Free chapter · Read without an account
First cut
Bayan sun kwashe kusan awanni biyu a hanya, sun shigo garin abuja .Nuwayrah wadda kusan rabin tafiyar tana kallon titi ta window, ta ɗago kanta Finally, ta faɗa a hankali. Mubeen ya juyo ya kalle ta.Finally me?mun kusa isa yaya mubeen , Rayyan ya dan jiyo ya kalleta ,Kin gaji ne, Big Head?Ba gajiya ba ce. I’m just excited and nervous at the same time ban san me ke jirana ba ,khairan inshallah mimi ki cire fargaba
Bayan wani ɗan lokaci, Rayyan ya shiga cikin harabar presidential villa hotel Nuwayrah ta ɗago kanta tana kallon wajen.“Wow…masha Allah this is beautiful,big head kar ki mana kauyenci maintain your steez ,rayyan ya fada cike da tsokana yana parking din motar ,harara nuwayrah ta galla masa tana tura baki .
duk suka fito daga motar rayyan ya ɗauko wasu daga cikin kayanta yayin da Mubeen ya ɗauki sauran.Nuwayrah ta bi su zuwa reception.Bayan an tabbatar da sunanta da details ɗin program ɗin, aka ba ta key ɗin ɗakinta. “Your accommodation and meal are fully covered for the duration of the residency,” matar da ke reception ta faɗa mata. ba sai kin fada min ba nasani nuwayrah ta ayyana a ranta , ta amsa room card din tare da mata godiya
rayyan kuwa tun ranar da mimi ta tura masa screenshot yaga hotel din da zaa sauke ta shima yayi booking daki ,details dinsa ya nunawa receptionist din bayan ta duba ta computer ta bashi room card din
Your room is also confirmed ,Nuwayrah ta kalli Rayyan.
“Ka yi booking dama ?I thought gidan anty zee zaka sauka (anty zee babbar yayarsu rayyan a abuja take aure )
haba mimi wani irin rashin capacity ne haka da grimana zan sauka a gidan anty zee ,rayyan ya fada yana jan box din nuwayrah mubeen yana biye dasu shi dayake magana ba damunsa tayi ba be cika shiga hirar rayyan da mimi ba ,ba kyau girman kai ray ,menen da gidan anty zee din ?ga enough rooms ga challet daban befi maka zaman hotel ba ? whatever dai mimi ,am not going
Nuwayrah ta girgiza kai tana murmushi.lamarin rayyan sai shi
duk suka nufi rooms dinsu mimi tana shiga ɗakinta ta fara dube dube .Room ɗin ya hadu ga mirrows ga clean bed komai perfect dai
Gudun Ac ta kara tare da bararrarajewa akan gadon ,gabadaya a gajiye take duk da kaduna to abuja ba nisa amma ji take kamar kwana tayi a hanya ,gyanyadi ta fara ,ringing din wayarta ya tashe ta cike da kasala ta dauki wayar ,ganin sunan dake yawo a screen din yasa dan wartsakewa
“Hello, Love.ina yini?
lafiya Pookie ya hanya ?alhamduillah mun iso maybe like 20mins ago ,masha Allah dama na kira naji ya kuka isa ne .
thank you love ya su Anty Hajara
?duk suna lafiya tana gaishe ki bamu dade da rabuwa ba
,ina amsawa love ,duk sukayi shiru na few seconds anyways ki huta lafiya pookie make sure kinci abinci ,and don’t stress yourself Allah ya bada saa ,
ameen ya Allah nagode talk later,love you pookie ,love you too .
mama da abba ta Kira idan suka kara mata addua da fatan alkairi. jim kadan aka knocking kofar ta ,abinci ne daga hotel din , ta karba tare da godiya ,sosai tachi abinci ta nufi toilet tayi wanka tayi sallar azahar
bayan sallar magrib Ta zauna a room ɗinta tana ɗan duba wasu daga cikin designs ɗinta, aka turo mata message.
PARTICIPANTS’ ORIENTATION & BRIEFING — 8:00 PM
Venue hotel conference hall
by 7:30 ta shirya cikin farar abaya tasha blacks floral designs masu kyau ,tayi rolling mayafinta da kyau ,lips gloss kawai ta shafa kamshin nan nata daya zama Kamar signature yana manne da ita ,tun ranar data taga email takewa kayyan da zata taho dasu kabbasa , wayarta ta dauka da card din dakin.
