Free chapter · Read without an account

After Everything

by ZAHRA B MRS · Nuwayrah the foreigner’s passion

Mimi kiyi hakuri Kinji ki  daina zubar da hawayenki masu tsada you’re our little princess,kuma Zan dauki mataki Akan jawad I promise you ko ba yanzu ba .

Yaya yanzu shikenan haka Zan cigaba da rayuwa ,duk yadda nake kokarin kiyaye bacin ran jawad nake kokarin Kara masa girma da daraja a idon ku  shine zai min haka ?yaya this is the same Jamila dayake yawan fadan min ko a kafa aka sa masa bazai aure ta ba ?Yaushe suka fara soyayyah ?the last time a check ya ma yi blocking dinta ,Uhmm mimi kadan daga cikin Halin maza kenan ,Gara da hakan ya faru ki godewa Allah mimi am telling you ,yanzu yaya me zancewa friends dina ?yaya har anco sunyi ,ya zaayi da Kayan da aka siya min? nuwayrah ta fada muryarta a dishe Sabida kuka ,kar ki damu da wanan mimi kayan kitchen kuma store din gidan yaya nabil zaa Kai su idan Allah ya kawo miki wani Mijin Kinga Shikenan ,ba auren da zanyi na hakura da auren Zan cigaba da karatu na Ina Neman kudina inshallah 

Kiran sallar laasar yasa Sadîq fita zuwa masallaci ,itama laasar din tayi ,Bayan ta idar ta rasa wace Addua ma zatayi ,Karan bude kofa ne ya dawo da ita ga tunanin data shiga ,mamace rike da tray ta jero abinci harda ruwa ,taso nan mimi zo kici  abinci Kinga yau da kaina na dafa miki favorite dinki danwake ,mama tafa tana bude flask din ,Kinga  har cabbage da albasa na yanka miki a kai ,a Kwai na dafa Kamar yadda kike so ,on normal basis nuwayrah tsalle zatayi ta rungume mama ,amma halin da take ciki sam danwake be birge ta ba  

Sallamar yaya nabil suka ji ,ya gaishe da mama fuskar sa ba walwala ,yana office  abba ya Kira shi ya bashi labari akin da be karasa ba kenan ya biyo gidan ,kiyi hakuri mimi is for the best Allah ya Baki Wanda yafishi, a hankali nuwayrah ta Gyada masa Kai. Sai cusa danwaken take badan yana mata dadi ba .ganin yadda take cin abinci mama ta kalle ta cikin Farin ciki ,Yauwa auta ko Kefa maza cinye ga kunun aya nan mai sanyi ki kora dashi 

Kiran   jawad yayi nabil yayi tare da sawa a speaker 

Yana ɗagawa, Jawad ya fara rawar baki Yaya Nabil Nasan by now labari ya same ka amma tsaya ka ji dalilina na yin hakan….

No need, ba sai na ji dalilinka ba, Yaya Nabil ya katse shi cikin sanyi  da wata irin murya mai cike da kwarjini . Ba mu buƙatar wani bayani daga gare ka. Account Dinka zaka tura min Zan dawo maka kudin da kuka kawo 

Bai jira amsar Jawad ba ya yanke kiran,Yauwa nabil maza maza mayar masa da kudinsa ,cewar mama cikin fusata ko sunan jawad bata so taji an Kira ,Ka hada masa da kudin tsabar da ya 

taba kawo mata zuwan shi umrah ,iya kyautar da Nasan ya taba mata kenan cewar mama tana Jan tsaki ,Banda wanan mama ,mimi ce ta siyo tsabar da kanta ta kawo a matsayin shine ,muryar sadiq ta katse su ,da mamaki nuwayrah ta dago ta kalli Sadiq ,ya akayi ya sani ?Kamar yasan tambayar dake ranta ya karasawa shigowa dakin ,na tsinta receipt din siyyyar da kikayi a Hajja camp tun lokacin shiru kawai nayi miki ,wata irin kunya ce ta lullube mimi ,tafa hannu mama ta shiga yi ,ikon Allah mimi haka kika zama ? Wani Kallo ta watsa mata ta fice daga dakin 

