Free chapter · Read without an account
PAGE 26
Ya dan girgiza kansa ya ce, "trust me abbah bazai katse maki karatu ba nasan mai zanyi".
" Amma f.....". Shiiiiiiiiiiii ya dora yatsansa akan bakinta, "Karkice komai just trust me".
" Shikenan , Allah ya bamu Sa'a". Daga nan suka cigaba da hirar su har lokacin tashin su yayi sukayi sallama ya tafi.
Washe gari bayan sunyi sallar magriba ya ɗauki Nashed suka tafi gidan su Maesha kasancewar Faez baya nan ya samu kiran gaggawa daga hospital.
Sallama sukayi mai gadin ya fito suka gaisa sannan ya ce, "Da allah me gidan fa?".
"Yana ciki".
"Ko zaka iya mana sallama dashi da Allah".
"To ba damuwa". Ya faɗa yana shigewa. Knocking ƙofar falon yayi, Abbah yace Ameer duba kaga wake knocking?"
Tashi yayi ya nufi ƙofar yana buɗewa yaga me gadi tsaye, "lpy dai?". Ameer ya tambay yana kallon me gadin.
"Dama wasu samari ne awaje suke sallama da alhaji.
"Su waye?
"Eh to gsky nima bansansu ba, amma dai suna waje.
" To jeka, ina zuwa". ya fada yana sakin kofar ya koma ciki, "Abbah Kayi da wasu zasu zo ne.
"Ah ah banyi da kowa ba, Wasu ne sukazo ne?
"Eh wai wasu samari ne a waje suke san ganinka". Dan jim yayi Kana yace, "Je ka shigo dasu".
Da toh ya amsa sannan ya sa kai ya fita, a jikin motar ya same su sun sha manyan kaya, "Assalamu alaikum". Ya fada Yana mika masu hannu suka gaisa sannan yace, "Kune kuke sallama da Abbah .
" Eh". Moha ya fada.
" Ohk yace ku shigo". Ya faɗa yana wucewa gaba, bin bayansa sukayi har parlourn inda suka tarar da Abbah zaune. Durƙusawa sukayi suka gaishe dashi, da fara'a ya amsa musu, Ameer dai kitchen ya wuce in da ya tadda su suna shirya abincin dare, Maesha dake tsaye tana marinating kifi zatayi grilling ɗin sa hannunta duk ya ɓaci ganin shigowarsa yasa tace, "Yauwa Ameer dan gyaramin dankwalin kai na kar ya fado.
"Ke da Allah rabu dani. Ummu kunyi baqi fa".
"Baqi kuma su waye?".
"Whl ban sani ba, samari ne dai su biyu suna falo ".
"Wani falon?".
Saida ya balla mata harara kafin yace, "Falo nawa ne damu a gidan nan".
"Innalillahi, Allah yasa dai ba daɗewa zasuyi ba in ba haka ba ai ni na kamu a kitchen din nan".
Ummu data haɗa refreshment ta miqa masa tana faɗin, "Ungo miqa musu wannan". Karba yayi ya fice.
A bangaren su moha kuwa bayan gaisuwa abbah yace, "Sai dai ban shaidai ku ba yan samari".
Bayanin kansa moha ya farayi kafin ya dora da bayanin abinda ya kawosu sannan ya dora da faɗin, "Abbah kafin nazo nayi bincike na kuma san dokar gidan ka ba kuma nazo bane dan na karya ma, nazo ne dan a san dani a kuma bani damar neman auran, zan iya jira har lokacin da zata kammala karatun".
Nisawa Abbah yayi yace, "To Malam Muhammad ban tari numfashin Ka ba, amma ni ban yiwa yayana dole kamar yadda nake basu umarni suke bi, haka Nima nake bin abinda suke so, duk da kuwa naji Ka kwantamin arai kuma har cikin raina naji zan iya baka auran A'isha, amma da sharadi daya wato Saida yardarta da kuma amincewarta, idan har ta amince to zan yarjema ka turo iyayenka ayi magana amma ban yarda da zuwa taɗi ba saboda hakan zai iya distracting din karatun ta takasa maida hankali, dan haka haɗuwa daya zakuyi in har kun daidaita kanku to shikenan".
Cikin jin dadin yadda abun yazo yace, "Hakan ma nagode Abbah, Allah yakara lpy da nisan kwana me albarka".
"Ameen ya Allah, ga wayar nan kasa number Ka a ciki duk yadda mukayi da ita zan kiraka". ya fada yana mika masa wayarsa.
Karba yayi da hannu biyu ya saka masa sannan ya miƙa masa wayar, karba yayi ya miqe yana faɗin, "Zauna bari ai mata magana sai tazo ku gaisa". Ya faɗa yana miqewa a lokacin da Ameer ya shigo da refreshments ɗin.
