Free chapter · Read without an account

Chapter 15

by Amina Abubakar Yandoma · RIKICIN DUNIYA

CHAPTER 15
..."Yaya mun shiga uku kamar fa bata yin motsi." Suwaiba ta fada a rikice.
Da kyar suka shigar da ita daki ruwa suka hau shafa mata suna jero mata sannu.
bude ido sakamakon zazzaɓi da ciwon kan da ke dawainiya da ita.
"Suwaiba! Tunda ta farka ki lallabata kuje a dora girkin rana"
Kande ta fada.
"Gaskiya ko da rarrafe ne idan tana iyawa ta fita su hau aikin nan muma duk da haka muka sabawa bakar wahalar nan, sakin jiki za kiyi ki maida himma."
Cewar Jummai.
"Amma yaya mu muje muyi mana, idan Malam ya dawo sai mu fada masa ita bata lafiya"
Dafe ƙirji Jummai tayi tare da fiddo ido.
"Ni kaza! Ban manta da abinda ya faru da Ni ba a shekarun baya lokacin da irin haka ta faru dake an kawoki amarya. Na ce bari inyi miki aikinki ke ki huta, a karshe sai da nayi kwana biyu ba ci ba sha sannan ba bakin magana. Don haka idan kin ganni lahira kaini akai"
Tana kaiwa nan ta fice da sauri. Take mata baya Kande ta yi. 
Sa'ade da Sharifa dake tsaye bakin kofar Nadiya tuntsurewa suka yi da dariya.
"Kinga wadda baba ya samo?"
"Sharifa na gani mana. Kyakykyawa da ita. Amma dai ba ƙarko"
Sake bushewa da dariya suka yi suna tafa hannu.
Suwaiba dake rike da Nadiya a fusace ta lalle su.
"Me kuke yi a nan?"
Tsoki Sa'ade taja. "Mutum da gidan ubanshi sai a rika yi masa wata tambaya maras ma'ana wai me muke yi? To abin da kuke yi shi muke yi. Kuma wallahi mu mun fara jin yunwa a san yadda za a yi da mu"
"Ke kika ga zaki iya tsayawa kuna maida magana da wannan munafukar. Nifa dama can ba sonta nake yi ba. Har kara wannan amaryar da ganinta ita mai wayo ce"
Sharifa ce ta amshe zancen. "Ni fa ban hango kayan Gara ba a cikin ɗakinta ko ba a kawota da ita ba?"
"Ke kam Sharifa ai Allah ne ya kamata, nema ta zo yi shi ma Baba ya nwmawa kansa mafita"
Ɓaɓɓakewa da dariya suka yi.
"Ku dai baku da kunya sannan abin da kuka yi za a yi maku saboda nan da ɗan lokaci gidan wani zaku je. Sannan ku sani kome kuka yi kanku kuka yi mawa."
Matsawa suka yi daga wurin suna mata dariya.
Guntun hawayen fuskarta ya share dana mai jingina Nadiya jikin gado.
"Bari In dauko miki wani magani a dakina. Idan kika sha sai mu je In kama miki kiyi aikin can. Saboda muddun ba kiyi aikin nan ba kasancewar ki amarya bazai hana malam ya gana miki azaba ba”
Tana kaiwa nan ta fita ta dauko mata. Ruwa ta bata tasha cikin kankanin lokaci taji zazzabin da kan duk run lafa mata.
Da taimakon Suwaiba ta kama mata suka fito, tankaden gari ta hata ita kuma ta cika tukunya da ruwa ta kunna wuta..

Katsina State
A hankali ta fara kokarin buɗe idanunta. Da sauri ta mayar da su ta rufe tana cije lebenta na kasa sakamakon radadin azabar daya kawo mata ziyara.
"Sannu!"
Ta ji Muryar mace ta furta. A dan rikice ta kalli gefe ta. Zainab ce zaune ta haɗa uban tagumi. "Me ya faru dani, ina Kasim ɗin?"
"Yi a hankali. Kina bukatar taimako ki jingine batun Kasim saboda ba zaki sake ganinsa ba sai zuwa dare.
"To me ye ya faru dani, Kasim ya ga halin da nake ciki amma ya fita ya barni?"
"Hmm! Amarya ba za ki gane ba. Na fahimci kamar ba ki san me ya faru ba. Kinsha abinda ya kawo miki ne?"
"Nasha mana"
Wasila ta fada murya na kyarma.
"Shi kenan. Abin da ya faru dana baya kema shi ne zai faru dake, naso a ce daga kaina wannan mummunar ƙaddarar ta gama fadawa kowa. Sai dai kash! Ga dukkan alamu hakan bazai faru ba"
Miƙewa zaune Wasila tayi mai fiddo ido waje.
"Me ya faru? Wace ƙaddara ce kike magana a kai?"
"Zan baki labari amma ki shiga daga ciki ki watsa ruwa idan kika fito, kika ci abinci sai muyi magana"
Zainab ta taimaka ma Wasila tayi wanka ta shirya. Duk da bata marmari komai haka ta matsa mata sai da ta ci wani abu.
Gaba daya hankalin Wasila ya na kan Zainab, babban burinta shi ne ta ji abinda Zainab ke son fada mata.
Jikinta babu kwari amma ba ta shi take ba hankalinta ya kasa kwanciya game da Kasim. So take ta ji wannan sirri.
"Ni bakuwa ce bansan kowa ba sai ke. Don Allah ki fada muni abinda ke faruwa. Tun daren jiya bayan shigowar Kasim da wani mutum wanda na fahimci mahaifinsa ne na kasa gane batutuwan da suke fada. Fita da naga Kasim na kokarin yi ta barni da mutumin ya saka na yunkura zanbi bayansa. Daga nan bansan me ke faruwa ba sai yanzu dana bude ido"
Matsanancin kuka Zainab ta fashe da shi.
Nan hankalin Wasila ya sake tashi ta hau rarrashi ta tana tambayarta.
"Ba da Kasim kika kwana ba, da mahaifinsa ne. Abinda ya faru da yan baya kema shi ne zai faru da ke"
Dafe kirji Wasila tayi ta na mai ja da baya.
"Ban gane da mahaifin Kasim na kwana ba. Kina hauka ne kina nufin mahaifinsa ne ya rabani da mutumcina ba Kasim ba. Kada ki ruɗa mini ƙwaƙwalwa kada ki rikita mini tunani"
Hawayen fuskarta ta share ta kamo hannun Wasila ta zaunar da ita gefenta.
"Ki kwantar da hankalinki in yi miki bayani. Irin wannan tashin hankalin da kika shiga nima na shiga fiye da haka lokacin da na samu labarin sirikina ne ya kwana da ni"
A yanzu kam rushewa da kuka Wasila ta yi "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Wannan wace irin masifa da bala'i ne na fado ciki. Ko a zamanin jahiliyyah ba a yi wannan ƙazantar ba. Dama  ba Kasim ya aureni ba mahaifinsa ya auro mawa?"
"Kasim shi ne ainahin mijinki. Mahaifinsa kuma yayi abinda ya saba yi ne da duk matar da Kasim ya aura."
Cak kukan Wasila ya tsaya. "Kina nufin Kasim ya auri mata da dama kafin Ni, sannan haka aka yima kowacensu?"
"Kwarai kuwa. Bayan wannan ma akwai sauran masifu da tashin hankali da zaki ci karo da su. Wanda sai kin kwammace mutuwa kika yi akan rayuwa...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.