Free chapter · Read without an account

DA JININSA NAKE RAYUWA

by Sayyid · DA JININSA NAKE RAYUWA

“Dimple ko?” 

Husna faɗa tana sake kallonsa, sai dai kamar ba dimple bane abin da ya riƙe idonta, domin suma Ashir ɗin su yana da dimple, sai dai ko yankan da ke girarsa ɗin, wanda bata ma kula da shi ba sai da Said Kibiya ta faɗa.


“Zaki taho ko zaki tsaya.”

“Tun da gidan ubana ne ba.”

Ta bata amsa tare da bin ta suka tafi, Husna ba ta  san yanda aka yi ba ta tsinci kanta da tunanin bawan Allan nan, ita dai taga kamar kallonta yake, sai da kuma taga kamar da na kusa da shi yake magana, haka kawai ta hau bawa Ali Kaita labarin sa.


“Kinga wani da na gani yanzu, baƙi siriri mai kyau, har da dimple, kayansa riga da wando na jeans.”

“An shiga uku, ke Abubakar Sheshe kina da lafiya kuwa? Na tambayeki mutanen da kika gani a waje ne?”

“Ku banzaye ne ba damar mutum ya baku labari.”

Husna ta faɗa, tare da kwantawa a kan gado ta ƙyale su ba ta sake bin takansu ba har azahar, ko abincin rana ma ba taje ta karɓa ba dan wata kewar gida da ‘yan uwanta ce ta dabaibaye ta,  haka ta yini gaba ɗaya bata jin daɗin school ɗin, duk yanda ƙawayenta suka yi haka suka barta.


Tun daga wannan ranar ta fara ganinsa, kullum sai ta gansa sai daga baya ta fahimci ashe malami ne a makarantar, amma kuma a ɓanagren senior yake dan baya ɗaukan ‘yan junior, duk lokacin da ta gan shi haka za ta ji tana sha’war kallon sa, tun tana ɓoyewa har ƙawayenta suka fahimta, sai dai magana ɗaya bata taɓa haɗa su ba har aka yi hutu aka dawo lokacin da suka shiga Ss one, a lokacin ne ya fara ɗaukan su General maths, ba ƙarya ya iya koyarwa, ya iya magana cikin nutsuwa yanda kowa da ke cikn ajin zai gane abin da yake koyarwa.

 A ranar da ya fara shigowa ne ya gabatar da kan sa Sunansa Iliya D Musa, amma students ba kiransa da Uncle Dee, ita dai Husna bata ga aibu a cikin sunan ba, amma su Said Kibiya suka sata a gaba suna ta yi ma sunan dariya har da cewa yana kama da inyamurai, Husna ba tasan me ya sa ba amma taji haushinsu sosai da sosai kan yanda suka dinga yi wa sunansa rashin mutunci suna kwaikwayar yanda yake magana a aji suna dariya, a lokacin sai da ta ji kamar ma ta fita daga sabgarsu ta kama gabanta, sai dai kuma ba zata iya ba har cikin zuciyata ta amince su ɗin ƙawayenta ne kuma tana son su. 


Ranar da Ƙaddara ta ƙulla zai fara yi mata magana ranar juma’a ne a wajen Assembly da ake yi bayan an tashi, tana tsaye a layi daga can baya su kuma suna bayan su shi da wasu malaman, kamar daga sama ta ji yana cewa. 

“Asma’u Abubakar, stay properly.”

Wani irin shock ta ji, ashe wai ya san sunana, ikon Allah. Tsayuwarta ta gyara sai dai duk yanda ta so ta nutsu abun ya gagara, sabida wani irin gudu da zuciryata take tamkar ana tseren dawakai, a hankali ta juya ta saci kallonsa, sai dai cikin rashin sa’a idonta ya faɗa cikin na sa, ya ɗage mata gira ɗaya, da sauri ta mai da kan ta gaba tana sauke ajiyar zuciya, ashe shi yake ta kallonta shi ya sa ta gagara nutsuwa, a haka aka ta shi assembly ɗin suka kamu hanyar hostel, ta so ta faɗawa su Said Kibiya sai dai bata son rashin mutunci da zasu yi ma sa, ba wai dan tana tsoronsu ba, kawai dan bata son abin da zai ɓata rainta a yau, suna shiga cikin Hostel Ali Kaita ta ce.

