Free chapter · Read without an account
Chapter 3
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsar Arewapen
Wattpad: umma mustapha
PAGE 3
Washegari da sassafe, Nihla ta farka da wani irin nauyin zuciya. Ta zauna ta jingina da gado, idanuwanta suka sauka kan wayarta da ke gefen pillow.
Abu na farko da ya zo mata a rai shi ne Irfan.
Ta ɗauki wayar da sauri, ta duba ko akwai wani kira ko saƙo daga gare shi. Amma babu komai.
Har yanzu shiru.
Ta lumshe idanunta, sannan ta sauke ajiyar zuciya.
"Ya Allah, ina Irfan yake?"
Ta sake buɗe wayar, ta duba lambarsa. Hannunta ya tsaya kan sunansa na ɗan lokaci, amma ta kasa danna kira. Wani irin tsoro ya hana ta.
A wannan lokacin ne aka kwankwasa ƙofar bedroom ɗin.
"Nihla?"
Muryar Fatima ce.
Nihla ta goge fuskarta da sauri kafin ta amsa.
"Shigo."
Fatima ta buɗe ƙofar ta shigo, tana kallon Nihla da fuskar damuwa.
"Kin tashi kenan?"
"Eh."
Fatima ta zauna kusa da ita.
"Yaya jikinki ? Har yanzu kina jin ciwon kai?"
Nihla ta yi shiru na ɗan lokaci. Cikin sanyi da karyewar murya ta ce:
"Da sauƙi."
Fatima ta kalle ta sosai, kamar tana son gano abin da take ɓoyewa.
"Nihla, akwai wani abu da nake son tambayarki tun jiya."
Nihla ta ɗaga idanunta.
"Me?"
Fatima ta ɗan yi shiru kafin ta ce:
"Ina son sanin damuwarki."
"Ba ni da damuwar komai. Kamar yadda na faɗa miki, kaina ne ke ciwo, sai ɗan zazzabi," Nihla ta ba ta amsa.
Shiru Fatima ta yi kamar ba za ta ƙara cewa komai ba, sai can ta nisa.
Ta saka hannu ta kama hannun Nihla.
"Kalleni, Nihla. Kin sani babu wata magana da za ki faɗa min da zan yadda da ita. Kina cikin damuwa. Damuwace take damunki, ba wai rashin lafiya ba. Hasalima, damuwar ce ta saka miki ciwon kai da kuma zazzabi.
"Akwai abin da kike ɓoyewa, ya kamata na sani, ko don mu taru mu samu mafita. Nihla, barin kashi a ciki baya maganin yunwa. Don Allah, ki sassauta wa zuciyarki."
Murmushi dole Nihla ta kakalo ta yafa a fuskarta, sannan ta kalli Fatima.
"Ba ki yarda da ni ba? Ko ba ki yarda da abin da na faɗa miki ba?"
"Da gaske, kawata, babu wani abu da yake damuna, bayan abin da na faɗa miki."
Fatima ta sauke numfashi.
"Nihla, kar ki manta, duk wani motsinki na san abin da yake nufi. Zan iya cewa ko yayenmu ba su kai mu fahimtar juna ba da sanin halin juna. Ni na san akwai wani abu da kike ɓoyewa. Amma ba zan takura ki lallai sai na sani ba. Maybe matsayina da muhimmancina bai kai na san damuwarki ko matsalarki ba.
"Zan ba ki lokaci, na gani."
Murmushi Nihla ta sake yi a karo na biyu. Ta saka hannu ta lakace hancin Fatima, tana mai cewa:
"Babu wani abu da zan ɓoye miki a rayuwata, ke ma kin sani."
Ita ma Fatima murmushi ta yi, ta yunƙura ta miƙe. Ba wai don ta yadda da maganar da Nihla ta faɗa mata ba, kawai ba ta son takura mata.
"Ki tashi ki yi wanka mu karya, lokaci ya ɗan ja."
Ba ta da zaɓi illa ta miƙe ta shiga bandaki, ita kuma Fatima ta fice ta koma kitchen tana haɗa musu abincin safe.
Bayan ta fito daga wanka, ta shirya a cikin riga da wando falazo. Kayan sun amshi jikinta sun yi mata kyau. Ta ɗauko ribbon ta ɗaure kalabar da ke kanta tana lilo, ta ɗauki hula ta saka a kanta. Wayarta ta ɗauka ta fice daga ɗakin ta nufi falo.
