Free chapter · Read without an account
PAGE 35
Daga ɗaya bangaren Maryam tace, "Meelah yanzu zakuyi printing takardar nan ne?".
"Eh yanzu zamuyi idan mun fita".
"A cafe ɗin cikin school ko ta waje?".
"A ta waje".
"Okay to dan Allah kuyi min printing guda ɗaya zan same ku a cafe din, zan tura miki kuɗin ne ko sai nazo".
"Ki bari sai kinzo ɗin kawai".
"Okay to Nagode". Ta faɗa tana kashe wayar.
Ita dai Maesha ko da suka fito layin Moha ta fara kira amma baya picking, sosai hankalinta ya ƙara tashi Meelah tana mata magana ma bata kulata ba har suka ƙarasa inda za'a musu printing din, Maesha tace, "Barin karbo ruwa a shagon nan kafin ki tura musu". Ta faɗa tana nuna mata shagon dake jikin cafe din.
"To kardai ki dade dan naga ba wani layi sosai". Bata ba ta amsa ba ta ja ƙafafunta da suka mata nauyi ta ƙarasa shagon, bottle water ta ɗauka guda ɗaya tana juyawa juyawa suka haɗa ido da Maryam data ɗauki bottle water din itama, "A'a Maesha ashe kece?".
"Maryam ykk, kwana biyu".
"Whl fa ina Meelah?".
"Tana cafe din can zata mana printing" .
"Eh munyi waya da ita nace ta min printing din ɗaya ni ma". Ta faɗa a lokacin da take miqa kudin ruwan guda biyu.
Maesha tace, "Da kin barshi ma ina da canji nima".
"Dan Allah kar muyi haka tunda dai har na biya".
"To Nagode". Ta faɗa tana ficewa.
Maesha bata koma cikin cafe din ba ta yi zamanta nan kan dakalin tana cigaba da kiran Moha.
Anan Maryam ta sameta, kusa da ita ta zauna tare da ajje tata robar ruwan kusa data Maesha, Wasu course mates dinsu ne suka zo shiga suka tsaya suna magana da Maesha, ganin hankalinta yayi wurinsu yasa tayi mucanjen robar ruwan ta maida nata mazaunin na Maesha.
Maesha tana kallon lokacin da Maryam ta sauya robar ruwan ruwan sai mamaki ya kamata amma ta nuna kamar hankalinta baya wurin. "Sannu Maryam miye duniyar?". Daya daga cikin course mate din nasu dake magana da Maesha ta faɗa.
"Ykk Nana". Nan suka shiga gaisawa aikuwa Maesha ta faki idonta itama ta maida mata ruwan nata data jawo gabanta.
Sarkewa Maryam tayi ta hau tari tana juyowa ta ɗauki ruwan ta sha kusan rabi sannan ta ajje, Meelah ce ta fito tana faɗin, "Au Ashe kuna nan ku duka?". Ta faɗa tana miqawa Maryam takardar da ta mata printing ɗin. Ta karba tana faɗin, "Thank you Meelah". Ta ɗauko kuɗin zata bata Meelah tace ta barshi.
Tashi Maesha tayi ta dau robar ruwanta amma sai ta ɗan tsaya tace, "Ni ruwan nan kamar na gabana kika ɗauka ko?".
A hautsine Maryam tace, "Ta gabanki kuma? Tawa ce fa?". Ta faɗa a rikice. Maesha tayi dan murmushi tace, "Haka ne fa ashe ban gani da kyau ba, sai anjima".
Kasa bata amsa Maryam tayi dan ta shiga tunani ko dai da gasken wadda ta zuba maganin ta turawa Maesha gabanta ita ta dauka ta sha? Tana cikin tunani har bata san sun bar wurin ba.
Jikin Maesha ne ya sakeyin sanyi tace, "Allah ka gani ban taba cutar kowa ba, ba kuma ni da niyyar cutar da wani ya Allah karka bada damar wani ya cutar dani".
Tsayawa Meelah tayi tace, "Meke faruwa ne wai? Tunda aka kiraki a waya duk kika sauya".
"Bari kawai Meelah duniya abun tsoro".
"Ni sai kara lullubeni kike ki min bayani".
"Wani abu nake zargi amma ban tabbatar ba ". Ta faɗa tana jefar da robar ruwan dake hannunta dan sai taji ita ɗin ma bata yarda da ita ba.
"Tunda baza ki faɗa ba ki shanye abunki a zuciya". Meelah ta faɗa tana tsare musu abun hawa.
MOHA
Suna gama waya ya tashi yaje ya ɗauro alwala ya dauki Alqur'ani ya fita zuwa garden din gidan ya zauna ya hau karatun a fili cikin suratul baqara, yayi wurin shafi hudu sai ya farajin bishiyun wajen na kaɗawa da karfi kuma karfin iskar da ake baici ace har suna wanna girgizar ba dagowa yayi yanabin wajen da kallo sai yaga sun tsaya cak, maida kansa yayi ya cigaba da karatun sai yaji sunci gaba da kadawa fiye da da, bai ɗago ba ya cigaba da karatun sai kuwa ya fara jin kamar ihu ihu dagowa yayi idon sa ya tsaya akan kaskon wata flower dake tsalle ita kadai kamar wanda wani abu yake neman fitowa aciki da sauri ya tashi da qur'anin a hannunsa ya matsa kusa da flower, daga ɗan nesa ya tsaya sai yaga itama ta tsaya, karatun ya cigaba da yi daga tsayen sai kuwa yaji wata ƙara Kamar zata fasa gidan daidai da lokacin da flower nan tayi tsalle kaskon ya fara barewa, murfin kwalbar kuma ya fara buɗewa.
Durkushewa Moha yayi rungume da Alqur'anin ilahirin jikinsa ya hau rawa nan ya fara karanto ayatul kursiyyu saidai bai ida ba ya cafko Alam tara kaifa saboda wata guguwa data hau zagaye shi tana ihu, can kuma aka gaggabe da wata iriyar dariya sai kuma kuka ya biyo baya, wasu maganganun da baya ganewa yaji an shiga yi sai kuma yaji kamar ana gudu can kuma yaji tsit. A hankali ya dago kamar me tsoron ganin wani abu sai yaga wayam ba kowa ai bai san lokacin da ya tashi a guje ya fice daga garden din ba.
Nashed daya fito daga kitchen ganin yadda moha ya shigo yasa shi komawa cikin kitchen din yana ƙoƙarin danna kofa, shi kuwa Moha bai ma bi ta kansa ba ya karasa daki ya ɗauki key mota ya ajje alqur'anin dake hannunsa ya fito, kofar kitchen din ya doka da ƙarfi, Nashed yace, "Waye?".
"Kai dallah bude gidan nan yau ba lpy, gwara ka fito muyi ta kan mu tun kafin labari ya sauya". Ya faɗa yana barin ƙofar kitchen ɗin da sassarfa.
Jin haka yasa Nashed fitowa da sauri har yana shigewa gaban Moha, ya kuwa ture shi ya wuce, a haka suka shiga mota Moha yaja da wani mahaukacin gudu yana danna horn ɗin da tasa masu gadin cin tuntube kafin su buɗe gate din.