Free chapter · Read without an account
Chapter 31
SULTANIM
Na
Mss Samher
Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher
Page31
A parking space suka rabu, Hisham ɗin yayi motarsa shima Faruq ya shiga tasa, ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya fiti daga company ɗin, idanuwansa na bisa titi yana wani tunanin na daban.
Nadrah bata wani jima da zuwa part ɗin Mami ba su Anty Mama sukazo da gaba ɗaya yaranta Hanan ce kawai babu, sai gidan ya cika da hayaniya don sun jima basu haɗu haka a gidan ba.
Duka a parlorn ƙasa suka yaɗa zanzo, sai Nadrah ta dinga jinta sakayau zaman kaɗaici sam bashi da dadi, hirar tasu ta ɗinga debe mata kewa duk da ba wani magana takeyi a cikinsu ba
“Ƙiri ƙiru Umar yaƙi kawomin ke, aure ya kama hanyar rabin shekara” Anty Mama tace da Nadrah wanda ke lallabewa Zaina kanta da manyan kalba.
“Kiyi haƙuri zamuzo in sha Allah.” Ta bata amsa tana murmushi.
“Ina nan ina zuba ido.”
Mahmud ba mutun bane bai baƙunta koda ya shiga parlorn ya baƙi hankalinshi kwace ya ƙarasa, yadda suke hira da Anty Mama kamar sun san juna tun farko.
Baisan me yake ɗaukar hankalinsa zuwa gidan ba, ya tabbatar dai zuwa lokacin wannan yayan nata da Hisham ya faɗa masa ya dawo, ya kanji ƙunci sosai a zuciyarsa idan ya tuna yadda yaga hannunsa cikin na juna ranan.
Wani sashen na zuciyarsa na tuhumarsa.. shin meye damuwarsa da hakan?yayanta ne fa…. yayin da wani sashen ke bashi amsar
“Matarka ce ai.”
Bayan tafiyar Mahmud, Mami da Anty mama kawai suka bari a parlorn, suma ciki suka shiga.
Lokaci zuwa lokaci kunnuwanta na sauraren hirarrakinsu da suke sanyata dariya a ƙasan ranta, ko da yaushe idan suka zauna zancen aure ne dai musamman Zaina da Hanifa, itakam bata taba tsintar kanta da jin wannan cikin zuciyarta ba, ko don bata rayu da mutane irin rayuwar da kowacce mace budurwa ke yi ba shi yasa batasani ba.
A natse yayi sallama ya shigo, daga tsayen da yake suka gaisa da Anty mama, tana dan dubansa yadda yayi wani kyau da cikar hankali kamala na sake bayyanar masa.
Dubansa ya bayar kan Mami dake kallonsa da ɗan mamakin dawowan nasa da wuri, dan kwana biyun nan yana daɗewa sosai a office.
“Anan zanci abinci ne ko chan? Ya faɗa bayan ya gama ƙare ma parlorn kallo baiga alamunta ba.
“Alhaji ƙarami gashi nan a dining bari na duba maka, Nadrah a nan ɓangaran ta wuni” cewar Abu dake ƙoƙarin fara serving nashi”
“Da kin rabu dashi muga ƙarshen mutun mai izza, kai Umar Allah ya shiryeka, kawai kace kana neman matarka wani salo ne kuma wannan?” Anty mama tayi maganr taba dariya.
“Kara dai yake mana, sunan da ake kira ai na zamani ne” Mami ta faɗa tana murmushi, dan ta fara lura da akwai chanji sosai a zamansu.
Bai kula kowa ba ya cigaba da takawa zuwa dinning ɗin.
Ya ɗauki tsawon lokaci zaune yana danna wayarsa bayan gama cin abinci, yayin da a fakaice yake satar kallon ta inda zata ɓullo amma shiru babu ita babu alamarta, gajiya yayi kawai ya miƙe bece dasu Mami komai ba ya fice don yana buƙatar watsa ruwa ya ɗan huta kafin magrib.
Fitowanshi sallah yayi daidai da fitowar Mahmud, sai a lokacin suka juna tun zuwanshi, cikin girmamawa Mahmud ya gaisheshi, Faruq ya amsa fuskarnan dai kamar ko yaushe, a haka suka taka zuwa masallaci tare.
