Free chapter · Read without an account

4&5: The Last Goodbye

by Hauwa Jibrin Sulaiman · The Unwanted Daughter

    “Sometimes, the people who love us the most are the ones we lose too soon. Yet, their love stays with us forever.”


Five years later…


Du’a and Amrah were ten years old, while Aryan had just turned fifteen. Da yammacin wata ranar Litinin, family driver ne ya dawo da su daga makaranta.


Da motar ta tsaya a driveway, Du’a ta fito da gudu, school bag ɗinta na rawa a bayanta, ba ta tsaya ko’ina ba, Kai tsaye ta nufi ɗakin Mommy ɗinta


A lokacin, Aneesa na mopping ɗakinta cikin nutsuwa


“Mommy!” Du’a ta kira da muryar da ta cika da farin ciki kafin ta rungume ta da ƙarfi, Aneesa ta ɗan yi dariya “My princess…”


Da sauri ta ɗaga Du’a sama tana juyawa a hankali


 “I have a beautiful daughter…” Ta sumbaci goshinta “I have the most talented baby…”


Du’a ta fashe da dariya “Mommy… stop!” ta faɗa tana dariyar da ta cika ɗakin


Sai Aneesa ta ƙara juyawa da ita “I have a brainy little princess…” Ta taɓa hancinta cikin wasa “You’re one in a million…”


Daga ƙarshe ta rungume ta sosai “And I’d choose you over everything…”


Ta ɗora goshinta a kan na Du’a ”…because you’re my greatest blessing”


Du’a ta lumshe idanunta tana jin daɗin rungumar “This is the best day ever!” ta faɗa cikin farin ciki


Aneesa ta murmusa “So… tell me, what happened?”


Da sauri Du’a ta ciro result slip daga school bag ɗinta “Mommy… I came first again!”


Aneesa ta karɓa tana dubawa, da ta ga 1st Position, murmushinta ya ƙara faɗaɗa “I’m so proud of you sweetheart, you’ve made me proud once again”


Du’a ta yi murmushi, amma bayan wasu secs sai ya fara dusashewa


Aneesa ta lura, ta ɗaga haɓarta a hankali

“What’s wrong, darling?”, Du’a ta sunkuyar da kai “I know Daddy doesn’t like me…” Ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ci gaba “He probably won’t even care about my result” Kalaman suka fito a hankali, amma sun bugi zuciyar Aneesa kamar kibiyar da ba a gani


Ta zauna a gefen gadon, sannan ta zaunar da Du’a a cinyarta “Look at me sweetheart”


Du’a ta ɗaga idanunta, Aneesa ta share mata wata ƙwalla da ta fara taruwa

“Never say that again, okay?”


Du’a ta yi shiru, Aneesa ta ci gaba cikin murmushi “I believe… one day, your father will love you the way you’ve always wished”


“And when that day comes… He’ll realize what an amazing daughter he has”


Du’a ta ɗan murmusa “I pray for that every day, Mommy”


Aneesa ta sumbaci goshinta “And Allah never ignores sincere prayer”……


Aryan na fitowa daga ɗakinsa domin ya ɗauko ruwa, sai ya hango Du’a tana fitowa daga ɗakin Aneesa, result slip ɗinta na hannunta, fuskarta cike da farin ciki


Da ta gan shi, ta yi saurin ƙarasa wajensa “Yaya Aryan!”, Ya tsaya yana kallonta


“Guess what?”


“What?” Ya tambaya yana murmushi


Ta miƙa masa result slip ɗin

“I came first… again!”


Aryan ya karɓa ya duba, da ya ga First Position, fuskarsa ta cika da farin ciki

“Wow… our princess” Ya ɗan tsugunna har daidai tsayinta “I’m proud of you, baby”


Ya miƙa mata hannu “Congratulations”, Du’a ta yi dariya tana shaking hand ɗinsa “Thank you, Yaya”


Aryan ya ɗaga hannu zai shafa kanta… Sai idanunsa suka sauka kan Zahra da ke tsaye a bakin parlour


Ba ta ce komai ba, amma kallon da ta yi masa ya isa ya sa murmushinsa ya ɓace


A hankali ta ɗaga gira, Aryan ya haɗiye yawu ya san wannan kallon sosai bcos kallon gargadi ne like… “Don’t you dare”


