Free chapter · Read without an account
SAFIYYA PAGE 1
by Safiyya Muhammad · SAFIYYA
........TO CHAT ME UP ONLY ON WHATSAPP ***
THIS NOVEL IS FREE LET'S START 💃💃💃💃💃💃
Bismillahi
Page 1
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Safiyya🗣️Safiyya🗣️Safiyya🗣️,shiryayya yar albarka kina inane kinaji ina kiranki kinyi burus ko oho dani,daga can naji muryar wata matashiyar yarinya da bazata gaza shekara sha biyu a duniya ta ansa da na'am ummanmu nafa ansa ruwa nake ba dabbobi ganinan zuwa,ta zagayo cikin wani matsakaicin gida da bazaka kirashi na masu kuɗi ba kuma bazaka kirashi da namai rufin asiri ba,illa ka kira gidan kawai gidan wani talaka tulusssssssssss.........tana zuwa ta tsuguno a gaban wani kitchen da duk rabin shi ya rushe ana kara wani ruwan damunan ba abinda zai hanashi idasa rushewa,tace umma gani,umma ta kalleta tace yanzu tsakani da Allah safiyya abinda kikayi kin kyauta,safiyya ta murguɗa baki tace umma nifa in abbanmu zai kasheni akan waccan matar tashi wallahi a shirye nake, bazaiyiyu ba insha wahala in debo ruwan da za'ayi amfani dashi a gidan nan ba,sannan tana kallon yaranta na ɗibar ruwan suna wasa dashi bata hanasu ba,sai dan nayima salisu fada akan zubar da ruwa shine ta fadama abban namu umma?ta karashe maganar da alamar tambaya,umma ta girgiza kai tace dauki abincin ki gashinan kije ɗaki ina zuwa tace to umma.......
Ta dauki wata ƙoƙaƙƙar langa da aka zuba tuwo miyar karkashi tayi cikin dakin su,tana shiga taja ajiyar zuciya ta ajiye abinci ta jawo wata tabarma dana gani jingine a bayan ƙyauren su ta shimfida,ta matsa daga bayan ƙyauren ta ɗebo ruwan ta mai sanyi acikin wata tsaftatattar randa ta ajiye gefe kenan saiga umma ta shigo ta galla mata wata harara data sa naga ta tashi simi simi ta fita waje ta wanko hannunta ta dawo tace Bismillah,umma tace kull karkici abincin nan,safiyya ta ture abincin gefe tai shuru tana sauraran me ummanta zata fada mata,umma tace har kullum safiyya ina gayamaki idan yau nice gobe bani bace🥹safiyyakizama mai biyayya ga mahaifinki da auntyn ki komai banza safiyya uba ubane bazaki gane hakan ba sai kin kara girma zakisan da uba ake ado safiyya bada riga ba, safiyya ta lumfasa tace amma umma kina gani kullum inna rabi batada abokin fada a gidan nan sai ni,narasa mena tsone mata a gidan nan jiya kinajin ta sarai tana cewa bazan gama da duniya lafiya ba ta karashe maganar fuskar ta nayi rau rau kamar zatayi kuka🥹umma ta matso kusa da ita tace safiyya bakin auntyn ki rabi bazai taɓa kamaki ko kin manta kinceman malamin ku yace, Allah yace bakin iyaye ne kaɗai yake saurin kama yaransuuu, shiyasa ma kikace man tunda kikaji wa'azin nan baki kara in saki aiki ba ki gudu🤣sai ta fado kan cinyar umma tana dariya tace Allah umma tun danaji wa'azin nan nayi alkawarin kyautata maki har ƙarshen rayuwata, shiyasa naketa so baba yayiman uniform kinga kowa ya fara zuwa makaranta umma bandani, yanzu fa umma muka shiga js1 ace ni har yanzu ban fara zuwa ba,kuma kinsan burina in zama likita umma kodan wannan ciwon naki inmaki maganinshi,umma inyi kudi in saimana gida ki huta da wahalar gidan nan,kofa baki lafiya umma sai abbanmu yace tilas sai kin fito kinyi girki🥹kuma duk saboda inna rabi ne amma ita idan ranar aikin ta ne umma sai tabar gidan haka zamu yini munajin yunwa idan kuma dare yayi abbanmu yace bazata ɗora girki ba,kinga umma idan nayi kuɗi yadda nake gani a television kema yar aiki zan samomaki nikuma in cigaba da zuwa asibiti ina taimakon al'umma ko umma?