Bayan yayyenta nata Sun Kara mata nasiha nabil ya Kama hanyar gida ,Sadîq ya shiga dakinsa ,kiran rayyan ne ya shigo,

Am sorry mimi am very sorry jawad be kyauta mana ba ,yanzu nake ganin status dinsa he is a bastard wallahi ,Uhmm ba komai ray it’s part of life Kunyi kokarin nuna min halin shi na kasa ganewa ,it’s fine ,ta fada a sanyaye ,haka rayyan ya cigaba da kwantar mata da hankali har aka Kira sallar magrib short message ta turawa salima gambo ,Salam salima pls pass this information zuwa ga sauran Kawayen mu ,an daga bikina till further notice for personal issue,am very sorry for the inconvenience Nagode .

tana shirn fita da WhatsApp message ta gani daga jawad

Na rabu da ƙe ne saboda kin fi ƙarfina. Tunda kika fara samun kuɗi da  ɗaukaka kike min magana ba respect. Duk abin da na siyo na lefe, sai kice bai miki ba. So kinga gara Jamila tunda ita ba ta da son abun duniya. Ƙe kuma ki je ki aura ɗaukakar taki.

Nuwayrah na karanta saƙon, tayi  murmushin takaici ,a taƙaice ta rubuta amsa guda ɗaya Ok.👍 

 screenshots tayi ta  tura wa Rayyan. Nan take Rayyan ya amsa I told you! Ba komai ba ne illa  bakin cikin ɗaukakarki yake yi. Bai cika namiji ba tunda bazai  iya tsayawa kusa da mace mai nasara ba,asarar sa ne .

Mubeen ma ya kira  Nuwayrah a waya . Muryarsa cike da ƙwarin gwiwa  Mimi, ki gode wa Allah da ya toni asirinsa tun yanzu. Kin fi ƙarfin auren mutumin da yake buƙatar ki rushe girmanki don kawai ya ji shi namiji ne. 

 dangin Mama da na Abba kuwa, abun nema ya samu sai gulma ce gulmace ake kowa da abinda yake fada ,Wanda ba wanda ya isa Tara mama da maganar dan Sun San halin ta ,bata daukar wargi ,Anty Fido har gida ta zo ta dauki mimi suka tafi gidanta ,sai lallaba ta ake Kamar Kwai ,ita yadda taga yan uwansa kowa is there for her kawai taji wani Farin ciki Alhamduillah she is loved ,Rayyan kuwa bawan Allah ba abinda zata ce masa sai Addua ,ya cika aboki nagari .

Watanni biyu sun wuce , auren Jawad ya zama tsohon labari, amma sauyin da ya bari a tattare da Nuwayrah ba a boye yake ba 

Ta rage walwala sosai Ta koma  shiru-shiru, Ta maida hankalinta gaba ɗaya kan keken ɗinkinta 

Sallamar Rayyan taji a bayanta dan fitowar ta kenan tana shanya undies dinta ,Yau kuma kaine da yamman nan ray ?ta fada cike da mamakin ganinsa dan da safe ma sunyi waya be fada mata zai zo ,

"Big Head! Big news na kawo miki muje ciki 

Tare suka karasa falon Wanda yake tsit mama na ciki tana hutawa Yau off take .

Nuwayrah... kin tuna samples ɗinki da na amsa months ago?" Rayyan ya tambaye ta yana gyara zamansa.

Nuwayrah ta ɗan tsaya ta tunani sannan ta gyaɗa kanta a hankali.  Eh, na tuna Ray. 

Rayyan ya sanya hannu a aljihun rigarsa ya fito da wata  envelope mai tambarin 

 Aura & Heritage Couture London

Ya miƙa mata ita yana kallon cikin idonta.

Alhamdulillah Mimi Offer ce ta fito miki... Za ki yi aikin contract na shekara ɗaya (1-year contract)  A ,Aura & Heritage Couture da ke birnin London, United Kingdom

Nuwayrah ta tsaya cak,. Envelope ɗin ta bi da kallo, sannan ta kalli Rayyan cikin rashin yarda da abin da kunnuwanta suka ji...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.