Wayar Maesha Moha ya Kira Yana murmushi, tana wanke hannunta a sink taji ringing ɗin wayar, ko ba'a faɗa ba tasan shi ne dan haka ta zare hannun nata tana gogewa da towel ta fakaici idon ummu ta dauka tana wucewe bayan kofar store, "Hello qalbi".
"Na'am Angel, gani fa nazo taɗi". Dif yaji kamar daukewar nefa, "Me....me kace?". ta tambaya da rawar muryar.
"Ki nutsu mana Angel, gani fa a parlourn gidanku..." Bai karasa ba taji muryar Abbah yana Kiran sunanta. "Mamana, kina ina ne?".
Juyowa tayi da sauri tana kashe wayar tace, "Gani abbah".
"Kije ki shirya kinyi baki, suna parlour".
A ɗan tsorace take kallon abbah kamar wata marar gsky kafin tace, "To tou abbah gani nan zuwa".
"Ki kwantar da hankalinki ki nutsu kinji, karki damu abin da kike so shi zan miki". Gyada kai kawai tayi shi kuma ya juya ya fita, Ameer Maesha ta dannawa Kira yana dagawa tace, "Dan Allah ameer ka daukomin hijab adaki please". Ta faɗa tana satar Kallon ummu taga aikin ta kawai take kamar bataji ma me abban yace mata ba.
Kashe wayar Ameer yayi ita kuma ta tsaya jiransa, ba jimawa ya shigo da hijab ɗin ya miqa mata, karɓa tayi ta sanya sai kuma ta tsaya dibi dibitu, Ameer yace, "Hala sai an daukeki an kai masu parlourn ko?".
Hararar sa tayi sannan ta fice, tunda ta shigo parlour idonsa akanta zama tayi tana raba Ido, ya ɗan zakuɗo yace, "Yau gani ga Angel a cikin gidan su, ai dama na faɗa Miki".
"Na jinjina ma jarumi na". Ta faɗa tana juyawa Wurin Nashed suka gaisa yace da Moha zaije daga waje ya jira shi ya amsa da to shi kuma ya fice.
Maesha ta juyo garesa kana tace, "Wai dan allah me kacewa abbah?".
"tsoron dai". ya faɗa Yana dariya sannan ya zayyane Mata duk yadda sukayi.
Ajiyar zuciya ta sauke, "but kace abbah yace haduwa ɗaya kawai zamuyi wato ta yau kawai, shin menene cigaban to?". Ta fada ƙasa ƙasa.
"Akwai mana, yanzu dai anyi me wuyar tunda yace na turo manya".
Sun ɗan jima kafin ya mata sallama ta rakashi ya tafi, abbah bai neme ta a ranar ba sai a washe gari ya kira ta, bayan ta masa barka da war haka ta zauna Abbah yace, "Jiya ya kukayi da baqin naki?".
A kunyace ta sunne kai tace, "Munyi magana Abbah kuma na amince Allah ya zaba mana abinda yafi alheri".
"Mamana kin tabbata ya miki, kun daidaita?".
Cikin kunya ta gyada Kai alamar eh, yayi murmushi yace, "shikenan to zan nemeshi in sha allah". Da haka ta tashi ta wuce daki .
Tana fita Abbah ya kira moha ya sanar masa yadda sukayi sannan ya sanar dashi ya turo iyayensa, aikuwa baiyi ƙasa a guiwa ba ya kwashu su Faez sukaje suka samu papi a bangarensa suka sanar masa. Cikin farin ciki papi yace, "To alhamdulillah dama abinda na dade ina jira Kenan, Muhammad Kai kadai Allah ya bani zanso ganin yayanka da raina, dan haka in sha allah zan yiwa sauran iyayen naku magana sai suje gidan su yarinyar ayi magana ko".
Faez ya dan sosa keya yace, "To papi nima dai dama umm, akwai... Akwai.." sai kuma ya kasa ƙarasawa moha ne yace, "Papi wai shi ma ya samu matar ne kuma duk neighbor's ne, kawaye ne ma da ita yarinyar da za'a je tambaya min shine dai yake ta wannan nuqu nuqun".
Faez ya sake kasa da kai tare da mintsinin Moha. "Au dama ka samu na taimakeka na sanar masa shine kake mintsinina, to gaba tafi baya yawa".
Dariya irin ta manya papi yayi yace, "Shikenan babu damuwa in sha Allah duk zamuyi magana akai, sai ka sanar da yarinyar yaso sai a haɗa gabaɗaya kawai a tsaida Ranar ma daya".
Cikin farin ciki ya amsa da, "To papi godiya muke Allah ya kara girma".
"Ameen, to kai kuma fa". ya fada Yana duban nashed .
Murmushi ya danyi yace, "Mu dai har yanzu papi, saidai a taya mu da addu'a".
"To allah ya kawo ta gari amma idan har ka amince Ni zan zaba ma mata".
"Nagode sosai papi jazakallahu khairan".
Hakan ya nunawa papi ya amince kenan dan haka yace, "To Allah ya muku Albarka". Amsawa sukayi da ameen sannan suka tashi.