Free chapter · Read without an account

013

by Kansa'u Bello · MEERAH

*MEERAH*

      *013*


   Doctor ta cire gilashin dake sanye a fuskarta ta ajiye a saman table, sannan ta fuskance sa da kyau tace.

   "Tana fama da ciwon mara ne wanda wasu matan ke fama da shi yayin fara al'ada (Menstruation), yanzu haka mun yi mata duk abinda ya dace. Zamu iya sallamar ku zuwa gobe in sha Allah, don ma nata yazo da tsanani ne da kuma firgici da ta shiga, shi yasa ta suma."

   "Yanzu Doctor babu wata matsala zata ji sauƙi?." Nawaz ya tambaya.

   "In sha Allah zata samu lafiya, mata da yawa suna fama da irin wannan matsalar. Mun yi mata allurar bacci ne saboda ihun kukan da ta rinƙa yi bayan fitar ka" bayani sosai Doctor ta ƙara yi masa yanda zai fahimta.

   Godiya sosai ya yi mata sannan ta wuce gida bayan ta sanar masa Akwai Nurse ɗin da zata kula da ita cikin dare.

   Ɗakin da take kwance ya koma, a hankali ya murɗa ƙofar ya shiga tamkar mai tsoron kar ya tashe ta. Zama ya yi kusa da ita ya zuba wa kyakykyawar fuskarta ma'abociyar kwarjini idanu, kallonta yake yi cike da tausaya wa. Wani irin abu mai girman gaske yake ji game da ita, tun lokacin da ya ɗora ido a kan fuskarta.

  Agogon hannunsa ya kalla, ƙarfe 10 na dare. Kamata ya yi ace ya tafi gida saboda ya san Mama na can tana zuba idon ganinsa yaje ya ci abinci. Don kullum bayan isha yake komawa ya ci abincin dare, idan yaso ya sake fita. In baya son fitar kuma ya zauna cikin ƴa'uwansa suyi hira, ko su kunna kallo idan an kawo wuta.

   Kiran JB da ya shigo masa ne ya dawo da shi daga tunanin daya tafi.

   "Nawaz ka koma gida ne? Yaya jikin yarinyar?." Ya jera masa tambayoyi. Ajiyar zuciya ya sauke cikin sanyin muryarsa da yau ta ƙara sanyi sosai yace.

   "Har yanzu ina asibiti JB, yarinyar kuma har yanzu bacci take yi. Ban samu na amshi lambar da zan kira ahalinta na sanar da su halin da take ciki ba."

   "Okay to yanzu miye abin yi? Ba dai a asibitin zaka kwana ba?." JB ya kuma tambayarsa.

    "No Doctor ɗin ta haɗa ni da Nurse ɗin da zata kula da ita kafin safiya, kawai dai ji nake bana son in tafi in barta ita kaɗai ne JB." Nawaz ya faɗi gaskiyar abinda yake ji a cikin zuciyarsa.

   Ajiyar zuciya JB ya sauke sannan yace.

   "Ai kuwa ba zai yiwu ka kwana da ita ba, tun da ba muharramarka bace. Sannan kuma su Mama na can suna jiran ka ka sani." 

   "Kaga ka jira ni gani nan zan zo asibitin na ɗauke ka mu wuce. In yaso da safe sai mu dawo, kaga lokacin ta farka sai a kira wo dangin nata." Cewar JB yana miƙewa ya fice daga Studio ɗinsu da ya koma ya mayar da kayan da suka je da su wurin birthday partyn da aka gayyace su.

   "Okay, amma please ka biya ka sayo mata abinci da fruits ko zata farka cikin dare." Cewar Nawaz.

   "Okay ba matsala." JB ya bashi amsa daga nan suka kashe wayar.

***** Ba'a fi 30 minutes ba JB ya ƙara so asibitin da Nawaz ya kai Meerah, wanda wani ƙaramin private hospital ne ya kai ta dai-dai karfinsa.

   Nurse ɗin da ya bawa amanar kula da ita ya danƙawa kayan da JB ya kawo.

  "Please Sister, ki kula da ita sosai, sannan idan ta farka komai dare ki sanar da ni, ga contact ɗina." Nawaz ya faɗa yana miƙa mata lambar wayarsa da ya rubuta a ƙaramar paper.

   "In sha Allah." Nurse ɗin ta bashi amsa tana karɓar guntuwar paper da yake bata. Godiya ya yi mata sosai ya ciro kuɗi ya mata alkairi sannan suka wuce shida JB.


___________★


   A can H. A. M. G Mansion kuwa ƙarfe 8 na safiya dai-dai Honorable Abbas Mamman Gwangwazo tare da Yayansa Alhaji Bashir Mamman Gwangwazo mamallakin Companies ɗin B. M. G MOTORS. Tare da zaratan yaransu, Ajmal Bashir Mamman Gwangwazo, da kuma Sultan Abbas Mamman Gwangwazo suka isa babbar Police Head Quarter don jin halin da ake ciki game da case ɗin Meerah da aka fara bicikawa tun a daren jiya da abin ya faru.

