Free chapter 路 Read without an account
10
馃挄NUFIN ALLAH 馃挄
By
Anisa Muhammad yahaya
Page 馃敓
Dan murmushi ne ya kubce masa a zuciya Amman Bai fito kan fuskar sa ba, dan azahiri ranshi a ha蓷e yake kallon ta.
Ita fa harga Allah bata ji dadin zuwan shi ba, dan tasan harya 茩are hutun shi ya koma a gidan zai zauna, im badai zai je ziyara ba, Amman yana gama ziyarar dangin zai dawo ya tare a gidan itakam gaba 蓷aya hanata sakat yake, dan tsoron shi take ji kamar ace tak ta zura aguje in Yana guri.
Ita ta fara janye idon ta dan shi Bama shi da niyyar hakan, tayi saurin jan hannun jalila sukayi 蓷aki, duk a takure take jin ta a gurin, Saboda yanda idon shi ke yawo a kanta,tarasa wannan kallon kurillan dayake mata yau,
"se kace wani wanda yaga dodo, yana wani bin mutum da ido" yanda take cuno bakin tana 茩un茩uni ne yasa ya Kara kureta da ido, dan yasan dashi take,
"Man kallon yaisa haka, ammi na ganin ka"
Shifa ya manta mafa ammi na gurin infact ba Wanda yake gani a parlourn se ita, dabadan yanzu da Ahmad yamai magana ba shi yasa ya 蓷an ankara,
Ha蓷e rai yayi ya 蓷auke idon shi daga bin bayanta da kallo, a hankali ya蓷an saci kallon Ammi, karaf ya ga idonta akan shi,
kawai murmushi tayi tana girgiza kai ta tashi ta nufi 蓷akinta,
Kai ya蓷an susa ya tashi Ahmad na biye dashi suka nufi sashin maza,
Dan gidan plat ne babba me 蓷auke da part uku, da part din ammi, sai part din maza ko ba茩i maza idan sun zo, sai part din daddy, Dan in sun zo 茩asar anan suke sauka.
"Ke wai me kika ma ya Umar yake binki dawani deadly look?"
"Ni ina nasani, kodai sun ga sanda muka shigo ciki da gudun nan ne ko maybe yaji ammi na fa蓷a, kisan shi da mugunta 5 and 6 ne, idon shi idon mugunta, ba abinda yake so kamar punishing mutum"
"Hmmm kedai bari, da kyar na iya 蓷agowa na kalle shi na gaida shi fa"
"Uhmm ni bar zancen dan Allah yasan banji da蓷in zuwan shi ba, gidan Ammah zan koma duk sanda ya gama hutun ya tafi sai in dawo, ke ki zauna da ammi nidai na koma gurin Ammah ta"
"Tabb ai wallahi baki isa ba,tare zamu tafi, dan bazan zauna ni kadai ba, se su batul su zo"
"Kin san halin su ai sedai kullum yayi punishing na su wallahi dan kiriniyar yaran nan ba zasu dena ba"
"Nidai bacci Nike ji"
Ta gyara kwanciyar ta taja bargo tana addu'a.
Anisa Kam wayar ta taja ta kunna Film dinta ta cigaba da kallo, baita ta kwanta ba saida ta gama kallon gaba 蓷aya 8 episodes na wani horror film if wishes could kill, yanzu kuma ta kasa bacci, dan data rufe ido sai taga tana ganin yarinyar a idonta.
Kawai sai ta kai hannu tana bubbuga jalila,ahankali kamar ra蓷a take kiran
"Pickles!!, pickles!!!"
"Na'am meya faru?"
"Muje ki rakani bakin toilet fitsari zanyi kinji!!"
"Kin kalli Film din kenan hmmm ai ya Miki kyau seda nace ki bari da safe Amman kika 茩i ji, wallahi kar ki kara tashina in na raka ki" tayi maganar tana mi茩e wa ta nufi bakin toilet din ta tsaya
"Ni zan miki fitsarin halan da zance ki taso kohh??"
A 蓷arare ta taso ta shiga toilet din Amman tadan bar door din toilet din bata jashi duka ba danta 蓷an ringa ganin jalilan
"Matsoraciya kawai, one day shegen tsoron Nan naki shi zai jamiki" ta fa蓷a tana hararar ta, itama hararar ta tayi tunda ai koma dai menene ta riga da ta raka ta.
