Free chapter · Read without an account
SAFIYYA PAGE 4
by Safiyya Muhammad · SAFIYYA
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Safiyya ta dawo daga ɗibar ruwan ta ta tarar da inna rabi batanan haka taita jidar ruwan nan saida ta gama ta shigo dakinsu ta samu ummanta tana bacci bata tasheta ba saida tagama tayi wanka tayi Sallah sannan tace umma umma ummata🗣️cikin bacci umma tace ummm yar albarka kingama tace eh umma ki tashi kiyi sallah har magriba ta kusa bakiyi la'asar ba tace to safiyya,umma ta yunƙura da kyal safiyya ta taimaka mata tayo alwala ya idar da sallah kenan umma ta juyo ta fuskanci ƴar tata tace safiyya komi ya faru dazu dukka naji gaban safiyya ne ya tsinke ya faɗi rassssssssss tace ummm umma,umma tace nasan kinajina duk da bansan waye wannan mai son taimakon naki ba amma inaji a jikina safiyya alkhairi ne,nidai ina maki da umarni idan abbanki yace zaya aurar dake ga mutumin nan ki yarda safiyya nagaji da ganin ki cikin ƙunci, safiyya nata kuka tace umma banso in tafi in barki gidan nan yaya kamal fa kano yake😭😭😭
Nan safiyya ta kwashe labarin tass ta fadama umma yadda akayi har suka haɗu da yaya kamal dinta,umma tayi shuru tace to safiyya tunda yace taimakon ki zayayi inaji a jikina taimakon naki zayayi goben idan ya dawo safiyya kice kin amince zaki aure shi nikuma ai kinga naji sauki ko,kuma zan samu waya saimu dinga waya dake ta wayar kamal dinko,safiyya ta lumfasa kawai ta amsa ma umma badan ranta yaso baa,saidan kawai batason ɓacin ran ummantaaa,daganan sukayi shuru ita umma na addu'a Allah yasa abbanta ya yarda da auren ita kuma safiyya tana tunanin taya zata fara rayuwa ba tareda umman ta ba💔
Rabi muka hango kan babur tafiya ake da ita kamar ta yada shege ana tafiya da ita cikin wani ruƙuƙin daji, sunfi awa suna wannan tafiyar a dashi su shiga wannan kuyya su fita wannan kuyyi haka dai har suka iso wani wurin da nagani hankali na yayi mummunan tashi wata nahiya ce guda ta wani riƙaƙƙen ɗan tsubbu daga bakin kofar shiga gidan an zuba wani cubci ga wasu ƙwarangal dana gani rataye nan gefe guda kuma wasu narka narkan bakaken karnuka ne sunfi talatin suna shawagi,suna wata irin gumza ta nama kawai suke jira daga saman bukkokin su kuma wasu shu'umannin biraye na hango kwakwkwance daga gefe guda ga wasu fararen awaki dana gani sukuma ban iya kirga ko guda nawane a wurin ga wani irin mugun wari kamar ana ƙona wani abu hayaƙi ya turniƙe sama ta ƙara hazo bakajin komai sai kuka muggan namun dashi,wata irin guguwa ce ta taso mai ƙarfi tareda wasu ƙaimi wasu maganganu na gigga giggan aljannu bakajin komai sai wasu surutai da baka gane gabansu bare bayan su,haka naga inna rabi ta zube a kofar gidan nan guguwar nan ta dauketa tayi wani sama sama da ita ta juya ta ƙara juyawa sannan naga ta dire rabi gaban wani azzalumin mutum baƙin shi bai misaltuwa ga wani irin gashi ko ina jikin shi ga wata ƙwarya gabanshi cike take da jini taff yana zaune akan wani jan buzu yana mazurai,rabi tace a gaisheka mai ifiritai da sarkin rahi,agaisheka mai yar mairo da masha ruwa, agaisheka bokan mu da baya saba lamba,angaisheka boka nakange ya lumfasa ya yafasa wata gigitattar ƙara yace rabi tun kina hanya aka shaidaman zuwanki rabi ta kara russunawa tace wannan haka yake ajikina naji kasan da zuwana,ya kara buga wani uban ihu yace yihuhuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu rabi itama ta maimaita yihuhuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu,yace rabi wannan yaro sunanshi kamal kuma soyayya gaskiya yakema safiyya abinda na fara bincike kenan kafin ki iso yanzu mikikeso ayi?rabi ta gyara zama tace boka nakange so nake a rabasu a saka mashi tsanar safiyya da duk wani namiji ko wani mahaluki indai na duniya ne a saka mashi tsanar safiyya da uwarta,boka na kange ya ƙara wani irin kwartsa ihu ya dake kwaryar jinin nan saiga wani haske ya fito fauuuuuuu ya kashema rabi ido da saida ta dauki minti biyar bata ganin komi
Saida ta dawo daidai boka na kange yace rabi rabuwar wannan yaro a hannunki take ta dafe ƙirji tace boka hannuna?yace eh ba yace auren ta zaiyi ba to muddin kika bari yaron nan ya auri safiyya to rayuwarki fa zata lalace,saboda yanada addini sosai itama yarinya tanada addini dan haka yanzu zan baki wannan hayakin kije gida gobe yana zuwa ki turara wannan hayakin karki sake ki kiyi magana da kowa ga laya nan zan baki ki bude ƙasan bakin ki ki sakata,duk juyin duniyar da za'ayi karkiyi magana har sai yaron yazo ya tafi sannan ki ciro layar ki sami rijiya ki sakata ciki yadda kika saka layar nan cikin rijiya haka yaron nan zaiji sha'awar aure ta fita daga ranshi gaba daya haba sai rabi ta washe baki,boka na kange yayi dariya yace banan gizo ke saƙar ba amma bazai rabu da yarinyar ba,abinda nakeso dake duk abinda kika gani karki sake kiyi magana mahadin maganin kuma yana tareda da mijinki zai ƙara tsanar matar sa da ita kanta safiyyar rabi tace boka nagode ta fiddo wannan kuɗi da kamal yaba safiyya ta ajema boka na kange tace boka ga wannan ya kalli kuɗin yace rabi masha ruwa na godiyaaaaaa
