Free chapter · Read without an account
7: Back to reality
Back to Reality
“Healing doesn’t mean the pain disappears. It simply means you learn to live with it”
Du’a ta turo ƙofar ɗakinsu a hankali, tana shiga, ta tsaya cak, the room was a complete mess, books a warwatse, uniforms na watse a kan gado, takalma a tsakiyar ɗaki, sweet wrappers kuma ba adadi a ƙasa
Amrah na zaune a bakin gado tana shan sweets, tana jefar da wrappers ɗin ba tare da damuwa ba
Du’a ta sauke ajiyar zuciya
“Amrah…” Ta kira cikin nutsuwa “Why are you scattering the room like this?”
Amrah ta ɗaga kai a hankali, ta kalleta da wani kallon raini
“And so?” Ta faɗa tana yamutsa fuska “Let me make one thing clear, Du’a…”
“I’ll do whatever I want” Ta miƙe tsaye “If the room annoys you…” Ta nuna ƙasan ɗakin “You can clean it”
Ta nufi ƙofa, sai kuma ta tsaya ta waiwayo “Oh… I’m warning you, don’t ever try talking to me again”
“Stay away from me Or…” Ta yi murmushin raini “You know exactly what will happen”
Ta buɗe ƙofar, a dai-dai lokacin Fatima ke shirin shiga, Amrah ta buga mata kafaɗa da gangan kafin ta wuce ba tare da ta ce komai ba
Fatima ta bita da kallo ta girgiza kai cikin takaici
Du’a ba ta ce uffan ba ta durƙusa, ta fara tattara books ɗin, ta ɗauki wrappers ɗin sweets, ta gyara bedsheets, a hankali ta maida ɗakin kamar yadda yake
Fatima ta ƙarasa kusa da ita “Dua…” Ta kira cikin sanyin murya “I heard everything”
Du’a ta ɗaga kai ta yi mata murmushi, duk da cewa murmushin ba ya kai zuci ba, Fatima ta zauna kusa da ita “Always remember this…”
“Whoever remains patient in difficult times will never lose their reward”
Du’a ta gyada kai “In shaa Allah thank you, Sister Fatima”
Fatima ta shafa kanta “You’re a strong girl Never forget that”
Ta miƙe tsaye “I only came to check on you” Du’a ta yi murmushi“Thank you for caring”
Fatima ta fita, Du’a ta tsaya ita kaɗai a ɗakin, ta ɗaga kai ta kalli hoton Mammy ɗinta da ke gefen gadonta
A hankali ta yi murmushi “I miss you…” Ta furta cikin ƙasa-ƙasa da murya
A parlour Amrah ta fito tana taɓe baki, Zahra ta ɗago kai daga wayarta
“What’s wrong, sweetheart?”
Amrah ta zauna kusa da ita “Mom you still haven’t bought my phone”
Zahra ta ɗan yi dariya “Oh.. so that’s why you’re upset?”
Amrah ta gyada kai “I’m the only one among my friends without the latest iPhone, I feel embarrassed yadda kika san bani da gata”
Zahra ta kama hannunta “Relax, to me na damun kanki Akan waya? You’ll get yours tonight”
Da jin haka, fuskar Amrah ta sake nan take “Dagaske Mom?”
“Of course za’a saya miki Yau din nan”
Amrah ta yi tsalle cikin farin ciki “I love you, Mom!” Ta juya da gudu zuwa ɗakinta tana waƙa, Zahra ta bita da murmushi
Da misalin ƙarfe 3:30 na yamma Du’a ta idar da Sallar La’asar ta shiga toilet ta yi wanka cikin sauri
A yau dai ba ta son sake yin latti bcos Mu’alliminsu ya riga ya gargaɗe su jiya, a gurguje take shiri, da ta fito tana saukowa stairs, sai ta ji sallama
“Assalamu Alaikum”
Fuskar Du’a nan take ta sake shi “Ayesha!” Ta ƙaraso da sauri ta rungume ƙawarta
Amrah ta ɗan ɗaga kai daga game ɗin da take yi ta harare Ayesha, sai ta ci gaba da game ɗinta
Zahra kuma ta yi wani ƙaramin murmushi “Munafukai kawai, duk wai saboda addini toh idan na hanata tafi sai muga ta tsiya”
Ayesha ta ji maganar amma kamar kullum basu da ta cewa kawai ta ƙarasa kusa da Zahra “Good afternoon, Ma”
Zahra ba ta amsa ba ta ci gaba da kallon TV, Ayesha ta saba saboda haka ba ta damu ba, ta juya ta kalli Du’a tana murmushi “Ready?”