Komawa sukai suka kwanta taji still baccin ya gagara,sai ta kara mikewa taga jalila ta koma baccin ta,
Tashi tayi ta fita daga 蓷akin ta nufi 蓷akin Ammi.
Tana shiga taga itama tana bacci, se kawai ta hau gadon ta kwanta ta bayanta ta cusa fuskanta jikin ta ko zata daina ganin matar a idon ta, ahaka har bacci ya 蓷auke ta.
Da asuba ne da Ammi ta tashi sallah ta juya taji ta kamkame a jikinta, hannunta da tasa ta matse ta ta cire tana tashinta tayi Sallah,
Bayan ta idar ne ta gaida Ammin sai tace bara ta koma daki, jinjina mata kai tayi ita kuma ta fita,
Tana baro corridorn 蓷akin Ammi suka ci karo, ta bugu da jikin shi har ta kusan yin 茩asa yayi saurin ri茩e ta, baya ta dan ja da sauri sai kuma tayi saurin juyawa zata bar gurin, jin ta kawai tayi tayi 茩asa zata fa蓷i amma bata karasa ba, ya ri茩o ta,
"Wai ke da forehead kike tafiya halan ko?, baki iya gaisuwar bane?"
Kamar daga sama taji Muryar tashi, itafa tayi tunanin ta kai 茩asa dan ta hasaso irin fa蓷uwar da zatayi
"Ina kwana" kawai abinda ta fa蓷a kenan tana 茩o茩arin fita daga hannun shi,
Kara ri茩e ta yayi yace
"Jiya wa kike ma 茩un茩uni da wannan bakin naki awajen"
Ido tazaro tana fadin
"Nifa ba abinda nace kuma ai bada kai Nike ba" tana kara 茩o茩arin barin jikin na shi, kwalla na 茩o茩arin Zubo mata, amman ya茩i bata dama
"Yahh ka 茩yale ni zan koma gurin pickles"
Sakin ta yayi yana 蓷an 茩o茩arin ha蓷e fuska,shifa ya rasa in dai tana guri duk Wannan kar a raina shi attitude din ajje wa yake,
kuma yasan be kamata yana ajje wa ba ai itama raina shin zatayi.
Har ta juya ta fara tafiya Ahmad ya bude kofar ya shigo, hango su yayi ita ta nufi 蓷akin su har ta bu蓷e ta shiga, shi kuma yana bin bayanta da kallo
"Iska na wahal da mai kayan kara in ance ma mutum abu sai ya dinga denying Amman Kuma yanzu ka wani bita da kallo, man kayarda ko karka yarda Ni dai nasan that the truth"
ya wuce shi ya shiga 蓷akin Ammin,shima baya ya rufa mai yana 蓷an susa 茩eya
茦un茩uni kwai take aranta Dan ita fa wannan sabon salon yi mata maganan bata gane ba dan a da banda gaisuwa ba abinda ke ha蓷a ta da shi ko a hanya zasu ha蓷u sai ya wuce ta wuce banda ta gaishe shi ya amsa ko watarana ma ba amsa mata yake ba ba sa magana, daman ta fi son haka, dabadan yanda yake sa punishment ba ko gaisuwar ma ba samu zai yi ba saboda yanda idan mutum ya gaida shi wani lokacin ba amsawa yake ba, ga shegen ha蓷a rai kamar wani hadarin Gabas duk wai don kar a raina shi.
"Nifa pickles gwara ma mu koma gidan amma su Khadijah su dawo ita da batul din"
"To ba kece kike wani wai zai runga punishing din su dan basa ji ba, ai in suka kiyaye ina ruwan shi dasu"
"Ki ha蓷a kayan ki ko Ammi karta san mun gudu muce abu zamu amso acan inyaso idan mun je se mu kirata mu fa蓷a mata"
"Yauwa haka ma za'ayi wallahi,dan bazan juri zama yahh yana gidan nan ba,mutum kamar wanda yake gumtsa bitter leaf"
"Hmmm" kawai tace tana tuna yanda suka kaya dazu
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 馃尯