Free chapter 路 Read without an account
CHAPTER 12
*HARAMTACCIYAR GADA.*
_*{Ha蓷uwar rayuka da 茩addara ta tattara wuri guda.*馃敟馃挃}_
*NA*
*HAFSAT MUSTAPHA ('Yar Mutan Naija).*
*SADAUKARWA GA UWAR茒AKI NA: HAJIYA ZAINAB AHMAD (Hajiya Mama). Amincin Allah da ni'imominsa su tabbata a gareki Uwata.*
*BOOK 1*
*Page 12.*
*SAMHA.*
"What?? Yanzu Jidda bata son min aiki yadda ya kamata. Amma bari in 蓷auki kafa inje in sameta tun kafin lokaci ya buga ta sa kai tabar gidan tunda ga dukkan alamu ta koma aiki kamar agogo sannan ta zama ku蓷i masu ba茩ar wahalar samu."
Samha ta furta da zafinta bayan ta gama karance sa茩on Jidda na sanarwar da ta bayar a group. A gurguje ta shirya, duk da laulayin daya 蓷an tasata gaba a cikin 'yan kwanakin nan wanda fita ma ya zamar mata dole amma haka ta 蓷aure ta nufi gidan mata.
***
Saffy na fita gida ta tsaya daidai junction tana waige-waige amma bata hango ko mai kama da Muwaddah ba, duk napep 蓷in daya gifta sai ta leka ko zata hangota ciki amma bata. Hakan yasa ta nemeta a waya, hakuri ta bata tace gata nan karasowa. Matsawa daga gefen titin tayi, ta tsaya tsayuwan jiranta.
Wata toyota yaris fara kal ce taga ta tsaya gabanta, har zata matsa gefe taga an sauke glasses kasa, idanunta yayi arba da wasu wayayyun mata biyu. Wacce ke tuki ta makala wani kafcecen baby pink glasses a idanunta me 蓷aukar ido wanda ya rufe mata rabin fuska, ita me zaune a kujerar me zaman banza kai tsaye ake kallon cikin 茩wayar idanunta don ita bata sa madubi ba.
Kallo 蓷aya ta musu ta 蓷auke kai sannan ta nemi barin wajen.
"Ke! Where are you going? Come back, kamar dai baki shaida wacce kike ta tsayuwan jira ba ko? Kodayake ba laifinki bane baki yi tsammanin ganinta cikin me 茩afa hu蓷u ba, a ranar da kuka fara ha蓷uwa cikin tricycle ne shiyasa."
Budurwar dake zaune a kujerar me zaman banza ta fa蓷i hakan tare da tunsirewa da dariya.
Cak! Saffy ta tsaya a waje 蓷aya gabanta na mugun harbawa jin irin cin fuskar da aka yi mata.
'Kan uba! wacce me 茩arfin halin ce wannan 蓷in da take 茩o茩arin ci mata mutunci?'
Ta ayyana aranta.
Kafin ta ce wani abu sai ga 蓷ayan yarinyar me gilashin ta fito hankalinta a mugun tashe, ta zare glasses hakan yaba Saffy damar shaidata.
"Muwaddah!"
Ta ambaci sunanta, sannan ta girgiza kai ta kuma cewa "Ashe dai yau tafiyar ta manya ce bata yaku bayi ba, shiyasa naga wata har tana ci min fuska, hakan na nufin kin bada labarin ha蓷uwata dake kenan. Dama Sa茩on kenan? cin mutunci? ba damuwa nagode."
Tayi niyyar barin wajen don muddin ta tsaya ci gaba da jin abin da zai sosa ranta to kuwa zuciya na iya 蓷ibanta ta kakkarya 'yar mutane a kan titi.
Da sauri Muwaddah ta riko hannunta ta marairaice ta ce"Don girman Allah 茩awata kiyi hakuri, dana san haka zai faru da ban taho da Raihan ba, pls karki biye mata ita haka halinta yake, cin mutuncin wani ba komai bane a wajenta, ina zuwa bari na 蓷auko miki sa茩on naki a cikin mota."
Bata ce da ita komai ba, Allah sarki Muwadda a rikice ta koma mota don dakkowa saffyn sakonta, tatass tayi ma Raihan kan abin da tayi wa Saffy sam bata kyauta ba kuma bata ji da蓷insa ba. Hakika ta kunyatar da ita, ta tabbata Saffy za tayi tunanin ko haka itama halinta yake. Hakan da tayi ya fusata Raihan ainun!
