Free chapter · Read without an account
PAGE 18
Fitowar su Kenan daga office ɗin head of department din su, kowacce Ka kalla fuskarta dauke da farin ciki, maesha duka nata A's ne daga A+ sai A- yayin da Meela take da B's da C ɗaya amma bata da CO. Ji sukayi ana kiran su ta bayansu suna juyawa suka ga Maryam ce course mate ɗinsu kuma kawar Hameedah ba, washe baki tayi da faɗin, "Kuma kun shigo duba results din naku kenan?
Meela tace, "Eh whl, kinga baiwar allah data kwaso ni nan ba shiri, daga jin an saki result ta hana kanta zaune tsaye". Meela ta fada tana nuna maesha
"Ai gaskiyarta ne kam, to yaya ba kaya dai ko?
Cikin farin ciki Maesha tace, "Inaa we are cleared ni duka ma A's na samu Meela ma kuma bata da carry over alhamdulillah, Amma kafin muzo kinga fargabar da nake". Ta karashe tana murmushi har hakoranta na bayyana, Maryam taji wani abu ya dunkule mata a makoshi, ba tun yau ba take cike da Maesha kawai dai tana nuna masu komai normal ne dan ta samu kusanci da Maeshan Dukda ma ba wani sakewa take da mutane ba kullum tana maqale da Meela ita kaɗai.
Dariyar yaqe tayi tace , "Ai dama haka ne, kai amma congratulations, na tayaki murna dan an zubar da gayu kasa wanwar amma ku Allah ya tsallakar da ku".
Meelah tace, "Hala kema kin dan kwasa ne".
Cikin halin ko in kula tace, "Kema kinsan ai baza ayi yawo tsirara ba, za dai muje muga abinda zai yiwu ".
"Ummm sai da ku, kuke sha'anin ku". Meelah ta faɗa tana dariya. Maesha tace, "To mu zamu wuce Maryam kar dare yayi sai anjima". Jin haka yasa Meelah ma faɗin, "To Maryam sai Anjima ki gaida gida". Ta faɗa tana wucewa.
Da harara Maryam ta bisu tana cizar yatsa, cike da mugun quduri tace whl sai naga bayan ki Maesha, in dai kere na yawo zabo na yawo sai na durƙushe ki". Ta ƙarashe tana jan ƙwafa sannan ta wuce.
NOTE
YAR UWA KARKI YADDA KI BAYYANA BAIWAR DA ALLAH YA MAKI KO TA KYAU KO TA ILMI KOMA TA MIYE KI BARI TA BAYYANA KANTA DA KANTA DAN A ZAMANIN DA MUKE HASSADA DA BAKIN CIKI YAYI YAWA TA YADDA HAR YA ZAMO KO TARE KAKE DA MUTUM BAYASO YAGA KA FISHI KO CIGABAN KA, BA KOWA NE YAKE DA MENTALITYN CEWA ALLAH NE MAI YI BA, SHI YAYIWA WACCAN KUMA IN YAGA DAMA NI MA ZAI IYA MIN, BA WAI LALLE ABINDA WACCAN TA SAMU NI NA SAI NA SAMU BA TUNDA BABIN QADDARAR KOWACCE DABAN TAKE. ALLAH YASA MU DACE AMEEN.
*CIGABAN LABARI*
HAMEEDAH
"Yauwa aunty safna kinsan gidansu wanna kawar taki wadda tazo gidan su momma ranar har kuka tafi gidanki tare
"Wai xeena kike nufi
" Su dai masu kamar sadakar yallan nan". Ta fada tana tabe baki dan itafa ba dan momma data matsa Mata ba baza ta wani gayyaci wata Maesha ba.
Safna tace, "Baki da mutunci Hameeda, wai sadakar yalla, to larabawa ne in gaya miki in baki sani ba".
"Whatsoever dai, ina ne gidan ?".
"Eh to na dai san wajejen kwanar Magi suke Amma ba zan iya ce miki ga layin ba, amma meya faru ?
"Wai momma ce tace a gayyaci wanna kanwar tata biki, wa ma take da suna?".
"Ke ya fa isheki, mai suka miki da zakizo kina irin maganganun nan, bana son irin haka gsky". Ta fada in a serious tone.
Hararar yayarta ta tayi a fakaice kafin tace, "Ummm ai dole kishigar musu, ni dai yanzu Kira kawar taki ta miki kwatancen gidan nasu in Kai mata in huta".
"Ai ni tsoro nake ma kije gidan, karkije ki zubar min da mutunci".
"In bakyaso ba shikenan ba sai ince da momma ke kika hana a kai mata".
Shuru Safna tayi kafin ta ɗan ja tsaki tace, "Mikomin wayar gata can a charge".
Tashi tayi ta ɗauko Mata wayar tana buntsire buntsire. Karba tayi ta kira ya Zeenah suka gaisa sannan tace, "kawata gashi ke kinyi nisa, dama bikin amra cousin dina za'ayi shine nace zan aikawa Maesha iv ta wakilceki tunda ke bakya kusa".
Shiru ya Zeenah ta ɗan yi tana nazari dan bata san ko ummu zata yarda ba amma sai tace, " Ba damuwa yaushe ne bikin?".
"Next week in sha Allah, ga gate pass din nata ma a hannuna, amma bansan gidan ba na san dai a nan kwanar Magi ne ko?".
"Eh anan ne bari na turo miki address ɗin, amma dan Allah idan akwai wani katin extra ki haɗa musu biyu saboda nasan Ummu ba zata bar Maeshan taje ita kaɗai ba amma in biyu za'a samu me rakata.
"Ahh ah ba matsala za akai mata biyun in sha allah.
" To shikenan nagode Safna, Allah ya sanya alheri ya basu zaman lpy.
"Ameen ameen ngd dear a shafemin Kan su Nabil.
"In sha allah". Da haka sukayi sallama ta kashe dake a handsfree wayar take Hameeda taji komai ai kuwa tana kashewa, tace "Aunty Safna ni fa Kati ɗaya ne a wuri na shi ma na wata ne na bata dan haka in har baza taje ba kar ma na wahalar da kai na".
Girgiza Kai kawai Safna tayi kafin tace, "Na wani event ne katin da zaki bata?".
"Na dinner ne". Ta fada a yaqune . Tashi safna tayi ta shiga daki ta ɗauko mata dayan ta bata, "Gashi nan saiki tashi kikai mata, zan tura miki address ɗin da ta Turo". Bata ce komai ba ta karba ta wurga a jaka sannan ta mike ta Mata sallama ta wuce.