Free chapter · Read without an account
Page 13: The arrival
Safiyar ranar… Daddy da Aryan suna kan hanyarsu ta zuwa Nnamdi Azikiwe International Airport domin tarbar Alhaji Abubakar Tukur da iyalansa
Cikin motar shiru ne ya mamaye shi
Aryan yana tuƙi, Daddy kuma yana kallon titi ta window.
Bayan wasu mintuna Aryan ya yi gyaran murya “Daddy…”, Daddy ya ɗan waigo “Yes, son?”
Aryan ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce
“There’s something I’ve been wanting to ask you for a long time”, Daddy ya yi murmushi “Go ahead, yuh know you can ask me anything”
Aryan ya sauke numfashi “But kayi alkawarin ranka ba zai baci ba?”
Daddy ya ɗan yi dariya “Never, you’re my only son ka faɗi abin dake ranka”
Aryan ya matse steering wheel ɗin da hannunsa, da ƙyar ya sami ƙarfin gwiwar cewa ”…Is Du’a really our biological sister?”
Daddy bai ce komai ba, hakan yasa Aryan ya ci gaba “I mean… Is she truly your daughter? Kai ne mahaifinta?”
Kalaman haka suka sauka kamar wani mashi a zuciyarsa, hakan yasa Daddy ya yi shiru, amma fuskarsa ta sauya gaba ɗaya, kamar an tuna masa da wani abu da ya daɗe yana ƙoƙarin mantawa
Aryan ya kalle shi da gefen ido, gabansa ya faɗi “Maybe I shouldn’t have asked…” Ya maida hankalinsa kan tuƙi
Motar ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwa, sai bayan wasu daƙiƙu…, Daddy ya yi magana cikin ƙaramar murya “Aryan…”
“Yes, Daddy?”, Daddy ya lumshe ido na ɗan lokaci “I honestly don’t know why…”
”…but sometimes… I feel like there’s something missing” Ya dafe ƙirjinsa a hankali “Duk lokacin dana kalli Du’a… my heart feels strange, I can’t explain it”
Ya girgiza kai “Kamar dai na manta da wani bangare daya shafe ni a rayuwa, kuma something very important”
Aryan yana sauraren shi cikin mamaki, Daddy ya ci gaba “But dalilin daya sa nake Jin haka ɗin, …I honestly don’t know”
Aryan ya sauke numfashi a hankali ya ce “Amma Daddy whatever the case may be Du’a har yanzu ‘yarka ce, hakan ba zai taɓa goguwa ba, she’s still the youngest in this family kuma abun tausayi ce ita ɗin duba da cewa ta rasa mahaifiyarta tun Dana da kananun shekaru”
“All she needs now… is love and care”
Daddy bai amsa ba, ba don bai ji abin da Aryan ya faɗa ba sai don zuciyarsa ta sake nutsewa cikin wani irin tunani
Har suka isa airport, ba wanda ya sake cewa komai, a gida kuma Amrah tana tsaye gaban mirror ta a kunna music a wayarta, tana gwada rawar da za ta yi a birthday party na Rumaisa, ta yi juyi ta sake gwadawa, sai dariya take yi
“Perfect!” ta faɗa tana tafa hannu
A downstairs… Zahra ta kira sunanta sau biyu amma shiru bata amsa ba, still ta sake Kira, har yanzu babu amsa
Ta ɗauki wayarta ta kira Amrahn, but no response, ta ja dogon tsaki “Kar dai yarinyar nan ta fita…” Ba tare da ɓata lokaci ba ta haura upstairs
Ta tura ƙofar ɗakin sai ta tarar da Amrah tana rawa gaban mirror, Zahra ta tsaya tana kallonta Amrah ta hango ta ta mirror da sauri ta juya “Mom! Yaushe kika shigo?”
Zahra ta haɗe fuska “From the look of things… gaba ɗaya kinma mance cewa Yau muna da very important baki da zasu zo ko? Kuma in other hand surakananki ne fah?”
Amrah ta turo baki “Mom… bafa maganar auren za’a yi Yau ba fah, and daga zuwansu Yau ba cewa za’a yi za’a ɗaura auren ba, kuma ni ba zuwa wajensu zanyi ba, can’t all that wait till tomorrow?”
Zahra ta ɗan ɗaga gira “Haka kika ce Shikenan let’s forget the whole thing then”
Ta juya zata fita, da sauri Amrah ta riƙe hannunta “No, no, no… I’m sorry Bari na shirya yanzu” Sai lokacin Zahra ta yi murmushi a ranta ta ce “That’s better”
Bayan ƴan mintuna Motar Daddy ta tsaya a harabar gidan, Gatekeeper ya yi saurin buɗe gate da suka shiga…
Ma’aikata suka fito domin karɓar luggage
Alhaji Abubakar Tukur ya sauko daga motar yana murmushi
Daddy ya rungume shi da sauri
“Welcome to Abuja, my friend!”