Babu shiri ta banko kofar motar ta fito tana kuka, ta ce" Muwaddah don kin yi sabuwar 茩awa shine zaki wulakantani? a kan wata 'yar ghetto kike zagina? Nagode, amma wallahi ki sani ba zan ta蓳a sonta ba tunda ta nemi shiga tsakanina dake kuma ki sani sai su Ammi sun ji zancen nan."
Tana gama fa蓷in haka ta fara 茩o茩arin tsai da abin hawa, Muwaddah duk tabi ta ru蓷e sai rokonta take.
"Raihan don girman Allah kiyi hakuri in maidake gida, kema kin san baki kyauta ba be kamata ki ci mutuncinta ba. Na tabbata idan nayi ma wata 茩awarki kwatankwacin abin da kikai ma Safiyya sam ba zaki ji da蓷i ba."
Ko bin ta kan jawabinta ba tayi ba ta tsai da wani 蓷an sahu ta afka ciki, tare da masa kwatancen inda zai kaita. Mai babur yaja suka yi gaba ko sake kallon 蓳arin da Muwaddah take ba tayi ba, balle ta saurareta.
Juyowar da za tayi sai gani tayi wayam! babu saffy, tuni kanta ya kara 蓷aukar zafi. Can ta hangota har ta mika layin cikin unguwarsu tana lafta uban sauri kamar zata kifa kasa.
Sauri-sauri, gudu-gudu haka ta bi bayanta tana 茩walla mata 茩ira, Saffy sai 茩ara uban sauri take don kar ta cimmata. Tana shan kwanar layin, taga wani gida me gate ba tare da tunanin komai ba ta afka cikin gidan mutane, ita ce harda tura 茩ofar ta rufe da sakata.
"Ke! Kehhh! tsaya daga nan! Ya zaki fa蓷o cikin gidan mutane hadda rufe 茩ofa? wannan 茩arfin hali da me yayi kama?"
Me gadin gidan ya furta da zafinsa daga inda yake zaune, ya daka wani uban tsalle rike da sandarsa sai gabanta ya dira. Hakan kuwa ba 茩aramin tsoratar da Saffy yayi ba.
Ja da baya tayi ta ce a rikice"Don Allah kuyi hakuri biyoni a kayi."
"Uban wa ya biyoki? barayin waya ko 'yan bindiga?"
Ya watsa mata tambaya yana 茩o茩arin kai hannu domin ya zare sakatar, shi a dole ga jarumi kuma takamarsa me gidan jami'i ne.
"Don girman Allah karka bu蓷e, wallahi kwata-kwata bana so ta kusanto inda nake, ta takura wa rayuwata ni wallahi."
Wani irin kukan shagwa蓳a ne ya kufce mata, a sanyaye me gadi ya komo da baya yana me kwantar da murya ya ce"Wacece take bibiyar ki? Ko dai 茩wacen saurayi kika mata ne? Don 'yan matan wannan zamanin baku da wani aiki sai rigima kan samari a 茩arshe kuma a yaudareku."
Wani kallo ta watsa masa wanda yasa dole ya shiga taitayinsa.
Kafin ta kai ga bada amsa suka ji daga bayansu an ce"Wai kai Iliya meyasa bakinka sam baya da control ne? Ka tasa mace gaba ka tsareta da tambayoyi sai kace 蓷an jarida, maimakon kayi abin da ya dace ka tsaya shirme, ina ganin lokaci yayi daya kamata na sauyaka da wani."
Jin haka yasa Iliya yayi saurin kamewa tun kafin uban gidan nasa ya karaso ya ce" Mon sir! don Allah kayi hakuri na tuba zan gyara."
Ko sake bin ta kansa Abuturab be yi ba ya kalleta, ita ma 蓷in kallonsa take tare da yin tasbihi ga Allah da irin halittan daya 茩era a nan. Har ya bu蓷e 茩aramin bakinsa zai mata magana sai suka ji Muwadda daga waje tana tambayar wani almajiri inda Saffy ta shige. Abinka da yaro ba wayo sai kawai ya nuna mata gidan. Godiya ta masa sannan ta isa gate 蓷in ta fara bubbugawa har tana kuka.
"Safiyya don Allah kiyi hakuri karki guje min akan abin da Raihan ta miki."
Hakan ba 茩aramin kashewa Abuturab jiki yayi ba, da sauri ya kai hannu zai zare sakatar kofa, Saffy tayi 茩o茩arin dakatar dashi.
Karon farko da yayi mata magana ya ce" Kiyi hakuri ba a haka, komai na rayuwan nan hakuri ake kin ji ko?"
Jikinta ne yayi sanyi, sai kuma ta tsinci kanta da daga masa kai alamun ta saduda, ya sakar mata kayataccen murmushinsa don sosai ta birgeshi.