“Abubakar Sheshe kamar na ji Uncle Dee ya yi miki magana ko?”

Banza ta yi da ita kamar bata ji ta ba, ta sake cewa. 

“Har sunanki ya kira ko?”

“Ashe kin ji mene na tambayata?”

Said Kibiya ta ce.

“Ah lallai ne, ƙauna ta ɗaure shine ko ki fesa mana.”

“In fesa muku ka hau yi min hulaƙanci?”

Husna ta faɗa, muryarta cike da ɓacin rai.

“Allah Ya baki haƙuri, mufa ba wai bama son sa ba ne? Kawai munga yanda kika zama so deep ne, kuma you’re not sure that yana sonki ko a’a.”

Said Kibiya ta faɗa, Husna kam dakatawa daga abin da take ta yi, ta kalli Said Kibiya da ta yi magana ta ce.

“Said Kibiya, yaushe kuka ji na ce ina son sa? Bana son wannan sharrin naku.”

Suka ƙyalƙyale da dariya a tare, sannan Ali Kaita ta ce.

“Kinga lets talk serious, Husna kin faɗa son Uncle Dee.”

Da sauri Said Kibiya ta ce.

“No no, no, no! Baki iya faɗa ba, Husna you’re in love with Baby Deeeeee.”

Sai kuma suka tuntsire da dariya, kamar wasu mahaukata sabbabin kamu, ita dai kallon su take tana bin su da idona, mene haɗinta da shi da har za ta faɗa soyayya da shi? A wannan ƙananan shekarun nata kamar ba ita ce, Yaya Abdul ya ce sai ta yi har masters za ta yi aure ba, to ita mene ma zai kaita faɗawa soyayya da malaminta? Haka ta yi ta bin su da ido suna haukansu har suka gama, ganin bata ce musu ci kan ku ba suka nutsu. 

“Husna.”

Said Kibiya ta kira sunanta, ta ɗaga kai ta kalleta ba tare da ta amsa ba.

“Kinga idan har kina son sa, wallahi ki saki zuciyarki ki so shi, ni dai banga aibu a wajensa ba, yana da kyau daidai gwargwado.” 

“Ni wai kun ji na ce ina son sa ne? Kawai kun zo kuna yi min ihu akai, sai na sake faɗa muku wani abu nawa.”

Ta faɗa tana sake juya kwanciyar da ta yi a kan gadon Said Kibiya, duk yanda suka so ta haƙura na yi banza da su. 

Tun daga wannan ranar bai sake kiran sunanta ba sai da aka ɗauki lokaci mai tsayi, ya kira sunanta a cikin aji ya ce.

“Asma’u Sheshe ki haɗa min Test ɗin nan kikai min ofis.”

Yana fita su Said Kibiya suka hau iskancin tsokanarta ta yi banza da su, jikinta har ɓari yake ta haɗa takardun ta tafi ofis ɗin, sai dai ko a ofis ɗin yana amsa ya ce da ita.

“You can go.”

Kamar kazar da aka tsamu daga ruwan sanyi haka ta dawo cikin aji, jikinta duk ya yi sanyi, sabida ta yi tunanin wata maganar yake so ya yi da ni shi ya sa ya ce ta haɗa mai takardun test ɗin ta kai masa. Duk yanda ta kai ga faɗawa ƙawayenta gaskiyya amma sunƙi yarda, gani suke sabida ta ce ba zata sake faɗa musu wani abu ba shi ya sa ta ɓoye musu, har Ali Kaita ta ce.

“Abubakar Sheshe ba uwa ɗaya muke ba, ba kuma uba ɗaya ba, amma zaman ƙaddara ya haɗa mu mun zama tamkar jini ɗaya, harshe da haƙori ma ai ana saɓawa kuma babu wani abu da ya kai su kusa.”
Duk da ta yi maganar sabida jin gulma, amma maganar ta taɓa Husna sosai da sosai, sai da ta kalleta kallon da zata yarda da abin da zata faɗa mata, ta ce.