Umma tace ummm safiyya Allah ya cika maki burinka yasa ina raye safiyya zanga burin nan naki ya cika,safiyya tace amin ummana ta rungume taaaaa❤️
Daga tsakar gida sukaji anata kwallo da bokitai da kwanoni ana hargagi gida ya kacema muryan wani babban mutum yanata surfa ashar yana ni za'ayima iskanci ta fake da tsinannen ciwo tana cutata yau gidan ubanki zaki kwana,gaban umma ya yanke ya faɗi rassssssssss, safiyya tace umma abbanmu ya dawo munshiga ukku,tana rufe baki malam hamza ya yaye labulen dakin su yace ke zuwaira ki tattaro kayanki tass wlh yau sai kin bar man gidana,umma ta saddar da kanta kasa saiga hawaye sun wanke mata fuska, safiyya na ƙanƙame da mahaifiyar ta umma tace malam kayiman rai idan na fita daga gidan nan bansan inda zanje ba wallahi banida uwa banida uba kaine gatana Allah ne gatana a duniyar nan idan na fita wlh bansan inda zanje ba yan uwana kaf an kashe su malam a yakin garinmu da boko haram keyi,ta tashi tasa gwuiwowinta kasa tace malam kayi hakuri idan laifi mukayi zamu gyara wallahi banyi komai da niyyar cutar da kowa ba,malam hamza yaja wani uban tsaki tsaaaaaaaaaaaaa kakeji yace aikin banza aini wallahi danasan haka baƙin halinki yake zuwaira da ban auroki ba ,yace baƙa mai baƙar aniya haihuwa ma kin kasa sai shegen ciwo kullum cikin jikin ki,sai wannan baƙar ɗiyar taki data fitini kowa a gidan nan wallahi idan na ƙara dawowa gidan nan rabi taceman kunmata wani abu kisani ranar zuwaira bakin auren ki,kuma ban riƙe maki wannan baƙar ɗiyar taki dan kiji ingayamaki ya wani saki labulen da karfi,suka sake rungume juna daga umma har safiyya suna wani kuka mai tsuma zuciya,saida sukayi mai isarsu sannan umma ta dago safiyya tace ya isa haka ci abincinki, safiyya ta kalli ummanta tace umma dan Allah mu gudu daga gidan nan mubarma abba gidan nan,umma tace Safiyya in mun gudu ina zamuje kinsani banida kowa sai Allah saike sai kuwa babanki yan uwana kaf boko haram sun tarwatsa kauyen mu nayi neman Dada ta itama a duniyar nan bansamu wani labarin ta ba safiyyan umma inmu gudu ina zamuje safiyya tace ABUJAAAAA,umma ta zaro ido tace Abuja safiyya ina kikasan Abuja tace a wayar yayan ƙawata idan muna kallo naga gidaje masu kyau sai muce mashi nan inane?sai yacemana Abuja ne shima can zaya tafi neman kudi,umma tace to ai kinga shi namiji ne neman kudi yake zayaje mukuwa idan munje Abuja kamamu za'ayi a kashe a banza tunda bamuda inda zamu zauna saidai muyi bara umma tace daga yau karna karajin kince mu gudu kinji ko addu'a danake koya maki duk rintsi ko inada rai ko banida shi safiyya karki bari,ki rike gaskiya da amana karki yarda a ɓatamaki rayuwa safiyya,duk abinda kikaga yafi ƙarfin ki a duniya safiyya baifi karfin Allah ba,ki dage kiyita gayama Allah kinji ko sannan duk abinda auntyn ki rabi tasaki kiyi,kinga idan bakiyi ba abbanku ni zaizo yaitama fada,safiyya tace to umma niba abinda yake bani haushi da abba irin gorin haihuwa dayake maki umma ɗa ɗaya fa gari ne ko?umma tace sosai kuwa safiyya ta idan nayi maki aure haka zaki haifoman jikoki goma sha biyu😁safiyya ta washe baki tace Allah umma?harta manta bala'in da baba ya shimfida masu yanzu,umma tace ƙwarai kuwa ga safiyya likita ga safiyya mai yara dozinnnnn😁
Tace kai umma ni babu yaron da zan goya ke zaki dinga goyasu umma tace kaiii mijinki nada aiki kedai kwata kwata bakison aiki rayuwarki gaki da tsafta amma baƙi ki ba ma ko wanka har yanzu inamaki ko,zatayi magana umma tace muci abinci suka fara cin tuwon su.