A reception ta haɗu da Mubeen da Rayyan kamar daga massalaci suke
.lalle Mimi kin samu duniya kin manta da yan rakiyar ki tunda muka zo biki kara bi ta kanmu ba ,oh common ray don’t be dramatic sai kace wani baby ?neman me zan maka ?abinci zan baka a baki ko diaper zan canza maka ?nuwayrah ta fada tana rolling Idonta.ba ko daya mimi just a bit of kindness won’t be bad ko ?kaga bari naje meeting din nan ray i promise to check on you idan na fito yaya zan dawo na same ka ?girgiza mata kai yayi nope bacci Zan shiga nayi ,sai dai safe ma hadu ,to yayana Allah ya tashe mu lafiya ,hanyar confrence room din aka nuna mata
A lokacin data shiga, ta sami wasu participants din a zaune . gaishe dasu tayi ta nema empty sit ta zauna ,bayan minti biyarda zaman ta organizers suka shigo tare da gabbatar da kansu
mrs veronica Amos ce ta mike
“Good evening, everyone, and welcome to the Fashion and Cultural Heritage Residency Program.hall din yayi tsit ana sauraran mrs veronica Ta ci gaba da bayyana yadda program ɗin zai kasance.daga ƙarshe ta shiga cikin abin da kowa yake jira.Competition.Tomorrow morning, the competition officially begins.(gobe da safe zaa fara gasar )Nuwayrah ta gyara zamanta.“Each participant will receive a specific design brief.Ta ɗan tsaya.“You will have two days to complete your outfit.(kuma ko wanne daga cikin ku yana da kwana biyu dan kammala aikinsa )Wasu daga cikin participants suka fara kallon juna.
“Your materials will be provided by the organizers.”(mun tanadar muku da Kayan Aikin da zakuyi amfani dasu )
nan aka fara fito masu dasu Silk,Organza,Velvet ,Gold metallic embroidery thread,Pearl beads,Zardozi materials,Sequins,Lining fabric.
Nuwayrah ta lumshe idonya harta fara tunanin yadda za ta haɗa gold metalic da zardozi .
mrs veronica ta ƙara da cewa ,And there is one important rule ,Hall ɗin ya ƙara yin shiru.you will not be completing the outfits privately in your hotel rooms( akwai wani rule guda daya ,baa dakin da aka sauke ku zakuyi dinkin ba ) Nuwayrah ta ɗago kai.“All participants will work in the designated competition hall, in front of the judges and invited guests.(akwai hall din da muka tanada dan gasar inda zakuyi dinki a gaban alkalai da bakin da aka gayyata
Nuwayrah ta ji wani irin excitement ya cika kirjinta.Ba tsoro ba ne Wannan karon challenge take so ,Ta kalli hannunta.Hannun da suka saba da needle,Hannun da suka saba da embroidery,Hannun da suka yi mata designs da yawa a cikin ɗakinta ,Gobe za su yi hakan…a idon duniya.
, bayan mrs veronica ta gama bayani , aka ba kowane participant damar gabatar da kansa, inda ya fito da kuma salonsa na dinki
good evening everyone "I'm anjola David from Lagos. anjola ta gabbatar da kanta da irin dinki fashion data kware a kai daga nan sai Chidinma okafar daga Enugu,Kwararriyar fashion designer wacce ta kware sosai akan harkar beadworks a jikin kaya sai amirah Alhasan daga katsina wacce ta shara a nata bangaren sai
al ameen saidu daga Abuja shima sharrare ne wajan dinkin kayan amare na gani na fada ,nuwayrah ce karshe inda ta gabbatar da kanta da kuma irin ayyyukan da ta fi kwarewa akai wato embroidery
kallo ɗaya zaka masu ka tabbatar da cewa kowanne participant yana auna kwarewar ɗan uwansa a fakaice. a reception ta sami rayyan yana jiranta sama sama suka hira kowa ya nufi dakinsa
next day
Ƙarfe bakwai na safe, Nuwayrah ta shirya tsaf simple dogowar riga ta sa . Rayyan da Mubeen suna jiranta a reception ɗin don raka ta zuwa babban hall din gasar (Competition Hall). hall ya sauya sosai daga daren jiya. An kafa wuraren aiki (workstations) guda biyar daban-daban, kowanne da kyamara yadda mutane zasu iya kallo daga nesa. duk an ajiye mutum mutumi (mannequin), da keken ɗinki na zamani , da kuma saitin kayan aiki.
Babban alƙalin gasar ya shigo tsakiya tare da abin magana barkan ku da zuwa Ranar Farko ta gasar mu ,Jimillar sa'o'in aiki yau sa'o'i 6 ne, Kuna da mintuna 10 kacal don zaɓar kayan aiki ,lokacinku ya fara YANZU!
gabadaya suke mike zuwa teburin tsakiya cikin sauri anjola ta kwashe Royal Blue Velvet mai yawa, al ameen ya kwashe kyallin Sequins da zaren Metallic threads, Chidinma ta ɗauki Organza da dutsen Pearl beads, Amirah kuma ta kwashe silikin Silk mai yawa.
