Free chapter · Read without an account

PAGE 19

by SultyWrites · BELOVED HEARTS

Maesha na shiga gida ta daka tsalle ta fada Kan ummu tana dariyar farin ciki ta ce, "Ummu adduar ki ta karbu, Allah abun godiya ".

" To dagani, ko sai kin karyani zaki fada min abinda kika samo ".

Abbah dake zaune ya ce, "Rabu da ita uwata, faɗamin me muka samu".

"Bude masa wayarta tayi ta nuna masa results din nata a waya". Karba yayi ya duba, da farin ciki yace, "Inye my daughter, Kai Kai Masha Allahu uwata, I'm so proud of you Allah yakara ilimi me amfani, gsky kinyi kokari sosai dole ma in sake canza miki waya a matsayin gift, wacce kike so?".

"Abbah ko 11 pro ma in na samu ina so.

"An gama, in sha allah 11 pro tana hanya". Tsallen murna tayi ta rungume abban nata tana dariya ummu ma murmushi tayi tare da yi masa godia, ameer ne ya shigo ya dawo daga ball, "Wai me ake rabawa a gidan nan ne naji wanna gyaren ta cika mana gida da ihu".

Bata bi ta kan tsokanar tasa ba ta nufe shi da gudu tana nuna masa results din, karba yayi ya duba sai ya hau rawa tana masa waka su Ummu na musu dariya.

"Kaiii Masha Allah, ashe akwai ƙwaƙwalwa cikin wannan tozon kan naki?".

Haɗe rai tayi kamar ba ita ba tace, "kai ma aka samu ƙwaƙwalwa a cikin naka fankon kan ballatana ni, an gaya ma kai na da naka daya ne, tafi ka bani waje da Allah". Ta fada tana juyawa zata bar wurinsa, dungure mata kai yayi ya wuce ta kuwa kawo masa duka sai ya kara a guje ya wuce ɗakinsa.

Ummu ta girgiza kai tace, "Allah ya shirye ku ku dai". Abbah ya amsa da Ameen yana dariya.

Ɗakinta ta wuce ta fada a gado tana murmushi kamar wata sabon kamu tayi dialing number ya Zeenah bata same ta ba, "To sai wa zan sanarwa kuma ya tayani farin ciki?".

Moha zuciyarta ta kawo Mata, dialling number sa tayi amma har ta katse bai daga ba tana ƙoƙarin sake Kira dan tama kasa jira ya dawo da kiran sai ga nashi ya shigo.

" Hello Mamy". Muryar sa ta daki kunnen ta bata bari ya idasa ba tace "Guess what?"

"Saikin fada". yace yana relaxing kan kujerar main parlour cox daga jin sautin Muryarta tana cikin farin ciki.

"Bari dai kawai in turo ma ka gani". Tana fadin haka ta kashe ba tare data saurari abinda zai ce ba ta shiga WhatsApp ta tura masa results din, minti biyu tsakani sai ga Kiran sa ya shigo, " Congratulations My Mamy, results yayi kyau Allah ya kara basira, gsky kinyi kokari sosai na taya ki farin ciki".

"Dan dakyar, ban yi tunanin zan tsallake ba whl". Da haka suka shiga hira har akayi kiran sallar magrib sannan sukayi sallama .

Tana idar da sallah ta fito dan taya ummu shirya dinner buga kofa taji anayi tasan dai su Abbah basa buga ƙofa saidai kawai su bude su shigo to sai dai in bako sukayi, karasa wa tayi ta tsaya daga jikin kofar tace, "Waye?".

"Bakuwa ce". Jin muryar mace yasa ta bude, hameeda ce tsaye tana pressing phone dinta, taji an bude kofar dagowa tayi suka haɗa ido da maesha, ta mata murmushi tana faɗin, "Kece ashe, shigo mana". ta fada tana bata hanya.

wucewa tayi ba tare da tace komai ba ta karasa ta zauna Kan kujera tana bin ko ina da kallo, maesha isko ta tana fadin, " Sannu da zuwa hameedah yasu momma ?".

