Free chapter · Read without an account
Page 11: A Victory Without Celebration
Chapter 11: A Victory Without Celebration
“Sometimes, the loudest applause comes from strangers… while the people you long to impress remain silent”
Daddy ya kira Aryan domin ya ba da cikakken bayani, Aryan kuwa ya faɗi komai, shiru ya mamaye wajen.
Daddy ya ja dogon numfashi.
“Na fahimta”
Amma Zahra ta miƙe cikin fushi
“Wannan ba abin da za a amince da shi ba ne, daga yau kar ka sake shiga ɗakinsu ba, dama kana namiji me zai mai ka?”
Aryan ya sunkuyar da kansa “Na yarda ba zan sake ba… amma dole ne a dakatar da ita”
Ganin ran Mummy ya baci Sosai hakan yasa Aryan ya kirasu both Amrah da Dua ya musu lesson na gobe
A wannan daren Aryan ya kasa barci, tunani ɗaya kawai ya ci gaba da dawowa cikin zuciyarsa ‘Yaushe Amrah ta zama haka?’
Washegari da safe.. ya kasance last paper ce
Tun kafin kiran sallar Asuba, Du’a ta riga ta farka. Bayan ta idar da sallarta, ta zauna tana karanta Qur’ani sannan ta ɗaga hannayenta sama
“Ya Allah… Ka ba ni sauƙin wannan jarabawar. Ka sa na zama abin alfahari ga mahaifiyata, ko da kuwa ba ta nan tare da ni”
Ta share hawayen da suka zubo, sannan ta ɗauki littafinta na Further Mathematics ta sake duba wasu formulas
A other side na ɗakin kuma, Amrah na shan bacci cikin kwanciyar hankali
Sai da Fatima ta shigo ta tashinsu kafin ta farka, as usual suka sauka suka gama everything within short period of time
A dining area… Kowa ya hallara domin breakfast, Daddy ya duba agogonsa sannan ya ce “Driver ne zai kai ku school today ma, Ina da meeting da wuri”
“Okay Daddy” Amrah ta amsa da fara’a, Du’a ma ta gyada kai cikin ladabi
Aryan ya kalli Du’a “Relax! You’ve prepared enough just do your best”
Ɗan murmushi ta yi “In shaa Allah”
Tun jiya bai sake yi mata coaching ba, amma kalamansa sun ƙara mata ƙarfin gwiwa
Zahra kuwa… Tun lokacin da ta zauna a dining table ba ta ko kalli Du’a ba, kamar ba ta ma cikin gidan
A school kuma, da aka fara distributing question papers, Du’a ta karɓa da addu’a a zuciyarta, da ta duba tambayoyin… Sai murmushi ya bayyana a fuskarta “Alhamdulillah…”
Yawancinsu sun fito daga abubuwan da Aryan ya koya musu jiya da kuma waɗanda ta yi ta maimaitawa cikin dare
A hankali ta fara solving babu tashin hankali, babu rudani sai confidence kawai, bayan kusan awa biyu.. “Pens down!” Teacher ya faɗa
Dalibai suka fara miƙa answer sheets ɗinsu, da suka fito daga exam hall…
Kusan kowa cikin farin ciki yake, Ayesha ta yi saurin rungume Du’a “We’re finally done!”
Alhamdulillah!” Du’a ta faɗa tana dariya
Haidar ma ya ƙaraso “So… who thinks she’s taking first position again?” ya faɗa yana dariya
Ayesha ta nuna Du’a “Ask our genius”, Du’a ta girgiza kai“Please…”
Haidar ya buɗe question paper ɗinsa
“Question number five… what did you get?”
Suka fara comparing answers.
