Free chapter · Read without an account

When Shadows Wake

by NorthernAngel · His Rose

Bayan kusan forty minutes na skin-to-skin care, Zafar ya yi wa neonatal nurse ɗin alama da hannu don ta matso ta karɓi Jasmine, saboda ganin yadda bacci ya gama ɗauke Zara gaba ɗaya kuma she seemed so uncomfortable a yadda take kwance ɗin. Miƙewa ya yi ɗaidai lokacin da neonatal nurse ɗin ta iso gabansa da girmamawa. Ya miƙa mata Jasmine a hankali, bayan ya yi pressing a soft kiss a kanta for the last time. Yana biye da nurse ɗin a kan kowane taku har ta maida ita cikin incubator ɗinta cikin tsaro, sannan ya juyo zuwa ga matarsa. Inda Zara ke kwance a kishingide ya ƙarasa, ya ɗan duƙa sannan ya sanya hannayensa biyu yana ɗago ta a hankali tare da janyo mayafinta dake ajiye ya yafa mata a jikinta, yana faɗa softly, "Come on, princess... let's head back. You need to get some real rest now." Buɗe idanunta tayi a hankali tana kalle-kalle a cikin private NICU suite ɗin. Ganin babu baby ɗin a jikinsa yasa ta tambaye shi da sauri inda take, shi kuma cikin lallashi ya ce mata an maida ta cikin incubator ɗinta, amman zasu dawo anjima da dare su sake ganin ta. Daga haka ya ɗaga ta ya ɗan rungumo ta a jikinsa for support, sannan suka fara tafiya a hankali suna fita daga suite ɗin. Bayan sun koma maternity wing ɗin suka tura ƙofar ɗakinta, suka tarar da Amrah, Imaan, Noor, da Mu'azzam a zaune—da alama ba su daɗe da ƙarasowa asibitin ba. Sannu da jiki suka shiga yi wa Zara a tare, wadda ko kallon ɓangaren da suke ba ta yi ba; ta gitta ta gabansu kamar ba ta gansu ba, ta wuce kai tsaye zuwa kan gado ta kwanta, sannan ne kuma ta miƙa wa Amrah hannunta tana sakar mata a faint, weak smile. Wani abu da Noor ta daɗe da lura shine, Zara ta daina yi musu magana kwata-kwata tun sanda aka kwantar da ita a asibitin nan. Ita Noor ɗin ba ta faɗawa ko Omar ba; da Imaan kawai suka taɓa maganar a tsakaninsu, inda Imaan ke faɗa mata abinda Yemma ta aikata ranar da suka dawo daga Dubai. Saboda ranar, bayan Imaan ta hau sama, ta sake fitowa inda tana tsaye a saman bene taji duk masifar da Yemma ke yiwa Zara—so Imaan na zargin a kan wannan abun da Yemma tayi ne yasa Zara daina yi musu magana gaba dayan su. Shi ma Zafar tun tuni yana lure da cewa ba ta kula ƙannensa idan sun zo duba ta, amma kafin ta haihu sam bai kawo komai a ransa ba—yayi tunanin kawai ɗan tana cikin halin jiki ne da intense labor stress, ga kuma unpredictable post-partum mood swings. But yau kam ya fahimci akwai wani abu da ke ranta, dan tunda suka turo ƙofa suka shigo, ya lura da yadda ta haɗe ranta a take tana ganinsu Imaan. Dukkansu dai basarwa suka yi a ɗakin don kauce wa matsala. Noor ta fara jan Zafar da hira don rage nauyin atmosphere ɗin, yayin da Zara ke magana tsakaninta da Amrah da Mu'azzam kawai. Imaan kam ganin yadda yanayin ya koma daban, miƙewa ta yi cikin sanyi ta ce za ta koma mota, daga haka ta juya ta fice daga ɗakin. Haka Zara ta riƙa magana da kowa a ɗakin ban da Noor. Ko Noor ta saka baki a maganar ko ta yi tambaya, Zara ba za ta acknowledging ɗinta ba sam—kamar ba halitta ke magana ba. Zafar, da tuni kansa ya gama ɗaurewa kuma ransa yayi masifar sosuwa da wannan halayyar ta rashin kara da ko in kula, bai ce mata uffan ba a lokacin, ya daure kawai yana kallon ikon Allah. Kusan 25 minutes suna zaune suna hira a ɗakin, yayin da Zara ke kwance ta ɗora kanta a kan cinyar Amrah. Noor kam gaba ɗaya jikinta ya gama yin sanyi; a da, duk abin da Zara ke yi mata ba ya damun ta saboda ta san ba har zuciyarta ba ne, amma na yanzu kam sosai ta fahimci tsantsar ƙin da Zara ke nuna mata. Hatta Mezyan ta daina ɗauka, Zwar kawai take ƙulawa idan suka zo. Mu'azzam kuwa sam bai ma lura da abin da ke faruwa ba, tunda daman can ba wani shiri na a-zo-a-gani suke yi da Noor ba. Miƙewa Noor ta yi tana gyara rigarta, ta yi ɗan gyaran murya tana faɗin, "I'm going to track down Yaya and just head out from there. See you guys later." Da ɗan mamaki Amrah ta ɗago tana kallonta, "Aah, thought we were all staying until tonight?" Juyawa Noor ta yi ta fara takawa zuwa ƙofa tana cewa, "No, I actually have some things