Free chapter · Read without an account

PAGE 41

by SultyWrites · BELOVED HEARTS

INA LABARIN HAMEEDAH DA MARYAM

Hameedah dai tunda akai kaita asibiti likitoci suka rufu a kanta daƙyar aka samu ta farfado, saidai kuma a yanayin data farfado ɗin yasa dole aka sake mata allurar bacci sai fisge fisge take tana yunqurin fita a guje. Hakan ba ƙaramin tada hankalin yan uwanta yayi ba aka shiga jiran farfadowarta, saidai ko da ta farfaɗo ɗin abu daya aka koma yi shi ne riqeta, hakan yasa likitocin bada shawarar suga likitan ƙwaƙwalwa.

Haka kuwa akayi bayan sunga likitan ya rubuta musu hoton kai da sauran gwaje gwajen da ya kamata ayi, bayan sakamako ya fito ya daura su akan medications saidai ko ta sha maganin ma kamar kara tirata ake dan mutane biyu uku basa iya riqeta idan ya fara fisge fisgen nan, ganin maganar nata fita yasa mahaifiyarta bada shawarar a dawo da ita gida a cigaba da neman na Hausa ko shafar aljanu ne. Haka suka shiga zirgatu wurin malamai da muna malamai, yau suna can gobe suna nan, dakyar suka wani me magani yana taimaka musu da rubutu har abun ya ɗan fara raguwa saidai kuma in ya motsa to saidai a daureta da igiya dan fashe fashe takeyi sosai ta illata kanta ta illata duk wanda yayi ƙoƙarin riqata. WANNAN KENAN.

Maryam kuwa bayan an samo iyayenta sunzo likitoci suka shaida masu kafarta ɗaya ta tashi aiki ya zama dole ayi aiki a yanketa in dai suna son lpyrta, haka suna ji suna gani ba yadda zasuyi Maryam takoma gurgurawar karfi da yaji. WANNAN KENAN.

BARI MU KOMA BANGAREN AMARE

WASHE GARI

Meela na hango akan cinyar Faez sai faman narkewa take yana tattarota, da alama dai shi ma Dr bai bar wanna dare mai Albarka ya wuceshi ba lol😂.

Abangaren su rash kuwa amarya taxo da bako wanda ya shigarwa Nashed hanci da kudundune ya hanashi murje sadakinsa.

Bari mu leqa wurin love birds mr and mrs Moh.

Daga ɗaki suka fito cikin shiga iri daya ta kananan kaya, shi yasa Black jeans da ash ɗin t shirt ita kuma ta sa Black palazzo da top ash, tana manne a jikinsa kamar wata baby yaja musu kujerar dinning din da kafarsa sannan ya dora ta shima ya zauna.

"Me kike so in zuba miki mrs Muhammad?". Ya fada yana kallonta cike da so kamar ya hadiyeta.

Turo baki tayi a shagwaɓe tace, "Ni banacin komai".

"A tausayawa Muhammad, kar a azabtar damu da yunwa". Kauda kai ta sakeyi, ya riqo hannunta tare da faɗin, "Fushin na miye Umm My Angela, ba nace na dai na ba, ai ba za'a ƙara ba sai kinji sauki ko?".

Kukan tabara ta sakar masa tare da fara kai masa dukan wasa, ya riqe hannun nata tare da rungumeta gabaɗaya a jikinsa yana faɗin, "Yi shuru Mana My Aysha, surukar Aisha kuma maman little Aisha me zuwa in sha Allah, haba shalelen Muhammad, yar fara me dogon hanci". Duk yadda ya tsare gida sai da ya sata dariya, haka yayi serving dinsu cikin farin ciki suka yi breakfast din.

10 YEARS LATER

Wani qaton estate na hango Mai kyau da tsari, gabaɗaya gida uku ne a ciki biyu suna kallon juna sai ɗaya daga tsakiya, amma kallo ɗaya zaka yiwa yanayin ginin kasa dollar tayi ihu, kuma basira tayi aiki dan duk wanda ya fidda plan din gidajen to ba ƙaramin kwaro bane, karasowa nayi daga ciki dan dauko maku rahoto da kuma ganin su waye mamallakan wannan estate ɗin.

Kai tsaye na tsakiyar na fara kutsawa, Wasu kyawawan yara na gano suna saukowa daga royal staircase ɗin da gudu, basu tsaya ko ina ba sau a gaban wata royal cushion dana ga wata damsel lady zaune tana bawa wani baby da baifi 1 year ba cerelac, sosai na ƙara murje idanuna dan ganin ko gizo suke min. Maesha ce zaune ta Kara girma da kyau kamar ba ita ba. "Mamy mun shirya". Ɗaya daga cikin yaran ta faɗa.