   A can gida kuwa Momy ce cikin tsananin damuwa da jiran tsammani, bata taɓa fuskantar tashin hankali irin wannan ba tun da take a rayuwa. Jawad da Aryan ne ke tare da ita suna bata kulawa.

  Ƙarfe 9 Mamy Safiya ta iso ita da ɗanta Halifa da ya kawo ta, sai ƙaramar ƴarta Huda wacce sa'ar Meerah ce.

   "Sannu da zuwa Yaya." Momy ta faɗa tana goge fuskarta.

   "Yauwa Laylah ai kece da sannu." Mamy Safiya ta faɗa tana zama kusa da Momy. Gaishe ta momy tayi ta amsa mata da kulawa sannan tace.

   "Ya muka ji da tashin hankalin daya same mu kuma?." 

  "Alhamdulillah." Momy ta bata amsa.

   "Wai ma garin yaya hakan ta faru ne?." Mamy Safiya ta tambaya, labarin yanda abin ya faru Momy ta bata cikin damuwa.

   "To Allah ya bayyana ta cikin aminci." Ta faɗa tana yin tagumi, nocking ƙofa aka yi, Momy ta umarci Bintu da taje ta buɗe. Ƴan gidan su Zeezee ne suka shigo, ita da Mom ɗinta da Yaya Abdul wanda yake cikin damuwa sosai a kan rashin sanin halin da Meerah take ciki.

   Gaisawa suka yi a mutunce, suka jajintawa juna abinda ya faru. Zeezee wacce idanunta suka yi ja alamar ta sha kuka sosai ta matsa kusa da Momy tana cewa.

   "Don Allah kiyi haƙuri Momy, Allah ban san cewa zata fito ita kaɗai ba, da ba zan barta ba. Kawai cewa nayi taje ɗakina ta kwanta kafin na gama sallamar friends ɗinmu, ashe ita tafiya tayi kuma aka samu wannan matsalar. Kuma bata da lafiya Momy, Allah yasa kar su cutar min da Bestie!." Zeezee ta ƙare maganar tana ɗora kanta saman ciyar Momy ta ƙara fashewa da wani kukan.

   Momy ta share hawayen da suka sauko mata ta saka hannu ta ɗago Zeezee tace.

   "Ba laifinki bane daughter kin ji ko, ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu abinda zai same ta. Su Dad ɗinku suna can suna bincika wa, zasu dawo da ita in sha Allah."

  "Allah yasa Momy." Zeezee ta faɗa tana share hawaye.


********

     A can Police Head quarter kuwa Su Dady ne zaune a ofishin Commissioner wanda ya kasance aminin Dady ɗin, bayan gaisuwa da ta gudana a tsakaninsu Dady ya tambaye shi halin da ake ciki game da binciken inda ƴarsa take.

   "Ka kwantar da hankalinka Honorable, kamar yanda na sanar da kai tun jiya jami'an mu suka fara gudanar da bincike. Ina zuwa." Commissioner ya faɗa yana ɗaukar kan wayar dake gabansa ya saka kira.

   "Meet me in my office." Ya faɗa lokacin da aka ɗaga kiran. Mintuna biyar aka yi nocking ya bada izinin shigowa, jami'in ɗan sanda ne ya shigo sanye cikin kakinsa. Yana zuwa ya sara wa shugaban nasa yana ƙamewa.

   "Inspector Alim, me aka samu game da case ɗin ɓatan yarinyar Honorable Abbas Mamman Gwangwazo?." Commissioner ya tambaya, sara masa ya ƙara yi sannan yace.

  "Muna kan bincika wa ne Sir, in sha Allah duk inda yarinyar ta shiga zamu dawo  da ita cikin aminci." Inspector Alim ya faɗa.

   "To me kuke jira kuyi hakan mana!." Ajmal ya faɗa cikin zafin zuciya.

   "Kwantar da hankali Son." Dady ya faɗa yana dafa kafaɗarsa.

   Gyaran murya Commissioner ya yi yace.

   "Ka kwantar da hankalinka Son, suna kan aikinsu ne kuma na yarda da aikin Inspector Alim, shi yasa na danƙa case ɗin a hannunsa." Yana kammala faɗa ya juyawa ya kalli Inspector Alim ya bashi umarnin ci gaba da bayani. 

   "Ranka ya daɗe tun lokacin da aka bamu umarni muka je unguwar da abin ya faru muka fara gudanar da bincike, mun fara da securities ɗin dake tsaron unguwar gaba ɗaya sun tabbatar mana cewa basu ga wani abin zargi ba a jiya gaba ɗaya." 

   "Yanzu wani mataki ake kai?." Commissioner ya sake  tambayar sa.

