Free chapter · Read without an account
PAGE 25
Wata irin soyayya ake yi ta bugawa a jarida tsakanin maesha da moha kamar zasu hadiye Kansu ta waya, ita dai Maesha bata taɓa soyayya ba bata santa yadda ake ji a sai akan moha shi ya nuna Mata Mai ake nufi da so madarar sa shiyasa duk ya susuta yar baiwar Allah.
Hameedah ce zaune agaban Maryam tana koro Mata jawabi ta rufe da faɗin, "Wallahi nayi tunanin, nayi tunanin babu wata hanya, moha bai bani wata dama ba, ni kuma gashi duk daran duniya kamar ana kara huramin wutar sonsa haka nakeji.
Maryam ce tayi wani murmushi tana sake saka a ranta tace wanna wata dama ce da zanyi amfani dake na wargaza farin cikin maesha lokaci guda, gyara zama tayi ta ce, "A gsky naga sokancin ki Hameedah kuna tare da namiji irin Moha amma kiyi saken da zai sabule miki".
"Wani irin sake Maryam, moha fa ba irin mazan da kike tunani bane, nayi iyakar bakin ƙoƙarina, saboda shi na baro gidan mu gaban iyayena na dawo gidansu, duk wani abun da zai ja hankalin da namiji nayi ke dai kinsan yadda in na fito samari ke daga min tuta to amma whl shi Kamar dutse haka yake, sam babu wani abun dake motsa masa zuciya. Ke kadai kikasan duk sirrina Maryam dan duk kawayena ina musu karyar soyayya muke ni da moha amma yanzu komai ya lalace sai kirana suke suna min jaje harda masu gaya min magana a fakaice duk saboda proposing ɗin mayyar can da yayi. Dan Allah ki ban shawara Maryam,mai zanyi ne Ni?".
Nisawa Maryam tayi tace, "Zamuje Inda zaa share maki hawaye Hameeda, akwai wani boka mai tsuburi nakan haye nasan da munje matsalarki takawo karshe.
Cikin zumudi tace, " To yanzu yaushe zamuje?"
" ummm ki bari zan duba kinsan yanzu mun koma school ba lokaci sosai.
"Haba mana dan Allah Maryam nice fa, saidai in bazaki taimaka min ba, amma whl ko mai zan iya yiindai zan samu moha na yarda in rasa komai.
" shikenan to, zanyi cancelled din lectures din da nake da ita gobe kizo by 10am sai muje.
" yauwa kawata ko ke fa Nagode sosai.
NOTE
Whl jama'a mu farka in dai har zaka dangana lamarin Ka da wanin Allah to kuwa baza Ka taba ganin daidai ba, ku da kanku ku san cewa babu mai yi sai allah tunda ko barinka akayi da faduwar rana da fitowarta kasan whl Allah yafi karfin wasa. Kuma in dai akan saurayi zaki kauce to ki sani Allah ya riga da ya rubuta miki mijinki tun kina cikin ciki, ki kwantar da hankalinki kiyi addu'a kowa da rabonsa kuma kowa da lokacin sa kamar yadda qaddarar kowa take daban, wani baya taba auran matar wani duk wanda Allah ya baki shi ne rabonki, idan da a karshen duniya mijinki yake to whl sai Allah ya kawo sanadin da zai zo gareki so just pray my sister, Allah yasa mu dace, AMEEN.
Hameedah ce da Maryam zaune gaban boka Mai tsuburi bashi da kyan gani baki Kirin dashi fuskarsa kamar faifai jikinsa kuwa kamar sandar rake, magana yafara kamar haka, "An gaya mana abinda yake tafe daku me kikeso a masu?"
Maryam ce ta riga cewa so muke a musu farraqu boka".
" ha ha ha ha". Ya fara wata dariya da saida jejin ya ansa, wani surkulle ya yayi kafin ya ɗago yace, "Ba zai yiwu ba".
