Free chapter · Read without an account

PAGE 34

by SultyWrites · BELOVED HEARTS

Sai da suka samu kansu a mota sannan Hameedah tace, "Maryam ashe dai ashe dai kema da naki qullin".

Ta girgiza kai kawai, "Bari ke dai Hameedah, yarinyar ta shigar min hanci ne yadda bakya zato".

Tayi dariyar mugunta tace, " Yanzu kuwa zaki fyatota ai, karkiji komai".

"In sha Allah, yanzu ke ya zakiyi da wanna kwalbar.

"Ai nan da kike ganina gidan zan nufa, na san bazan samu kowa ba dan suna wurin kamun bikin Nimra, ke koma suna nan sai nasan ya nayi na aiwatar da aiki na, kema kuma kiyi kokarin aiwatar da naki aikin yadda komai zai tafi daidai".

"Wait tsaya in duba time table Inga ko tana school yanzu". Ta faɗa tana zaro wayarta ta shiga dubawa. "Kash ita da school sai Friday, muna da lecture around 4".

"To dan Allah ki tabbatar kin aiwatar da aikinki, karki bamu matsala".

"Habaa tawan karkiji komai". Da haka hameedah ta kaita har kofar gidansu sannan ta sauketa ta wuce gidansu moha. A waje ta tsaya tayi parking motarta sannan ta fita ta nufi gate din gidan da kafarta, knocking tayi masu gadin suka buɗe, ganin itace yasa suka buɗe mata ta wuce ko takan gaisuwarsu bata bi.

Ji tayi gidan shuru ta kalli parking lot taga ba motocin su ko ɗaya sai ta Papi guda ɗaya da ba cika fita yayi da ita bama, ajiyar zuciya ta sauke tayi Murmushin samun nasara sannan ta nufi backyard, garden ɗin gidan ta shige kai tsaye.

Faez da fitowarsa Kenan daga wanka ya haɗa coffee yana sha ya dauki wayarsa dan kiran mechanic yaji ko ya gama gyaran motar tasa, iska ce ta taso hakan yasa curtain din windows ɗin fara ɗagawa, matsawa yayi wurin window saboda yana san irin wannan yanayin, kiran mechanic ɗin yayi suka gama magana sannan ya juya dan yaje ya shirya sai kuwa yaga kamar inuwar mutum a tsugunne, bude curtain ɗin yayi ya leqa sosai, Hameedah ya gani tsugunne tana kokarin saka wani abu a kaskon flower dake wurin, sake murza idanunsa yayi yana tunanin anya ba idonsa bane kuwa, Mai zai kawo Hameedah gidan a irin wannan lokacin bayan duk matan familyn suna wajen biki? Me take sakawa to?

Juye juyen da take gudun kar wani ma'aikacin ya shigo ya ganta ya bawa Faez damar ganin kan kwalbar da tasa, da sauri kuma ta cusa flower akai ta mike tana kokarin juyowa ya saki labulen idonta akan part ɗin nasu kuwa dan sai taga kamar mutum ne yake kallonta amma ganin ba kowa kuma tasan basa nan tunda bata ga motar kowannensu ba yasa ta basarwa da faɗin maybe dan a tsorace take ne, karkaɗai hannunta tayi ta fice daga garden din dama gidan baki ɗaya ta ɗauki motarta ta bar unguwar.

Tana fita Moha na shigowa, da farin ciki ya nufi part ɗinsu, samun Faez yayi yana shiryawa amma jikinsa a sanyaye, sam bai lura da yanayinsa ba ya shiga sanar dashi surprise din gidajen da iyayen nasu su kai masu, wannan ya sa Faez ma mantawa da batun hameeda, ya karasa shiryawa suka fito shi da Moha sai ga Nashed ya shigo moha yace ya juya su wuce gidansu Faez, haka kuwa akayi suka nufi gidan su Faez ɗin Inda suka tarar da Papi da kuma mahaifin Nashed suna zaune tare da Amb.

Gaishe da iyayen nasu sukayi sannan suka zauna, Amb. Ya miqa musu takardun gidajen sannan yace, "Gashi nan, wannan takardun gidajen da matan ku ne, mun yanke shawarar gina muku gida kusa da juna ba tun yau ba, to yanzu lokaci yayi, ga takardunku a hannunku in kuna son zuwa ganin su kuma mubarak na waje tare mukaje dashi sai ku dauke shi ya muku jagora. Godiya suka shiga yiwa iyayen nasu har saida Papi ya katse su yace su tashi suje su ga gidan.

Haka kuwa akayi suka tashi suka fito, Mubarak driver Amb. suka ɗauka dan zuwa ganin gidajen.

Gidaje ne jere guda uku fentin suma iri daya ne, na farkon suka fara shiga, gate din zai iyacin motoci biyar sai dakin mai gadi da toilet, entrance suka nufa suka shige ciki, babban parlour ne ya bayyana agabansu, sai daki ɗaya a ciki da dinning suka sake yin gaba sai suka tsinci kansu a wani falon, ga ƙofar kitchen a ciki daga gaba kuma wani corridor ne da zai sadaka da dakunan bacci guda biyu masu kallon juna, kowanne daki da toilet dinsa a ciki.