Abuturab yayi matukar 茩o茩ari na ganin ya sulhunta tsakanin sabbin 茩awayen biyu, sannan ya musu fatan alheri kana ya koma ciki tare da rufo 茩ofar gidansa a kan idanunsu.
"Na zaci nan 蓷in gidanku ne ai, kuma shi 蓷in yayanki."
Muwaddah ta jefo mata tambaya bayan sun kama hanya.
"No, ba gidanmu bane kuma kamar ke, nima yau 蓷in na fara sakashi a ido, kawai dai na afka cikin gidansu ne domin na kauracewa ganinki."
Muwaddah ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Na fahimta, amma dai ya kamata yau ki min izini in fara sanin gidanku kafin daga baya nima ki ziyarci gidanmu don muamala ta tsakani da Allah nake son mu kulla ni dake Safiyya bata 茩arya ba."
"Gaskiya wanda nake zaune wajensa baya so ana kawo masa mutane gida amma kiyi hakuri zan nemi alfarma a baki damar zuwa wajena."
Muwaddah ta saukar da wata kalar ajiyar zuciya don ta fahimci Saffy ba gaban iyayenta take ba, ri茩onta ake kuma ga dukkan alamu ana takurata.
"Ba damuwa, mu je ki kar蓳i sa茩on da nake ta ja miki rai."
Saffy ta ce"Na fito kar蓳an sa茩o aka ci mutunci na. Ko karyawa ban yi ba amma na karya da takaicin wata."
Muwaddah ta tuntsire da dariya ta ce"Au! Dama baki karya ba? This is to 10 fa?"
"Serious ban karya ba."
Muwaddah tayi mata tayin karbo koda takeaway ne a wani restaurant da ke kusa. A farko taso bijirewa saboda outfit dake jikinta amma sai taga babu wani aibu tattare da ita tunda ta rufe jikinta har 茩asa da dogon hijab. Alkaleri's kitchen suka nufa saboda shine gidan abincin daya fi tashe a garin.
***
*YALLABAI.*
Manyan ba茩i yayi daga 茩asar Japan wa蓷anda suka wanko kafa na musamman domin jarraba kalolin girke-girkensa don tantance 蓷an蓷anonsu da ake ganin babu kamarsa kaf Africa.
A kwanakin baya sun gayyaceshi 茩asarsu a inda ya samu shiga wata gasa da suka shirya na kwararrun masana sanin sirrin girke-girke. Duka Nahiyoyin duniya bakwai aka gayyata, a inda Executive Chef Jalaludden Alkaleri ya wakilci nahiyar Afrika.
Cikin ikon Allah shi yayi nasarar lashe gasar ya samu ma蓷aukakiyar nasara domin ya bige sauran abokanan fafatawar tasa ne da abinciccikanmu na Afrika masu 蓷an蓷ano me da蓷in gaske. Ya samu lambar yabo tare da wasu manyan 茩yaututtuka na kayan aiki na girke-girke, sai kuma damar daya samu ta kafa gidan abincinsa a 茩asarsu wanda su ne zasu 蓷auki nauyinsa domin so suke su ha蓷a partnership business dashi.
Tun jiya da suka sauka gari ya kai su branch 蓷insa biyu na nan Kaduna for thorough inspection domin ganin yadda abubuwansa ke tafiya kuma sosai suka yabawa 茩o茩arinsa har suke ganin tabbas ya cancanci a bashi damar kafa shahararren gidan abinci a 茩asarsu wanda za a dinga siyar da abincin afrika ne zallah.
Farin ciki yake sosai ganin wata dama ta sake samu bayan wanda ya samu daga kasar birtaniya.
Gaban madubi yake yana na蓷a navy blue neck tie akan farar long sleeves 蓷insa, hannunsa ya kai wajen jerin turarukansa masu musulman 茩amshi me sanyaya rai.
Hannunsa ya kai kan 'OudTouch' wanda a duk cikin turarukan da yake sawa Jidda tafi son 茩amshinsa. Wayarsa ya 蓷auka ya sanya kiranta.
A daidai wannan lokacin tana zaune tana yagar kazarta data kar蓳o daga gidan abincinsa, tana ha蓷awa da shayi da bread. Zuwa yanzu ta kwashi 15mins babu wacce ta shigo ganinta.
Tana shirin neman Saffy a waya ta ji inda take, sai ga kiran Yallabai ya shigo ta 蓷aga.
"Sai yanzu ka tuna dani?" Ta fa蓷a cikin wasa.
