Free chapter · Read without an account
Chapter 8
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsar Arewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 8
Kwanaki suka sake ja.
Bayan an tabbatar da admission ɗin Nihla, gidan ya fara ɗaukar wani sabon salo.
Maganar makaranta ba ta ƙarewa a gidan.
"Yaushe za ta tafi?"
"Me za ta tafi da shi?"
"Me ya rage a saya?"
Waɗannan su ne tambayoyin da suke ta yi wa junansu.
Kowa yana cikin shirye-shirye.
Kowa yana ƙoƙarin ganin Nihla ta tafi da duk abin da za ta buƙata.
Amma ita kanta Nihla...
Duk lokacin da ta tuna cewa ranar tafiyarta tana ƙara kusantowa, sai jikinta ya yi sanyi.
Wani lokaci har ta kan zauna ita kaɗai, tana kallon kayanta da aka fara tattarawa, zuciyarta cike da tunani.
"Da gaske zan bar gida?"
"Da gaske zan kwana a wani wuri dabam?"
"Yaya zan yi ba tare da Hajiya Mama ba?"
Waɗannan tambayoyin suka dinga yawo a zuciyarta.
Nihla ba ta taɓa zuwa wani gari ta kwana ba.
Tun tana ƙarama, gidansu ne duniyarta.
A nan ta tashi.
A nan ta yi karatu.
A nan ta saba da muryoyin 'yan uwanta, da zolayar Hafiz da Fa'iz, da hayaniyar 'yan gidan da ta saba ji kullum.
Amma yanzu...
Za ta bar komai.
Ba don wasa ba.
Ba don yawon buɗe ido ba.
Saboda ilimi.
Burin da ta daɗe tana mafarkin cikawa.
Wani lokaci idan fargabar ta yi mata yawa, sai ta lumshe idanuwanta ta yi dogon numfashi.
"Jami'a fa..."
Sai ta yi murmushi a hankali.
A nan ne burinta yake.
A nan ne za ta fara wani sabon babi na rayuwarta.
Tana son ta ganta a makaranta.
Tana son ta shiga aji da, ta zauna cikin sauran ɗalibai, ta ji ana kiran ta da 'yar jami'a.
Har ma wani lokaci idan ta tuna Hafiz da Fa'iz, sai ta yi murmushi.
"Yanzu kam ba za ku ƙara samun damar tsokanarta ko su dameta da labarin makaranta ba."
Sai ta ɗan yi dariya ita kaɗai.
Sai dai abin da Nihla ba ta sani ba shi ne, jami'a ba karatu kaɗai za ta koya mata ba.
Za ta koya mata rayuwa.
Za ta koya mata yadda ake mu'amala da mutane daban-daban.
Za ta koya mata cewa ba kowane murmushi ne yake nufin ƙauna ba.
Ba kowane mutum da ya kira kansa aboki ne yake zama alheri ba.
Kuma za ta koya mata wasu darussan da ba za ta taɓa mantawa da su ba.
Shirye-shiryen tafiya kuwa suka ƙara kankama.
Babu abin da aka bari.
An saya mata sutura masu yawa, kayan abinci, kayan kwalliya, takalma, hijabai, jakunkuna da sauran abubuwan da za ta buƙata.
An shirya komai.
Kayanta suna killace a dakinta, ranar tafiya kawai ake jira.
Anty Asiya ma ba a bar ta a baya ba.
Tun daga Gombe, ta bayar da saƙo a kawowa Nihla.
Pant da bra, hijabai, takalma, da sauran abubuwan amfani.
Lokacin da Nihla ta buɗe kayan, sai ta yi murmushi.
"Anty Asiya tawa... ina matuƙar ƙaunarki."
Ta buɗe kayan tana dubawa, murmushin na ƙara bayyana a fuskarta.
Hajiya Mama kuwa, tun ranar da aka ce Nihla ta samu admission, bakinta bai huta da nasiha da faɗa ba.
Kullum sai ta tunatar da Nihla.
"Ki kula da kanki, Nihla."
"Ki riƙe mutuncinki. Kada ki bi ƙawayen banza. Ki san irin mutanen da za ki yi mu'amala da su. Duk inda kika je, ki tuna mutuncin gidanku da kuma martabar gidanku."
A duk lokacin da Hajiya Mama take mata irin wannan tunatarwar, sai Nihla ta ce:
"In sha Allah, Hajjajuna."
Kullum maganar kenan.
Idan karatu ne, yaci ace Nihla ta haddace.
A ɗaya ɓangaren kuma, 'yan uwan Nihla sun yi rawar gani, kowa da irin gudunmawar da ya bayar.
Yaya Umar ya aiko mata da sabuwar waya kirar Apple tare da power bank.
Lokacin da Nihla ta ga wayar, sai ta yi ihu da farin ciki.
"Wayyo! Yaya Umar!"
Ta ɗaga wayar sama tana murmushi.
"Allah Ya saka masa da alheri."
Kowa ya yi dariya.
"Yanzu kam 'yar jami'a ta samu waya."
"Ki kula, kar ki je kina danna waya ki manta da karatu!"
"Wallahi, za mu dinga kawo miki ziyara mu ga kina karatu!"
Nihla ta yi dariya.
Ba ta ba su amsa ba saboda hankalinta yana kan sabuwar wayarta.
Irin waɗannan hirarrakin da suke yi da kuma dramarsu sun sa ta ji kamar ba ta son tafiya.
Tabbas ta san za ta yi kewarsu sosai.
Za ta yi kewar hayaniyar falon.
Za ta yi kewar Hajiya Mama.
Za ta yi kewar gidansu.
Uwa uba kuma, za ta yi kewar rayuwar gidansu mai cike da farin ciki.
An gama komai.
Ranar tafiya kawai ake jira.
Ana gobe Nihla za ta tafi, Yaya Babba ya zo gidan da daddare.
Ya ce wa Hajiya Mama:
"Nihla ba za ta samu ta fiya gobe ba. Maybe sai zuwa wani satin, saboda har yanzu ba ta samu accommodation ba."
Hajiya Mama ta ce:
"Ba damuwa. Da gobe da wani satin, duk ɗaya ne ai. Allah Ya sa hakan ne mafi alheri."
Shiru ne ya biyo bayan maganar tasu.
Kowa da abin da yake cikin zuciyarsa.
Shi Yaya Babba yana tunawa da wayar da suka yi da abokinsa dazu, da kuma irin shawarar da ya ba shi a kan Nihla ta zauna a off-campus, tunda ba ta samu accommodation ba.
Sam, shawarar ba ta kwanta masa a rai ba.
"Yaran da suke zaune a cikin hostel ma ya aka kare su, bare kuma waɗanda suke off-campus? Sai wanda Allah Ya tsare."
Yana ganin idan Nihla ba ta samu ɗaki a cikin hostel ba, to sai dai ta hakura da karatun.
A jira wata shekarar.
Ko kuma ta hakura da karatun gaba ɗaya.
Domin bai san da wane irin mutane za ta haɗu ba.
Zai ba shi sati ɗaya kamar yadda ya ce masa.
Nan da sati ɗaya zai ƙara bincikawa.
Idan an samu, zai sanar da Abubakar.
Da wannan tunanin, ya musu sallama ya tafi nasa gidansa.
Umsar ✍️
***