Free chapter · Read without an account

Chapter 22

by Umma mustapha · WA ZAI FUSKANCE NI??

WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 22
Bayan kwana bakwai...
Sai da Nihla ta kwashe kusan tsawon sati guda tana jinya kafin jikinta ya fara warwarewa sosai.
A wannan satin, makaranta ta zama kamar wani abu mai nisa a gare ta. Ba ta samu damar zuwa ko kwana ɗaya ba. Duk lokacin da ta yi ƙoƙarin tashi, sai jikinta ya nuna mata cewa har yanzu tana buƙatar hutawa.
Fatima ce kawai take zuwa makaranta.
Da safe za ta fita, ta halarci darussa, ta yi wa Nihla attendance, sannan da zarar an tashi sai ta dawo gida.
Amma a cikin wannan satin, akwai wani abu da ya fi ɗaukar hankalin Fatima.
Irfan.
Babu ranar da ta wuce ba tare da Irfan da Jabir sun zo kofar gidan Nihla ba.
Kullum suna zuwa.
Kuma ba sa zuwa hannu wofi.
Kowacce Rana Akwai kalar abin da za'a kawo Musu.
Abin mamaki shi ne, duk da cewa Irfan ba ya samun damar ganin Nihla, hakan bai hana shi zuwa ba.
Wasu lokutan ma, Fatima ce kawai take fita ta karɓi kayan.tun Fatima tana Jin kunyar karba har ta hakura.
Sai ta karba tayi godiya.
Idan tace baza ta karba ma, Irfan ba Wani sauraronta yake ba, daga karshe ma sai ya ajiye mata kayan a kofar Gidan ya tafi.
So Bata da Wani zabi illa karba.
JABIR ya so ya dakatar da irfan da yawan zuwan da yake Yi Amma yaqi sauraronsa.
Ina ga da hakura mukayi da zuwa, mu bari sai ta samu lafiya gaba Daya, tunda idan munzo bama samun Damar ganinta kake Yi ba, Kuma ko a wayar Fatima zaka iya Kira kaji ya jikin nata, Amma Irfan yaki yadda da shawarar jabir.
JABIR ya fuskanci makauniyar soyayyace take dawainiya da abokinsa, Wani lokacin har tausayi yake bashi. Babban fatansa da Kuma addu'ah da yake masa Allah yasa NIHLA ta karbi soyayyar Irfan a duk lokacin da ya bayyana mata.

Fatima ta riga ta fara fahimtar inda Irfan ya dosa.
Sirrin da yake ƙoƙarin ɓoyewa ya fara bayyana kansa, ko da kuwa har yanzu bai furta komai da bakinsa ba. Amma duk wasu alamomi sun bayyana kansu.
Domin duk Wanda ya Kalli Irfan yasan ya fada cikin tarkon so.
Wata rana bayan Irfan da Jabir sun tafi, Fatima ta zauna a bakin ƙofar gidan tana kallon hanyar da motarsu ta bi.
Ta yi murmushi kaɗan.
"Hmm..."
Shukura ta kalleta.
"Me ya faru?"
Fatima ta girgiza kai.
"Babu komai."
Amma a zuciyarta, tambaya guda ce take yawo.
"Shin Nihla za ta karɓi Irfan a matsayin masoyi?"
Tun da Fatima ta san Nihla, ba ta taɓa ganin ta kula da wani saurayi ba. Ba ta taɓa jin ta ambaci wani namiji da sunan saurayin ta ba. Ko irin yadda mata suke magana game da wanda suke so ba.
Shi ya sa take ganin abin zai zama mai ban sha'awa.
Ko Nihla za ta lura da abin da Irfan yake ji?
Ko kuwa za ta yi watsi da shi?
Fatima ta ɗan yi murmushi.
"Bari dai mu gani."
Ta yanke shawarar cewa ba za ta tsoma baki ba.
Za ta tsaya gefe.
Ta saka ido.
Ta kalli yadda abin zai kasance.
Domin wasan Zai bada ma'ana... 

Umsar ✍️ 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.