“Wallahi kawai ce min ya yi you can go, daga haka bai ce min komai ba.”

“To amma ke kike tsammanin zai faɗa miki?” 

Said Kibiya ta tambayeta, ta yi shiru baga san me zai ce mata ba, amma tabbas ko ma menene daga wajensa tana buƙata, bata san yanda ake soyayya ba amma tana jinsa a cikin zuciyarta. Tun daga wannan lokacin suka fahimci tana son sa, su ka kuma kasance masu bata ƙwarin gwiwa a kai, sai dai shi ko sau ɗaya bai taɓa magana da ita ta wata sigar daban da ta huce malami da ɗalibi ba, tun suna ƙarfafa mata gwiwa har suka sare, Ali Kaita ce ma kwanaki ta kawo gurguwar shawara wai su rubuta mai wasiƙa, Husna da kan ta ta ce aa ba da ita ba. Abu kamar wasa suka shiga Ss 2, a lokacin ne kuma aka ba shi form master ɗinsu, ya zama malamin ajinsu. 

Husna ta sare a kan lamarin ta kuma cire rai har ƙawayenta suka ba ta shawara a kan ta haƙura mussaman da suka ga irin amincin da ke tsakaninsa da Aisha Sharif monitan ajinsu. Kullum cikin shan tsinuwa take wajen Husna, ɗan taƙi kaɗan Husna take nema Aisha Sharif ta shiga sabgarta ta haɗa mata jini da majina, ko korarta za ayi daga makarantar ma sai da a koreta. Bisa tausayi Aisha Sharf ta rubutu sunan Husna cikin masu surutu a aji, Displine ya yi Husna bulala biyar, aikuwa suna shiga aji Husna ta yi wani wawan tsalle ta damƙi wuyan Aisha sharif ta haɗa ta da jikin bango, ba ta ma kula wanda take faɗan a kan sa yana ajin ba, tun da can ofis ɗin Malamai suka je aka dake su, sai bayan ta gwara kan Aisha da bango ta sake gwarawa ta ji muryarsa, cikin fushi ya yi maganar.

“Asma’u Sheshe leave her alone.”

Sai a lokacin Husna ta ji muryarshi, ba dan ta so ba ta cikata. 

“Go Outside and kneel down.” 

Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba, wani haushinsa ne ya tokare ta shima, ta ji kamar taje ta damƙeshi su bugata da shi, ai shine ya jawo komai, ya rasa wa zai ce yana so sai wannan mai warin ƙashin. Fita ta yi kneel down ɗin, tana gunguni tana harar ajin, har ya kammala kiran sunansa ya fito, fuska a haɗe ya kalleta ya ce.

“Follow me.”

Miƙewa ta yi tana binsa, tana tafe tana hura hanci tana harare harare, Allah Ya kawo wani mai tsautsayin ya tanka, ita so take ma ta yi abin da za a kore ta daga makarantar kawai. 

Cikin ofis ɗin ya ce ta biyo shi, tana shiga ya sa ta durƙusa kaman za ta yi kneel down ɗin, ya ce.

“Me kika yi ɗazu a aji? Me ta yi miki.”

Kallonsa ta yi ƙasa ƙasa, taga ko inda take ma baya kallo, cikin haɗe rai ta ce.

“Wai sunana ta sa a cikin ‘yan vanacular.”

“To ai ba yau ta fara sa sunanki ba, me ya sa sai na yaune zai zafafeki, faɗa min gsky.”

Turo baki ta yi gaba, ta fara magana ƙasa ƙasa.

“You better open your mouth and talk, idan ba haka ba jibgarki zanyi anan.”

“Harara ta take.”

Husna ta faɗa, ya kalleta sosai yana son ya fahimci shin daman haka take ko a’a, a ganin da yake mata ya san tana da tsiwa amma bai yi tunanin ta iya faɗa haka ba, har wani harare harare yaga tana yi yau.

“A yaushe ne ta harareki?.”