Washe gari tunda sassafe safiyya ta tashi ta fito tsakar gida ta haɗa kayan wanke wanke da sauran ruwan da suka kwana dashi ta wanke kwanoni tass tazo tayi shara ta gama kenan umma ta fito tace safiyya me kika tsayayi anan baki tafi debo ruwan ba kuma kinga gidan ba ruwa karaf inna rabi ta fito daga dakinta tace wannan watsatstsar ce zuwaira ubanta zai gindaya sharadi tayi mashi shi cikin dadin rai ai shiyasa bazakiyi albarka ba ta nuna safiyya da hannu tace inji nan yau ba'a rufa sati ba naji ubanki na cewa asubar fari ki fita kije rijiya kafin ma ya tashi sallah asuba ki tabbatar kin cika gidan nan da ruwa amma dayake shegen kunnen ƙashi gareki irin naku na bare bare dangin matsafa shine baki debo ruwan ba har gari ya waye zan dora karin kumallo ba ruwa ko ƙwandafe a gidan wanda ya rage kin diba ke uwar tsafta kin wanke kwanonin uwarki kin tsala wanka tunda uwar safiyya za'a fita yawon ibada yawon karuwanciiiiiiiii,umma zuwaira taja numfashi tace haba auntyn su safiyya fa yarinya ce bai kamata kina mata irin wannan furucin ba idan laifi tayi ki fadaman wallahi kiga yadda zan hukuntata,inna rabi ta nuna umma tace ke zuwaira kedin zaki hukunta safiyya ahayye malam malam malam yace na'am rabi minene tace a'a fito kaji wata watsuwa nan da kunnen ka danni tafi karfina,saiga malam hamza ya fito da wata koɗaddar babbar riga yace rabi ya akai?tace wai zuwaira ce da wannan ɗiyar tata zasuyiman watsuwa safiyya dai nace ta ɗebo ruwa ta dubi tsabar idona taceman rabi ban debowa sannan uwarta ta fito tana kareta sunata zagina malam har ceman sukeyi in Allah ya yarda saina mutu nabar masu gidan nan,malam yace zuwaira jiya ya mukayi dake?tace wallahi wallahi wallahi malam ba haka akayi ba.....
Malam hamza yace karya kike munafukar banza munafuntar wofi ana fara magana kiyi ƙasa dakai kamar mummunar karya,ya juya yace ke zaki tafi dibar ruwan ne ko kuwa saina fasa maki hanci da shegen idon ki tsakar kai nikuwa nace kai abbanmu easy🤣🤣🤣da gudu safiyya ta fice daga gidan tana kuka ta nufi rijiya,haka ta dinga jido ruwan nan akai tana zuwa Abba yace saita fara cika kayan ruwan inna rabi tass haka ta dinga zuba mata ruwa tana cewa bai isa ba saboda zatayima ɗan son ta salisu wanki😁har azahar bata gama ɗibar ruwan nan ba ga tayi bala'in gajiya da kyar dai ta idasa rebo ruwan nan ta haɗama dabbobi abinci ga har lokacin ko ruwa batasa a cikinta ba🥹tana gamawa ta shigo dakin su ta iske ummar ta zaune kan abun sallah ta idar da sallah tana shigowa umma tace koma kiyo alwala kizo ta koma tayo alwala tashigo tana zuwa umma tace maza kalli gabas kiyi sallah ki gayama Ubangiji bakiyi laifin da akace kinyi ba sannan Allah ya tsareki daga sharrin rabi, Allah kada yaba rabi galaba a kanki tace amin umma ta kabbara sallah ta umma na kallonta wata natsuwa na zuwar mata,tanajin ba dadi a ranta inama tanada wasu dangin da zatakai safiyya wurinsu wallahi dasai ta raba safiyya da gidan nan.....