Hameeda ce ta kalli Maryam da alamar tambaya irin ke dama kinsan akwai abinda bazai iya yi din nan ba kafin ta ce, "Haba Malan taya zakace bazai yiwu ba saidai in bazaka iya bane, amma meye sa ake zuwa wurinku ai saboda babu abinda yake gagarar ku ne".
wata uwar tsawa ya katsa Mata da batasan lokacin data dale Kan cinyar Maryam ba, "Keeeeee ɓatacciya, ki iya bakinki ba komai ake faɗa mana ba, aiki ne ba zai yiwu ba especially akan yarinyar tunda aljanu ne zasuyi aikin ita kuma tanada tsari sosai bata wasa da sallah akan lokaci sannan tana azkar ɗin safe da maraice bata zama ba alwala ko da jini take, a karshe dai bata da abokin fada ballatana su samu shiga jikinta ta wannan dalilin, saidai kuma in shi kaɗai za'ayi wa".
Maryam tace, "To ai mu boka hakan ma yayi shi din a masa ya rabu da ita ya fita harkata in son samu ma ya haɗa mata da wulakanci da zai iya sa mata hawan jini".
"Ha ha ha, muguwa, ku ɗauka aikinki ya gama".
Cikin farin ciki tace, "To me za'a bayar boka".
"bakin dan akuya zaa bawa aljana yar masurutu.
" to ya zaayi abasu boka?". ta fada tana ture hameeda da har yanzu kusan rabin jikinta Yana Kan Maryam dan dama ita a tsorace take tunda ba saba zuwa irin wurin tayi ba .
Mika hannu yayi saiga wata kwarya ta faɗo ajjewa yayi a gabansu yace, "ku saka mata kudin a ciki".
Maryam ce ta kalli hameedah tace, "Kawo kuɗi?".
Hannunta na rawa ta sa hannu a jaka ta dumbuzo duka kudin bata tsaya irgawa ba ta saka a kwaryar, bat ta bace. Ai a dari hameedah ta suri jakarta da takalmin ta fara gudu Maryam na Kiran sunan ta amma inaaaa saida taji ta a cikin Mota sannan taji daidai, Maryam ta karaso tana Mata dariya, " Kai hameeda amma dai kin bani kunya whl". ta fada still tana dariya sai kuma tace, "Zaman duniyar nan fa is not for the weak dole ki karfafa zuciyar ki in dai kinason biyan buƙatar ki".
"Allah ya biya mana ke dai". Hameedah ta faɗa tana sauke numfashi, Maryam ta watsa mata wani kallon gefen ido tace, "Allah fa kikace? Wanda yasan da Allah ai ba zaije in da mukaje ba, ke dai Allah ya yafe mana ".
(Kai wannan Maryam, wannan Maryam ta cika shaidaniyar ƙawa me jefa mutum a rami, to ta Allah ba taki ba in sha Allah ba abinda Maesha zata gani sai alheri.)
MOHA
Yana cikin bacci ya fara wani mugun mafarki da maesha wai suna tsaye tana masa murmushi sai ya fara baya baya rami ta gani a bayansa ta fara kuka tana miqo masa hannu shi ma hannun yake miqa mata amma bai daina tafiya ba harya fada ramin yaji ta kwala masa Kira juyawa yayi acikin ramin hameeda ya gani rike da wani jug tana masa dariya jini na fita ta tsakanin hakoranta.
Firgigit ya tashi da addua abakinsa La ilaha illallah, auzubi kalimatillahi tammat min qadabih wa iqabihi wa sharri ibadih wa min hammazatish shayadin wa an yahdarun, allahumma Inna naj aluka fi nuhurihim Wana uzubika fi shururuhim. Ya Ƙarashe karanto addu'oin yana haki kamar wanda yayi gudun kilometer dubu, ga wani gumi da ya shiga tsatsafo masa, kallan su Nashed yayi baccin su suke hankali kwance, tashi yayi yaje ya dauro alwala yazo ya fara nafilfili, ko da ya idar addu'o'i ya musu sosai har da Hameedan sai da ya mata addu'a in itama wani sharrin ke bibiyarta Allah ya kareta.
Janyo wayarsa yayi a lokacin 3am, number maesha ya fara Kira fitowar ta Kenan daga toilet fitsari ya tashe ta karasawa tayi ta dauka hello, idonta a rufe saboda bata so baccin ya wartsake tace, "Hello qalbi".