Bayan mintuna kaɗan… Haidar ya dafe kai “Subhanallah! It seems Du’a ta fi mu score this time too”
Ayesha ta kalli answer sheet ɗinta sannan ta yi dariya “Wallahi gaskiya ne”, Du’a ta girgiza kai kawai “No one knows please”
Suna cikin hirarsu wata baƙar mota ta tsaya a gabansu, wani saurayi ya fito daga driver’s seat
Dogo ne, fari ne, cikin shigar smart casual, da murmushi ya ƙarasa wajensu “Haidar, you’re done?”
Kai Haidar ya gyad’a masa ya ce“Ya Ahmad!”, Ya Ahmad kallonsu Dua yake
Haidar ya yi murmushi juya ya ce, “These are my classmates. Yaya, this is Ayesha and this is Du’a”
Ahmad ya yi murmushi “Nice meeting you” Duk gaishe sa suka yi, ya amsa da fara’a , sai kallonsa ya koma kan Du’a na ɗan lokaci ba don komai ba, sai don yadda nutsuwa da kunya suka bayyana a tare a fuskarta, ya ɗan yi murmushi
“Du’a… are you Shuwa Arab?”
Ta girgiza kai ta ce “No”, Ya ce “Then… which tribe are you?”, Du’a ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ce a hankali, “I… I don’t know”
Ahmad ya ɗan yi mamaki ya ce “You don’t know your tribe?” Ya tambaya da mamaki a muryansa, ta sake girgiza kai ta ce “No”
Ya yi murmushi “It’s okay, when you get home ask your mum, Next time we meet, you’ll tell me”
Yana gama faɗin hakan murmushin da ke fuskar Du’a ya ɓace, Idanunta suka cika da ƙwalla
Haidar ya yi saurin cewa “Ya Ahmad she lost her mum when she was ten”
Nan take fuskar Ahmad ta sauya “Oh…I’m so sorry”, Du’a ta yi murmushin dole “Thank you”
“See you next time,” Ahmad ya faɗa cikin tausayawa, Haidar ya ce “Bye” Suka shiga mota suka tafi
Ahmad dai… Har motar ta bar school premises, hankalinsa yana kan yarinyar nan “There’s something unusual about her… And I intend to find out”
Bayan motarsu Ahmad ya tafi… Du’a da Ayesha suka koma wani side, a hanya, Ayesha ta lura Du’a ta yi shiru fiye da yadda ta saba, ta taɓa hannunta a hankali “Dua…”
Ta ɗago ta kalle ta, Ayesha ta ce “Are you okay?” Da ƙyar ta yi murmushi “I’m fine”
Ayesha ta girgiza kai “No… I know you wani abu yana damunki”
Du’a ta sauke ajiyar zuciya “Lokacin da Ya Ahmad ya ce na tambayi mummy tribe ɗina…” Sai muryarta ta dusashe. “…na tuna da mummy na ne kawai, bcos I just need her”
Ayesha ta riƙe hannunta “Allah Ya jiƙanta”, Ta amsa da Ameen, Ayesha ta rike hannunta “Kuma ki daina damuwa. In shaa Allah, one day komai zai yi kyau”
Du’a ta yi murmushi kaɗan “In shaa Allah”
Two Week Later… Yau ce ranar Speech and Prize Giving Day, tun da safe makarantar ta cika da iyaye da baƙi, An yi ado a school hall cikin tsari mai kayatarwa
Students kuma kowa cikin uniform ɗinsa mai kyau, Du’a da Ayesha suna zaune tare suna kallon yadda iyaye ke shigowa ɗaya bayan ɗaya
A hankali Ayesha ta ce, “Duba…” Ta nuna wani yaro da mahaifiyarsa ke gyara masa tie
Can kuma wani mahaifi yana ɗaukar hotuna da ’yarsa, Du’a ta yi murmushin dole ba ta ce komai ba sai dai zuciyarta ta yi nauyi
Bayan an fara taro, principal ta hau stage, ta yi jawabi mai kayatarwa kan ƙoƙarin ɗaliban makarantar sannan aka fara kiran waɗanda suka yi fice a wannan term
An fara da Best House, sai Best Discipline, sai Best in Debate Hall ɗin ya cika da tafi mutane.. Daga bisani Principal ta buɗe wani envelope ta ce
“Now… we’re moving to the overall academic awards”, Nan take hall ɗin ya yi shiru “SSS2…”
“Third Position…” Aliyu Haidar Suleiman! Tafi ya cika hall, Haidar ya miƙa ya karɓi kyautarsa cikin farin ciki tare da familynsa
“Second Position… Ayesha Muhammad Inuwa!, Ayesha ta miƙe cikin murna ta karɓi certificate da medal ɗinta
Da ta dawo ta zauna, ta riƙe hannun Du’a “Your turn”, Du’a ta yi murmushi kawai, sai Principal ta sake cewa “And finally…”
“Our Overall Best Student… As usual…”
“DU’A MUHAMMAD USMAN!”