Tana idarwa umma ta miko mata wata waina tace ungo kici saiki kwanta ki huta kafin la'asar kiyi wanka ki tafi islamiyyar tace umma nagode ta karbi wainar tanaci tana sake sake a ranta...
Tana gamacin wainar wani baccin wahala ya figeta anan inda take,umma na kallonta tanajin tausayin ɗiyar ta ɗaya tilo da Allah ya bata amma gata a gidan ubanta batada damar rabar ubanta taji dadi kullum itace wahala duk wata bauta ta gidan duniya safiyya tasanta🥹umma ta daga hannu sama tace Allah kayi gaggawar fitar man da safiyya daga cikin halin ƙunci kafin girma ya kamata💔
Umma zuwaira yar asalin garin Maiduguri ce anan aka haifeta ta taso a garin Maiduguri a gidan mahaifinta wanda babban malamin addini ne a garin Maiduguri,duk da basuyi boko ba amma sunada ilimin Islama da kuma wayewa daidai gwargwado, Allah ya jarabci mahaifinta da rashin haihuwa wanda umma zuwaira ita kadai Allah ya azurtashi da ita wanda a wurin haihuwar ta Allah ya dauki ran mahaifiyar ta wacce take itama yar uwa ga baban zuwaira hakika malam lawal ya girgiza rasuwar matar sa zuwaira,wanda ranar suna ta zagayo malam ya maidama umma sunan mahaifiyar ta wato zuwaira suna kiranta da TALLE baa wani jima da rasuwar zuwaira ba dangi sukayima malam caaa akan yayi aure yana babban malami bazai zauna ba mata ba duk da TALLE tana wurin yar uwarshi wadda suke kira da Dada da ita ke shayar da umma zuwaira nono a lokacin,haka malam ya hakura dangi suka kara aura mashi wata yar uwar shi halima,suka ci-gaba da zaman su lafiya amma Allah baiba halima haihuwa ba har lokacin da TALLE ta isa yaye Dada ta yayeta ta kawo ma halima ita dan tacigaba da rainon ta dan itama a lokacin ta samu sabani da mijinta dayasa ta taho gida har tace bazata koma da auren mijinta ba da yake Yobe....
Haka rayuwa taita tafiya yau daɗi jibi akasin haka amaryar malam na kulla da TALLE kmr itace ta haifeta Dada kuwa ta zamoma TALLE uwa da komai take so a lokacin ta koma gidan mijinta haka zata dinga yi masu aike a kawoma tallen ta...
Kwanci tashi ba wuya wurin Allah har halima ta fara girma sosai ta isa aure dayake Allah ya mata kyau kawai ita baka ce amma tanada wani irin tsananin kyau,masoya nata fito mata malam yana cewa a'a shi cikin almajiran shi zai duba mai hankali ya aurama talle tun samarin na zuwa har suka bar zuwa a lokacin ne malam yanemi shawarar halima kan tana ganin idan yaba Hamza auren talle bai kwarewa ba? halima tace duk wanda ya samu miji kamar hamza ya gode malam yaro mai ladabi da biyayya ko aiken shi zakayi bayasa idon shi cikin naka, halima tayi na'am da wannan malam kuma yaji dadi....