Nuwayrah ta tsaya a gefen tana kallon teburin. dik sun kwashe kusan komai , ta ɗauki ragowar Champagne Gold Silk , ta haɗa da Royal Blue Velvet don fito da kwarjinin sarauta, sannan ta ɗauki Organza da zaren zinare na Gold Metallic Thread tare da saitin Zardozi frames. ta koma mazauninta, Mubeen da ke kallo daga nesa ya raɗawa Rayyan
rayyan , kalla duk sun fara yanka amma Mimi fensir ta dauka tana zane
Rayyan ya saki gajeren murmushi yana kallon yadda take aiki cike da ƙwarrewa
"That’s her strategy. She plans before she cuts. Irin aikinta ke nan.( Tana fara tsara lissafi ne kafin ta sa almakashi a kan kaya .)
Lokacin Hutun Sallah da Abinci yayi , aka busa karar Lunch & Prayer Break
Duk masu aikin suka dakata. Nuwayrah ,wuce dakin ta don gudanar da Sallar Azahar. Bayan ta idar da sallah, ta samu Rayyan da Mubeen a restaurant ɗin hotel din inda suka zauna ta ci abinci suna kara karfafa mata giwuwa
Bayan an dawo daga hutu, participants suka cigaba da aiki, lokacin Sallar La'asar ya yi aka sake basu gajeren hutu na minti 20 don gudanar da sallah.bayan sun dawo
Sa'ad da alƙalai suka ƙaraso wajen Nuwayrah , Madam Veronica ta tsaya tana duba yadda Nuwayrah ke amfani da allurar Zardozi wajen saka zaren zinari a kan siliki.
"Interesting choice of colors, Nuwayrah, Madam Veronica ta faɗa tana kara duba aikin nuwayrah ,but Zardozi hand embroidery takes a lot of time. Do you really think you can finish this detailed motif before tomorrow's deadline?"
(Zaɓin launukanki na da ban sha'awa, Nuwayrah. Amma adakar hannu ta Zardozi tana ɗaukar lokaci mai yawa sosai. Shin kina tunanin zaki iya kammala wannan zanen adakar a gobe ?)
Nuwayrah ta ɗago kanta tana murmushi mai cike da ƙwarin gwiwa, ta gyara gilashin idonta
"Yes, Ma'am. Hand embroidery requires patience, but accuracy is faster than rushing to fix mistakes later.
(Ƙwarai kuwa, Ma'am. Adakar hannu tana buƙatar haƙuri, amma yin aiki cikin natsuwa da rashin kuskure ya fi sauri da gaggawar da za ta kai ka ga tsayawa gyara kuskure daga baya.)
Alƙalan suka jinjina kai cikin burgewa suka wuce.time up aka masu
Kowa ya ajiye kayan aikinsa. Rigar Nuwayrah ta riga ta sami fasali mai kyau a jikin mutum mutumin ta ,Rigar silikin ta ɗinku cif kuma aikin Zardozi da kayan pearls a gaban rigar sun fara fitar da wani irin kyan sarauta wanda yake ɗaukar idon kowa a hall din .
Sanda suka fito zuwa harabar hotel ɗin bayan sun yi Sallar Magriba da Isha'i, Mubeen ya taɓa kafaɗar Nuwayrah
Mimi, gaskiya rigar ki ta hadu idan kika ƙarasata gobe babu mai ƙamo ƙafar ki.Weldone auta ban taba tunanin kwarewar ki ta kai haka ba .
Akwai sauran aiki gobe Yaya Mubeen. Aikin gyara na ƙarshe (finishing) da saka beading ɗin mayafin shine babban aikin hopefully dai na gama kafin lokaci ya cika
Rayyan ya mīƙa mata bottle water mai sanyi yana kallonta cikin alfahari
Kinyi abin a-yaba a yau, Big Head. kiyi bacci da wuri Gobe inshallah zaki ƙarasa abin da kika fara.
da kyar take iya daga kafa har ta isa daki ya rabbi ,zanyi iya kuwa ?ta fada cikin rashin tabbas text message din jawad ta gani kamar haka
pookie na san kinyi dinki yau kin gaji sosai Fatan kinyi nasara a matakin farko? Allah Ya ba ki nasara a matakin ƙarshe na gobe. I am so proud of you. good night i love you
Nuwayrah ta tura masa saƙon godiya a taikace
Nagode sosai love . Addu'arku nake buƙata. Goodnight love you too
Ta ajiye wayar a kan teburin kusa da gadonta, ta kashe fitilar ɗakin gaba ɗaya. Saboda irin gajiyar da take ɗauke da ita a jikinta da ƙafafuwanta, ba ta daɗe tana saƙa tunani ba bacci mai nauyi ya kwashe ta
(mimi da bacci 5&6😂)