Free chapter · Read without an account

Final Stitch

by ZAHRA B MRS · Nuwayrah the foreigner’s passion


A safiyar day 2 , gajiyar jiya har yanzu bata saki jikin  Nuwayrah ba , Ƙafafuwanta duk  tsami suke mata , yatsunta wasu duk ta cike da allura garin sauri ,bata taba dinki under pressure ba ,duk ba wanna bane a gaban yanzu ,gabadaya tunaninta yana kan unfinished rigar ta . ta dauke  littafinta na zane (sketchbook) tana sake nazarin sauran aikin da ke gabanta.

 yanzu da take sake nazarin  mayafin Organza veil ɗin da za ta haɗa da rigar, sai ta gane cewa idan ta bi ainihin original plan ɗinta na ɗora shi ta hanyar ɗinkin cikin gida (internal seam), nauyin zaren Zardozi zai janyo kyallen, ya sa shi yin yamutsewa (wrinkle). dole ta canza shawara dan hakan zai iya janyo mata matsala ,abincin da aka kawo mata ta dan tsakura gabadaya bama ta jin yunwar sabida tunanin me zai faru anjima ,it’s better ko na biyun karshe taci  akan ta zama ta karshe dan a yadda taga sauran sun dage ba lalle ta kamo kafarsu ba 

A cikin Competition Hall, yanayin hall din  ya sauya sosai  ba kamar jiya ba . babu wannan zumumdin a fuskar sauran masu gasar ,  fuskar kowa  ɗauke da gajiya kuma matsin lamba wajan gama dinki a specific time.

 Anjola  tana ta gaggawar gyara gefen rigarta saboda amfani da Velvet mai nauyi da ta yi ya sa rigar guntulewa a gefe guda. Chidinma tana ta ci  gaba da tsara aikin Organza ɗinta cikin  kwarewa da natsuwa, tana fitar da wata rigar al'ada mai kyaun gaske .

Al ameen  ya ƙera wata Gown ta Couture mai ɗaukar ido saboda ƙyallin Sequins da ta sha.

 Amirah ita ma tana gab da kammala aikin rigarta ta Silk street fashion. Tabbas, duk masu gasar  gwanin kansa ne, kuma kowa yana auna ƙwarewar ɗan uwansa a fakaice.

Babban alƙalin gasar ya matso tsakiya tare da ba da umarnin ƙarshe

designers , barka da zuwa sa'o'i na ƙarshe! Kuna da  awa  hudu nan gaba don kammala ɗinki, gyara na ƙarshe, da tsara abin gani a jikin robar gwaji. Ku tuna, ba ɗinki kaɗai muke dubawa ba. Za a gwada ku a kan  Manufa, Ƙwarewar aiki, Gyara na ƙarshe, Tsari na musamman, Adana al'ada, da kuma Tsarin gabatarwa. Kayayyakin da kuka kammala za su tafi kai tsaye zuwa filin nune-nune 

Nuwayrah Ta ɗauki mayafin Organza ɗin ta fara ɗaure shi a gefen kafaɗar rigar Silkɗin domin gani da idonta.Maganar dazu   ta tabbata.

Ɗinkin ya ja kyallen Organza ɗin, nan take ya fara guntulewa yana yamutsewa a jiki. 

Nuwayrah ta tsaya cak. salatin annabi kawai take a zuciyarta wani irin disaster ne haka ?ya rabbi juyawa tayi suka hada ido da amirah wacce komai nata yayi prefect ,dariyar rainin hankali amirah tayiwa nuwayrah ,jiki a sanyaye nuwayrah  Ta cire allurar da ta sanya a jiki, ta ajiye kyallen a kan tebur, sannan ta sa hannu ta gyara gilashin idonta. Ta ja numfashi tana sake nazarin rigar .Maimakon ta matsa lamba tayi  dinki (internal seam), sai ta yanke shawarar sauya dabarar (finishing technique). Za ta yi amfani da dabarar sakawa ta hanyar invisible hand-tacking da tsara kananan duwatsun Pearl beads a saman mahaɗar don ɓoye ɗinkin, tare da samar da nauyin da zai sa Organza ɗin ya kwanta ba tare da ya ja kyallen ba.

Daga nesa, Mubeen yana kallonta cikin fargaba, ya rada wa Rayyan .. kamar akwai matsala a wajen mayafin can. Za ta iya gamawa kafin lokacin kuwa ?

Rayyan ya zuba mata ido ta nesa. Ya lura da yadda fuskarta ba ta nuna firgici ba, kawai jikinta ba karsashi 

A lokacin gajeren hutun , Nuwayrah ta fito shan ruwa da samun natsuwar zuciya dan she is almost running mad ,kiran jawad ne ya shigo 

Ta ɗaga wayar tare da manna ta a kunnenta

Hello, love 

pookie ya aikin ? Fatan komai yana tafiya daidai ?muryarsa ta fito daga ɗayan ɓangaren. muna kan aikin love . mun kusa gamawa 2 more hours  ta amsa a taikaice .