Watarana da safe angama karatun safe an tashi malam ya tsaida almajirin shi hamza yai mashi tayin auren diyar shi daya tilo,hamza yayi shuru saboda yanajin nauyin malam ne dan shima ya dade yanason tallen malam😁nace Allah ko Abba😁malam yayi murmushi na manya yace tashi ka tafi na baka izini kanemi so wurin talle idan Allah ya daidaita ku ina fatan hakan,hamza ya tashi yayi godiya ya tafi dadi fall ran shi shine malam yaima tayin auren yar sa guda daya tilooooooo,
×××××××××××××××
Soyayya mai karfi tashiga tsakanin Hamza da TALLEn malam,a lokacin ne malam yacema hamza ya koma gida kano ya sanar da dangin shi kasancewar sa maraya shima yana bukatar ganin danginsa domin a saka rana a fara shirye-shiryen aure su ranar zokaga murna wurin hamza da tallen sa,haka ya kama hanya ba inda ya sauka sai kano a cikin kanon ma a ƙauyensu mai suna (Kwankwaso)hamza yazoma da magabatan shi da maganar auren yar malamin su akai na'am suka saka lokacin zuwansu Maiduguri neman auren Hamza da TALLEn malam nan da wata ɗaya .......
Haka rayuwa ta cigaba a inda biki komai ya guda har lokacin biki ya karato zo kuga sha tara ta arzikin da Dada tayoma diyar ta daga Yobe saboda tana auren wani mai rufin asiri a garin duk wata karfin hidima itace dan malam bawasu kudi gareshi sosai ba,haka biki ya matso kwana gaf kusa,Ranar wanka ba'a boyon cibi yau al'ummar garin Maiduguri da kewayenta suka shaida daurin auren yar malam
Zuwaira Lawal
DA ANGON TA
Hamza Kabir Kwankwaso
Akan sadaki Naira dubu hamsin lakadan ba ajalan ba sai muce mama zuwaira Allah ya bada zaman lafiya amin
Fans ya kukaji labarin nan? Karfa ku manta littafin nan kyauta ne💃💃💃TO CHAT ME UP ONLY ON WHATSAPP ***......Yanzu ma aka fara labarin SAFIYYA tausai,uƙubar kishiyar uwa da mahaifi,rashin dangi na kusa,daga karshe zazzafar ƙiyayya da zata riɓanye ta zama soyayya da tausai🥹💔 I love You all let's go my people 💃💃💃💃💃💃💃💃💃🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
Ranar kai amarya malam ya zaunar da talle shida matar shi halima yayi mata fada sosaiiiiiiiiiiiiiiiiiii mai ratsa zuciya kan ta kula da mijinta ta kuma kula da hakkokin auren shi da ke kanta,daga nan kuma yan daukar amarya aka runguda daga Maiduguri akayi kauyen kwankwaso da zuwaira, Dada tayi kuka an rabata da yarta guda daya saboda ita gaba daya yaran da Allah ya bata duk maza shiyasa Allah ya dora mata son zuwaira a ranta,yan kai amarya sun iso kwankwaso lafiyar da ɗan madaidaicin gidan da hamza ya tada gini gidanshi na gado dada kuma kuma tayima amarya kayan daki gado kai harda kujerunta da tv zo kuga tururuwa wurin yan ƙauye ana zuwa ganin kayan ɗaki hamza ya auro ɗiyar malamin sa mai hali harda tv aka kawota dashi😁
Bayan sati biyu da auren hamza suna zama gidansu cikin so da kaunar juna hamza ko fita yayi baya nisa yake dawowa kawai dan ya dawo yaga zuwairar sa,anan ne wani kanen babansa yashi a harkar gwari saboda karatun allo aka tura yanzu ya dawo harda iyali dole ya koyi sana'a kodan kula da iyalin shi,hamza nada amana tun yana zuwa kawun nasa na koya masa harkar tar takai ta kawo hamza shike zuwa sarin kayan gwari ya dawo kuma ya saida ba tareda anji su ko sau daya ba a bakin tasha anan ne suke sana'ar su idan hamza ya fita gida tun safe baya dawowa gida sai magriba,haka zai dawo ya iske zuwaira wacce a yanzu yake kira da yar aljanna ta gyara gida ga abinci mai rai da lafiya ta kawo masa......rayuwa nata tafiya a kwana a tashi yau har gasu sun shekara da aure amma zuwaira ko ɓatan wata bata tabayi ba,a lokacin ne kuma Maiduguri suka fama da iftila'i na boko haram tun sunajin abun nesa har ya fara shigowa cikin garin,nan fa zuwaira ta tashi hankalin hamza tace itadai tanaso taje gida ta gano iyayen ta shikuma yayi mata alƙawarin idan ya kwashi adashen shi karshen wata harda shi zasu tafi tare domin shima yanaso yaje ya gaisheda malam,nan zuwaira ta kwandar da hankalin ta suka ci-gaba da gina soyayyar su cikin tsafta da ƙaunar juna da soyayya mai cike da tsantsan Addinin Islama.....