Sai kawai ta fashe masa da kuka, kukan da ya yi matuƙar ɗaga masa hankali, ya ji kamar ya taso da ita ya lallashe ta, sai dai kuma yana son kare dokokin makaranta da kuma haƙƙinta, tun ranar da ya ganta ya ji zuciyarsa ta kamu da son ta, idanunsa sun kamu da son ganinta kuma ya fuskanci hakan a tare da ita, sai dai me? Ya sani akwai bambamcin addini, kuma na ta addini ya haramta masa aurenta, bai kamata ya biyawa son zuciyarsa ba ya sanya ta a wahala, shi ya sa yake gujewa duk wani abu da zai haɗa shi da ita, ranar da ya ce ta kawo mai takardun test ɗin ‘yan ajinsu, ya yi niyar ko ya ne ya samu ya yi hira da ita ko na minti biyu ne, ya san zai ji sauƙi abin da ke damun zuciyarsa, sai dai kuma ya tuna da tarin ƙalubalen da yake shirin janyowa kansa, shi ya sa ma ya ce ta tafi, da gangan ya janyo Aisha Sharif jikinsa ko hakan zai goge soyayyar da yake gani a tare da ita, sai dai kuma abin da ta yi yau ya nuna masa zallan kishinsa da ke ɗawainiya da zuciyarta. 

Jin kukan nata yake har cikin ransa, bai san da wani irin kalmomi zai rarrashe ta ba, baya son ya buɗe zuciyarsa ya zuba mata abin da zai janyo musu tarin wahala a gaba, a kullum kalaman da yake faɗawa kan sa shine. ‘Life is very easy, please don’t make it difcult for both of you.’ Ya san muddin suka ce zasu gina soyayya to wahala ce mai girma.

“Dan Allah ki yi shiru.” 

Ya yi maganar kaman wanda yake koyan Hausa, tsit ta yi shiru da bakinta kamar ba ita ke kuka ba. 

“Me ya sa ki kuka?”

“Na ce maka hararata ta yi, amma baka yarda ba sai ita kayarda da ita, sabida ita ce kake so.”

Tabbas ya ji shigar maganar kamar ansoka masa allura ba tare da saninsa ba, jikin sa ya yi sanyi ya tabbata abin da yake gudu ya afku, sai da ya sai ta nutsuwarsa sannan ya ce.

“Ni na ce miki ina son ta?”

“Gashinan na gani.”

“Me kika gani?”

Ya tambayeta, yana binta da wani irin kallon mamaki, tana ta zaro abin da ke cikin zuciyarta, she is very young gaba ɗaya ba zata wuce 17years ba, amma wai tasan kishi da soyayya, shi da yake 29 years ma bai san yanda zai bayyana soyayya a cikin kalamansa ba kamar yanda take yi, koda yake malaman soyayya da dama sun ce baka sanin lokacin da kalamanka ke bayyana abin da ke zuciyarka. 
Husna kam sai a lokacin da ya tambayeta me ta gani ta tuna abin da ta aikata, ta saki baki kenan tana ta zuba shi da a yanzu ma take jin haushinsa, miƙewa ta yi za ta fita ya ce da ita.

“Ina zaki?”

Shiru ta yi ba ta tanka ba, ya sake tambayarta, sai da ya tambayeta sau uku sannan ta ce.

“Na tuna ma ma daina kulaka, kasani Kneel down.”

Murmushi ya yi na ji zallan ƙuruciya a tare da ita, a haka tana da sauƙi amma kuma wuta ce ita, ba ta da haƙuri ya fahimta sosai, ga zafin kishi haka kuma ga taurin kai. 

“To ki yi haƙuri, i will never do it again i promise.”

Dawowa ta yi yanda take ɗazu, ya sake cewa. 

“Me kika gani kika ce ina son Aisha sharif?”

“Babu komai.”

“Babu komai kuma?” 

Ya yi maganar muryarshi na nuna alamun mamaki, gaba ɗaya yarinyar a burkice take. Idan bata so ba ba zaka taɓa gane kan ta ba. 

“You can go.”

Ya faɗa yana mayar da hankalinsa kan littafin da ke gabansa, har za ta fita ya ce.

“Make sure kin bata haƙuri kin ji ko?”