Hall ɗin ya kaure da tafi, wasu malamai suka fara murmushi, a hankali Du’a ta miƙe, tana tafiya zuwa stage absentminded , sai ta hango yadda iyaye da dama suke ɗaukar hotunan ‘ya’yansu, wasu suna tsaye suna musu tafi
Da ta karɓi certificate da medal ɗinta… Principal ta yi murmushi “Congratulations sweetheart, we’re proud of you”
“Thank you, Ma” Daga haka ta juya, Idanunta suka fara neman Daddy ko Mummy ko da murmushi ɗaya ne ta gani Yau a fuskansu
Sai dai, fuskokinsu babu wani canji although Daddy na zaune cikin nutsuwa Zahra kuwa kamar wanda aka Mata mutuwa
Du’a ta haɗiye ƙwallar da ta cika idanunta, a hankali ta sauko daga stage, ta rasa wa za ta kai certificate ɗinta
Sai Aryan ya miƙe tsaye yana murmushi “Bring it here”
Nan take ta ƙarasa gare shi, ya karɓi certificate ɗin ya kalle ta cikin alfahari
“I’m proud of you, little sis”
Da ƙyar ta yi murmushi “Thank you, Ya Aryan”
Ahmad, wanda ya zo domin bro dinsa Haidar ya tsaya yana kallonta, sosai ta tsaya masa a rai, lokaci guda ya fahimci Daddy de Mahaifinta ne though bai san Zahra ba amma ya gane kamar itace Wanda ke rike da ita. Ya ga yadda sauran iyaye suke rungumar ‘ya’yansu
Ya kuma ga yadda Du’a ta sauko daga stage ba tare da iyayenta sun taya ta murna ba, ya ɗan yamutsa fuska “Something isn’t right… Why would parents treat such a brilliant daughter this way?” Ya ci gaba da kallonta, karo na farko ya fara jin cewa akwai wani Abu
Bayan an kammala rabon kyaututtuka, Principal ta sake komawa kan podium, ta yi murmushi tana kallon iyaye da ɗalibai “Alhamdulillah, wannan shekarar ta kasance mai albarka ga makarantar mu”
Ta ɗan dakata kafin ta ci gaba “Kamar yadda muka saba a kowace shekara, akwai wasu ɗalibai da aka zaɓa domin wani special academic training a ƙasar Germany”
Hall ɗin ya kaure da tafi, wasu ɗalibai ma suka kasa ɓoye murnar da suke ji
Principal ta ci gaba “Training ɗin zai ɗauki two weeks ne kawai”
“Kuma idan ɗalibi ya yi outstanding performance, akwai yiwuwar samun full scholarship zuwa Oxford University a London domin karatun gaba”
Da jin haka… Muryoyin masu farin ciki suka ƙara cika hall ɗin
Principal ta fara kiran sunayen waɗanda aka zaɓa “Aliyu Haidar Suleiman!Congratulations” Haidar ya miƙe cikin farin ciki
“Ayesha Muhammad Inuwa” Ita ma ta miƙe tana murmushi, Sannan Principal ta sake kallon takardarta “Our overall best student…”
“Du’a Muhammad Usman”
Tafi ya sake tashi cikin wall din, Du’a ta ji zuciyarta ta buga ba don komai ba…
Sai don wannan ne karo na farko da ta ji kamar wata babbar dama ta zo Mata a rayuwarta, A hankali ta juya ta kalli Daddy sai kuma ta mayar da kallonta ga Mummy
A zuciyarta tana addu’a “Please… ku yarda kar ku ce No”
Principal ta ci gaba da bayani
“Ba za a tafi da kowane ɗalibi ba sai da cikakken yardar iyayensa”
“Saboda haka, za a ba kowanne parent consent form domin ya sanya hannu”
Teachers suka fara rabawa iyaye forms ɗin, da aka kawo wajen Daddy ya karɓa ya fara dubawa, Zahra ma ta matsa kusa da shi ta karanta bayanan cikin nutsuwa
Aryan ya yi murmushi wanda zuwansa wajensu kenan ya ce “This is a great opportunity Dua deserves it”
Daddy bai ce komai ba.
