Free chapter · Read without an account

PAGE 27

by SultyWrites · BELOVED HEARTS

Kamar yadda Papi ya faɗa ya haɗa kan iyayen su Faez anje anyi magana gemu da gemu dan a gidan su Maesha suka tarar da daddyn Meelah dan haka abun yazo musu da sauki, sukayi tambaya aka basu sannan suka buqaci sa rana ba musu Abbah ya sanya musu wata goma, bayan sun gama makaranta da wata daya kenan, take suka sauke dukiyar aure harda sadaki, akayi addu'a taro ya tashi.

Gidan Papi suka koma dan sanar masa yadda sukayi yaji dadi sosai yace Allah ya kaimu sannan ya sanar dasu akwai wata tambayar next week". Ya fada da harshen nasara yana kallon mahaifin Nashed.

"Tambayar wa kuma?". Alhaji Idris mijin Mama fatima ya tambaya da mamaki a fuskarsa.

"Akwai yarinyar abokin kasuwanci na rashida, na tambayawa Nashed kuma Mahaifin nata yace ba damuwa muna iya zuwa so na tsaida masa Next week sunday, dan ni nafi so a hada auran nasu lokaci guda".

Murmushi mahaifin Nashed yayi Kana yace, "Ai baka buqatar sanarmin, Nashed is your son you have the right to choose what's the best for him". Godiya sosai Papi ya masa sosai kafin suka cigaba da tattaunawa yayin da Daddyn Hameedah kuwa ya gama ƙulewa, sam baiji dadin abin ba tunda ga yar sa agidan amma duk suka tsallake suka nema wa yayansu aure a waje, abinda ya hana shi cigaba da zama tare dasu kenan ya tashi ya musu sallama ya tafi a zuwan yana da wani uzuri da zai gabatar.

************

Tun daga kofar falo yake kwalawa mahaifiyar Hameeda kira, tana fitowa yace, "Ke yanzu Fatima abinda dan uwanki yayi adalci ne Kenan? kika tattara yar taki guda kika sallama masu yanzu kuma suka tashi suka tsallake ta a gidan suka nemawa yayansu auren bare, to idan ma yace dan nasa ba zai aura masa Hameedar ba shi kuma wannan yaron dan ambassador fa.

Mama Fatima ta katse shi da faɗin, "Haba alhaji Ka zauna mana, daga shigowarka ka hau bambami ai ka zauna dai muyi magana ko, nasan tabbas yaya bai kyauta ba amma ai da ka zauna ɗin yadda zamu yi magana ta fahimta.

"Kinga ni fa ba wata magana da zan zauna ayi, mutumin nan bawani kaunarku yake ba....... hameedah ce tayi sallama ta shigo juyawa yayi a fusace yace, "Ke daga gidan uwar wa kike?

Dan baya taja kafin tace, "Daga gidan aunty samna.

"Karaso ki zauna nan".

Kallon Mama fatima tayi kafin ta ƙarasa ta zauna kusa da ita tana maida hankalinta kan Mahaifin nata, "To ki tsaya ki saurara abinda zan fada maki da kyau daga yau bake ba can gidan.

" Wani gida Kenan daddy ?

"Gidan shi wancan kawun naki, dan haka duk abinda kikasan na amfanin ki ne ki tattaro ki dawo gida ai kema kina da gidan uba kuma kina da gata.

Turo baki tayi tace, " Ni gaskiya daddy bazan dawo ba wai mai papyn ya ma ne kake ta masifa haka?".

Mari ya wanka mata yana faɗin, "Yaushe kika lalace har haka, ina magana kina magana, to ubanki ya min nace ubanki ya min, wawiya wadda bata kishin kanta to ni dai na gama magana". Yana gama fadar hakan ya fice.

Fashewa tayi da kuka tana faɗin, "Wai ni kam Mama, Mai su Papyn sukayi masa ne Dan Allah? Ya zai yanke wannan danyen hukuncin?".