Du’a ta gyada kai
“Let’s go”
Suna daf da fita sai muryar Zahra ta dakatar da su “Du’a”
Ta tsaya “Yes, Mummy?”
“Make me a cup of tea”
Du’a ta kalli Ayesha, Ayesha ta yi mata murmushin ƙarfafawa irin “It’s okay, I’ll wait”
Du’a ta nufi kitchen, ta haɗa tea ɗin da kanta nan take, da ta kawo…
Zahra ta ɗan ɗanɗana
“Hmm…” Ta ajiye cup ɗin “I need some snacks too”
Du’a ta ɗan kalli Fatima dake can tana sharan yamma, ta sauke idanunta Mummy ta san Fatima na nan, ta san Amrah ma na nan amma duk da haka…
Ita aka aika sbd zata Madarasa, ba tare da ta yi gardama ba ta koma kitchen
A tare da Fatima da Ayesha suka taimaka mata suka shirya cookies nan take, within minutes har ta gama
Da ta kai wa Zahra, Agogo ya nuna 4:30 p.m already, ta kalli Ayesha cikin damuwa “I’m sorry”
Ayesha ta kama hannunta “Come on, we’re already late mu tafi” Suka fita tare ba ɓata lokaci
Bayan sun bar gidan… Du’a da Ayesha suka dinga sauri wajen tafiya Islamiyyah
Ko da suka isa already darasi ya riga ya fara, Mu’allim ya ɗago ya kalle su “Again?” Ya tambaya cikin sanyin murya
Du’a ta sunkuyar da kanta
“Kayi hakuri Mu’allim”
Ayesha ma ta ce “Hakan ba zai sake faruwa ba, In shaa Allah”
Mu’allim ya yi shiru na ɗan lokaci, ya tuna cewa jiya ma sun yi latti
A ƙarshe ya nuna musu kujerunsu
“Zaku iya zuwa ku zauna”
“Thank you, Mu’allim”
Suka samu waje suka zauna cikin nutsuwa, a duk lokacin darasin, tunani ɗaya ne kawai ke yawo a zuciyar Du’a
“Da Mammy tana nan, da ba zan taɓa yin latti ba” Ta lumshe idanunta na ɗan lokaci
Sai ta ji muryar Mu’allim “Du’a”
Ta miƙe tsaye
“Yes, Mu’allim”
“Complete the verse” Cikin nutsuwa ta karanta ayar ba tare da kuskure ba
Mu’allim ya yi murmushi
“Masha Allah, Allah Kara ilimi mai Albarka”
“Ameen” Dalibai da dama suka amsa, Ayesha ta yi mata murmushi cikin alfahari
Washegari da safe… Maria da Farida suka zo gidan domin duba Du’a kamar yadda suka Saba time to time, yanzu kuma sun yi kwanaki biyu ba su samu damar zuwa ba saboda aiki
Tun kafin su iso ƙofar parlour Maria ta ce “I’ve been thinking about her”
Farida ta gyada kai “Me too, tun ba yau ba abun ke rai na amma komai sai Allah ya kaddara, sai dai hankali na baya kwanciya bcos we promised Aneesa, nd we must keep that promise”
Da suka shiga parlour, ba kowa sai Fatima ce, ta tarbe su
Bayan sun gama gaisawa ta ce
“Tana ɗaki” Fatima ta faɗa tana nuna musu hanyar ɗakin Du’a
Daga haka suka nufi sama,suka yi knocking a hankali
“Come in” Da suka shiga, Du’a na zaune a kan carpet Books ne a gabanta, tana solving Mathematics
Da ta gan su, fuskarta ta cika da farin ciki “Anti Maria! Anti Farida!” Ta miƙe da sauri ta rungume su
Maria ta sumbaci goshinta
“How are you, sweetheart?”
“I’m fine, Alhamdulillah”
Farida ta shafa kanta “Are they treating you well yanzu?”