Da sauri ya janye hannunsa

“I’m… happy for you” Ya faɗa cikin sanyin murya kafin ya juya ya haura sama


Du’a ta tsaya tana kallonsa har ya ɓace, ba ta fahimci dalilin da ya sa ya canja ba


Da Aryan ya tafi, Zahra ta ƙaraso inda Du’a take tsaye, ta ƙwace result slip ɗin daga hannunta, ta duba taga First Position


Fuskarta ta canja nan take, “Again?” Ta yi magana a hankali “Every single time…”


Ta kalli Du’a “Why do all your teachers like you this much?”, Du’a ta girgiza kai “I don’t know, Mummy”


Slap! Mari kawai ta kai mata, Du’a ta dafe kumatunta

“If you think you’ll keep embarrassing Amrah in this house, then you’re mistaken!”


Hawaye suka cika idanun Du’a “Mummy, wallahi ban…” Zahra ta katse ta “Keep quiet!”


A tsorace Du’a ta juya da gudu, abu ɗaya kawai take tunani Mammy…


Ta san idan ta je wajen Aneesa, za ta samu nutsuwa amma kafin ta isa corridor… Amrah ta fito daga parlour


Da ta ga Du’a na gudu… sai murmushi ya bayyana a fuskarta a hankali ta miƙa ƙafarta


Du’a ba ta lura ba sai kawai ta yi tuntube ta faɗi “Ahhhh!” Ta faɗi da ƙarfi


Bakinta ya bugi tiles nan take jini ya fara fita “Mammyyyyy!” Ihun da ta yi ya cika gidan gaba ɗaya


Fatima ce ta fara fitowa daga kitchen “Ya Salam!”


Ta yi saurin ƙarasa wajen Du’a. A lokaci guda… Aneesa ta fito daga ɗakinta cikin firgici “Du’a!”


Aryan ma ya fito daga sama da gudu, da ya ga jinin bakin Du’a… Zuciyarsa ta tsinke


Ya fara daga saukowa stairs


Sai Zahra ta yi magana cikin tsawa “Aryan!”


Ya tsaya cak

“If you take one more step…” Ta nuna Du’a “…I swear you’ll regret it”


Shiru ya mamaye wajen, Aryan ya kalli mahaifiyarsa sannan ya kalli Du’a


Ganin Idanunta suna neman taimako ga jini dake zuba daga bakinta, zuciyarsa ta ƙi barinsa ya juya


Amma… ya san Mummy ba ta yin barazana a banza


A hankali idanunsa suka cika da ƙwalla

“I’m sorry…” Ya furta cikin murya mai rauni “In shaa Allah zai warke da wuri”


Ya juya ya koma ɗakinsa, yana shiga… Ya jingina bayansa da ƙofar, hawayensa suka zubo


For the first time… He hated himself for being too weak to protect his little sister


Aneesa ta isa wajen Du’a da gudu

“Oh my baby…” Ta rungume ta cikin firgici “Where are you hurting?”


Du’a ba ta iya magana ba, sai kuka take yi, Fatima ta kawo first aid box da sauri


Su biyun suka taimaka suka tsaftace jinin, suka yi mata dressing


Aneesa na shafa kanta a hankali

“It’s okay… I’m here”


Da kalmar nan kaɗai, kukan Du’a ya ɗan lafa


Fatima ta fito daga ɗakin bayan sun gama, da ta wuce parlour… sai ta haɗa ido da Zahra


Zahra ta watsa mata wani kallon gargaɗi, Fatima ta sunkuyar da kanta


Ba ta ce komai ba, ta san iyakar aikinta kuma, a cikin zuciyarta…ta yi wa Du’a da mahaifiyarta addu’a “Ya Allah… Ka zama Garkuwarsu”


Bayan wannan ranar… rayuwa ta ci gaba da tafiya, amma ba cikin sauƙi ba, bcos kowace rana, Du’a da Aneesa suna fuskantar wani sabon ƙalubale


Zahra ba ta daina ƙoƙarin wulaƙanta su ba, Amrah kuwa tana girma ne tana kwaikwayon duk abin da mahaifiyarta ke yi


A duk lokacin da Aryan yake gida, Du’a kan ɗan samu sauƙi, yana ƙoƙarin kare ta gwargwadon ikonsa