Ana gobe zasu tafi Maiduguri ganin gida zuwaira tashiga wurin maƙociyar ta maman hafsa tayi mata bankwana dan tunda aka kawota garin kwankwaso ba wanda ta yarda dashi irin maman hafsa saboda zuwaira Allah baiyita mai shige shige ba,ita kuma maman hafsa yar shiru shiru ce shiyasa taso tazo daya tana gidan wurin maman hafsa har magriba bata dawo gida ba saida hamza ya dawo ya aika yaro gidan yace acema zuwaira ya dawo haka sukayi bankwana da maman hafsa saboda gobe asubanci zasuyi subi motar kano daganan su hau ta Maiduguri
MAIDUGURI.............
Malam na zaune zaure angama karatu yara kowa ya tafi yaji sallamar da bazai taba manta muryar nan ba ta tallen shi,ya dago dattakun shi na kamala idon nasa ba gizo yake masa tabbas talle ce mijinta hamza suke tafe,suna zuwa suka zauna akan tabarma suka gaida malam yana fara ya ansa masu bakin sa walkam yanajin dadi da yanayin daya gansu cikin kwanciyar hankali,bayan sun gaisa zuwaira tashiga cikin gidan wurin matar malam halima murna wurin halima ba'a magana saboda dadi ta rasa inama zata saka kanta taji dadi,satin su biyu sun sha ziyara kaf gidan dangi ba inda basuje ba a garin nasu,taso taje har Yobe wurin Dada sai ta samu labarin Dada sun koma kano da zama saboda mijinta sana'ar saida furnitures yakeyi suka rabe da niyyar idan sun koma gida takanas zata taka har kano domin ta dubo Dadar taaaa
Hamza da zuwaira haka suka dawo gida kwankwaso zuwaira ranta taff da kewar iyayen ta da yan'uwa ta, rayuwa ta fara canza ma zuwaira a inda malam abokan sana'ar shi suka fara zugashi dafa ya kara aure ya shekara amma matar shi bata haihu ba kar yazo ya mutu ya rasa magaji ita kuma matar tashi ta koma garinsu daganan fa malam hamza ya fara canzama zuwaira yana nuna mata shifa haihuwa yakeso kota haihu ko ya kara aure😳😳 hankalin zuwaira ya tashi a lokacin ta nuna mashi haihu ta Allah ce da ita ke badata da tuni taba kanta a lokacin inaaaa malam hamza zuga shi akeyi bayaji baya gani baya gane karatun da yar aljanna ke masa, zuwaira kullum kuka maman hafsa kadai take fadama damuwar ta,ta bata hakuri tace mata indai Allah ke bada haihuwa zuwaira kema watarana zai baki🥹💔ya Allahu duk macen da ko namijin da suke neman haihuwa Allah ya basu masu albarka,ya Allahu kasa wanda basuda yara ka basu kasa sunada rabon ganin gudan jinin su a duniya👏🙏 Allah na rokeka da sunayen ka tsarkaka Allah karka jarabce mu da ƙunshi na rashin haihuwa ameen💔👏
Kwanci tashi abokan malam hamza sun hadashi da wata yarinya nan dake kawo masu taliya bakin tasha rabi,rabi kaf cikin matan talla ba bala'itatta irin rabi, babu mai rinton kudi irin rabi,ga son maza kamar zatakai kanta😁😂rabi wani abokin malam hamza yana mata tayin malam hamza tayi na'am dashi sbd dogo ne ƙaƙƙarfa ga saje rabi ranar ina aljanna ta tsoma kanta ranar da malam hamza zai fara zuwa zance gidansu zokaga iyayi itada uwarta sun samu malam hamza mai kayan gwari aka haɗama malam hamza sha tara ta arziki baban safiyya ya karkace kuwa ya ɗiɓi kauna lol😜