Haka rabi ta dawo gida ranta fall daɗi tana zuwa ta iske malam kwance kan gado,ko kallon shi batayi ba tace mi kakeman cikin daki kwance ya karkato yace rabi ina kikaje tace iyyi hamza yaushe muka fara wannan wasan?yayi shuru sannan ya tashi zaune yace rabi yaron nan da yace yanason safiyya nike neman shawarar ki gobe idan yazo ince ya bada sadaki kawai a daura masu auren da waccan baƙar ɗiyar haka yayi ko?rabi tayi zumbur tace kull malam wallahi bakasan mutum ba bakasan daga ina yake ba kawai ka dauki safiyya ka bashi ita,kuma idan ta tafi ubanwa zai dinga mana bautar gidan nan,ai safiyya bata ba aure harta mutu indai ina numfashi nan gidan zata dawwama abinda nakeso dakai gobe yaron nan na zuwa kaje kace mashi ka fasa aurar da safiyya kai makaranta boko zatayi malam ya zaro ido yace rabi boko tace eh boko,yace toooo sannan rabi tace kace mashi yasai mata littattafai da inifom na makarantar idan ya kawo nikuma zan barta taje bokon saboda akan hanya yadda na lura dashi dan iska ne can zai dinga tareta yana lalata da ita kaga tana dawo mana da ciki saimu koreta kaga babu maice maka danmi aiko take fuskar malam ta fadada murmushi yace gaskiya rabi kinfini hankali tace daman mana,kaga dai ƙauyen nan ba makarantar boko kullum saita hau abun hawa taje cikin Jigawa sannan zatayi bokon yadda take jakkar nan ita da kanta zatabar zuwa makarantar ina nan dakai hamza yace gaskiya ne rabi🤣
Washe gari haka kamal ya kamo hanyar roni ya iso kofar gidansu safiyya ya samu yaro yace aje ace yana sallama da abban safiyya yaro na zuwa yayi sallama yace wai ance ana sallama da abban su safiyya malam na tsakar gida yace jeka kace ganinan zuwa,rabi tunda aka tashi yau ba wanda tayima mgn ga uwar laya ta tausa a bakinta🤣tanajin sallama ta dauko kasko ta zuba garwashi ta turnike gidan da hayaƙi malam dai baice komi ba ya dauki tabarma yayi zauren,yana isa ya shimfida yacema kamal yaro Bismillah kamal ya shigo ya russuna yace abba ina wuni daidai nan kuma yaji kamar an caka mashi a tsakiyar saida wuta ta dauke mashi na ɗan wani lokaci sannan ya zauna,malam yai shuru yana tunano maganganun da inna rabi ta bayyana mashi jiya da niyyar dama yau in kamal yazo zaya fadamasa,malam ya gyara zama suka kara gaisawa yace yaro maganar auren safiyya ta kawoka gaskiya na canza shawara yarinya ta karatu zatayi kamal baisan meyasa ba kawai sai yaji hankalinshi yafi natsuwa kan karatun safiyya,kamal yace nima Abba ba maganar auren ta kawoni ba saboda na yanke hukuncin bazan auri safiyya ba malam yace ahaf faduwa tazo daidai da zama kenan kamal ya nisa yace eh Abba, Abba ya kara gyara zama yace zan amince safiyya tayi karatun bokon nan amma batada inifom batada littafi kuma ni banida kudin motar da zan dinga bata kullum tana zuwa jigawa makaranta,kamal yace baba zansa ayimata uniform da komi da komi makaranta zuwanta kuma inaga bazai gagara ba indai ka amince yanzu ma ana iya kirawoman safiyya muje can jigawar makarantar inyi mata registration na komi malam yace ahto ba matsala bari in turo maka itaaaaa
Koda malam yashigo direct dakinsu safiyya yayi ya yaye labulen yace ke safiyya kije ga wannan yaron nan yazo zai kaiki makaranta,dama abinda kikeso kenan kita yawo titi titi kina gogayya da maza to burinki yacika keda uwarki ya nuna umma da take zaune kan abun sallah alamun sallah azahar ta gama,safiyya batace komi tace to abba tana tunanin to meya canzama Abba shawara kan auren dayace zayayi mata,Abba ba tafiya ta dauko hijabinta tazo gaban umma tace umma kinje me abba yaceman inje umma kawai kai ta daga mata tace Allah ya tsare gabanki da bayanki,safiyya tace amin tana fitowa inna rabi ta dalla mata harara itama kuwa ta maida mata ta dauke kanta tayi hanyar soron gidansu tana zuwa ta samu kamal gaban mota ko kallon ta baiyi ba yace shiga ciki,tayi jimm ta kama gaban motar ta bude ta shiga ya falla motar da gudu suka dauki hanyar shiga jigawaaaaa,inna rabi najin haka ta tashi tayi waje da laya a bakinta taje bakin rijiya ta jefa sannan tace haba yarinya dani rabi kike magana baki ba labarin ki wallahi nagama da uwarki balle ke baƙar daga…..