"Sorry Angel, na tasheki kina bacci ko?". Dan zama tayi bakin gadon tana faɗin, "A'a fa, dama na tashi nayi fitsari zan koma kuma naji kiranka, amma lpy bakayi bacci ba har yanzu?
Ajiyar zuciya ya sauke kana yace, "Bakomai, Amma tunda idonki biyu kije kiyi alwala ki yi nafila ki roka mana Allah kariyar sa kinji Angel".
A sanyaye ta amsa da, " To qalbi amma ni duk ka sani a damuwa, gashi har a muryarka naji kamar akwai damuwa".
Murmushi ya ɗan yi dan duk bayajin dadin jikinsa yace, "Karki damu bakomai in sha Allah, ke dai kiyi abinda na faɗa Miki, saida safe kinji".
"Tohm". Ta faɗa kamar wata doluwa shi kuma ya kashe wayar.
Bayin ta koma ta sake alwala dauro alwala ta fito ta sanya hijab din sallarta ta tada salla, har akayi sallar asuba tana kan abun sallar ta tashi tayi sallar tayi azkar ɗin safe, wuraren 6:18am ta sake Kiransa, shi ma idonsa biyu dan ya kasa komawa, sun ɗan yi magana ta kusan 30 minutes kafin suyi sallamar ta tashi ta fita ta fara aikin gida dan morning lectures gareta amma tasan idan ta dawo ta fara bacci sai Allah.
Moha dai bai fadawa kowa mafarkin da yayi ba saidai daya dawo daga aiki zai tsaya yayi ta rabawa almajirai sadaqa dan whl har yanzu mafarkin yaqi gogewa a zuciyarsa.
Sati daya, sati biyu sati uku suka wuce Hameedah taji shuru gashi yanzu in ma tana waje Moha baya zama, ita tarasa Kan wanna abun dan haka ta dauki kafa ta koma gidansu Maryam ta labarta Mata halin da ake ciki, Maryam tayi shuru cikin jimami kafin tace "Ki shirya mu koma wurin boka gobe".
Haka kuwa akayi washe gari suka koma amma ba boka ba dalilinsa haka suka dawo Hameedah na kuka yana fadin Maryam ta kaisu wurin dan damfara, dakyar Maryam ta kwantar mata da hankali akan zata nema masu wata mafitar ta saurareta, da haka suka rabu.
Faez dai kam ya kan zo wajen meela zance but maesha ba dama saboda Dokar Abbah, duk wanna soyayar saidai awaya ganin haka yasa Moha ya nemi su dinga haduwa a school time to time, dukda tsoron Kar Abbah ya samu labarin tana haduwa da wani awaje da take sam bata iya Musa masa ko ta hanashi.
Yau ma kamar kullum suna zaune a cikin Motar sa da misalin karfe biyar dan tashin sa daga aiki kenan yace mata zai biyo dan tace masa sai 6 zata bar school, tana da lectures ɗin 4-6 amma haka ta fito da uzurin zata amsa waya ne. Sanye take da Black jilbab me Noes mask ta sauke mask din saboda boabab drink ɗin da ya zo musu dashi suna sha, a hankali yace, "My angel ".
Ji yadda ya kira sunan in a serious tone yasa ta amsa da Na'am qalbi". Tana me bashi dukkan hankalinta.
"Ina so in zo wurin Abbah". Zaro Ido tayi cikin tsoro tace, "Nima zan so hakan. Amma dan Allah ka rufamin asiri kar Abbah ya san ina saurarar wani dan tsaf zai iya datsemin karatun nan yace in hakura dashi inyi auran tunda shi nasa a gaba kaga kuma saurana baifi nine months bane, kar wahalar da nayi a baya ya tashi a banza. Ni kai na nasan ina fuskantar qalubale amma na jure tunda dai an kusa kai karshe".
Murmushin gefen baki yayi kana yace, "Wai kina ganin wanna haduwar da muke wataran abbah ba zai samu labari bane ? Hmmmmm". Ya dan girgiza kansa ya ce.........