Alhaji Tukur ya yi dariya
“It’s been a long time, Muhammad”
“Indeed…” Daddy ya amsa “Too long”
Aryan kuwa ya ƙarasa wajen Sultan suka yi musabaha sannan suka rungumi juna.
“Welcome home, bro” Sultan ya yi murmushi “Thank you, ka ganka kuwa? Ka canza Sosai fah”
Aryan ya yi dariya
“Same goes for you”
Abidah ma ta fito daga motar cikin nutsuwa, Fatima da sauran ma’aikata suka karɓi kayanta
Bayan sun gaisa, kowa ya nufi babban parlour, bayan da suka zauna…
Hira ta kaure tsakanin Daddy da Alhaji Tukur Business ne, Old memories… University days…
Dariya ce kawai ke tashi lokaci zuwa lokaci
Aryan da Sultan ma suna tattaunawa a gefe
Hajiya Abidah kuma shiru tayi tana kallon wayarta, bayan wasu mintuna sai aka ji sallama
Zahra ce ta shigo, fuskarta cike da fara’a ta ƙarasa ta gaisa da su ɗaya bayan ɗaya
Abidah ta amsa cikin mutunci ko da yake har yanzu ba ta saba da Zahra ba
Zahra ta yi murmushi
“Kun yi tafiya mai nisa, Ina ganin ku fara yin sallah, sannan ku ci abinci after that, you can rest”
Alhaji Tukur ya gyada kai
“That’s a good idea”
Suna shirun su miƙe ne, sai ga takun Amrah, ta shigo cikin wata doguwar riga mai kyau
Ta yi light makeup, ta ƙarasa cikin ladabi ta ɗan rusuna “Assalamu alaikum”
Kowa ya amsa, Zahra sai murmushi take yi, ta fara gaishe da Alhaji Tukur, Sannan ta gaishe da Abidah, daga ƙarshe ta juya wajen Sultan “Good afternoon”
Sultan ya yi murmushi “Good afternoon” shi ke nan babu wata hira mai tsawo
Sai Alhaji Tukur ya yi dariya ya kalli Daddy
“Muhammad… Is this your little princess?”
Daddy ya yi murmushi “Yes ita cr Amrah”
Alhaji Tukur ya girgiza kai “Masha Allah ta girma kam”
Daddy ya yi dariya “Time flies”, Amrah ta yi murmushi cikin kunya, ta nufi upstairs
Abidah ta bita da kallo ba ta ce komai ba sai dai a ranta ta lura da abu guda “She’s beautiful… but beauty alone isn’t enough”
A wannan lokacin kuma… Du’a da Ayesha suna kan hanyarsu ta dawowa daga Islamiyyah, littattafansu na hannu, suna ta bitar darasin da malaminsu ya koya musu
Ayesha ta kalli Du’a
“You’ve been unusually quiet today”
Du’a ta yi murmushi kaɗan “I’m listeningl
Ayesha ta girgiza kai “No… tunani fah kike yi” Du’a ta yi dariya “Maybe”
Sai Ayesha ta ce cikin zolaya “By the way… kin Lura da wani abu kuwa?”
Du’a ta ɗago gira “Like what?”, Ayesha ta yi murmushi “Ya Ahmad”
Du’a ta yamutsa fuska “Who?”, Ayesha ta buɗe baki “Bani son iskanci kar ki ce har kin manta da sunan Haidar’s elder brother ba?”
Du’a ta yi dariya “Wallahi, I barely know him, kin San bamu taɓa magana na 10 mins ba, that’s all kuma kike expecting na rike sunansa”
Ayesha ta matso kusa da ita ta rage murya. “Duk ba wannan ba but the way he looks at you is different”
Du’a ta tsaya cak “Different?” Ayesha ta gyada kai tana dariya “Yes wlh Ina ma tunanin Yana Sonki ne fah”
Da sauri Du’a ta ɗan bugi kafaɗarta “Stop it! Kawai sai kiyi ta imagining abubuwa?”