Saida ta yatsina kafin tace, "Lpy kalau itace ma ta aiko akawo maki Katin bikin cousin din mu amra".

Ummu ce ta fito tana fadin, "Maesha ke da waye?".

"Ummu baquwa mukayi, kanwar aunty safna ce kawar ya Zeenah". Maesha ta fada tana kallon ummu.

"Ina wuni". Ta fada, a zuciyarta tana fadin ashe de ba banza ba take da kyau kamar aljana ashe gado tayi dan ita sai take ganin ummu ma tafi Maesha kyau.

"Lpy kalau, yasu mamar taku?".

"Duk suna lpy sunce a gaisheku.

"Muna amsawa". ta fada fuskar ta dauke da murmushi ta juya ta koma kitchen din, Maesha ta miqe tana faɗin "Bari in kawo maki ruwa.

"Aa da kin barshi tafiya ma zanyi, a hanya nake.

"A'a dan Allah ki tsaya". ta fada tana wucewa ciki da sauri.

Binta da kallo Hameedah tayi tana ayyane ayyane, ashe dai bata ga komai ba a ranar da sukaje gidansu, haka Allah yayiwa yarinyar nan baiwar kyau, gsky ta more dan ko ita da take yar uwarta mace saida ta yaba. Dowowar maesha ya katse mata tunanin ta, robar ruwan take kokarin ajje Mata da cup gashinta ya kunce, sakin baki da hanci hameedah tayi tana kallon ikon Allah. Ajje ruwan tayi ta shiga kokarin daure gashi dan ita in dai ba fita zatayi ba to bata sawa kan ribbon, ganin tana kokawa da gashin kuma tana kokarin zuba Mata ruwa yasa hameedah cewa "Barshi kawai zan zuba.

"Thank u". ta fada tana komawa ta zauna ta karasa daure gashin. Hameedah dan ta sake tabbatarwa gashinta ne yasa tace, "Dan Allah a ina ake miki wannan fixing ɗin gsky yayi kyau.

Murmushi tayi tace, " Ba fixing bane gashi na ne".

"Kai dan allah, to gsky zaki sammin kadan in jona". dariya tayi kawai, hameedah dake da niyyar tashi sai gashi ta shafe wurin 30 mins, "kinga barin baki katin nan, guda biyu ne ke da yar rakiya ya Zeenah tace mamarku baza ta bari kije ke kadai ba saidai a bada guda biyu".

karba tayi da fadin, "Hakane Kam ashe kunyi waya.

" Aa aunty safna ce takirata don tai mana kwatancen gidan.

"Oh Allah sarki to barin Kira ummu kuyi sallama". Ta ɗan daga murya tace ummu zata tafi".

Fitowa Ummu tayi tana faɗin, "Hameeda har zaki tafi ?

" Eh ummu .

"To shikenan ki gaida gida da su mamantaku kinji .

"Zasuji kuwa in sha allah.

Maesha ta tashi ta rakata har bakin kofar parlour sukayi sallama ta wuce dawowa tayi tana fada wa ummu dalilin zuwan hameedar, wayar ummun dake Kan dinning tayi Kara maesha taje da sauri ta duba ganin ya Zeenah ce yasa ta amsa, bayan sun gaisa take fada mata dazu ta neme ta ta fada Mata results dinta ya fito wayarta bata shiga nan take ce mata hameedah ma kanwar safna tazo.

" Eh nima ai akan maganar nakira ina ummu ?".

"Gata". ta fada tana mika Mata, karbar wayar tayi ta juya ta bar wurin, kusan minti biyar ta fito ta miqawa Maesha wayar ta a fadin, "ungo riqe, zakije amma sai na tambayi abbanku in ya barki to, wanna katin kuma ki ajjewa Jamila shi sai kuje tare.

Da to ta amsa tana karbar wayar ta koma daki.

Aikuwa sam Maesha bata fadawa moha zancen zuwan hameedah ba domin suprise take san masa tunda har dinner ne ai tasan zaije kuma cousin dinsa ce.


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.