"Alkhairi kiyi hakuri ni ban isa in manta dake ba. kodayaushe kina nan makale a raina, kawai dai mutanen Japan ne suka shiga hakkinki."
Ta ce"To, Jay Allah ya tabbatar da alheri."
"Ameen, Ki tayani da addu'a yanzu nake shirin zuwa in 茩arbi offer 蓷ina a wajen ba茩in nawa sannan in sallamesu don yau za su koma 茩asarsu. Jidda shiyasa na ce ke alkhairina ce, tun daga lokacin da kika shigo rayuwata nake ta samun 蓷aukaka da ci gaba a harkar kasuwanci na. Bayan haka kuma ga natsuwar da nake samu idan ina tare dake. Jiddatulkhair I love you so much, indeed you're the rahma that Allah sent to me, alhamdulillah!"
Sosai kalamansa suka ida gigitar da ita, sai murmushi kawai take tayi abinta har ya bukaci su yi vidiyo call domin taga shirin da yayi na fita.
Nan fa suka shiga vidiyo ya ga ashe har tana gidan mata.
Girgiza kai ya yi ya ce"Jidda, wannan gidan matan dai na kusa rabaki da shi amma komai lokaci ne. Ina nan ina shirin da baki san da shi ba amma na tabbata za kiyi farin ciki."
Bata ce komai ba sai murmushin da tayi da yake iya jiyo sautinsa.
"Idan na 茩arbi offer 蓷inmu zan zo mu yi celebrating."
"To shikenan sai na ganka, Allah ya tabbatar da alheri.."
Daga haka suka yi sallama, Bayan Yallabai ya sauke waya ya ce kasa-kasa,
"Jidda! In sha Allahu na kusa rabaki da GIDAN MATA na har abada, dama zuba idanu kawai nayi domin in ga iya gudun ruwanki. Ni ya dace ki bauta wa ba 'yar cikina ba."
Ya ida magana yana kallon cikin madubi yana me 茩arewa kansa kallo. Girgiza kai yayi alamun something is missing, ya tafi wajen jerin gilasai na idanu, hannunsa ya kai kan wani farin eyeshade me farin kwalba, me shegen kyau, ya 蓷akko ya makala kana ya koma gaban madubi, sosai ya yi masifar ha蓷uwa ta ko'ina. Sai daya gamsu cewa tabbas ya fito sannan a gurguje ya jawo navy blue suit 蓷insa ya aza saman farar rigarsa sai kuma cover shoes baki da safa, sannan ya fice a hanzarce 蓷auke da briefcase yana waya da ba茩insa dake zaman jiransa.
Kafin ya tafi sai daya shiga side 蓷in Haj. Nafeesa ya sallameta. Sai dai kuma ya fahimci kamar tana cikin damuwa don ya nuna a fuskarta. Koda ya tambayeta ta nuna masa babu komai 蓷an zazzabi ne take ji kawai. Ya mata Allah ya sawwake sannan ya bar gidan zuwa inda za su gana da ba茩insa.
Tuni mutane suka yi ma Jidda caaa! akai a cikin ofis, ana biyan ku蓷in haraji. Wasu kuma kayan abincin wata suke bin bashi, amma ba fanninta bane dole sai sun jira dattijan matan da suke incharge a wannan 蓳angaren sun zo.
Korasu waje tayi tace dasu zata nemi officials a waya sannan ta maida hankali kan masu biyan ku蓷in haraji, a yayin da SALA ke tayata shigar da bayanai.
Azagwai ce ta gaba da zata biya ku蓷i, Nan take Jidda ta tuno abin da tayi mata.
Tsaki ta ja ta maida dubanta kan wacce take bayan Azagwai 蓷in ta ce"Don Allah next person please."
Azagwai ta tattare wuri taki ba ta bayan nata hanya.
"Ki bani guri mana ko baki ji tace in matso kusa ba?" Yarinyar ta furta tana hararan Azagwai.
Azagwai ta ce"Wallahi kin ma raina wa kanki hankali da har kike tsammanin zan bari ki matsa kusa da wannan tebirin bayan kin san da cewa bana bari a ci min layi. To ki sani sai ta gama sauraron bukatuna kafin azo kan ki."
Cikin zafin rai Jidda ta ce "Azagwai ba zan saurareki ba! Kin ji ko? Ina so in ga 茩arshen rashin kunyarki, idan yaso ni kuma zan nuna miki 茩arfin isa da ikona a gidan nan."
Jidda ta ida magana da zafinta, har da mi茩ewa tsaye da buga tebirin gabanta wanda shi ya mata tsakani da matan dake tsastsaye gabanta.