Daga wurin dinning kuma akwai Kofar da zata fitar dake BQ, ga wani ɗan ƙaramin garden da ya sha furanni masu kyawun kallo, gidan ya haɗu perfect for newly married, haka suka fita suka shiga na biyu shima tsarinsa iri ɗaya ne da dana farkon haka na ukun ma, Faez yace Moha ne zai dau na tsakiya, daga nan kuma suka shiga batun furnitures, Moha beyi kasa a guiwa ba ya kira Maesha yana tambayarta ko akwai irin furnitures din da takeso da kuma colour, amma sai tace duk abinda yayi daidai ne, aikuwa yasa Faez a gaba ya kira masa Meelah ta nan ne ya samu duk abinda yake son sani game da zaɓin maesha, daga nan suka wuce restaurant abunsu zuciyarsu fes.

FRIDAY

Yau aka daura auren Nimra kuma yau ake yini don Anjima za'a kai Amarya, Su Hameedah an qule cikin daki da yan matan amarya wajen su 10 sai shewa ake, a compound kuma masu kidan kwarya ne suke ta kaɗawa. Ganin la'asar tayi yasa Hameedah tashi ta shige toilet ta kira Maryam tana dagawa tace, "Ya ake ciki ne Maryam?".

"Kwantar da hankalin ki mana Hameedah, yanzu ta shigo school ɗin ma".

"Karfa ki bamu matsala Maryam, dan ni kam yanzu inaji ajikina duk Inda Moha yake hankalinsa na kaina sauran naki aikin kawai".

"Nima baza a samu matsala ba ki qaddara har an gama".

"To shikenan zan saurare ki". Da haka sukayi sallama ta kashe.

MAESHA

suna cikin lectures taji vibrating din wayarta yaki tsayawa sai Kira ake Meelah dake kusa da ita tace, "Wayarki na haske fa kamar kiranki ake".

"Naji whl, bansan wani dan nacen bane kalan su sa a kori mutum a aji". Ta ƙarashe tana ajje pen din hannunta ta zaro wayar kasa ƙasa, zubawa screen ɗin wayar tayi ganin Moha ne ke ta jera wannan kiran, sai taji gabanta ya faɗi dan bai saba mata irin wannan kiran ba, miqewa tayi ta dau sannan ta fita tana amsa wayar. "Hello Qalbi".

Tana iya jin ajiyar zuciyar da ya sauke daga cikin wayar yace, "Angel kina Lpy?".

"Ina lpy mana Qalbi, wai ba yanzu muka gama waya ba da zan fito daga gida, ko akwai wani abu ne?".

Runtse idanunsa yayi yana jin yadda sautin bugun zuciyarsa ke karuwa kamar zata fasa kirjinsa ta fito yace, "Angel gabana sai faɗuwa yake sai nake jin kamar wani abu ne zai faru, dan Allah yau ki haƙura da lectures ɗin nan ki koma gida".

"Ba abinda zai faru Qalbi kawai shaidan ne, ka tashi kayi alwala ka dauki qur'ani Kayi karatu, in sha allah Khair kaji nawan, Ka kwantar da hankalinka duk abinda kaga ya faru da bawa dama can a rubuce yake a cikin litttafin qaddararsa bai kuma isa ya kaucewa hakan ba". Ta faɗa cikin ƙarfin hali dan whl itama sai ta tsinci kanta cikin faɗuwar gaban kafarta har rawa take amma bata son ta ƙara tada masa da hankali.

"Zanyi yadda kikace in sha allah, yanzu kin ƙarasa school din ne?".

"Eh ina ma class na dinga ganin kiranka shi ne na dau excuse na fito ".

"Shikenan ki koma, inaga idan an tashi zanzo in maidaki gida ".

"To amma....."

Katse ta yayi da fadin, "Angel manaa".

"Shikenan Allah ya kaimu". Ta faɗa tana kashewa ta karasa kan kujerar data gani ta zauna tana sauke numfashi ta shiga karanto duk adduar da tazo bakinta.

Sai da ta ɗan samu nutsuwa sannan ta tashi ta koma ɗin jiki a sanyaye, sai dai duk yadda taso concentrating ta kasa, gabaɗaya hankalinta yana kan Moha, ganin wannan sauyin ya sanya Meelah tambayar, "Wai lpy dai Maesha, wani abu ne ya faru?".

Girgiza mata kai tayi tace, "Ba komai fa". Ba dan Meelah ta yarda ba ta barta a zuwan in an tashi zataji menene ya janyo mata wannan sauyin. A haka har suka gama lectures ɗin sai ga kiran Maryam ya shigo wayar Meelah.

Dagawa tayi da faɗin, "Hello Maryam".

Daga ɗaya bangaren Maryam tace.......


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.