Sai bayan sunyi sallan isha sannan driver yazo ɗaukar su, hannun Nadrah Anty Mama ta kama suka fita, curo wata leda tayi daga cikin jakarta
“Musamman nasa a kawomin na aika wa Hanan da nata wannan naki ne, Allah yasa kina amfani dasu….”
Wani kunya ce ta kamata matuƙa lokacin data kalla tambarin dake jikin ledan, ko wanda baisan na meye ba idan ya duba zai gane dan akwai bayani baro baro a jiki, a kunyace tasa hannu ta karba tana faɗin
“Nagode Anty mama”
“Bakomai,amma akwai wani a ciki miƙo kigani, ki shanyeshi yau zuwa gobe, don idan ya dade yana lalace.”
Ta amsa da “toh” ba zata iya ce da ita komai ba saboda kunya da kuma nauyinta da takeji.
“Ahh Anty mama harda wariya kuma, da gani abun dadi ne wallahi” maganar Zaina wacce basusan ta biyo bayansu ba ta katsesu.
“Matsa kanna kafceki, saiki jira sai anzo kanku marasa kunya”
“Allah nifa bansan na meye ba, na ɗauka wani abun dadin ne”
“Saiki sauke ai tunda kin ɗauka, kuma karki basu komai a ciki dan ba hankali suka cika ba”
Ta ƙare maganan tana duban Nadrah dake tsaye tsuru tsuru, kanta ta girgiza tana murmushi ita kuma Anty mama ta wuce mota dan yaran duk suna wajan ita suke jira.
Kasa komawa wajan Mami tayi sai tana ganin kamar tasan me Anty Mama ta bata, saita wuce ɓangaransu kawai tunda dare ya riga tayi.
A parlor ta zauna harta fara ciro kayan da Anty maman ta ɓata, sai kuma ta mayar iya wanda tace ta shanye yau zuwa gobe ta bude roban ta kai bakinta a hankali tana kuma ɓata fuska….
Sosai abun yayi mata dadi a baki tana sha garɗinsa yana ratsa harshenta, a hankali sai gashi ta gama dashi, harshe tasa tana lashe labbanta tana adduan Allah yasa suma sauran haka suke da daɗi.
Kwase komai tayi ta wuce dasu ɗakinta, kai tsaye ta shige banɗakibayan ta fito ta shirya cikin wasu pink and soft fabric, skirt ne irin mai buɗewa haka ta ƙasa, ya wuce gwiwanta amma bai kai ƙasa ba, haka ya baiwa fararan ƙafafunta da suka sha lalli damar fitowa, sai shirt off shoulder kafaɗunta dake ƙyalli duk a bayyane suke, hakama albarkatun ƙirjinta sun zauna daram daga ƙasan rigar, yadda ko yaya ta sunkuya za’a iya ganinsu.
Kayan sun mata kyau matuƙa, rashin nauyinsu yasa ta sanyasu ta kuma ji dadinsu sosai a jikinta.
Harta kwanta amma wani bakwan yanayi da takeji a jikinta shi ya hanata rintsa ido sam, sau biyu kenan tana shiga banɗaki tana chanza pant tare dayin tsarki daga dawowanta zuwa yanzu, gaɓoɓin jikinta ta kamesu waje guɗa yayin da abin da takeji yake ƙara ƙarfi, ko wace gaɓa a jikinta ya fara amsawa, kuka takeso tayi ko zata samu sauki amma ina hakan yaƙi samuwa….
A hankali ta mike ta fara yakawa zuwa farlorn ko ina na jikinta rawa yake…..
Ta isa wajan fridge ta ɗauko ruwa mai sanyi ta soma sha da tunanin samun sauƙin abin da takeji.
A natse ya buɗe ƙofar farlon ta shigo, idanunsa basu sauka a ko ina ba sai saman farin batan bayanta, cikin jarumta ya cigaba da takowa yayin da yaƙe ƙarewa shigan jikinta kallo.
Zuwa lokacin da ta ajiye roban ruwan ko gabanta bata iya gani, tafiya kawai takeyi amma idanunta sun gama rufewa, ƙafafuwanta sukayi wani irin sanyi daya tilasta mata zamewa ta tafi luuuuuu…….