Ta tarar da Fatima ta gama musu komai. Don haka zama suka yi, suka fara breakfast. Dankali da soyayyen ƙwai ne, sai tea da kuma bread.
Ita dai Nihla iya tea da bread ta ci, sai ƙwai da ta haɗa da shi. Ci kawai take, ba don daɗi ba, sai don kawai ta yi maganin yunwar da ta addabi cikinta. Amma ji take kamar tana haɗiyar magani. Haka dai ta samu ta tuttura.
Bayan sun gama, Fatima ce ta gyara wurin, ita kuma Nihla ta nufi kitchen. Ta buɗe fridge ta ɗauko ruwan lemon tsami ta sha, don ya zamar mata jiki. Duk lokacin da ta ci abinci sai ta sha ruwan lemon tsami. Idan ba ta sha ba, amai za ta yi. Wannan dalilin ne ya sa ba ta rabuwa da shi a gida ko a school.
Sai da ta leka cikin fridge ɗin ta ga saura roba nawa ne suka rage mata. Sannan ta rufe ta bar wurin, ta dawo falo ta zauna.
Fatima ta ce mata:
"Yau fa za mu fita karatu. Na ji za a gudanar da tutorials a cikin IJMB."
"Da to," Nihla ta amsa mata, don tasan ko ta ce mata ba za ta je ba, Fatima ba za ta rabu da ita ba. Amma ita ta san ko ta je, babu abin da za ta fahimta ko ta gane.
"Karfe nawa za a fara?" ta faɗa tana kallon Fatima.
"10:00 zuwa 12:00 ne," ta ba ta amsa.
Agogon da ke falon ta kalla. Goma da kwata ya nuna. Ta mai da hankalinta kan Fatima.
"Kinga, 10:15 ma ta yi."
"To, sai ki tashi ki shirya mu tafi," Fatima ta faɗa tana miƙewa, gami da nufar bedroom domin ɗauko kayan karatunta da kuma mayafinta.
Har Fatima ta fito, Nihla tana zaune a inda take, ba ta motsa ba. Fatima ta kalleta.
"Zaman me kike yi kuma?"
"Ko za mu ɗan ƙara lokaci? Kinga, har yanzu Rabi ba ta zo ba. Shi ma Tasi'u, kinga bai zo ba."
Agogo Fatima ta kalla, sannan ta ce:
"To, bari mu jiransu zuwa goma da rabi."
Rabi yarinya ce da ba za ta wuce shekara goma sha biyar ba. Ita ce take yi wa Nihla ɗan aike-aike, shara, mopping, wanke-wanke da sauran ayyukan gida.
Shi kuwa Tasi'u almajiri ne ɗan kimanin shekaru goma sha biyu. Aikinsa kawai shi ne share harabar gidan da kuma ba furanni ruwa, sai idan shara ta cika ya zubar.
Zama suka ci gaba da yi suna jiran tsammani. Can Nihla ta dubi Fatima ta ce mata:
"Kin yi magana kuwa da Jabir?"
"Mun kwana biyu ba mu yi magana ba. Naga ya shiga busy ne, shi yasa na bar shi ya huta."
"Ya faɗa miki ranar da zai dawo?"
"Ah-ah, gaskiya bai faɗa min ba. Amma dai na san ba zai wuce Saturday ko Sunday ba."
Suna cikin wannan tattaunawar ne suka ji ana buga ƙofar gidan.
Fatima ta tafi ta buɗe, Nihla kuma ta nufi cikin bedroom don ɗauko hijab ɗinta.
Wani babban hijab ta ɗauko ta saka, wanda ya daukar mata har ƙasa. Wannan dokar Irfan ce; baya barinta saka mayafi, sai dai idan abaya ta saka, sai ta yafa mayafin abaya. Amma idan ba abaya ba ce, ko wane irin kaya ta saka, hijab za ta ɗora masa. Haka ya koyar da ita.
Shi yasa kayanta ma abaya suka fi komai yawa. Ba ta rabo da su, kullum cikin siyo mata abayoyi yake.
Turare ta ɗan fesa sama-sama, sannan ta janyo ƙofar bedroom ɗin ta rufe.
A falo ta tarar da Fatima tare da Rabi.
Rabi ta rusuna.
"Anty Nihla, ina kwana?"