  "Eh ranka ya daɗe mun buƙaci ɗaukar duka CCTV pottage na layin gaba ɗaya, har yanzu abinda muke jira kenan kafin mu shiga mataki na gaba." 

   "Okay, please ayi duk abinda ya kamata ayi ina buƙatar a nemo min yarinyar nan a cikin awanni ashirin da huɗu (24 hours)." Cewar Commissioner.

   "Oky Sir." Inspector Jibrin Yusuf ya faɗa yana ƙamewa.

   Dunƙule hannu Ajmal ya yi ya kai wa table ɗin dake gabansa duka, jin ana ambatar 24 hours. Ji yake da zai ga wanda ya yi gangancin taɓa masa ƙanwa babu abinda zai hana ya yi masa dukan mutuwa. Sultan dake kusa da shi ne ya riƙe hannun nasa yana kwantar masa da hankali.

  Nocking aka yi aka nemi izinin shigowa, wani jami'ine ya shigo ya ƙame ya sara wa manyan sa sannan yace.

  "Sir ga CCTV pottage ɗin an samu."

   "Good." Inspector Alim ya faɗa yana karɓsr USB ɗin yayi connecting da na'urar dake saman table ɗin gabansa, dai-dai lokacin da aka sanar musu Meerah ta fito daga gidan su Zeezee suka fara dubawa.

  Gaba ɗaya kowa ido ya zuba wa allon Computer suna kallon lokacin da ta fito tana tafiya da ƙyar tana runtse ido, haɗi da dafe ƙasan mararta tana yatsine fuska. Gaba ɗayansu ji suke kamar su miƙa hannu su cirota daga cikin computer.

   Ajmal kuwa rintse ido kawai ya yi yana cije baki, lokacin data durƙushe ta fashe da kuka kuwa idanunsa tamkar za su yi aman wuta tsabar kaɗewar da suka yi. Ba shi kaɗai yake a cikin wannan yanayin ba, Sultan, Dady da Abby ma duk suna cikin damuwa sosai.

   Lokacin da motar matasan nan ta tsaya a kusa da ita, da   yanda suka riƙa binta tana ƙoƙarin gudu kuwa ba zaka so kallon ƙwayar idanun Ajmal ba, domin kuwa shi ɗin mutum ne mai tsananin fishi da zafin zuciya. 

  Koda aka zo inda Nazy ya ɗauke ta kuwa ya saka cikin motar, kasa danne fishinsa ya yi sai da ya ɗauki glass Cup ɗin dake ajiye saman table ya maka shi da ƙasa ya tarwatse. Cikin tsananin fishi ya fara magana.

   "Sai na tabbatar da cewa kun yi nadamar rayuwarku a duniya, tunda har kuka taɓa ta. Sai na wulaƙanta rayuwarku na ɗai-ɗaita ko da Uban waye ya tsaya muku kuwa!." Ya ƙare maganar cikin matsananciyar tsawa da ƙaraji. 

   Shima Yaya Sultan duk haƙurinsa a wannan karon ransa ya bala'i n ɓaci, don basa haɗa mutuncin ƙanwarsu da komai a rayuwa. Suna tsananin kula da ita, suna kiyaye duk abinda zai taɓa mutuncinta tun tana ƴar ƙankanuwarta.

   "Dole ne su amshi hukuncin gangancin da suka aikata kam!." Ya faɗa shima cikin fushi. Dady kuwa kasa cewa komai ya yi tsabar ɓacin rain da yake ciki.

  "Sir da buƙatar ku kalli wannan." Inspector Alim ya faɗa yana juyo musu da fuskar Computer. Duk juya wa suka yi suka kalli fuskar computer.

    Dai-dai lokacin da Nazzy ne ya saka Meerah a cikin mota yana ƙoƙarin rufe ta , sai ga wani matashi ya riƙe murfin, a dai-dai lokacin kuma kira ya shigo wayar Sultan.

  Ƙin ɗauka Ya yi ganin baƙuwar Number ce ya mayar da hankalinsa a kallon yanda Nawaz yayi wa yaran duka ya fito da Meerah daga cikin motar, su kuma suka tashi da ƙyar suka shige motar suka gudu.

  Wani kiran ne ya sake shigowa don haka ya ɗauka, don jin ko wanene.

  "Meerah! Kece? Kina ina ne?." Ya furta maganar da ta saka duk aka zubo masa ido.......


   (Barkanmu da dare, zan yi amfani da wannan damar na sanar da masoyan Labarin Meerah ranakun da zaku riƙa samun update. In sha Allah zan riƙa update Monday to Friday, sai muyi hutun weekend. Sai dai idan naga kuna bada haɗin kai sosai zaku iya samun 2 pages a rana, ko kuma update sau biyu, safe da Yamma, na gode.)

  Oum Fatima 
    ***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.