"Sai ina kuma?". Maesha ta tambaya ba tare data dube su ba.

Wata yarinya mai tsananin kama da Maesha da baza ta wuce 9 years bane tace, "Mamy gidan Ummi mana, kin manta sati ya zagayo ne, sai nan da two weeks kuma mu da ki gan mu".

Wani yaro da shima bazai fi 9 years din bane yace, "Whl karya take Meemi, ai bamu gama week din mu anan ba".

Wata yarinya da baya kai su ba itama tace, "Kai Zafran yau fa mun cike one week din mu, hala ka fara bata a lissafi ne saboda baka so kayi nesa da Mamy, mu kawai sai muyi tafiyar mu kai ka zauna in baza kaje ba" .

Sallamar Moha ta katse musu doguwar muhawarar da suke yi, yayi kyau, cikar haibar sa ta sake fitowa saidai ba abinda ya sauya daga daukar wankansa, gabaɗaya yaran wajen sa suka nufa suna ihun Oyoyo Abie, oyoyo Abie.

Rungume su ya dinga yi one by one, ƙananun kuma ya dinga daukansu yana basu peck. Sai da ya gama dasu sannan ya kalli Meemi da faɗin, "Uwata ta kaina ina zuwa haka?".

Ɗan turo baki tayi wanda ya ƙara bayyana kamanninta dana mahaifyarta kafin tace, "Wurin Ummi".

"Ahh to Masha Allah, har satin ya zagayo kenan zaku kwashe ku tafi, to ku gaida min da Ummi da Daddyn naku da kyau".

"Zasuji Abie, Mamy mun tafi".

"To Allah ya tsare a gaida Ummi". Suka amsa da to suna ficewa.

Saida ya sake rufe ƙofar sannan ya karaso ciki ya zauna kusa da Maesha yana me zagayo da hunnunsa ta waist dinta ya kwantar da kansa a kafadarta yana shafa Kan baby boy ɗin da dayan hannu yace, "Aji dani mana Angel, a kyale Baba haka shi baya gajiya".

Murmushi tayi ta kalle shi ya kashe Mata Ido ɗaya, tace, "Ai kai ya gado. Inno, inno". Ta shiga kwalawa Inno me rainon Sameer junior kira.

Da hanzari ta shigo falon tana me faɗin, "Gani Uwar ɗaki na".

"Yauwa inno ga Baba nan yaci abinci kije dashi ai masa wanka".

"To uwar daki na, Alhaji barka da dawowa". Ta faɗa tana karbar Baba Sameer.

"Yauwa". Shi ne kawai abinda Moha ya faɗa. Suna wucewa kuwa ya suri maesha sukayi sama yana faɗin, "Yau dai a barni in sake da matata, babu wani Excuse ɗin yara kuma". Murmushi kawai ta masa as response.

Yaran Maesha shida ta farkon mace ce da aka maida Mata sunan maesha kuma sunan momma suke cemata Meemi sai triplet ɗinta Raheela suna ce mata bushra sai saifuddeen da suke ce masa bashshar sai mai sunan Faez da suke Kira da Bassam, sai me sunan ya Zeenah sai kuma auta Baba Sameer .

Meelah nada huɗu Harris shine babba sa'an Meemi ne sati daya tsakanin su kuma sunan Moha yaci suke ce masa Harris, sai Nashed da Mahvir sai kuma auta Amrish .

Rashida nada biyu Ninah da deena sai kuma unborn da ake sa ran saukarsa yau ko gobe.

Yaran sun taso kansu a hade dan Saida aka sasu a school sannan suka fara fahimtar ba mahaifansu daya ba, dan kowanne ji yake dukkansu yayansa ne, kaunar da zai nunawa nasa ya'yan shi zai nunawa na yan uwan nasa. WANNAN KENAN.

TAMMAT BI HAMDULILLAH

ANAN NA KAWO KARSHEN NOVEL DINA MAI SUNA "BELOVED HEARTS". DARUSSAN DAKE CIKI ALLAH YA BAMU IKON AMFANI DASHI, KUSKUREN DAKE CIKI KUMA ALLAH YA YAFE MANA. AMEEN.

GUYS THIS IS THE FIRST NOVEL I WROTE, SHOW ME SOME LOVE PLEASE🥺🥺

~YOUNG WRITTER~ (The golden pen🖋️)

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.