"Lafiya lau, Rabi. Kin karaso?"
"Kinga, fita za mu yi, kuma maybe za mu ɗauki lokaci kafin mu dawo. Don haka idan kin gama komai, ki kulle gidan ki tafi da mukullin. Idan mun dawo, za mu biyo ta gidanku mu karɓa.
"Idan kin tashi tafiya, ki duba cikin fridge, akwai abinci a wata roba ki tafi da shi."
Rabi ta amsa da "To," gami da yin godiya.
Daga haka suka sa kai suka fice daga gidan.
Cikin nutsuwa suke takawa. Yau ba ta nemi Malam Musa ba, da ƙafa suke tafiya. Nihla tana son tafiyar ƙafa, ko don motsa jiki da kuma kallon gari.
Shekararta huɗu kenan ko biyar, idan ka haɗa da yajin aiki da kuma hutun coronavirus da aka yi, da zuwanta garin. Amma har yanzu ba ta san ko ina a garin ba. Daga makaranta sai hostel, sai kuma IJMB. Ita ma ba ta cika zuwa da kanta ba, sai dai Irfan ya kaita sannan ya ɗaukota.
A hostel, bayan Fatima, ba ta san kowa ba, kuma ba ta saba da kowa ba. Saboda Nihla ba mace ce mai sakin fuska ga kowa ba. Tana da shiru-shiru da rashin magana, ga uwa uban kuma miskilanci.
Kaf faɗin jami'ar, idan ka cire Fatima da Jabir, sai Oga kwata-kwata, wato Irfan. Babu wanda take lulawa.
Wannan dalilin ne ya sa mutane da yawa suke mata kallon tana da girman kai. Sai dai ba haka ba ne. Nihla tana da kirki sosai kuma tana da son taimakon mutane. Abin duniya kuwa kwata-kwata bai dame ta ba.
Tafiya suke yi. Nihla tana yan kalle-kallenta, gefe ɗaya kuma zuciyarta cike take da tunani da kuma faduwar gaba da take fama da shi.
Haka dai suka ƙarasa har cikin IJMB. Suka nemi class ɗin da ake gudanar da tutorial ɗin, suka shiga. Guri suka samu suka zauna. Ba laifi, yau an cika, ko don students sun ga jarabawa ta matso.
Class rep ne yake gudanar da bayani akan wani course na Accounting. Kowa ya yi shiru yana saurare.
Ita kuwa Nihla kwantar da kanta ta yi akan benci. Ba bacci take ba, idonta biyu , amma dai hankalinta baya kansu.
Shi kansa class rep ɗin ya yi mamaki, don Nihla tana ɗaya daga cikin overall students na class ɗin. Amma yau ya ga ta yi wani irin shiru. Sai dai ya mata uzuri, maybe ba ta da lafiya jiki da jini.
A haka dai aka kammala aka tashi. Malam Musa ne ya zo ya kwashesu, suka biya gidan su Rabi suka karɓi key.
Daga nan suka yi gida. Sun kwaso rana da gajiya, don haka suna dawowa kowacce ɗaki ta shiga ta watsa ruwa.
Fatima kwanciya ta yi a bedroom ɗinta, ta fara bacci. Nihla kuwa wayarta ta ɗauka ta saka musu order ɗin abinci a restaurant ɗin makaranta, sannan ta saka Malam Musa ya je ya karɓo musu.
Magungunanta ta ɗauko ta haɗiye, sannan ta zame ta kwanta. Ba ta fi mintuna uku da kwanciya ba, ta fara lumshe idanunta. Da alama bacci ke son ɗaukarta; a cikin magungunan akwai na bacci.
Bingirewa ta yi, ta fara bacci a wurin.
Ko da Malam Musa ya kawo abincin, sai Fatima ce ta fita ta karɓo. Tazo ta tarar da ita tana bacci, don haka sai ta saka abincin a fridge, ta koma ta kwanta.
Ba su tashi daga wannan baccin ba sai da aka yi kiran sallar La'asar.
Nihla ta farka da kasala da mutuwar jiki. Da ƙyar ta miƙe ta shiga toilet ta yi wanka, sannan ta yi alwala. Ta saka kaya ta tarar da sallah.
Bayan ta idar da sallahr, ta nufi falo. Ba kowa a falon, sai ta nufi ɗakin da Fatima take ta iske ta tana sallah. Kujerar da ke gaban mudubin ɗakin ta je ta zauna a kai.