Miqewa itama Mama fatiman tayi tare da faɗin, "An tsayar da ranar auran Muhammad, faez da kuma nashed Nanda 10 months". Tana gama fada ta shige.

Kumatun ta da ta dafe inda daddyn ya mareta ta ciro, ta kalla hannun saita mai da shi Kan kumatun, zunbur ta mike kamar wadda aka tsikara tace, "An tsayar da ranar auran Muhammad, faez da nashed, kaiiiii Inaaa". Da sauri ta zari car key da jakarta tayi waje. Ikon Allah ne kawai ya kaita gidansu Maryam dan Kure motar tayi tana tuki tana kuka ko parking bata tsaya yi daidai ba ta shige.

A parlour ta samu maman Maryam din ko tsaya gaisheta batayi ba ta shiga tambayar ta ina maryam, daki kawai ta nuna Mata. Cikin sauri ta wuce, da kuka ta karasa Maryam dake waya da saurayinta tayi saurin kashe wayar ko sallama basuyi ba tana faɗin, "kawata mai zan gani haka, me ya faru kuma ? ".

"Menene ma bai faru ba Maryam, Maesha ta zamemin karfan kafa, Maryam wai ansa ranarta da moha yau din nan, wai an yiwa moha baiko da wata bani ba, na shiga uku Maryam". Ta karashe tana sakin wani sabon kukan.

Dafata tayi tana faɗin, "Na tabaki da alheri ƙawata, in sha Allah kukanki yazo karshe, yanzun nan nake shirin kiranki dan na samu labarin wata bokanya ana ce mata tsunburbura ance aikinta kamar yankan wuqa, dan haka can zamuje aruguza komai, wannan auran sunan sa rusasshe, ki kwantar da hankalinki moha naki ne.

"Hankalina bazai taba kwanciya ba Maryam, in dai kina son nuna min kin damu da damuwa ta to ki taso muje yanzu".

Kamar zatace ta bari zuwa gobe sai kuma dai ta miqe tace muje". Ta faɗa tana zira bedroom slippers dinta ba tare data damu da sauya kayan dake jikin ta ba dukda kuwa camisole ce kawai sai boyfriend jacket data daura a sama, dan siririn bakin gyalen dake daure akanta ta kunce ta yafa suka fice. Ba kowa a parlourn kuma bata damu data sanarwa uwar ta ba sukayi ficewarsu.



NOTE



YAKU IYAYE MATA KUSA IDO AKAN YAYAN KU ESPECIALLY MATA A YANZU MAZAN MA YA SUKA ƘARE BALLE MATAN, KI JA YARKI A JIKI KI ZAMA ABOKIYAR SHAWARAR TA. ITAFA YA MACE BAKAMAR NAMIJI BACE, BAI KAMATA ACE TANA RAYUWA IRINTA DABBOBI BA ADUK LOKACIN DATA KESO TAFITA A DUK LOKACIN DATA KESO TA DAWO, DOLE TANA BUKATAR TSAWARTARWAR WANI BABBA TANA BUKATAR TSARO DA LURA DA IRIN MUTANEN DA TAKE MU AMALA DASU, KAR KIBAR YARKI SAKAKA TANA YAWO A GARI KAMAR WATA AKUYA KI KULA DA KIWON DA ALLAH YA BAKI, DAN DUNIYA TA LALACE WANDA YAKE SON KA SAN SHI NA KIRKINE YAKE NUNA MAKA SHI NA KIRKIN NE, MASU FUSKA BIYU SUNYI YAWA, ƘAWA/ABOKI NA TAKA MUHIMMIYAR RAWA A RAYUWA, KI ZAMA UWA TA GARI WA YAYANKI, DOMIN IN SUKA ZAMA NA GARI, RAYUWARSU TA GYARU TO FA ZAKI KASANCE ME SAMUN ADDU'A DAGA GARESU.


MOHA


Wayarsa ya dauka ya kira Maesha bayan Papi ya sanar masa yadda akayi da su Abbahn maesha, tana dagawa yace, "Hello wifey".


"Har ma na zama wifeyn kenan.