Ayesha ta ƙyalƙyale da dariya
“We’ll ask Haidar when school resumes”
Du’a ta bi bayanta tana ƙoƙarin dukan ta, su biyun suka ci gaba da gudu suna dariya
Duk cikinsu basu ma Lura ba daga ɗayan gefen hanya Ahmad yana kallonsu cikin motarsa
Murmushi ya yi a hankali a karon farko cikin kwanaki, ya ga Du’a tana dariya daga zuciya, ya sauke numfashi “At least… She’s smiling” Ya kunna motarsa ya ci gaba da tafiya
Amma har sannan zuciyarsa ta ƙara tabbatar masa da abu guda, lallai akwai wani ɓoyayyen labari a rayuwar Du’
Da daddare.. Dua ta daɗe zaune a bakin gadonta bayan Amrah ta fita. Idonta na kan ƙofar ɗakin, zuciyarta cike da tunani
“Ya Allah… Amrah ta fita da dare haka, If mummy finds out…” Ta girgiza kanta“No… it’s none of my business”
Ta ɗauki Qur’aninta ta fara karantawa a hankali, duk lokacin da zuciyarta ta cika da damuwa, abin da ke kwantar mata da hankali shi ne karatun Al-Qur’ani
A gefe guda kuma… Jackson ya tsaya da motarsa a gaban wani luxurious event centre da aka kawata da golden lights
“Happy birthday to Rumaisa!” mutane suka riƙa ihu yayin da ake shiga cikin wajen
Amrah ta sauko daga motar cikin confidence. Black designer gown ce a jikinta, light makeup, sannan ta saki dogon gashinta
Jackson ya miƙa mata hannu
“Beautiful as always”
Amrah ta yi murmushi “Thank you” sannan ta Mika masa hannunta
Suka shiga tare, Rumaisa da Firdausi suka yi tsalle suka rungume ta “Finally! Kinga yadda muke fa jiran ki?”
DJ na kunna waƙa, matasa na rawa, ana ɗaukar hotuna, Party ɗin ya cika da ‘ya’yan masu kuɗi ne kawai
Amrah tana jin kamar ita ce star of the night.
Meanwhile Aryan yana fitowa kitchen ya hangi Dua tana ɗauke da tray na cups “Dua”
Ta tsaya “Yes, Ya Aryan?”
“Ki bari, Bari na taimaka miki”
Da sauri ta girgiza kai
“No… if mummy sees you helping me, she’ll be angry”
Aryan ya yi murmushi mai ciwo
“So you already know”
Ta sunkuyar da kanta
“I don’t want another misunderstanding.”
Aryan ya karɓi tray ɗin duk da haka“I don’t care”Bai gama kaiwa parlour ba sai Zahra ta fito, ta tsaya cak “Aryan!” Ya juya “Yes, mummy?”
“Me kake yi haka ban gane ba?”,
“Helping Dua” Ya amsa mata, “Me na fada maka jiya?”
Aryan ya sauke numfashi
“Mummy… helping someone isn’t a crime”
Zahra ta matso kusa da shi
“I warned you to stay away from that girl Aryan”
Aryan ya ɗan yi murmushi
“And I warned myself not to stop being human”
Kalaman nasa suka ƙara ɓata wa Zahra rai hakan yasa tayi magana cikin very strictly tone “Take that tray back to her”
Ya tsaya yana kallonta ta ce “I said take it back!”
“No, mummy”
Parlour ɗin ya yi shiru
Dua kuwa jikinta har rawa yake, ta san duk abin da zai biyo baya… a kanta zai ƙare.
A daidai lokacin… Abidah tana tsaye daga saman balcony tana kallon komai
Ta ga yadda Zahra take magana da Aryan ta kuma ga yadda Dua ta tsaya a gefe cikin tsoro
Ta ɗan haɗe gira
“Something isn’t right in this house…”Tun da suka iso ta Lura , Duk lokacin da Dua ta shiga cikinsu everyone changes, especially Zahra
Abidah ba ta ce komai ba sai dai ta fara analyzing wasu abubuwa a zuciyarta….
Bayan dinner na wannan ranan, Sultan ya fito garden domin ya ɗan sha iska dan bai Saba da zafi ba
Yana duba flowers ɗin gidan ne ya ji footsteps a bayansa ya juya Ashe Dua ce
Ta tsaya da sauri
“Oh… I’m sorry, I didn’t know someone was here”
Sultan ya yi murmushi “It’s okay”
Shiru ya biyo baya sai Sultan ya ce
“You love reading?”
Ta ɗaga ido “Yes”, Ya ce “I noticed”Ta yi murmushi kaɗan “It’s my safe place”
Kalmar ta tsaya masa a rai “My safe place…” Yana son ya ƙara tambayarta…
Sai wata murya ta katse su “DUA!!” Zahra ta kwala kira cikin ihu
Dua ta firgita
“Coming mummy!” Ta juya da gudu
Sultan ya bita da kallo
“Why is she always scared?”
A can wajen birthday party… Jackson ya miƙa wa Amrah cup “Just take a sip, Amrah ta karɓa “Me a cikin cup din?”
Ya ce “Just fruit punch”, Firdausi ta yi dariya “Come on… stop acting like a baby”
Amrah ta ɗan yi shakkar sha, daga ƙarshe saboda maganganunsu ta kai cup ɗin bakinta…
ayi following acc dina🥹