Sai dai da zarar ya fita makaranta ko wani wuri… Du’a ta sake komawa ita kaɗai cikin gidan da babu wanda ke kare ta sai mahaifiyarta


Life wasn’t fair… But Aneesa never stopped reminding her daughter of one thing


    “No matter how people treat you, never let them change your good heart” 


Du’a kan gyada kai ko da yaushe “I promise, Mommy”


Bayan wasu watanni… Rashin lafiyar Aneesa ta sake tsananta, abin da likitoci suka yi fatan zai lafa…


Sai ya ƙara muni, the cancer had become aggressive, ta gama ramewa kamar mai ciwon aids, karfinta ya ragu sosai, har yakai da tafiya ta fara mata wahala


Duk lokacin da Du’a ta gan ta tana jin ji… Sai zuciyarta ta tsinke, tayi rauni fiye da yadda zaka zata


“Mammy…” Ta kan kira cikin kuka “Does it hurt?”


Aneesa ta kan yi murmushi duk da azabar da take ciki “A little”


Ta shafa kan Du’a

“But Allah is with me”


Saboda Alhaji Muhammad ya ƙara nesanta kansa da Aneesa…Fatima ce ta zama tamkar ‘yar uwanta


Colleagues ɗinta daga private healthcare facility ma ba su taɓa mantawa da ita ba, kusan kullum sai ɗaya ko biyu daga cikinsu sun zo duba lafiyarta


Especially Maria and Farida, sai sauran ma’aikatan da suke ƙaunarta su ne suka zama familynta a lokacin da ta fi buƙatar kulawa


Wata ranar Juma’a.. da misalin ƙarfe goma na safe.. Aneesa ta tashi cikin matsanancin ciwo


“Ahh…”Ta dafe ƙirjinta tana numfashi da wahala


Fatima ta yi saurin riƙe ta

“Ma Aneesa!”


Maria da Farida ma suna wajen, nan take suka fahimci ba ƙaramin ciwo ba ne


Maria ta miƙe tsaye “I’ll call Alhaji, gaskiya ya zo asan abun yi Tana ji da jiki fah”


Ta fito da sauri zuwa parlour, sai dai bata haɗuwa da shi ba Alhaji Muhammad sai Zahra 


Ta zauna cikin nutsuwa tana shan tea

“Good morning, Hajiya” Maria ta gaishe ta cikin gaggawa


“Please… Aneesa is in serious pain, weneed Alhaji to take her to the hospital immediately”


Zahra ta ɗaga kai ta kalle ta, ba alamun damuwa ko kaɗan a fuskarta ta ce


“So?”


Maria ta ɗan yi mamaki “Hajiya… her condition is getting worse fah kuma ki ce So?”


Zahra ta ɗora cup ɗinta a hankali kan table na gabanta

“And what exactly do you want me to do?”


Maria ta yi shiru na ɗan lokaci

“Please… just call her husband ki taimaka mana, or ki bani na Kira sa”


Zahra ta yi murmushin rainin hankali

“If she wants him…” ta dakata


“She can call him herself” Ta miƙe tsaye ta nufi ɗakin Aneesa


Da ta shiga, ta tarar Aneesa na kwance tana wahalar numfashi, ta tsaya tana kallonta na wasu mintuna


Sannan ta ce cikin wata murya mai sanyi… amma cike da kaifi a kalaman nata “Hope your good luck can save you now”


Ba tare da ta jira amsa ba, ta juya ta fita, Maria ta tsaya cak, ta kasa yarda da abin da kunnuwanta suka ji


A cikin ɗakin Du’a ta rungume Mammy ɗinta tana kuka


“Mammy… Please don’t leave me”


Aneesa ta yi ƙoƙarin murmushi

“I’m not going anywhere…”


Amma ko ita kanta… ta fara jin cewa jikinta na bata wani saƙo


Du’a ta rungume Mammy ɗinta da ƙarfi, hawaye na zuba ba ƙaƙƙautawa

“Mammy… please don’t leave me”


Aneesa ta ɗora hannunta a kan Du’a cikin rauni, ta yi ƙoƙarin murmushi

“I’m not leaving you now, sweetheart…”


Haka nan ta fara jin cewa lokaci nata na ƙara kusantowa


Maria ta dawo ɗakin da sauri

“We can’t wait any longer”


Ta kalli Farida “Let’s take her to the hospital plsss”


Fatima da Farida suka taimaka wajen ɗaga Aneesa, Du’a ta tsaya tana kuka


Ta ga yadda Mammy ɗinta ke wahala wajen numfashi, nan take ta ji tsoro fiye da kowane lokaci, kawai ta hango wayar Aneesa a gefen gado


Ta ɗauka da sauri

“Mammy… Can I call Daddy?”


Aneesa ta gyada kai a hankali, da hannayenta masu rawa, Du’a ta nemo number ɗin Daddy ta kira


Bayan ringing na ɗan lokaci ya ɗaga

“Hello?”


“Da… Daddy…” Muryarta ta katse saboda kuka “Mommy is very sick, Dan Allah ba mu ba Daddy please come wallahi we need you”


Daga ɗaya ɓangaren wayar, Alhaji Muhammad ya sauke ajiyar zuciya

“I’m in a meeting, I can’t leave now”


“Daddy please… She’s in pain ka taimaka mana”


Sai ya katse ta “Du’a stop disturbing me while I’m working”


“I’ll come when I’m free” Click ya kashe wayan


Du’a ta tsaya cak, ta sauke wayar a hankali, wannan karon not like before ba kuka ta fara ba kawai shiru


Shirun da ya fi kuka ciwo shi tayi


Maria ta karɓi wayar daga hannunta, ta rungume ta “It’s okay… We’ll take care of your mom”


Ba tare da ɓata lokaci ba, suka garzaya da Aneesa zuwa asibiti


Throughout the journey Aneesa ba ta daina kallon Du’a ba, kamar dai tana ƙoƙarin haddace fuskarta ne, kamar tana jin cewa, wannan ne karo na ƙarshe


Da suka isa emergency unit…


Likitoci suka yi saurin karɓar Aneesa

“Please wait outside” Ƙofar emergency room suka rufe


Du’a ta tsaya tana kallon ƙofar “Mammy…” Ta furta a hankali


Fatima ta rungume ta, Maria kuwa ta fara karanta addu’a a hankali Farida kuma na ta kai da komowa cikin tashin hankali


Mintuna suka zama kamar awanni kowa ya rasa abin yi sai addu’a


Bayan kusan awa guda Doctor ya fito, fuskarsa cike da damuwa

“She’s asking for her daughter.”


Da gudu Du’a ta bi shi, ta shiga ɗakin


Mammy ɗinta na kwance, jikinta ya yi rauni sosai amma da ta ga Du’a, sai ta yi murmushi “My brave girl…”


Du’a ta ƙarasa gefenta ta riƙe hannunta

“Mammy… You’re going to be fine In shaa Allah”


Aneesa ta girgiza kai a hankali

“No sweetheart.. Listen to me”


Du’a ta fara girgiza kai tana kuka “No…Please don’t say that”


Aneesa ta share mata hawaye da yatsunta masu sanyi

“You’re stronger than you think, promise me… you’ll never stop praying


Du’a ta girgiza kai

“I promise”


“You’ll continue your education ba zaki yi wasa da shi ba”


“I promise” Du’a ta amsa


“You’ll respect everyone, even those who hurt you”


Du’a ta kasa amsawa ta fashe da kuka, Aneesa ta matsa hannunta

“Don’t let hatred change your beautiful heart, bcos Allah sees everything and one day…


“He will reward your patience”


Ta juya ta kalli Maria da Farida da shigowarsu kenan

“Ina roƙonku please… kada ku manta da Du’a”


Maria ta fashe da kuka “We won’t, I promise”


Farida ma ta share hawayenta

“Za ta kasance tamkar ’yarmu, balle ma zaki warke da yardan Allah”


Aneesa ta lumshe idanunta na wasu mintuna sai ta sake buɗe su ta kalli Du’a


“I love you… My precious daughter and I’ll always love you”


Du’a ta ɗaura kanta kan ƙirjinta

“I love you too, Mammy but Please don’t go”


Aneesa ta ɗan motsa laɓɓanta


“La ilaha…”


“…illallah…” Kalmar ta tsaya, monitor ɗin da ke gefenta ya fara canza sauti


Beep…


Beep…


Beeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeeep…


please kuyi following acc dina, sannan kuyi liking na book din, yin hakan tamkar kunce nake yin update na 5 chapters ne a rana


Hauwajay writes ***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.