Jawad ya ɗan sauke numfashi,

To ki yi ƙoƙari dai, Pookie. Amma kar ki manta da cewa akwai sauran abubuwan da za mu shirya game da aurenmu idan kika dawo. Kada gasar nan ta ɗauke miki hankali gaba ɗaya.. Nuwayrah ta dafe  goshinta, cikeda takaici  "Zamu yi maganar idan na dawo Kaduna  yanzu ba lokacin maganar biki bane tunda ba gobe zaa daura auren ba .zan koma wajen aiki.Ta kashe kiran, ta ajiye wayar a gefe. ko ta kan su rayyan bata bi ta koma table dinta,gabadaya haushin su take ji gani take kamar so suke fasa mata kai na bogi har taji kamar zata iya shiga gasa irin haka ,yanzu idan baayi hankali ita zata ci na karshe . 

2 more hours muryar alkalin wasa ta ratsa kunnan ta 

cigaba tayi da abun take yi Hannayenta sun gaji,  amma idanunta a buɗe suke sosai 

Zaren  Gold metallic thread yana wucewa ta cikin rigar . Ta sanya ko wane dutsen Pearl daya daya  a mahaɗar Organza da Velvet. Kowane ɗinki yana shiga cikin lissafi da kiyayewa.

Ta gyara zamantawa, ta ɗaga gilashinta don goge idanunta daga gajiyar hasken fitilu,  Organza veil ɗin a ƙarshe. Mayafin ya sakko daga kafaɗar rigar , ba tare da kowane irin yamutsewa ba.Ta ja baya taku biyu, ta tsaya tana kallon robar gwajinta (mannequin).

Rigar Modern Northern Royalty Couture ta kammala tsaf! Kyallen Champagne Gold Silk da , Royal Blue Velvet da ke gefen kafaɗa, da datsan adakar Zardozi masu sheƙi  sun haɗu sun fito da wata rigar sarauta mai kwarjini 

TIME UP (LOKACI YA ƘARE!)

Duk masu gasar  suka ajiye kayan aikinsu table tare da mikewa ,gabadaya hall din ya kaure da tafi 

aka sauya fitilun hall zuwa fitilun (runway lights). Sakamakon kowane participant an fito da shi gaban alƙalai da 'yan kallo.

Masu gabatarwa suka fara kiran kowa daya bayan daya  don nuna rigarsa.

Lokacin da aka kira sunan Nuwayrah, ta taka zuwa tsakiyar filin nune-nune kusa da robar gwajinta. Ba ta yi tafiyar models (catwalk) ba ta tsaya cikin  natsuwa, tana fuskantar alƙalan.

Babbar  alƙali Madam Veronica ta gyara zamanta, ta kalli Nuwayrah ta amsa abin magana

"Nuwayrah, yusuf moddibbo what inspired this design?" (Nuwayrah, miye ya ba ki shawarar ƙera wannan samfurin rigar?)

Nuwayrah ta ɗago kanta, muryarta ta fito cike da confidence .Tunanina ya fito ne daga asalina na Arewacin Nijeriya mutunci, kamun kai, da kwarjinin sarautar al'adarmu. Ina son na tabbatar da cewa ƙwarewar aikin hannu na al'ada kamar Zardozi da adakar hannu ba na daɗaɗɗen tarihi kaɗai ba ne. Suna iya fitowa a kowane dandamali na duniya na zamani, su fito cikin 'yanci da kwarjini, ba tare da sun rasa asalinsu ba.tafa mata akayi both masu kallo da alkalai .

Alƙalan guda uku suka tattara littattafansu na maki.  suka shiga wani ɗaki na musamman don gudanar da tattaunawar ƙarshe  (final score aggregation).

hall din yayi  shiru. Masu gasar  duk suna zaune a table dinsu cike da  fargaba.banda kiran Allah ba abinda nuwayrah take a zuciyarta ,ita dai burinta kar tazo ta karshe .

Bayan mintuna sha biyar na jiran tsammani, ƙofar ɗakin alƙalan ta buɗe.

Madam Veronica  ta fito tare da sauran alƙalan guda biyu. hannunta rike da ,  (golden envelope). Ta taka zuwa tsakiyar dandamalin, ta gyara abin magana

All contestants, please come forward. (Duk masu takara, ku fito zuwa gaba.)

Nuwayrah ta miƙe tsaye,, ta taka a hankali tare da sauran masu takarar zuwa gaban dandamali.Madam Veronica  ta kalle su gaba ɗaya, sannan ta fara yaga bakin rufin envelope ɗin...

hall din ya dauki wani irin shiru . Kowa ya riƙe numfashinsa 

Designers, sakamako ya kammala. Daga cikin maki 100 na Ƙwarewa, Sabon Tsari, Gyara na Ƙarshe, da Gabatarwa, zan fara kiran sunaye daga matsayi na biyar

Zuciyar kowa ta doka.