Du’a ta yi shiru, ta tuna abubuwa da yawa, sai dai ba ta son kowa ya shiga matsala saboda ita, ta yi murmushi
“Alhamdulillah”
Maria da Farida suka kalli juna sun san akwai abin da take ɓoyewa, amma ba su matsa mata ba
Maria ta kama hannunta
“We know things may not be easy for you, saboda dole zaki ga banbance shiyasa hausawa kan ce uwa bangoje, amma don’t ever lose hope”
Farida ta ci gaba
“Allah never abandons those who trust Him, kiyi ta addua kamar yadda muma muke miki”
Du’a ta gyada kai
“In shaa Allah”
Maria ta miƙa mata wata ƙaramar pack na chocolate “For my brilliant girl”
Du’a ta yi dariya
“Thank you sooo much”
Sun ɗan zauna suna hira suna ba ta shawarwari, suna ƙarfafa mata guiwa, lokacin da suka tashi zasu ya fi
Du’a ta ji kamar an sauke wani nauyi daga zuciyarta “At least… someone still remembers Mammy”
Suna shirin fita sai suka haɗu da Zahra a corridor, ta tsaya ta kalle su daga sama har ƙasa ta ce
“Oh… So you people are here again?”
Maria ta yi murmushi cikin ladabi
“We only came to check on Du’a ne kin san yana da kyau hakan”
Zahra ta yamutsa fuska
“I think it’s time you stopped coming kun ji? Saboda she’s living with her family, we can take care of her”
Farida ta yi magana cikin ladabi
“Hajiya… we only came because we made a promise, amma bada wata manufa bace ki fahimce mu”
Zahra ta katse ta
“I don’t care about your promise, wannan gidan nawa ne nd I don’t want unnecessary visitors”
Shiru ya biyo baya, Maria ta sauke ajiyar zuciya “Alright Mun fahimta”
Suka juya suka fita, amma kafin su shiga mota, Maria ta kalli window ɗin ɗakin Du’a, ta ga tana tsaye tana kallonsu, ta ɗaga mata hannu tana murmushi
Du’a ta mayar da murmushin, duk da cewa idanunta cike suke da hawaye….
Yau a makaranta kafin break, Principal ya sanar da ɗalibai cewa za a manna Examination Timetable
Can kuwa sai gashi an manna timetable ɗin, Makarantar gaba ɗaya ta cika da hayaniya
Kowa na ta preparation na exams, amma ba wannan kaɗai ba, akwai wata sanarwa da ta fi jan hankali
Principal ya sake cewa,
“This year’s overall best graduating student…”
“…will receive a fully funded scholarship”
Hayaniya ta ƙaru, kowa ya fara kallon wanda yake ganin zai ci.
Malamai da yawa kuwa, sun san sunayen da ake sa ran za su fafata sai dau sanarwan zai sa wasu ma suyi karatu ko dan scholarship
Though wannan 3 musketeers wato Du’a, Ayesha and Haidar su ne manyan contenders
Da ala fita break, su ukun suka haɗu a ƙarƙashin wani babban mango tree Wanda akwai cooldown a wajen kuma ya zama kamar permanent spot nasu ne
Haidar ya buɗe notebook
“We have less than month, we need a serious reading timetable”
Ayesha ta gyada kai
“I agree, saboda yanzu na fara sanyi”
Du’a ta yi murmushi “I’m in”
Haidar ya fara rubutawa
“Morning revision, afternoon practice”
Sai ya ɗago ya kalle su
“And… I think we should also wake up in the middle of the night to study kamar ya fi shiga fah, ko ya kuka ce?”
Ayesha ta yi murmushi
“That’s actually a good idea na yarda!”
Du’a ta gyada kai
“In shaa Allah”
Suka tsara komai cikin nutsuwa, kafin break ya ƙare… sun riga sun fara revising Biology tare
Ba wanda ya lura da Amrah na tsaye daga nesa, tana kallonsu fuskarta babu annuri
Bayan sun koma gida, Amrah tsaye ta nufi Mommy ɗinta “Mom!”
Zahra ta ɗago kai
“What happened?”
Amrah ta zauna kusa da ita
“Our exam timetable is out sannan akwai scholarship for the best student”
Ta taɓe baki “Dua is taking it too seriously, kuma gaskiya bana son tayi kokari wannan karan ma, saboda zai iya zama mata greatest achievement”
Zahra ta yi murmushin da ya sa Amrah ta nutsu, ta kamo hannunta
“Calm down I have a plan” Ta ɗan matsa kusa da ita “I’ll make sure she doesn’t get enough time to study ko kadan ba zan barta ba”
Amrah ta yi dariya
“I knew I could count on you, Mom”
Zahra ta jingina da kujera, ta yi murmushin nasara “Let’s see, zata sha mamaki”