka nuna damuwa akan shi.

" To yanzu wace ranar kake jira?

"Kai fa ka iya sa ido irin ku ne ana ruwa suna irgawa, ranar birthday dinta nake jira, next month ne on 8 in sha Allah".

"Toooo, to ai sai kace proposed day kake jira".

Gyada masa kai yayi alamar tabbatar wa yana smiling yace, "I plan for that day

" To Allah ya nunamana". Nan suka koma Zancen tafiyar Nashed Switzerland Kan wani aikin da zai wakilci company Moha next week.


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.