Free chapter · Read without an account

A Troubled Morning

by ZAHRA B MRS · Nuwayrah the foreigner’s passion

Bayan sun tashi daga aikin around 5pm Taxi    Nuwayrah tsayar inda ta fada masa sunan super market din da zai kaita dazu Mrs Elizabeth ta fada mata sunan Wajan a cewar zata samu Abubuwan Africa a Chan 

Ta shiga babban kantin , ta zaɓi duk abubuwan da take buƙata daidai gwargwado—daga kayan miya, shinkafa, sinadaran ƙamshi Halal, nama ,kifi ,madara  da sauran abubuwan amfanin yau da kullum

gidan nasu shiru as usual 

Nuwayrah ta wuce kitchen ta gyara duk abubuwan da ta sayo ta shirya su daya bayan daya a wuraren da suka dace. Daga nan ta fara  girki.

Cikin ƙanƙanin lokaci, ƙamshin shinkafa da miya   ya cika ko'ina a cikin kitchen ga salad dinta ta tayi  yadda take so  dashi ,Bayan ta kammala, ta zuba a plate ta dauki ruwa sai falo ,Karon farko ta zauna a sofa tare da kunna tv a haka har ta gama wanke plates din da duk wani Abu datayi anfani dashi kitchen din tas Kamar ba girki akayi ba  ta dauki wani  madaidaicin food flask mai hawa biyu , ta zubawa Kiara shinkafa da miyar ,bata sa mata nama ba Sabida tasan wasu Indian basa cin Nama addinin su ya Hana ƙaramin sticky note tayi rubutu a Kai 

(ga Abincinki . — Nuwayrah)

. Ta wuce ɗakinta abinta, tana azkar suna chatting Sama sama da Rayyan dan bacci take ji 

Cikin ƙanƙanin lokaci, barcin kuwa mai nauyi ya kwashe ta...

A cikin  barcin,  yanayin ɗakin ya sauya zuwa wani irin  sanyi mai ratsa kashi . Nuwayrah ta tsinci kanta a cikin wani daki duhu  a cikin mafarki.

A tsakiyar duhun, wata mace ta fito a hankali tana takawa zuwa gare ta 

Mrs Eleanor Whitmore  sanye da blue din dogowar rigar tana yi mata wani irin sanyayyan murmushi tana miko mata hannu Alamun tazo 

Nuwayrah ta riƙa ƙoƙarin ja da baya  wani irin nauyi da firgici da suka danne mata ƙirji, gashi dai murmushi Mrs Elenor take mata amma ji take  tana  riƙe makogwaronta ,a firgice nuwayrah ta tashi tana tari ,ta Laluba fitilar gefen gadon ta kunna,glass dinta ta dauka tare da duba lokaci ,3:30am Addua tayi a Kara kwanciya ta mamakin irin Wanann mafarki 

The next morning 

A  gidan Chris, Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa saboda gajiyar da ke jikin sa dan tare suka kwana da Amelia 

Yana ƙoƙarin tashi ya zauna a bakin gadon, Amalia ta juya daga ɗayan ɓangaren tana kallon shi 

Chris, ya maganar engagement ɗinmu?

Chris ya dafe goshinsa , yana jin wani irin takaici yana rufe shi. Ya waigo ya dubeta fuska a murtuke, Amelia na gaya miki idan kika ƙara yi min maganar aure ko engagement, zan rabu da ke for good (har abada).

Ya miƙe tsaye yana kokarin sauka daga gadon . Duka-duka shekarasa  29  kacal a duniya, kuma aure ko settling down ba sa cikin tsarin rayuwarsa a yanzu ko kaɗan.

Amalia ta buɗe baki , idanunta cika da ƙwalla Ta kalle shi tace "To na ji, Chris! Tunda  haka ne, mu rabu kawai. I want to settle down (Ni ina son nayi aure na nutsu)

Ba tare da ta jira amsar sa ba, ta  fara saka kayanta  cikin fushi , ta fice  daga ɗakin tare da  bugo ƙofar da karfin gaske .

Chris ya tsaya a tsakiyar ɗakin yana kallon ƙofar da ta fice. ya ayyana a ransa cewa wannan karon kam rabuwarsu ta zama ta ƙarshe har abada—no amount of sex ko  sha'awa zai sashi komawa Wajan ta .

Tsaki ya ja a hankali,ta  bata masa safiyarsa . Ran sa a ɓace ya shiga banɗaki yayi wanka Bayan ya fito, ya shirya cikin sauri, ya saka  suit dinsa a usual 

Ya matsa gaban mudubi yana  gyara daurin tie dinsa. Dik sanda  ya kalli kansa a mudubi—idanunsa masu launin shuɗi (blue eyes) masu kaifi gami da kwarjini—shi da kansa yana admiring ƙyaun da Allah ya yi masa. Amma a yau, haushin kansa yake ji.

"Why will I keep on going back and forth with Amelia ?" (Me yasa zan riƙa komawa  Amelia kamar wani wawa?) ya tambayi cikin ɓacin rai.Kana da kyau Chris kafi  karfin batawa kanka lokaci Akan wata Amelia ya ayyana a ransa .

Yau ko driver be nema ba da Kansa yake driving ,Wayarsa da ke haɗe da tsarin motar ta fara ruri.

Sunan mahaifiyarsa, Lady Eleanor, ya bayyana a kan allo. Ya danna receive cikin gundura.

"Good morning, Chris," muryar Eleanor ta fito cikin nutsuwa Ina fatan kana lafiya ? Dama na kira ka ne domin na tunatar da kai game da yarinyar nan da muka gani jiya... Uhmm bakar yarinyar nan mai kyau . Please Chris, ina son ka ƙara sa mata ido da kulawa a wajen aikin nan. Jiya da na ganta sai naji ta bani tsausayi ganin ita kadai ce Baka 

Chris ya buga tsaki a fusace yana  karkata motarsa. "Oh Mom, please! Ni ina ruwana da wata worker da zan rika kulawa da ita? Babysitting din zanyi?

Eleanor ta yi shiru na daƙiƙa ɗaya daga ɗayan ɓangaren, Chris... kun yi faɗa da Amelia  ne ?

"Yes! And this time, it's for good," Chris ya amsa a taƙaitace.

"Kullum haka kake cewa, amma daga baya za ku koma  baza ku iya rayuwa ba juna ba Ni dai Amalia ce surukata, kuma—

Dif!

Chris ya yanke kiran ba tare da ya jira ta ƙarasa maganar da take shirin faɗa ba. Ba shi da lokacin sauraren maganganun mahaifiyarsa a wannan safiyar.

Ransa ya ƙara ɓaci. Wannan maganar ta Mom ɗinsa ta cewa ya ƙara sa ido kan wannan yarinyar da ko cikakken sunanta bai iya gama faɗa ba ya Kara bata masa rai 

mahaifiyarsa tana da wani irin  tausayi na daban a ranta ,ita kullum gani take yi kamar  baƙar fata yana cikin haɗari ko wariya a duk inda yake, don haka duk inda ta gansu a duniya sai ta nuna musu tsananin ƙauna da tausayi domin su ji su kamar kowa. 

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.