"Eh mana, to me ya rage, you re mine already daure mu ne kawai ba'a yi ba".


Murmushi tayi tana Kara kankame pillow a kirjinta, yace, "Yanzu faɗamin ".


"Me?"


"Irin farin cikin da kike ciki mana, dan nasan yanzu ana nan ana zumudi, Umm yarinya an fara girma".


Dariya tayi tana faɗin, "Allah bana so ka daina".


Shi ma cikin dariyar yace, "Stop pretending girly, yanzu dai an gama da wannan babin hankalinki ya kwanta, aure yazo nima na huta da fushin yau da gobe".


Rufe fuskarta tayi kamar yana gabanta tace, "Oh ni dai na shiga uku".


"Ba wani kin shiga uku, wato ranar saboda nace miki kina gama diploma zaki daura da degree harda masters shi ne harda fushi dani, to ai sai daga baya na fahimta". Da sauri Maesha ta kashe wayar tana dariya, sai kuwa ya sake dawo da kiran, saida ya kusan katsewa ta daga inda ya jiyo muryarsa shi ma da alama dariyar yake yace, "Haka akewa miji ke? Ai kya tsaya na gama jawabi na ko".


"To ina jinka".


Cikin wata irin romantic voice yace, "Ina cikin farin ciki Angel, ji nake kamar in janyo ranar nan, whl na matsu in ganki kusa dani a matsayin mallakina, kinga a huta da wayar dare kema ki huta da rungumar pillow, Amma yanzu faɗa min me ake shirya min?".


Maesha da taji kunya ta gama lullubeta ta sake kashe wayar tana mirginawa ta canza position din kwanciyarta tana murmushi, ita wani lokacin har mamankin Moha take yadda yake iya sakin wasu maganganun ko kunya bayaji, amma physically in ta kalle shi sai taga kamar ma bada shi take waya ba.


Bai sake kira ba sai romantic goodnight text da ya tura mata dan yasan ba lalle ta sake daukan wayar a yau ba kuma.


Shi kuwa Faez ta bangarensa shiryawa yayi ya tafiyarsa zance sai wajen 11pm ya baro gidan su Meelah dan ma shi kadai yazo dan da ya nemi moha ya rakashi amma sai yace shi fa bazai iya zuwa area su Mamy ba kuma bai haɗu da ita ba, shi kuwa Nashed dama ya fice.


Sati na zagayowa akaje aka yi tambayar Nashed mahaifinta yace ya bashi dan dama bata fi 3 weeks da gama secondary ba ko results dinsu bai fito ba, cikin ikon Allah aka samu daidaito aka tsaida rana daidai da nasu Maesha amma da sharadin idan results dinta ya fito zata fara uni yazo ta karasa a gidanta, ba jayayya su Papi suka amince aka ajje musu dukiyar aure da sadaki kamar yadda akayi nasu Maesha.


HAMEEDAH


Hameedah da Maryam na hango cikin wata bukka gaban wata mata idanunta jawur kamar garwashi gashinta a tsaitsaye kamar Mai shirin tashi sama, sai da ta gama tsubbace tsubbacenta sannan tace, "Meke tafe daku?". Ta fada da wata irin murya kamar wadda iska ta dauko.


Hameeda da yanzu takejin ko baza ta samu Moha ba to saita rabashi da Maesha ta shiga zayyanowa matar duk abinda ya kawo su.


Wani faifai ta dauko ta mika Mata tare da faɗin, "Dafa wanna".


Dafawar tayi da sauri, matar ta shiga wasu maganganun da ba fahimta suke ba, can kuma tayi shuru sai kuma tace, "Dauke hannun". Hameedah na cire hannun hotun fuskokin Moha da Maesha ya bayyana kowannensu yana murmushi, da hanzari Hameedah ta ɗan ja baya tana faɗin su ne, whl".


Bokanyar tayi wata irin dariya kafin tace, "Me kike so a musu?".


Hameedah da taji a ranta wannan aikin tabbas zasuyi nasara tace........



Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.