Kallon kanta take a madubi. Tabbas ta yi muguwar rama, ga ƙashin wuya har ya fito mata.
Fatima ta idar da sallah.
"Ga saƙo can Malam Musa ya kawo. Lokacin da ya kawo kina bacci, na saka miki shi a fridge."
Nihla ta ce:
"Bari na dumama mana shi. Abincin ne na yi mana order. Nasan ba za mu samu damar girki ba."
Miƙewa Fatima ta yi.
"Ke da ba ki da cikakkiyar lafiya ba? Bari na yi amfani da microwave na dumama shi, naga sun kawo NEPA."
Tare suka fito daga ɗakin. Fatima ta wuce kitchen, ita kuma ta zauna a falo.
Dambun shinkafa ne da gasasshen kifi, sai haɗin salad. Har sun zauna za su fara cin abincin, Nihla ta miƙe ta shiga kitchen ta ɗauko ruwan lemon tsamin ta. Ta ajiye shi a gefe, sannan suka fara cin abincin.
Bayan sun gama cin abincin, suka ci gaba da zama. Fatima tana TikTok tana kallon abubuwa. Lokaci zuwa lokaci takan nunawa Nihla wani abu idan ta gani, musamman abin dariya.
Nihla dai kawai kallon Fatima take. Tana jin dama ita ce a matsayin Fatima, ba ta da abin da yake damunta, ba ta da wata fargaba. Amma ita ta rasa nata sukunin da jin daɗi da farin ciki.
Yunkura ta yi ta miƙe ta shiga bedroom don sallar Magriba. Bayan ta yi sallar, ba ta tashi ba, ta ci gaba da zama tana tunanin rayuwarta.
Ba ta fito ba sai da ta yi sallar Isha. Sannan ta dawo falon, suka ci gaba da firar jefi-jefi. Ba wai don tana son firar ba, sai don tana so ta tabbatar wa Fatima babu abin da yake damunta, alhali kuwa can ƙasan zuciyarta...
Tayi ƙoƙari har suka kai goma, kafin ta tafi ta kwanta.
Bayan ta shiga ɗaki, ta yi ƙoƙari ta sauya kayanta zuwa na bacci. Sannan ta ɗauko body spray ta fesa, hasken ɗakin ta kashe. Ta ɗauki remote ɗin AC ta rage mata gudu, sannan ta saka hannu ta janyo abin lulluba ta rufe iya ƙafafuwanta.
Wayarta ta ɗauka ta shiga WhatsApp ɗinta. Chat ɗinsu da Irfan take dubawa, musamman inda suka yi exchange na kalamai. Daga nan ta koma kan gallery na wayarta, ta kalli hotunansu da kuma short videos da suka yi tare.
Idanuwanta ne suka ciko da hawaye. Ba ta hana hawayen zuba ba, kuma ba ta saka hannu domin share su ba. Tana buƙatar yin kuka, tana son ta zubar da hawaye ko za ta samu sassauci.
"Wai me ke shirin faruwa da ni ne? Wacce irin ƙaddara ce take shirin tunkarata?"
Shin ko guduwa Irfan ya yi ya bar ta?
Da sauri ta girgiza kanta.
"Irfan ba zai taɓa guduwa ya bar ni ba. Tare muka shirya komai, kuma ya yi alƙawarin tsayawa tare da ni. Ko da kowa zai guje ni ko ya juya min baya, Irfan yana tare da ni."
Duk duniya babu wanda zai yarda da ita. Irfan ne shaidarta, kuma shi ne hujjarta. Kuma shi ne zai zama lauyanta a duk lokacin da sirrin ya so buɗewa.
Damuwar cikin nan shi ne mabudin sirrin. Idan ba zubar da shi za ta yi ba, domin rufe sirrin da ke tsakaninsu, to amma ko ta zubar da cikin, wanne tabbaci take da shi cewa asirinsu zai ci gaba da rufuwa?
Duk girman gona akwai ƙarshen kunya. Dole wata rana asirinsu zai tonu, musamman yanzu da take shirin gama makaranta. Wani sabon babi na rayuwa za ta shiga.
Don haka ta yi shiru tana tunanin rayuwarta ta baya.
"WAIWAYE ADON TAFIYA," INJI MALAM BAHAUSHE.
Umsar ✍️
***