In  5th Place... with 72 points ,Amirah  from Katsina You walk away with a cash prize of ₦500,000. cike da rashin kuzari amirah ta karasa wajan mrs veronica ammsar check da lambar yabo sai murmushi yake take. ajiyar zuciya nuwayrah ta sauke ya rabbi nagode maka da bani bace ta karshe,tasan yanzu zaa kira sunan ta 

IN 4th Place... with 74 points—anjola  from Lagos! You also walk away with ₦500,000.

anjola ta karasa  ta amsa cike da ladabi jin sunan anjola yaba nuwayrah mutukar mamaki .

In 3rd Place... with 83 points Al Ameen from Abuja! Winning the cash prize of ₦1,000,000

Al ameen ya yi tsalle cikin murna ya amsa.  sauran mutane biyu kacal a kan dandamali Nuwayrah da Chidinma. suka kalli juna tare da rike hannun junansu 

In 2nd Place... with 89 points—Chidinma from Enugu! Winning ₦2,000,000 

hall  ya ɗauki tafi da ihu! Wannan yana nufin..."And the Grand Champion of the Cultural Heritage & Fashion Residency Challenge, scoring an incredible 96 out of 100... NUWAYRAH YUSUF MODIBBO from Kaduna 

alƙalan guda uku suka miƙe tsaye suna tafa mata. babbar  Alƙali Madam Veronica  Mr john da kuma Darakta Al-Mansur duk su  ukun suka jefa mata ƙuri'arsu .

Nuwayrah ta daskare a tsaye  Muryar "Winner" ta riƙa amsa a kanta kamar a mafarki. sai hawaye wani na bin wani 

You win the Grand Cash Prize of ₦3,000,000, a National Trophy, and an official 3-Month Brand Ambassador Contract with the Heritage Fashion Council

Cikin minti ɗaya, kyamarorin gidajen labarai (news reporters) da 'yan jarida suka bayyana a gabanta da hasken fitilunsu (camera flashes). Masu ɗaukar rahoto na gidajen gidan rediyo da talabijin suka miƙo mata abin magana suna tambayoyinta

, how do you feel right now?

Did you expect to win the 3 Million Naira and a brand contract? a takaice ta basu amsa sabida yadda taji kamar kanta na juyawa  mubeen ne da rayyan suka karaso tare da sata a tsakiya dan rakata dakin ta suna tafiya ta tunanin , wannan gasar kawai 'yar ƙaramar harkar ɗinki ce ta gwajin , ba ta taɓa tunanin abin zai faɗaɗa ya kai ga babban mataki na kafa tarihi, lambar yabo (award), takardar nasara (certificate), da sa hannu a babban kwangilar ambassador ba suna shiga dakin kuwa  Mubeen ya rungumeta 

Mimi  I told you! Wallah muna da Embroidery Queen a gida congratulations auta ,thank thank you yaya mubeen ta fada har yanzu hawayen farin ciki take .

Rayyan ya tsaya kusa da shi, fuskarsa ɗauke da wani irin murmushi da alfahari 

You did it, Big Head. You conquered Abuja nasan zaki iya congratulations mimi ,inshallah nuwayra’s stitches sai ya zaga duniya ,nagode ray nagode da endless support dinka ,muna komawa kano kai da yaya mubeen zan kai ku date bills on me .

bayan laasar aka kara kiransu dan sallama da bankwana aka kara daukan hotona .

Nuwayrah tana riƙe da katuwar takardar lambar yabo da takardun kwangila, wayarta da ke cikin jaka kuwa sai vibrating take . Saƙonni na Congratulations   ke ta shigowa ta kowane ɓangare, masu gasar duk sukayi exchanging numbers,nuwayrah taso su koma kaduna a yau rayyan yace su bari sai gobe 

da wuri tayi sallama dasu rayyan dan kafar ta har rawa take mata Sabida tsayuwa .sai yanzu ta sami damar daukar wayarta da messages din mama ta fara cin karo 

maman auta❤️ barakallah masha Allah mubeen ya tura mana ta waya ,Allah ya kara sa albarka a hannunki yasa kifi haka abban ku yana gaishe ki 

 Yaya Sadiq ❤️"Congrats Mimi! So proud of you, Little Sister. Real Champion

chan ta bude WhatsApp voice note din  Anty Firdausi & Yaya Nabil  "AlhamdulillahNuwayrah’s Stitches to the world ,Allah yasa albarka ,harda muryar afrah itama tana cewa a bata zatayiwa anty mimi magana

hajiyarsu rayyan ma da sisters dinsa duk sun tura mata congratulatry messages 

    haka tayi ta amsawa cikin nishadi ,message daya take ta anticipating jawad ,shiru be kira ba ,probably he’s busy ta ayyana a ranta 

 


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.