Duk da cewar Azagwai ta matukar ka蓷uwa da yanayin Jiddan, amma sai ta fuske ta ce,
"Jidda ina so ki ture duk wani personal issues dake tsakanina dake, yanzu a kan aikinki kike don haka ya zame miki wajibi ki saurare ni idan ba haka ba zanyi kararki wajen uwar蓷aki."
Jidda ta nuna kanta da 'yar yatsa ta ce"Are you threatening me? Shafa'atu bismillah je ki kai 茩arar tawa yau ina so inga iya gudun ruwanki."
Kafin ta kai ga bata amsa suka tsinkayi muryar Samha ta fa蓷o gidan tana tambayar matan dake zube a waje abin da suke zaman jira shanye a rana haka. Galibinsu 'Yan yara-yara ne wa蓷anda basu fi irin sha takwas zuwa ashirin ba.
"Shugaba ce tace mu 蓷an jira ka蓷an za tayi waya da masu ba da kayan abinci za su zo nan bada jimawa ba su sallamemu."
A cewar wata a cikin matan kenan.
Wata kuma ta ce cike da gajiyawa " Akalla mun shafe sama da awa 蓷aya da rabi muna jira amma har yanzu shiru kuma bana tsammanin ta kirasu awayan ma kamar dai ta manta da batunmu ne."
Ta ida magana kamar zata saki 蓷an marayan kuka. Hakan kuwa ba 茩aramin motsa tsokar ran Samha yayi ba don ita 蓷in me tausayi ce, bata 茩aunar ganin ana hora koda dabba ne da abinci balle kuma 蓷an mutum. Duk wanda kaga an masa horon kayan abinci a wannan gidan to lallai ya kaita bango ne, ya karya wani doka, to shine zaka ga ya fuskanci hukunci na 蓷an lokaci.
Gaban Jidda ne ya bada rass! Jin abin da yarinyar ta fa蓷a don tabbas ta sha'afa da batunsu. Da sauri ta daga waya zata kira Baaba Rabi wacce ita ce head incharge kuma gidanta na nan kusa cikin unguwa ne ma.
Sai ganin Samha tayi ta fa蓷o ofishin ranta a matu茩ar 蓳ace. 'Yan matan dake ciki ma na gaisheta hannu kawai ta daga musu idanunta kyam! a kan Jidda wacce ta sha jinin jikinta.
Duk iskancinka duk iya shegenka duk cika bakinka sam baka iya yin shi gaban Samha. 'Yar yarinya ce amma kwarjini take da shi na ban mamaki.
"Yanzu kike shirin kiran Baaba Rabi da kika ga zahirina a gabanki, haka ne?"
Ta furta cikin bayyana fushinta, shiru Jidda ta mata kanta a 茩asa.
"Sauke wayar kuma kiyi ending call 蓷in tunda dama bakiyi niyya ba."
Ta bata umarni, da sauri ta dago kai ta dubeta don already har Baaba Rabin ta daga kiran nata.
Jin muryata tana ta rangada sallama sai kuma Samha taga rashin dacewar a datse kiran, ta ce"Yi mata magana."
Kamar dama jira take ta ce a 蓷an rikice"Amm...Ammm. Baaba Rabi....dama...dama....akwai masu jiran ki ne kizo ki bada kayan abinci."
"To! To! To! shikenan gani nan tafe."
Ta sauke wayar daga kunneta tana "Ranki ya da蓷e barka da zuwa don Allah ki gafarce ni."
Ko kallonta Samha bata yi ba don wani irin bala'in zogi take jin 茩irjinta na mata tamkar wacce ake sossokawa mashi.
"'Yan mata ayi hakuri a 蓷an bamu wuri zan gana da Shugabarku."
Cike da girmamawa aka watse aka barsu iya su biyu a cikin ofishin. Matsowar Samha kusa yasa zuciyar Jidda mugun tashi sakamakon 茩amshin turarenta da tayi masa kyayyawan sha茩a, nan take taji wani irin abu ya taso ya tsaya mata a makoshi ya tokare.
Samha na "Lafiya kuwa?me yake damunki?"
Kakarin amai ta shiga yi, da sauri ta runtuma waje da gudu rike da wuya da hannu biyunta. Tun a bakin 茩ofar ofishin ta fara kelaye amai har zuwa tafkeken famfon dake tsakar gidan. Mutane suka rufu a kanta ana mata sannu, Ita kanta Samhar hankalinta ne yayi mugun dagawa. Da hanzari ta rufa mata baya 蓷auke da wayar Jidda da ake ta nacin kira...