I need to take care of at home. Sai kin dawo." Daga haka ta fice daga ɗakin ba tare da ta tsaya jiran amsar kowa ba. Zara, da ko sau ɗaya bata kalli inda Noor take ba, kawai ta ɗan  taɓe bakinta tana jin wani irin sanyi a ranta da ta tafi. Don ita yanzu duk abin da ya shafi Yemma, haushinsa kawai take ji—banda mijinta. Idanun Zafar kuwa na kanta a duk tsawon lokacin, don haka kowane reaction da take yi yana sane da shi, bai dai ce uffan ba. Wayarta da ke ajiye a gefenta ce ta fara kawo haske gami da vibration, wanda hakan ya sa Amrah janyo wayar tana miƙa mata ganin sunan Vicky na yawo a kan screen ɗin. Zara ta karɓi wayar, amma ganin Vicky ce ke kira ya sa ta ajiye ta a gefe saboda gaba ɗaya ta gaji bacci take son yi. Sai dai wayar ba ta fasa vibrating ba saboda yadda Vicky ke ta repeated calls. Ganin nacin kiraye-kirayen yasa Zara janyo wayar ta ɗaga cikin sanyi, saboda tunanin ko wani abun gaggawa ne ya faru a gida da yake sa Vicky kiranta haka, ko kuwa ko Mommy take nema. Picking call ɗin Zara ta yi, "Hello," ta faɗa cikin soft voice ɗinta mai cike da tsantsar gajiya. "Hey there, heartbreaker..." Wata croaky voice da ke cracking ce ta amsa ta, wanda muryar ta sanya Zara yi wa wani irin zabura a kan gadon tana zaro idanuta waje. Ko a tsakiyar mafarki ta ji wannan muryar, ta san mai ita sarai—sai dai a inda ta ji muryar ne ya sanya ta tsantsar mamaki saboda sam ba ta yi tsammanin hakan ba. Cikin mamaki da raw shock ta sake cewa, "Hello?" ɗan ta tabbatar da ainihin abin da kunnuwanta suka jiyo mata. Wannan short, breathy chuckle ɗin that she knows all too well ta sake ji, kafin muryar ta sake biyowa baya, "Yeah, it’s really me, Rose. You still out there tearing people's hearts to pieces?" Ya faɗa with a raspy voice cikin sigar tsokana da son kauda tension, but ita da ta sansa ta san ainihin abin da ke zuciyarsa yake gaya mata. Shiru Zara ta yi gaba ɗaya, ta gaza motsa koda yatsanta ne, ta kuma nemi kowane kalman magana a bakinta ta rasa kwata-kwata. Jin ba ta ce uffan ba ya sanya shi ci gaba da magana cikin wata broken, fragile voice, "I've been dying to reach you for so long, Rose. But I actually ended up in a really bad accident the moment I arrived in Nigeria months ago... things went completely south, leaving me in such rough shape that I only just woke up from a coma a week ago. Please, Rose, let me see you. I really need to talk—" Bai gama ƙarasa kalaman nasa ba, Vicky da ke tsaye a kusa da shi ta yi hanzarin ƙarɓar wayar daga hannunsa, "Rose, listen to me closely. Can you hear me?" Zara da ke cikin tsantsar paralyzing shock har lokacin ta ce, "Yes, yes... What on earth is going on? What happened to him?" Ta yi tambayar a daburce, dan kwakwalwarta ta gaza processing koda ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan a lokaci guda. Vicky ta fara magana cikin gaggawa da saurin muryarta, "Are you next to your husband right now? Keep your composure. Don't say our names out loud, just let him speak." Frowning Zara ta yi nan take, ta ɗago kanta a hankali ta kalli Zafar da ke zaune—idanunsa na maƙale tsam a kanta ba tare da ya kifta su ba. Ƙauɗa kanta ta yi da sauri daga gare shi tare da sauke idonta ƙasa, sannan ta ce, "Right, I'm all ears. Go ahead." Muryar Roman ta sake dawo wa a cikin kunnenta, "I need to see you, Rose... can you please come to the hospital where they're keeping me?" Kafin ma ta bashi amsa, ta tsinci muryar Vicky tana ce masa, "Visiting today is out of the question for her, Roman. I'm going to pass along the facility details, and she'll visit as soon as it's possible." Ɗan shiru ya yi na ƴan daƙiƙoƙi, kafin ya sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya mai rauni, yana cewa, "Why not today, Rose? I'm begging you... I really need to talk to you face-to-face." Zafar Zara ta sake kallo ta gefen idonta, gani tayi har yanzu idanunsa na kanta babu ko alamar kyaptawa. Bama shi kaɗai ba, kusan kowa da ke cikin ɗakin—wato Amrah da Mu'azzam—kallonta suke saboda she was acting extremely weird. Kana gani kasan tana ƙoƙarin ɓoye wanda take waya da shi ne, kamar wata marar gaskiya ko wacce aka kama