Ficewa ta yi wani haushinsa yana cin zuciyarta, ya tabbata dai Aisha Sharif yake so, a fili ta furta. 

“Allah Ka tsinewa Aisha Sharif dan ubanta.”

Ko da ta koma aji ba ta ce da kowa komai ba ta sami waje ta zauna, duk malaman da suka shiga suka fita bata fuskanci komai ba, har aka tashi suka yi hostel, sai dare Said Kibiya ta ce.

“Wai baki bamu labarin abin da ya faru ba ɗazu.”

“Me zan ce muku to? Ai nasan shegiyar nan yake so, wai dan Allah bakwajin tana warin ƙashi?”

Gaba ɗayansu suka kwashe da dariya, Ali Kaita ta ce. 

“Allah Ya tsinewa kishi irin naki Husna, abun har da sharri.”

“Ba sharri bane fa, warin ƙashi take.”

Daga nan kuma ta shiga basu labarin duk abin da ya faru ofis ɗin, sai da ta gama gaba ɗaya Ali Kaita ta ce.

“Shashasha irinki, to me kika yi? Ke daman duk son a baki ne ko me? Kina so ki ce baki fahimci yana son ki ba?”

Girgiza kai Husna ta yi, Allah ne ya so Ali Kaita a kan soyayya ne ta ce mata shashasha, amma wallahi da yau har gaban pc sai an kai su, wai shashasha. Said Kibiya ce ta ce.

“Ke dagaske in dai abin da kika faɗa mana shi ya faru to wallahi sonki yaki, kiji fa yanda ya dinga tambayarki, amma shiriritarki ta ja kika yi kasa ganewa, sa ki nutsu yanzu ki fahimci abin da ake faɗa miki.”


Tun daga wannan lokacin Husna taso sanyawa ranta nutsuwa, amma mai hali baya fasawa ta kasa gaba ɗaya, kullum tsanar Aisha Sharif take, kullum nemanta take da tashin hankali. Ranar friday da yamma lokacin ɗalibai suna compound suna ta hada hada wasu kuma suna cikin aji suna karatu, malamai da dama sun tafi gida weekend sai kuma waɗanda ke zaman quaters, shima wannan week ɗin kawai yaji bai son tafiya weekend, cikin ɗaliban da suka fito daga cikin aji ya hangota cikin ƙwayenta, su uku kullum a tare haka suke rayuwa, sun dawo daga aji ne dan duk weekend suna zuwa yi mata karatu inda suke mata dalla dalla da hausa sannan ta gane, ba wai dan ba ta iya turanci ba kawai bata kwashewa da huri ne. 


A baya ya dinga bin su har suka kusa hostel sannan ya ce.

“Asma’u Sheshe.”

Cak suka tsaya ita da ƙawayenta, kamar sunan su ya kira duka, sai da ya ƙaraso kusa da su sannan ya ce.

“Duka sunanku ɗaya kenan?”

Durƙusawa ƙasa suka yi, suka ce.

“Good afternoon Uncle Dee”

“Afternoon how are you.”

“Fine thank you.”

Duka baki a haɗe suke faɗa kamar masu bin waƙa, sai kuma suka fara tafiya suka ɗan yi gaba suka bar Husna kusa da shi. 

“Har yanzu fushin ne?”

Girgiza kai ta yi ba ta ce komai ba, ya sake cewa.

“Ba zaki yi min magana ba ne?”

“Ni ba fushi nake ba.”

“To me ya sa kika daina yi min magana?”

Shiru ta yi sabida abin da ya faɗa, wai ta daina yi masa magana, to daman magana take masa? Ko me yake nufi. 

“Ina so mu yi magana da ke, amma ina ga zan bari sai kun shiga next class lokacin kun zo final kuma kun ƙara girma.”

Da sauri ta girgiza kai, sannan ta ce.

“A’a ka faɗa min, yanzu ma na girma.”

Sai da suka tsaya jikin bishiya sannan ya ce.

“Ranar nan kin ce ina son Aisha Sharif ko? Me ya sa kika ce ina sonta? Me ya sa sai ita kika yi tunanin ita nake so ba ke ba?”



Legendspen
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.