Principal ta ƙaraso kusa da su “Sir, your daughter is one of our brightest students”
“We believe she’ll make the school proud”
Daddy ya ɗaga kai ya kalli Principal “Thank you” Sai ya sauke numfashi “Amma… Ina ganin har yanzu tana da ƙaramar shekaru”
Principal ta yi murmushi cikin ladabi “Sir, ba ita kaɗai ba ce, za su tafi tare da teachers da sauran students, they’ll be well taken care of”
Daddy ya yi shiru kafin ya yi magana… Zahra ta katse shi “No
Principal ta ɗan yi mamaki “I’m sorry, Ma?”
Zahra ta gyara zamanta“My daughter is not going anywhere. Ba zan iya bari ta yi tafiya zuwa wata ƙasa ba”
Principal ta yi ƙoƙarin lallashinta
“Ma, this is a very good opportunity.
Amma Zahra ta girgiza kai “I said no”
Aryan ya kasa haƙuri “Mummy… but why? Ba ita kaɗai ba ce fa, kuma wannan opportunity ce da ba kowa yake samu ba
Wani kallo Zahra ta watsa masa Kallon da ya sa ya yi shiru nan take
Daddy ya miƙa form ɗin ya mayar wa Principal “We’re sorry but we can’t sign it”
Hall ɗin ya yi shiru na ɗan lokaci, Principal ta kalli Du’a sai ta kalli iyayenta
Daga ƙarshe ta karɓi takardar cikin murmushin dole “I understand”
“Thank you”Ta juya ta tafi
Du’a kuma tun lokacin da Daddy ya mayar da form ɗin.. kamar an cire mata wani ɓangare na zuciyarta, ta yi iya ƙoƙarinta kada ta yi kuka
Amma idanunta sun riga sun cika da ƙwalla, a hankali ta sunkuyar da kanta “Maybe… this is not meant for me”
Ahmad daya ga komai, ya ga yadda Principal ta zo da farin ciki ya kuma ga yadda aka mayar mata da takardar ba tare da an sa hannu ba
Ya juya ya kalli Haidar “Haidar wai me ya sa iyayen Du’a suka ƙi?”
Haidar ya girgiza kai “Wallahi ban sani ba Yaya”
“Tun zuwan mu na daɗe ina lura, there’s something strange about that family” Ahmad ya sake kallon Du’a
Ta na tsaye ita kaɗai riƙe da certificate ɗinta babu wata murmushi balle farin ciki
Ba kuma wanda ya zo ya rungume ta kamar yadda sauran iyaye suke yi wa ‘ya’yansu
A zuciyarsa ya furta a hankali “One day… Zan gano dalilin da yasa idanunta suke ɗauke da wannan baƙin cikin
yanzu kuyi following dina shine aiki🥹?