da wani lefi. Gyaran murya ta yi tana gaggawar ɗauke idonta daga kan Zafar, "Um... I'm actually dealing with a medical issue right now, so I can't. Just have her text me the details." Roman, da ya gane address take nufi, ya ce cikin gaskiya, "Okay, but tell me the truth, are you safe? What's making you sick?" Da sauri cikin daburcewa Zara ta ce, "No, I'm fine... I'm just—I mean, I... I just had my baby two days ago, so I... I’m still in the hospital recovering." Ganin yadda take inda-inda tare da rashin natsuwa tana neman kalaman da zata fada ya sanya Zafar frowning deeply, nan take yanayinsa da kwarjininsa suka harba sama. Cikin mamaki, zafi, da wani irin sharpness daya mamaye muryarsa, yace, "Who the fuck are you talking to?" Cikin sauri Zara ta fara ƙoƙarin kammala wayar ta, tana cewa, "Got it, thanks. Go ahead and send over the details and the boutique location. I'll check out the setup as soon as I'm out of bed." Roman ya yi ɗan soft, raspy chuckle a ɗayan ƙarshen layin, yana faɗin, "Alright, understood… take care of yourself, Rose. Wish you a fast recovery, and give that little angel a kiss for me." Gyaɗa kai Zara ta yi cike da sauri tana cewa, "Okay, Anna, I have to go now. Bye." Daga haka ta yanke call ɗin a firgice, tana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ta ɗago tana kallon Zafar, wanda ke danna wayarsa distractedly tare da wata irin tense aura da ta cika gaba ɗaya yanayinsa. Mu'azzam da ke ta kallonta da dan yanayin mamaki ta kalla, dismissively ta fara bayani, "It was just Anna being her usual dramatic self, blowing up my phone." Ta ƙarasa maganar with a short, nervous laugh desperately trying to clear any suspicion. Daga haka ta koma ta kwanta a hankali, tana sake sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi. Kusan 10 minutes suna zaune suna hira a ɗakin, gaba ɗaya sai murna da farin ciki suke yi bayan Zafar ya sanar da su ainihin sunan da aka sa wa jaririyar. Har Omar ya shigo tare da Zwar shi ma, duk suka hau nuna tsantsar farin cikinsu jin cewa sunan Maamah aka sa wa baby girl ɗin. Zara dai tun lokacin she was completely distracted. Baccin da take so ta yi ɗin ma ta kasa yin sa kwata-kwata, gaba ɗaya tunani ne da overwhelming anxiety suka mamaye mata ƙwakwalwa. Tambayoyi marasa adadi ke ta faɗowa a ranta—musamman game da abunda ya samu Roman har ya tafi coma na tsawon watanni, da kuma dalilin da ya sa Vicky ta gargaɗe ta da kar ta bari Zafar yaji komai. Koda ma Vicky ba ta gargaɗe ta ba, ita kanta ta san ba za ta taɓa kuskuren barin Zafar ya sani ba. Saboda ta san ko sunan Roman kaɗai ta ambata a gabansa fada suke yi a kan kishi, balle kuma ya ji cewa shi ne da kansa ya kirata a waya. Sai dai abin da ke damunta shi ne, ba ta gane exact motive ɗin da ya sa Vicky ta ce a ɓoye masa ba. Daga ƙarshe dai sai kawai ta kawar da tunanin a ranta, tana cewa wataƙila out of concern don gudun jealous drama ɗin maza shi ya sa ta ce a sakar masa labule. Haka dai ta yini a ranar tana ta faman overthinking, sam ta kasa samun bacci ko kaɗan ta huta ma jikinta da ranta. Kowa a ɗakin na lura da yadda takura ta bayyana a fuskarta—musamman Zafar da ke maƙale a kusa da ita yana auna kowane motsinta—gashi tun ɗazu take ta faman ajiye ajiyar zuciya, wadda ta sauketa yafi cikin trailer…




Wdyt loveliess?😁

1. What are your honest thoughts on how Zara treated Noor and Imaan? Do you think her cold attitude towards them is completely justified because of Yemma's actions, ko kuwa ta ɗan yi overreacting over precious family bonds?

2. Do you think Zara is making the right call by keeping Zafar completely in the dark about Roman’s call? Or is she playing with fire by keeping a secret from a fiercely protective husband like Zafar?

3. Looking at how sharp Zafar’s instincts are, how long do you think it will take before he pieces everything together and discovers the truth behind that "Anna" call?

Drop your thoughts in the Z&Z conversation group, I’m eager to read all your theories! 

Ps: I missed youuuu guyssss liiikeeee hellllll🥹
Xoxo🤍💋

Obsessively yours🪽

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol