Free chapter · Read without an account
16
*DUHU BAYAN MURMUSHI*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 16.
Sarac Stars R Pen...✍️
Bikin saura sati biyu dai-dai Inna suka sauka a Kaduna, a wannan karan tayi mamakin irin kyakkyawar tabar da mama ta yi mata, ko da yake ba mamaki tunda ta ƙullo abun arziki da yawa ta kawo musu, ga kuɗi da 'yan uwa suka haɗa mai tsoka na gudunmawa, shiyasa Mama ta riƙa haba-haba da Inna, hatta abinci sai wanda Inna take so ake dafawa. Zuwa lokacin Mama tayi wa Aina'u gyara sosai dan musamman ta siyo mata magungunan mata wanda ba zasu yi mata illa ba ta bata, sannan anyi mata dilka da gyaran jiki duk da ta san ƙauye za a kaita, nan gaba wannan gyaran duk zai dusashe amma bai sa ta fasa ba duba ta tana so taje da kyawun ta a ganta fes a tabbatar daga Kaduna aka ɗaukota.
Saura kwana biyu bikin da daddare Inna tana zaune a ɗakinsu Aina'u tana yi mata faɗansu na manya, ita kuma ta takure guri ɗaya fuska cike da damuwa, sai take ganin in dai haka sha'anin aure yake da girma to dama bata yarda tayi ba, dan yadda inna take jaddada mata tayi biyayya kamar ta fashe da kuka dan ta tsorata da lamarin, suna a wannan yanayin ne Baba yayi sallama ya shigo ɗakin cikin nutsuwa.
Sannu da hutawa Inna, da fatan an yini lafiya.
Alhamdulillahi, Babangida an dawo.?
Mun dawo Inna.
To sannu da fama, Allah ya ƙara rufa asiri da ɗaukaka na alkhairi. Ai kana ƙoƙari sosai dan ɗazun naga motar kaya ta kwaso gadon Aina'u, nasan kasha kuɗi sosai.
Ai da yake ma kayan daga MG furnitures company ne mun same su cikin sauƙi gasu da kyau, dan na shaida quality ɗin kayansu, yanzu haka sune a ɗakin Uwale, ga kujerun falo duk kwaramniyar yaran nan da suke yi akai kin gansu daram da kyansu, kuma duk mutanen da nayi wa hanya da suka siya kayansu sai sambarka suke yi.
To Alhamdulillahi, ka ga da wannan yaro ƙalau yake da ka kai shi koyon aikin kafinta a gurinsu, saboda sana'a ce mai kyau.
Ai inna kamar kin shiga zuciyata nayi wa Mujaheed kwaɗayin haka amma ga dukkan alamu hakan ba zai yuwu ba, sai dai zan kai Harris wajen shi shugaban kamfanin MG Furnitures ɗin. Showroom ɗinsu yana nan kusa damu a freetime house dake kan titi Ali Akilu kusa da asibitin Giwa.
*Don odern kaya daga MG furnitures A tuntuɓe su a wannan number ***.*
Babangida menene shi shoron ɗin.?
Idan sun haɗa kaya a can copmany da suka yi, to zasu kawo nan showroom su aje a matsayin wajen ajiya saboda idan mutane suka buƙaci kaya zasu je can su zaɓi wanda yayi musu, to shi ne ake kira da showroom.
Auho haka abun yake, kai lallai wannan sana'a ce mai kyau, Allah yasa Harisu ya mayar da hankalinsa ya kowa aikin da kyau.
Cewar inna cikin farin ciki, baba ya muskuta yace.
Aneen, amma Inna zaki yiwa kishiyarki rakiya har can Magami ko.?
Zuwa kai, ai tafiya da ni a ciki, kuma da zarar mun dawo ba zan zauna ba zan koma gida, banda ma ina son komawa da Mujaheed ai da daga can zan wuce.
Baba ya jinjina kai yana ƙara saurayar da kai cikin son bayyana mata abun da ke cikin ransa.
Inna ai ina ganin ki bar Mujaheed a nan saboda na ɗaura niyyar tsayawa akansa sosai, kuma na tabbatar a can wahalar aiki zai ta saka ki, ni kuma wlh bana son abunda zai takura miki natsuwarki.
Haba Babangida lamarin Mujaheed ba zai taɓa zama takura ba, kuma gaskiya kunyi sake sosai akan matsalar yaron nan, saboda ba kwa bashi kulawar daya dace shiyasa ya ƙara haukacewa, amma kaga a Daura wlh ya sauya dan baya fita sai da dalili, sannan bai yi min fitsarin kwance saboda ina tashinsa da asubahi, sannan kullun sai na tasa shi a gaba yayi wanka da safe, daga kai har Uwale kun zura masa ido ne yana sharafinsa shiyasa ya zaɓi gantali akan zaman gida.
Ta ƙare maganar tana tsure shi da ido, jikin baba yayi sanyi dan gaskiya ta faɗa, da sakacinsu a ciki.
Inna shiyasa nace zan tsaya akan Tarbiyyarsa domin ina son na gyara abunda na kasa yi masa tun a farko, saboda bikin nan ne ma na dakatar da ƙudurina akan sai an gama komai zan je na yi masa registern boko da Islamiyya In Sha Allah, kuma ranakun ƙarshen mako zan riƙa janta kasuwa yana ganin yadda muke gudanar da komai.
Kai Masha Allah, in dai hakane to zan bar shi a nan yayi karatunsa dan makaranta nan da bambanci da namu, Allah ya bashi lafiya ya kawo masa ƙarshen wahala.
Baba ya amsa da amin kafin suka cigaba da hirar bikin da zai wakana a jibi In Allah ya kaimu.
****
Magami.
Duk wani shiri ango Idris yayi na tarbar amaryarsa, yayi sabon ɗinki kala uku kasancewar yana da ɗan rufin asiri, yana aikin noma yana kuma kasuwancin gwanjo a nan kasuwar Magami. Kuma kamar yadda suka saba na al'ada a nan cikin gidan gandu ya samarwa Aina'u ɗakinta ciki da falo kusa da na Uwargidansa Aliya, sannan a sashin iyayensa. Babban gidan gandu ne daya shafe Tarihi a haka, idan an shigo babban Zauren gidan ɓangaren 'yan haya ne farko za a shigo, wato sashin gadonsu Mama da aka ware musu nasu ake amsar kuɗin haya duk shekara ana basu, sai wani zaure da za a ƙetare a shiga sashin 'yan uwansu mama da suke 'yan uba su huɗu, kawu Mamman, Yahaya, Auwalu, da Sabitu, sannan sai a ƙarasa wani ɓangare dake can ciki shi ne na kawu Tijjani da iyalinsa, ɗakin Aliya shi ne farko ciki da falo, sai ciki ɗaya na yaranta maza sai ɗakin Amarya Aina'u, sai kuma a can cikin gidan ɗakin kawu Tijjani ne jere dana matarsa ciki ɗai-ɗai sai kuma na ƙannen Idris maza da suke ɓangaren hagu suma a jere guda biyu, can gaba akwai ƙaton fili da aka zagaye da danga suna kiwon dabbobi a ciki, wanda a hankali suke fatan ginewa saboda yara masu tasowa in sunyi aure su saka iyalinsu a ciki. Kawu Tijjani matansa biyu sai dai amaryarsa Safara'u ta rasu tabar yara mata biyu Jamila da Zinatu. wanda a yanzu duk sunyi aure, sai Uwargidansa Laure tana da shida, Hadiza ita ce 'yarsu ta farko tana aure a cikin Anka da yaranta bakwai kuma har ta aurar da biyu, sai Idris ke bi mata, sannan Ƙannensa mata biyu Hansa'u da Sharifa duk sunyi aure suna nan a Magami, sai maza su biyu da suke gaban iyayensu Shamsu da Abubakar.
Aliya mace ce mai haƙuri da yakana bata da zafi ko kaɗan, shi yasa zamansu yayi ƙarko da iyayen mijinta duk kuwa da zafin baba Tijjani, dan shi bahagon mutum ne yana son a girmamashi sosai kamar wani sarki, shiyasa baya shiri da ƙaninsa Sabitu dan bai yarda da mulkin mallakar da yake nuna musu ba, Auwalu ma baya-baya suke da shi sai Yahaya da Mamman sune kaɗai suke bashi wannan girman daya ke buƙata, amma kuma gabaɗaya matansu basu basu ƙofar kawo raini ga 'yan uwansu ba shiyasa suke tsoron kawu Tijjani dan duk lokacin da zai ƙetare sashinsu da ya yi gyaran murya ko wacce zata natsu, idan ya shigo da niyyar zai wuce nasa vmɓangaren to haka zasu zuɓe a ƙasa suna kwasar gaisuwa, zai amsa musu amma kansa a sama saboda gadara, sai ya wuce cikin takun ƙasaita sai kace wani basarake. Kuma haƙiƙa wannan girmamawan da yake samu a cikin gidan shi ne ya ƙara masa girman kai da ɗagawa, sannan ba ruwansa da yin sallama saboda ji da kai illa in zai shigo yayi gyaran murya, hatta 'yan hayan gidan suma haka suke yi masa wannan biyayyar, idan ko sashinsa ya shiga In Sha Allah duk abunda yaci karo dashi a hanyarsa zai shiga yin kwallo da shi yana masifa, shiyasa Aliya ta zama mai tsananin takatsantsan da kiyaye duk wani abu da zai kawo faɗan baba a gidan, ita Inna Laure saboda ta saba bata damun kanta dan bai isa yayi mata wannan mulkin mallakar ba dan itama hatsabibiyar kanta ne. Wannan biyayyar na Aliya ya sanya ta samu babban gurbi a zuciyar Idris har yake yi mata laƙabi da 'yar aljanna, sannan ma duk wani abu nasa mai muhimmanci ita ce akan gaba, ajiyar kuɗinsa ita ce, abinci kuwa ya bata ragamar ta riƙa yin duk abunda yayi mata ya bata zaɓi, wannan karamcin da ta samu na Idris yasa itama take yi masa biyayya kamar ta kwanta ya takata. A lokacin da ya zo mata da maganar yana son auren Aina'u taji kishi sosai, amma kuma ganin ragamarsa gabaɗaya yana hannunta sai ta nuna bata damu ba ta cigaba da kwantar da kai akan itama ta karɓi Aina'u a matsayin 'yar uwa, wannan sadaukarwa da ta yi ya ƙara mata matsayi a zuciyar Idris sannan ya sake mata bakin aljihunsa sosai na shirin wannan auren. Da aka kawo kayan ɗakin Aina'u a zuciyarta sai da taji kyashi dan shaiɗan sai da ya motsa mata hassada, amma tunawa da tayi daga binni aka kawosu sai taji sanyi ta kuma san yau da gobe dole kayan zasu tsufa tunda zama ne da ake fatan na din-din-din, tabbas Itama zata zama cikakkiyar baƙauyiyar Magami a nan gaba, zasu dawo dai-dai ne sai dai in bata fara haihuwa ba, wannan tunanin yasa ta shanye hassadarta ta kuma saki jiki aka cigaba da shirin tarban amarya da ita, su Hadiza suna ƙarfafa mata giuwa akan suna tare da ita matsawar bata sauya ba, duk da Aina'u 'yar uwarsu ce amma kuma ita bata yi musu wani abu da zasu guje mata ba, hakan da suka faɗa ya ƙara kwantar mata da hankali sosai, dan ta samu dannen ƙirji daga mutanen kwarai babu wacce ta nima zugata ko ta yi wani abu na shirka dan za a yi mata kishiya, gidansu na malamai ne dan haka wannan nason ilimin yayi aiki a cikin lamarinta, dan ko ɓangaren iyayenta haƙuri suka bata tare da nuna mata yadda suma suka yi zaman kishi a tsakaninsu mai tsafta, mahaifinta kuwa har aya da Hadisai ya jawo mata wanda ya sakata jin ko da Idris zai juya mata baya ba zata taɓa yin abunda zai cutar da amaryarsa ba In Sha Allah.
Yau Juma'a tun safiya ta tafi kisho bata dawo ba sai da ta dangana da gidan ƙanwarta Zainaba aka yi mata ƙunshin zamani kafin ta dawo gida ta cigaba da hidimarta. Washegari kuma da sassafe suka ɗaura tukunyan girki na bikin auren, Idris kuwa da abokansa biyu suka kama hanyar Kaduna dan suje ayi shagalin dasu a can, gobe In Allah ya kaimu kuma su tawo da amaryarsa.
*******
Safiyya.
Indo tana shiga ɗakin mama sai ta rufe da faɗa tana cewa.
Da girmanki ki riƙa abu sai kace wata sakarya, mun samu an samo ta da kyar zaki riƙa tsokanarta bayan kema kina gidanki kullun cikin kiran waye kike yi ya jikin Safiyya, daga yau karki sake tsokanarta magana akan Jabiru, kinji na faɗa miki.
Kiyi haƙuri mama In Sha Allah ba zan sake, Safiyya kema kiyi haƙuri wlh da wasa nake miki.
Cewar Indo jiki a sanyaye dan bata son ɓacin ran mama, sai Safiyya ta saki murmushi.
Ya wuce, kuma Allah yasa kin kawo min abu mai daɗi.
Kamar kin sani na zo muku da faten tsaki har da kashin tantakwashi a ciki, nasan kina so.
Cewar Indo tana murmushi itama, shikenan suka shirya sai suka baje anan falon mama suna shan faten suna hira kamar komai bai faru ba, mama itama tazo ta zauna dasu suka cigaba da zantawa. Da yamma wajen ƙarfe biyar Indo tayi sallama da iyayenta ta tafi, Safiyya ta yi mata rakiya tare da riƙe mata kular faten data kawo musu har titi ta samu abin hawa kafin ta dawo gida. Ko da ta shigo gidan ɗakin mama ta shiga tayi alwala ta fara Lazumi har aka kira sallar Magariba kafin ta miƙe ta gabatar, bayan ta idar sai ta cigaba da zama a gurin, ta karanta Azkar ɗin yamma tare da jan Salatin Annabi s.a.w ɗari, Istigafari ɗari, Laa'ilaha Illahu Wahdahu Laa Sharikala Lahul Mulku Walahul Hamdu Wahuwa Ala Kulli Shai'in Qadir shima ƙafa ɗari, sannan Subhanallahi Wabi Hamdihi ɗari, sai ta cigaba da Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil ƙafa ɗari huɗu da Hamsin. A haka lokacin sallar isha'i ya cim mata ta miƙe ta gabatar, bayan ta idar tayi Shafa'i, Wutiri Kuma ta bari sai in tayi sallar dare sai ta rufe da shi, tayi Addu'a kafin ta miƙe tana mai sauke ajiyar zuciya da jin wani nutsuwa yana shigarta, haƙiƙa duk in ta raya lokaci tsakanin Magrib da Isha'i cikin ambaton Allah tana samun kanta cikin yanayi mai daɗi sai duk wata damuwa taji yaye mata, tana tsaka da ninke dadduma taji yaro daga tsakar gida ya kwaɗa sallama yana cewa ana sallama da Safiyya, Hafsa dake tsakar gidan tana alwala tace cikin mamaki.
Safiyya aka ce maka.?
Eh ita aka ce na kira yana cikin wata baƙar mota.
To ka ce tana zuwa.
Cewar Hafsa, yaron ya ce to kafin ya wuce, Safiyya da mamaki ya cikata sai ta kasa ƙarasa ninke daddumar ta shiga tunanin waye yake nimanta, ko kuma ƙila Jabir ne ya zo mata, tana tsaka da tunanin Hafsa ta shigo tana dariya.
Anty kin yi baƙo yana waje, amma wlh nayi mamaki daga fitarki yau har kin yi sabon kamu.
Safiyya ta yarɓa mata daddumar alamar duka, Hafsa ta fice da sauri tana kyalkyala dariyar shaƙiyanci, da murmushi Safiyya ta rakata ta ƙarasa ninke daddumar ta aje, sai ta gyara zaman hijab ɗinta ta isa wajen madubi tana kallon fuskarta, fayau take ba komai sai ɗan sauran kwallin data saka tun safe, bata damu da ta gyara ba ta fice zuwa tsakar gida, a lokacin mama ta fito daga ɗakin mama ƙarama tana murmushi.
Yanzu nake shirin duba ki na tambaya ko ba zaki fita ba ne.?
Sallah na idar.
Safiyya ta faɗa tana murmushi, mama tace.
To sai kiyi maza kije ki dawo kafin Baffanmu ya dawo, sannan ki sanar da baƙon karya ƙara zuwa har sai yazo ya nima izini gurin Baffanku, kin san dai baya son kuna tsayawa da mutumin da bai gana da shi ba.
To mama.
Safiyya ta faɗa tana wuce, mama ta bita da kallon farin ciki, gabaɗaya sun bayar da fitar yau da ta yi ne ta haɗu da wani har ya biyo ta. Safiyya koda ta fita sai ta tsaya tana kallon baƙar motar dake fake daga ƙofar gidansu, ta kasa matsawa inda motar take, akan in mai son magana da ita ya masu ya fito dan tun asali basa hira a mota sannan sai da rana ko yamma suke zance, yanzu ma ta fito taga waye ne ta cirewa kanta shakkun ko Jabir ne. Shi kuma wanda ke cikin motar sai da ya ƙare mata kallo ganin ta rame sosai sai tsayinta ya fito ga haske data ƙara, ya sauke ajiyar zuciya yana addu'ar Allah ya bashi nasara akanta, sai ya buɗe motar ya zuro ƙafa, Safiyya ta kafe ƙofar motar da ido dan ganin waye.